x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - SU WAYE SU

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 172

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
irin banzan kallo yace; "Ni nake hauka, zakaga hauka kuwa ganin idon sa, yana faɗar haka ya caƙumi kwalar rigar sa, yana ƙoƙarin fara dukan sa, sauran sukayi saurin rirriƙeshi suna son su janye sa baya amma yaƙi sakin sa, gurin ne ya kaure da hayaniya sosai, Sir Suraj sai zage zage yake kamar ɗan maguzawa, kana jin yanda yake zagin kasan ba tarbiyya a cikin ta,

Beenish ce ta miƙe da sauri, sai ta miƙawa Aunty Babba hannu, Aunty Babba tasan me take nufi itama miƙewa tayi sannan suka taka zuwa inda suke babu wanda yasan da zuwan su, kawai tsugunnawa sukayi a ƙasa kamar zasu ɗau wani abu, a tare suka cafko ƙafafun sa kowa ya riƙe ɗaya, sannan suka ja su da ƙarfin su gaba ɗaya, yanda sukajawo sa babu wani musu dole ya bi inda ƙafafun sa sukayi, cikin tsoro baisan loƙacin da ya saki Dr. Aveed ba, jin ƙato kake timmmmm ya faɗi a ƙasa kansa ya bugu da sauri ya dafe kan dan yama kasa tantace a ina yake me ya faru dashi shidai kawai yajishi kansa kamar wani yummm kamar ba a duniyar yake ba.

Duk sauran matsawa sukayi suna mamakin su,

Aunty Babba ce tasa hannu ta ɗagosa tsaye tare da kaiwa fuskar sa wani lafiyayyen naushi a kuncin sa, take ta fasa masa, baki, duk da haka bata haƙura ba saida ta kuma naushin sa a ciki sannan tasaka ƙafa ta harbasa ya kuma faɗuwa ta kuma binsa da hannu ɗaha, ta kamo ƙafar sa, tafara jansa, babu wanda yayi yunƙurin dakatar da ita tunda kisan kai yake shirin yi, gwanda ayi masa haka,

Fita tayi dashi daga gurin bata dena jan sa ba saida ta kaisa tsakiyar makarantar mutane da dama suka taru a wajen wasu na ɗaukan hoto, gaba ɗaya baya cikin hayyacin sa, ita kam ko ajikin ta, barin sa tayi a wajen ta juya zata bar wajen muryar da taji ne ya sa ta saurin da katawa tare da juyo da kanta cikin sauri, ai ita kanta bata san loƙacin da ta ƙarasa gurin ba,

Yarinyar naganin ta nufota ta juya zata gudu saidai zafin naman Aunty Babba yafi nata, ba inda taje Aunty Babba ta cafko ta, ta baya, ta janyo ta tare da yin cilli da ita ta yardar da ita agefe, sannan tahau kan ruwan cikin ta, kawai fuskar ta kama ta ringa zuba mata maruka idan yarinyar ta buɗi baki zatayi ihu sai Aunty Babba ta zuba mata yawu a baki, haka taitayi mata tana ɗura mata yawu a baki, saida taga yarinyar ta daku iya dakuwa, sannan ta ɗagata ta kuma jefata kan Sir Suraj, tana watsa musu harara......

Dr. Aveed zama yayi akan kujera yana maida numfarfashi, Beenshi ce ta ɗau ruwan dake gabansa ta tsiyaya masa sanann, ta basa karɓa yayi shima ya hau sha, yana fara sha tunanin loƙacin da yabata shima ya faɗo masa,

Bayan ya gama sha ya ɗan samu peace of mind sannan ya kalli ragowar tare da sallamar sauron aka tashi daga taron,

Suma matan haɗa kai sukayi zasu fita suna daf da fita, sukajiyo muryar sa yana cewa; Thank you for save me, God bless you.

