x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - SU WAYE SU

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 164

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mata a dawo lafiya, loƙacin har ta kai gurin motar da take jiran ta a wajen.

Sai da taga tafiyar su sannan ta juya ciki tare da turo ƙofar, kallon ɗakin tayi da gefen ido tare da doka masa wata uwar harara taja tsaki cikin ƴar waƙar habaice tace "ayye masu zama a ɗaka ayye masu zama a ɗaka kullum sai aikin sa ido babu aikin fari bare na baƙi a hayye........

Wata filleliyar mota ce ta shararo layin a guje tana shigowa duk mutanen dake gurin suka shiga ɗagawa motar hannu tsayawa akayi da motar aka ɗan zuge glass ɗin bayan motar kaɗan kawai saiga kuɗi nan sun zubo ƙasa, nan aka fara gudu zuwa kwasar su, kirari suka shiga yi baura uwar kuɗi baura uwar kuɗi hajjaju me handarin naira kina tafe kuɗi na zuba, tayar da motar akayi aka cigaba da tafiya a hankali anayi ana watso kuɗi mutane kwa sai wawa ake ana kwasa, daga a zubo ƴan dubu dubu sai a watso ƴan ɗari biyar biyar haka ake ta watso kuɗaɗe har har motar ta shige cikin wannan babban gidan dake layin, sai loƙacin mutane suka dakata daga waje suna ci gaba da cewa baura uwar kuɗi baura uwar kuɗi....

Girman gidan ma sai ka shiga ciki yafi girma sosai, parking lot akayi da motar aka parker ta, da sauri na gaban motar ya fito ya buɗe bayan motar,

Ƙafafun ta ta zuro ba ɓata loƙaci ta karasa fitowa, gajeriyar macece kuma baƙa ga ɗan jikin ta tana da ƙiba amma ba can ba, amma kana ganin ta kasan ta juƙu da naira kuma tana da kyau ga hanci tubarkallah kallo ɗaya zakayi mata ka gane ne fara'a ce dan tana fitowa ma saida ta saki ƴar ƙaramar dariya tana ƙarewa gidan kallo,

"A bar kayan zuwa anjima saika shigo dasu, yanzu ina da baƙin da suke jirana a ciki idan sun tafi saka shigo dasu,

"To hajjaju angama.

Shigewa tayi cikin gidan, tana shiga babban falon bakin ta ɗauke da sallama mutanen da suke ciki suka amsa mata, tare da yi mata sannu da zuwa da fara'ar ta take amsa musu har ta samu guri ta zauna. Gaisawa suka kuma yi, kafin daga bisani tace ina baƙin suke,

Wata daga cikin ƴan aikin tace mata tana falon baƙi mutum ɗaya ce ma ai, falon baƙi Salma ce tace akai su can kafin ki dawo ita ta ɗan fita.

"Okay kawai tace tana miƙewa tsaye, tare da nufar hanyar falon baƙin.

Tura ƙofar tayi tare da cewa "Assalamu alai....... Kasa ƙarasawa tayi sakamakon tozali sa tayi da wacce bata taɓa tsammanin ganin ta ba.

Miