ya rotsa sa da ƙasa ya fashe hatta tvn dake falon saida ya fasa ta, komai na gurin saida yayi watse da shi, fridge yaje ya buɗe ya zaro kwalbar giyar sa ya ɓalle murfin daga inda yake ya ɗaga ya hau kwankwaɗa, yana girgiza kai idon sa ya kaɗa yayi jazur sai huci yake fitar wa da ƙyar wata mahaukaciyar ƙara ya saki yana doke kwalbar giyar a ƙasa..✍️✍️
*Wasu suna ta tambayata littafin kuɗi ne ko free to dai littafin SU WAYE SU paid dan na daɗe da faɗa saidai in wasu basu gani ba, to na kuɗi ne muna zuwa wani geji free zai ƙare dan haka kowa ya shirya yin payment babu tsada, duk da littafin na dabanne to ba'a saka masa kuɗi da tsada ba*
Kude kuci gaba da kasancewa da tadaban me littafi na daban, duk da kasan kuma masu karatun duk na dabanne musamman su O'o da o'o sumfi kowa na daban duk kowa ma na dabanne indai a cikin group ɗin SU WAYE SU to dole ka zama na daban....💃💃💃💃💃
[3/5, 12:16 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 29💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah..✍️
*PAID BOOK💸*
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*DANNAR*
___Bayan tafiyar ta daga gidan Hajiya Rabi, sunje wata kwana kenan drivern ya tsaya saiga wata mata nan fuskar ta ɗauke da fara'a ta buɗe bayan motar inda Dannar take ta shiga, Saida ta zauna sannan drivern yaja motar suka ci gaba da tafiya..
"Ya kuka yi da ita ta faɗa miki wani abun kuwa?
"A'a wallahi bata faɗi komai ba amma dai nayi nata gargaɗi sosai duk da nasan ya shige ta na sanya mata tsoro nasan zatayi yunƙurin yin wani abun anan mu kuma zamu kamata, tunda na samu dai wannan karan nasanya camera ta ko ina..
Zaro ido ɗayar tayi sannan tace "taya hakan ta tayiyu tunda naga itama gidan nata da tsaro ta ko ina...
"Da haɗin kan ma'aikatan gidan ina basu kuɗi duk na rufe musu baki nasan kuma babu wanda zai faɗa, nasaka ɗaya a falon da na shiga ɗaya kuma a main falon ɗaya a farfajiyar gidan ɗaya kuma a wajen gidan ta yanda duk zamu iya ganin shige da ficen ta da duk wani wanda zaizo mata, zamuji kuma tattaunawar da zasuyi, kinga nasan yanzu ta kuma tsorata da gaya matan da kikayi zaki kai mata ziyara, nasan yanzu duk inda take hankalin ba a kwance take ba, sannan kuma zata sanarwa da abokan aikin nata, anan ma zamu iya jin inda zasu haɗu sai mu samu mu hallaci wajen dan mu kuma gano ko SU WAYE SU.
"Eh kuma kinyi dabara ai yanzu duk zasu bayyana kansu, ni Bulama ma nake so mu fara gano inda yake indai ya fito sauran ma duk zasu fito, saidai kuma haɗa wasu hujjojin ne aiki dan yanzu nasan suma zasu ƙara taka tsantsan da sake sabon taku.
Dannar tace "ai duk wannan me sauƙi samun nasu da kuma kama su shine abu me wuya amma dan haɗa hujja ba wata matsala bace abun da zan musu dole su miƙa wuya da kansu saboda ba wata shari'a da za'ayi kowa zai amshi abun da shuka ne da kanmu zamu ɗaukar wa kanmu fansa tunda hukumar duk ta lalace yanda suke azabtar da mutane suna kashe batare da sauran al'umma sun ɗauka ba to dole suma ayi musu yanda suke wa mutane ɗaya bayan ɗaya babu wanda zamu ragawa,
Matar tace "gaskiya ne ai nasu cancanci a ɗaga musu ƙafa ba, ni gani nake ma duk hukuncin da za'ayi kamar bazamu rama abun da sukayi mana ba,
"Maryam zamu rama fiya ma da haka, kuma bama mu zamu rama ba waɗancen yaran zamu sa su rama, domin duk aikin soja zan tura su, tunda kinga tun suna yara suka samu training dan haka yanzu bazasu sha wata wahala ba, yanzu hanya kawai ya rage mana so nake su katse karatun nasu ma tun yanzu dan muyi mu cinma wani abun loƙaci yana ja, kuma ta haka ne kawai zamu iya yin komai batare da kowa yace wani abu ba suma kuma zasu shigar da case ɗin sai case ɗin ya koma hannun sojoji duk wanda ya kawo munafurci acikin case ɗin sai ya baƙunci lahira, inaso yaran suyi wasa da hankalin su suyi musu abun da basu taɓa tunani ba yaran da suka haifa da cikin su su zasu ɗau fansa akan su, mu namu taimako ne kawai kamar yanda muka saba mu ɗora su a hanya, nasan zasu iya komai.