Tsayawa sukayi batare da sunjuyo ba, su kace "Ameen sannan suka sa kai suka fita daga gurin zuciyoyin su cike da farin ciki da jin daɗin wannan maganar sosai sukaji daɗi gashi an ƙara musu ƙwarin gwiwa,

"Wai Su waye su?

Tambayar da ya kuma maimaitawa kansa kenan, saidai bashi da wanda zai basa amsa, haka ya ƙari zaman sa yana ta tunani, kafin ya tashi shima ya fita daga wajen.

Suna fitowa sukaga abun da yake faruwa loƙacin Aunty Babba ta gama jibgar yarinyar da ta munafurce su badan Allah ya taimaka musu ba, da tuni yanzu ya jawo musu matsala, suna zuwa suka kamo hannun ya suka nufi motar su, suka shiga a ranar dai basu sami shiga lecture ba,

Har suka fice muatane basu dena binsu da kallo ba.

Rasa wanda zai taɓa su Sir Suraj akayi, sai security ne suka zo suka fita dasu, amma asibiti suka nufa dasu domin sai anyi treatment ɗin su,

A falo duk suka zube suna sauke gajiyar da suka kwaso, gaba ɗayan su a matuƙar gajiya su ke, ga yunwa da suke ji.

"Beenish ce tace; Baby ki ɗan dafa mana wani abun mana, kowa yunwa yake ji,

Ɗan turo baki tayi cike da shagwaɓa tace; "yaya muyi order mana wallahi ko miƙewa tsaye bana sonyi, Allah nagaji.

"Daman nasan bayi zakiyi ba, a haka kike so in kaiki gidan babyn to shi baya son mace malalaciya, wallahi idan baki zage ba yana dawowa duk zan gaya masa abun da kike zance ya canza wata wannan bata dace dashi ba sam.....

Neman ta sukayi suka rasa a gun har ta shige kitchen ɗin saida ta shiga sannan tace; "kema fa kin san da wasa nake ni ba gajiyar danayi yanzu zanyi muku me daɗi ma kuma bani 30 minutes yanzu zan gama.

Dariya suka ɗanyi, Ameela na cewa; wai yaushe zai dawo ne, naji shi shiru ko a online bana ganin sa, makaranta ta ɓoye sa.

Beenish tace; "Ai jarrabawa suke idan suna jarrabawa baya hawa online munyi waya dashi shekaran jiya yace min nan da 2 weeks ko 3 zai dawo,

"To Allah ya kaimu da rai da lafiya, kice mun kusa yin babban baƙo, cewar Aunty baba, tana miƙewa daga gurin tana cewa; "Auta bari in zo in taya ki kar aikin yayi miki yawa koh,

Cikin jin daɗi tace "yauwa Babbar yaya wallahi kin fisu daman nasan bazaki barni ni kaɗai ba, loƙacin da take maganar loƙacin Aunty Babba ta ƙarasa shiga tana dariya, sannan suka hau aikin tare.

Su kuma Barazance ta jawo system ɗin ta ta buɗe, aikin da sukeyi suka ɗora dayi ita da Beenish,
Ameela kam baccin gajiya ne ya ɗauke ta a gun.


*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*MEDUGURI....*

'Wata mata ce ƙatotuwa fara tas ƴar lukuta tana zaune a kan kujera kana ganin ta kasan kuɗi ne ke magana muguwar me kuɗi ce domin sirikar dake jikin ta da kuma da kuma ɗankunnen da danƙwaleliyar sarƙa da awarwaro duk na gold masu tsada sai kuma ƴar barimar hanci dake kan hancin ta itama ta gold ce, babu miyafi a jikin kawai ta kashe ɗauri tana hakimce kan kujera da jarida a hannun ta, sai kayan marmari dake gaban ta a yayyan ke tana duba news paper ɗin tana ɗaukar kayan marmarin tana sawa a baki.