"Ina da hanya kuwa indai a aikin soja zasuyi, nasan mutane da yawa, saboda dana farfaɗo a hannun su na ganin saidai tunda suka ga naji sauƙi suka sallame ni to amma akwai wani wanda muke gaisawa, ko shikaran jiya muyi waya, ina ganin zanyi masa magana kawai sai yagaya mana yanda tsarin yake, kinga kwa wannan tunanin naki yayi ko ba hujja indai suna da wani muƙamin suma to bana tunanin za'a samu munafurci ya shiga saboda kowa zaiji tsoron su, tunda naji labari ma a yanzu haka ma ana shakkar shiga harkar su ta yanda suke dukan mutane, bare kuma ace yanzu sun zama sojoji abun zai kuma tsorata mutane.
"Matsala ɗaya ce yanzu zata rage mana samun haɗin kansu su ƴan matan bansan nasu tsarin ba hasali ma ban taɓa zana daya su naji ta bakin su ba, ga Ameela taƙi ta tsaya ta saurare ni bansan ya zanyi da yarinyar nan ba wallahi taurin kai ne da ita kamar jinjirin jaki,
Maryam tace; "a gaskiya Hajiya indai fa kina son samun haɗin kanta to kiyi mata abun da take so kigaya mata kawai ina ganin yanzu ai takawo munzalin da ya kamata tasan wacece ita waye mahaifin ta tasan gaskiyar lamarin kinga hakan zai ƙara basu ƙwarin gwiwa su maida hankalin su kan abun da ya shafi rayuwar su, idan kowa yasan waye shi da kuma abun da akayiwa iyayen sa to zasu maida hankali sosai dan ganin sun ɗaukar kansu fansa da hannu su, amma suyi ta rayuwa haka suna lalibe cikin duhu ai hakan da matsala danma suna da haɗin kai amma da tuni sun rabu wallahi,
Shiru Dannar tayi kafin ta ɗan numfasa tace; "Hmnm Maryam bawai hakannan naƙi gaya mata ba inajiran ta gano da kanta ta yanda zata yarda ni yanzu duk abun da zan gaya mata bazata yarda dani ba saboda abun da idon ta ya gane mata dashi take aiki har yanzu a ƙullace take dani, batasan wahalar da na sha s kanta ba, Ameela yarinya ce har yanzu bata da hankali amma nan da wani ɗan loƙaci zata gane abun da nake nufi, last zuwa na gurin ta da nayi nace mata indai tana son sani to zatayi min wani aiki amma dake zuciyar ta a ƙyanƙyashe take kinga har yanzu bata nemenin ba shiyasa nace bazata taɓa yarda da duk wani abu da zan gaya mata ba, amma yanzu tunda gaki sai kiyi ƙoƙarin wayar musu da kai amma sai kinyi da gaske dan zaman da sukayi da Hajja mama kinsan ta koya musu rashin yarda da kowa ta saka musu abun a zuƙatan su tun suna yara shiyasa kafin a samu wanda zai juya musu tunanin za'a sha wahala, tun farko saida nace mata iya faɗa zata koya musu amma dake itama ƴar kanta ce gaba ɗaya ta sauya musu tunani da ɗabi'un ta, yanzu gashinan ta tafi ta barni da wahala, yara sai shegen tsaurin rai da faɗin zuciya.
Ƴar ƙaramar dariya Maryam tayi tace "to ai gwanda da tayi musu haka da batayi musu haka ba kinsan da ba lalle su iya zama haka ba kuma su kare mutunci da tuni wasu sun shiga cikin rayuwar su, sun yaudare su ko kuma ma daga baya a nemi a lalata musu rayuwa ko a tarwatsa su, hakan sai yafi baku wuyar haɗa kawunan su da kuma zulumin kullum a wane hali suke hankalin ku ne zai rarrabu, amma yanzu ko banza kunsan duk inda suke suna tare kuma babu wanda zai shiga rayuwar su su yarda dashi sannan duk sanda kuke son zuwa gurin su kunsan inda zaku same su, kuma kun yarda da su kun san abun da zasuyi kunsan abun da baza suyi ba, ni wallahi wannan rayuwar tasu ma burge ni take, gashi basu lalace ba bakiga yanzu yanda ƴan mata suka lalace ba, wallahi yanzu da naje gurin yarinyar nan ta wajen rabi bakiga yanda maza da mata suka haɗu ba suke ta rawa har riƙe hannu suke kowace tayi shigar banza wai ana party da ƙyar ma na samu na shiga, saida na nuna musu yarinya ta zanbawa saƙo irin nasan koma me ake a ciki, sai loƙacin aka barni nashiga, abun da zai baki mamaki ma, wai a cikin gida ake wannan lalatar kuma iyayen yaron suna gidan, amma suka bari ake irin wannan baɗalar wai su wayayyu, abun abun kunya wallahi, yanzu rayuwa ta lalace gaba ɗaya yara suna gaban iyayen su ma ya tarbiyar yaran su ta kasance bare kuma ace mutum ba'agaban su yake ba, ba'a gurin su ya taso ba kinsan ai babu kalar rayuwar da bazai iya jefa kansa ciki ba, amma kinga hanyar da kuka ɗora su zuciyar su a tsarkake mazan ma basa gaban su bare su bari wani yazo ya yaudare su ya lalata musu rayuwa, wallahi hakan da Hajja Maman tayi musu shine daidai..
"Uhmm shine daidai ba ta wani fanni amma wallahi ta wani fanni baiyi ba idan ta sanya musu tsanar maza kamar yanda ta tsana haka suma fa zasu ƙaraci rayuwar su babu aure kinga kwa ai akwai matsala,
"Hhh kai Hajiya wallahi bama matsalar da za su samu da su da ita ai da banbanci kodan yare ma kuma ita ai kinga tana kallon mazan mu ne duk mayaudara ne bazata iya auren mutanen mu ba, gashi kuma da abun ta taso shiyasa bazata iya yin aure ba, amma yanzu da komai zai lafa mu gano inda take ai da sai mu ɗan nemo mata wani dattijon ko a can ƙasar tasu ne tunda bazata auri na nan ƙasar ba.
Itama Dannar ɗin dariya tayi tace "ai a kalar zuciyar nan tata wallahi banajin zata iya auren, ai ta taɓa yi tun muna yara saidai bansan me ya haɗa su ba suka rabu kuma bata taɓa haihuwa ba, kinga ka tunda jinin ta a kusa ma batayi ba sai yanzu duk da bansan ya ta koma ba yanzu amma nasan ta tsufa tayi laushi nasan ko masifar nan ta'ta babu yanzu...
Hirar suke tayi hankalin su kwance wannan tace wannan wannan tace wannan yayi da driver kuma yake ta faman kwarara gudu akan titi da yake fayau babu yawan motaci sai tsalli tsalli idan mota ta wuce sai ka daɗe baka ga wata ba, saida suka kazo bakin wata hanya sannan ya tsaya, Maryam ce ta buɗe ta fita tare da ɗaukar ƙatuwar jakar ta tace "To Hajiya ayi mana addu'a kar naje su lugudeni ko kuma ki gaya Ameela su san da zuwa na kar naje su fatattako ni, nasan yaran naki da saurin hannu...
Dariya Dannar tayi tace "kar ki wani damu kafin ki isa zan sanar da ita, sannan kuma sai kin kula da hanya sosai dan kamannin ki ba sauyawa sukayi ba, sannan kar ki saki bakin ki da yawa ba ko wane labari zaki basu ba, ki basu de abun da ya dace shima bawai kina zuwa ba ki bari ki fara karantar ko wannen su, dan Tata wani fanni suna da sauƙin kai ta wani fannin kuma sai kinyi haƙuri dasu zaki iya zama dasu, a dawo lafiya in ankwan biyu zan leƙoku, sannan duk abun da suke buƙata ko kuma kiga ma suna buƙata ko basu faɗa miki ba ki sanar dani in turo miki kuɗi sai kuyi amfani dasu, dan Allah ki kula da su sosai, kamar yanda na baki labarin Hajja Mama take musu kiyi haƙuri kiyi musu kema,
"Haba Hajiya ai kinsan babu ƴar haka tsakanin mu inban taimaka miki ta wannan hanyar dame zan iya biyan ki da abun kikayi min ai ki kwantar da hankalin ki in sha Allah ma zan basu kulawar da tafi ta Hajja Mama ma saidai damba ne kawai bazan iya koya musu ba amma zan basu wasu dabarun...,
"To shikenan fatan nasara yanu waccen tashar zaki shiga kina zuwa zakiji ana kano kano namiki kwatancen unguwar dama idan baki gane ba sai ki kirani in sake yi miki kwatan cen, ko kuma zan turo miki da number ta ko fitowa ne sai suyi su tafi dake,
" Ai nama gane ma, gurin ai ba ɓoyayyen guri ba ne, ko da tambaya zan iya ƙarasawa... Daga nan dai sukayi sallama ita ta nufi tashar ita kuma aka ɗauki hayar meduguri da ita.......