Wata budurwa ce ta shigo cikin tamfatsetsen falon tana sunkuyar da kai saida ta ƙarasa gaban ta ta zube a ƙasa tana gaishe ta amma yanda kasan ta gaida kujerar wajen haka tayi mata, saida ta ɗauki loƙaci metsawo bata ko kalli inda take ba, shiru matashiyar budurwar tayi tana jiran ta har tsawon loƙacin da zata ɗauka kafin tayi mata magana,

"Are you a verging?

Tambayar da ta watsawa budurwar kenan, da batayi tsammanin taba,

Ita abun ma kunya ya bata cikin sunnar dakai murya ƙasa ƙasa tace "Eh"

"Why kike son maida kanki haka, baki san me akeyi a gidannan ba kika kawo kanki?

Cikin sanyin murya tace "Nasani.

A jiye jaridar tayi tana kallon yariyar she is so calming.

"Zaki iya tafiya bana harka da irin ku, ki bari indan kinyi aure kin fito zan iya karɓar ki, amma bana harka da irin ku, ki sani duk abun da kikayi sai anyiwa wanin ki, dan haka kiyi abun da in kinsan kinyi akayi miki bazai cutar dake da yawa ba, ina fatan kin fahimta,

"Hajiya dan Allah kiyi haƙuri ki karɓe ni ni wallahi banda kowa nasan baza'a taɓa aura ta ba, nagaji da rayuwar shiyasa na zaɓawa kaina wannan kar kice haka wallahi daga guri me nisa aka kwatanta min gurin ki,

Shiru matar tayi tana ci gaba da ƙarewa yarinyar kallo hakannan taji batason saka yarinyar a harkar,

Ɗan numfasawa tayi, sannan tace zakiyi aiki a ƙarƙashina, sannan ki kula min da gidana, duk wanda zai zauna dani duk abun da yaga nayi kar yasake yasaka min baki indai bani nasaka da shi ba, sannan bana son sa'ido,gulma, munafurci, shiga abun da ba ruwanki, ko baƙo nayi ban yarda ko gaisuwa ta haɗa ku ba, idan muna tare duk wanda ya shigo inda nake ki tashi daga gurin batare da kin gaida shi ba, idan kikayi haka zamu zauna lafiya, duk wata zan ringa baki dubu ɗari biyar akwai wata tsohuwa a gidan tare zakuna aiki, ga ɗakin da take ciki can kije zata ƙarasa miki sauran bayani, tana gamawa ta miƙe cikin takun isa take takawa ta nufi hanyar fita daga falon.

Tana fita daga gurin ta kuma faɗawa wani ɗaki dake kusa da falon, tana shiga ɗakin ta hango sa yayi ɗaiɗai a akan makeken gadon dake ɗakin, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai, bathroom ta shige bata daɗe ba ta fita, ta ƙarasa gaban madubi ta shiga gyara fuskar ta duk da kasan cewar babu abun da tayi amma saida ta kuma gyara ta ɗau turaruka ta kuma shafe jikin ta dashi ƙanshi ya cika ɗakin, gurin wardrobe ta nufa ta ɗauko mayafi da cover shoe ta maƙala a ƙafar ta ɗauki jakar ta, kyau iya kyau tayi sa kuɗi sun zauna,

Hanyar waje ta nufa zata fita, da gudu ya sauko daga kan gadon ya tari gaban ta yana ta faman lullumshe ido yana kuma shaƙar ƙanshin turaren da tasaka,

Wani mugun kallo ta watsa masa, tana cewa; "meye haka maye ka koma bana son irin wannan kasani,

Please DANNAR ki taimaka min wallahi ina cikin wani hali, Allah ji nake kamar in mutu kidai cutar dani haka Please Dannar yafaɗa yana ƙoƙarin kamo hannun ta tayi saurin janyewa, tana nuna sa da yatsa tace; "RIMA, ka kiyaye ni ka fita daga ido na ko angaya maka na aure ka ne dan nabaka wani abu najiki na, ka manta contract ɗin da muka ƙulla kaci ka sha kai bacci babu ruwanka dani kuma zan fita zanyi sati guda kar kasa ke ka fita ko ƙofar gida, zaka iya kiran matar ka tazo nan ta sameka,

Tana faɗar haka ta sa hannu ta janye sa gefe ta fice daga ɗakin, tana tafiya tana juyi tana taku ɗaiɗai, manyan mata na tafiya.

Tana fitowa harabar gidan da gudu wani yazo ya buɗe mata mota amma sai ta tsaya, tana ya tsina fuska, tace; "Kai bakayi wanka ba bance maka zan fita ba, a haka kake son in fita dakai kana faman bugawa, dalla malam bani waje, kaje ka kirawo min Safwan, ko meyake yazo ya kaini airport.

Da gudu ya nufi wani part ɗin dake cikin gidan, tana tsaye agun, kamar wajen 5 minutes sai gasu nan, shi a gaba yaron a baya,

Cikin haɗe rai ya ƙaraso wajen yana kawar dakai gefe, ya haɗi girar sama da ƙasa, ko inda take bai kalla ba, ya shige gaban motar ya tayar da ita, yana jiran ta shiga,

Ni kake so inbuɗe motar da kaina, batare da ya kalle ta ba, yace; "baga sani nan ba,

"Kai nake so ka buɗe min in kuma ban isa ba sai ka gaya min,

Gunguni yayi a ransa ya fito ya zagaya ya buɗe mata gaban motar, sannan ya koma ya shiga shima, sai loƙacin ta motsa daga inda take ta taka a hankali taje ta shiga saida ta shiga taja ƙofar ta rufe,

Jan motar yayi me gadi ya buɗe musu suka fita daga gidan,

Shiru babu wanda yacewa kowa wani abun, tsawon loƙacin kafin tace; Kayi waya da yayar ka yau?

"Eh,

"Me ta ce maka?

"Meye naki a ciki?

"Hmm kawai tace tare da sakin ɗan ƙaramin murmushi sannan ta kuma cewa, zanyi tafiya zanje London ɗauko wasu kaya zanyi kwana biyar a can daga can kuma zan wuce gurin yayar ka ka sanar da ita idan kunyi waya anjima, sannan ka kula da kyau banda yawon dare, nasamu sabuwar me aiki zatazo part ɗinka zata kula da kai kafin nadawo, nasaka maka 1 million a account ɗinka, idan ka samu dama ka kaiwa SARATU abun da yasamu duk yanda kukayi da ita ka kirani, abu na ƙarshe ka sanar da ita wannan karon kar ta sake tayi tunanin ɓoye min magana zamuyi da ita me mahimmanci.

"Baki da number ta? Ki kirata ki gaya mata da kanki, ni bazan iya ba.

"Hmmm banda number ta ka kira min ita yanzu da wayar ka, koda ma ina da ita kasan idan na kirata bazata taɓa ɗagawa ba, duk maganar dake hankalin sa nakan tuƙin sa, hannu ya zira a aljihu ya zaro wayar batare da ya kalle ta ba ya miƙa mata wayar, karɓa tayi da kanta ta kira ta wayar nata ringin ba'a ɗaga ba, sake kira tayi tana sauke numfashi jira kawai take taji muryar ta, saida ta kira sau uku ba a ɗaga ba,

"Jikin ta ya bata kece shiyasa bata ɗaga ba.

Harara ta watsa masa, zatayi magana kenan saiga kira ya shigo wayar da sauri ta ɗauka tana dubawa kuwa taga itace ta kira, da sauri tayi picking ta saka ta a hans free,

"Hello! Lafiya naga miss call ɗin har 3 bana kusa da wayar ne sorry dear, shiru tayi amma sai taji baiyi magana ba.

"Hello kanaji na kuwa naji kayi shiru"

"Eh yanaji, ta bata amsa,

Ɗiff kake ji bata kuma magana ba,

Wajen minti biyu shiru kuma bata kashe wayar ba,

Daga cikin wayar suka jiyo muryar wata tana cewa zafa mu fara cin abincinmu kin san yunwa muke ji koh, wata ta kuma cewa wallahi ba jira nidai farawa zanyi.