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*SOKOTO*
______Su Salma na tasowa daga gurin partyn su wajen ƙarfe goman dare, suna kan hayan ta sakar musu kiɗa tare da ƙure musu volume kai kace badaga wajen wani casun suke ba, suna cikin tafiya, wasu mutane suka tari gaban su duk da wuƙaƙe a hannun su, da sauri ta taka burki cike da tsoro, jikin su har ya fara kyar ma, suna tsayawa suka zagaye motar, ɗaya daga cikin su ya buɗe gaban motar cikin wata iriyar murya yace ku fito duk da sauri Salma ta fito jinkin ta na rawa, itama fauziyyar buɗewa sukayi suka ce ta fito, tun ta fito tana ƙamƙame jakar ta, wanine ya gushe jakar nan ya zaro wayar ta da take ji da ita, saida ya kuma zazzage jakar saiga ƴan dubu dubu da ta kwaso a wajen leki suma duk kwashe su yayi ya cusa su a aljihu, haka jakar salmar ma saida suka zazzage suka kwashe komai sannan suka jefa musu jakunkunan, duk wannan abun da suke babu wanda yayiwa wasu magana,
Sude jikin su sai ɓari yake ko magana ma sun kasa, basu tsorata ba saida sukaga sun shige cikin motar tasu suna shirin ja su tafi sannan Salma taje gurin da sauri tana basu haƙuri nan kwa wani ya kaimata mugun bugu da saida ta faɗa da baya, su kuma suka ja motar suka bar wajen,
Sai loƙacin Fauziyya ta fashe da ihu tana kuka kamar ranta zai fita.
"Wayyo waya ta wayyo wayata sun ƙwace min waya ta.
Salma ce ta tashi da ƙyar tana watsa mata harara tace "dalla Malama rufe min baki ni da aka ƙwacewa mota bance komai ba ko wayata batafi taki tsada ba mtsww in zaki taho mu fara tafiya ki taho idan kuma zaki tsaya kuka anan sai ki zauna ki tayi ki jira su su dawo miki da ita da me yasa baki bisu ba, sai Ni zaki zo kisa agaba da kukan banza, tunda su barki da lafiyar ki ma ai sun miki arziƙi da sun yanka ki da wuƙar hannun su da kinyi me dalili, tana faɗa mata haka tayi gaba abun ta ko ajikin ta babu damuwa ko ɗigo a fuskar ta.
Fauziyya ba ƙaramin jin haushi maganar ta tayi ba, dan haka ƙin bin bayan ta tayi saida taga tana shirin yi mata nisa sannan tsoro ya kama ta ba shiri tabi bayan ta da sauri harda haɗawa da ɗan gudu gudun ta dan taga tana shirin yi mata nisa, suna cikin tafiya wata mota ta shawo gaban su tare da haske musu ido duk hannu suka saka suna kare idon su, a hankali Fauziyya tace "yauwa sun dawo mana da wayoyin mu kamar sune fa,
"Mtsaw ke wallahi baki da hankali mutanen da sukayi baya sune kuma zasu dawo ta gaban mu, to tunda sune sai kije ki karɓo,
Saboda haske sun da akayi yasa basu ga tahowar mutanen ba saida sukaji anriƙe hannayen su sannan suka ankara, kuka Fauziyya ta shiga yi ganin sunja Salma, da sauri ta riƙo ta tana janta suma suna janta, ɗaya ne ya janye Fauziyya da ƙarfi yayi baya da ita yana tura ta gefe ita kuma Salam suka tura ta har gurin motar tare da buɗewa suka turata ciki.
Kafin Fauziyya ta tashi har sunja motar sun bar wajen.
Hannu kawai ta ɗora akai ta fara sakin ihu tana kururuwa amma babu kowa agun ga duhun dare, ko gaban ta bata iya gani,
Kuka take sosai tafi tsawon minti talatin tana tafiya ita kanta batasan inda take saka ƙafar ta ba,
Allah ne ya taimake ta wata ƙatuwar mota shanu tazo wucewa zata shiga cikin garin, da har sun wuce ma ta bisu da gudu tana ta ɗaga musu hannu, sai da ƙyar suka tsaya, susu biyu ne a ciki, da ƙyar da ta gaya musu abun da ya