"Ɗif aka kashe wayar.

Wayar tabi da kallo tana runtse idon tare da furzar da iska me zafi daga bakin ta, tana jinjina kai,

"Hmmm a haka kike cewa zakije wajen ta kina tunanin zata saurare ki ne.....✍️✍️✍️
[3/5, 11:50 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 17💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

"Hmmm a haka kike cewa zakije wajen ta kina tunanin zata saurare ki ne.....

Shiru tayi tana nazarin maganar sa, kiran wayar ta kuma yi, ba tare da ta basa amsar tambayar da yayi mata ba,

Wayar ce ta fara ringing amma tana yi sau biyu, akayi rejecting, sauke numfashi tayi tana ƙara huro da iskar bakin ta, ta jingina kanta jikin kujerar ta lumshe ido,

Safwan kam tuƙin sa kawai yake bai kuma ce mata komai ba, har suka ƙarasa airport ɗin, guri ya samu yayi parking,

Jin ya tsaya ya sa ta, buɗe idon ta a hankali, ɗan juyawa tayi ta kalle sa tare da sakin ƙayatacen murmushi.

Jin kamar tana kallon sa yasa ya ɗan juyo kaɗan ya kalle ta, haɗa ido sukayi ganin tana murmushi yasa shi haɗe rai tare da kawar da kansa gefe, cikin haɗe rai yace; "Ina da abun yi a gida, zaki iya fita koh,

Batare da ta dena kallon sa ba, tace; "Ni kake so in buɗe ƙofar.

Kamar ya fashe haka yake ji cikin ɗacin rai ya fita daga motar ya zagaya ya buɗe mata yana kawar da kansa gefe, yana jiran ta fito ya rufe dan yasan ko ya tafi ma sai ta kuma kiran sa yazo ya rufe shiyasa yaja ya tsaya a gun yana jiran fitowar ta amma duk da haka taƙi fitowa har saida taga dama dan kanta, bayan ta kalli madubi ta ɗan gyara ɗaurin da fuskar ta, ta tabbatar de komai daidai sannan ta zuro ƴar duma dumar ƙafar ta, ta a jiye su a ƙasa sannan ta miƙe a hankali,

Ta ɗanyi masa rungumar gefe tare da manna masa kiss a kumatu tace; "lovely son zan tafi ka kula da kanka, duk abun da kake nema ka sanar da ni, sannan ka tura min number yayar ka da address ɗin ta kuma kar ka sanar da ita zuwa na, ka bar ta zanje har inda take kaji,

Kai kawai ya ɗaga mata bayan nan baice mata komai ba, ya juya ya zagaya ya shiga motar,

Duk da bai kulata ba saida ta kuma leƙawa ta ciki tana shafa sumar kansa da tayi luf-luf ta sha gyara irin na masu shi, "Me kake so in taho maka dashi ɗan auta na.

"Hmmm yace dan yagaji da abun da take masa so yake ta tafi yabar wajen dan jin sa yake kamar a kan ƙaya.

"Baka ce komai ba.

"Duk a bun da yayi miki ki siyo" yana fadar haka ya tayar da motar, jin hakanne kaɗai yasa ta matsa daga jikin motar ji take kamar kar tatafi ta barsa,

Tana gurin har yaja motar yabar wajen bata dena kallon gurin ba, ta jima tana saƙe saƙe kafin ta juwa ta nufi cikin gurin.

tana zuwa aka fara sanarwar jirgi zai tashi, basu daɗe ba jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar London,

Jirgin su na sauka, kowa ya fara shirin fitowa amma ita saida ta kuma tsayawa ta kuma gyara jikin ta sannan ta fito dan kusan ita ce ƙarshen fitowa,

Tunda ta fito wani Alhaji da kana ganin sa kasan naira ta zauna, fari ne shima kuma me ɗan jiki, yana ganin ta ya nufo ta yana washe baki, yana ɗan
End Ads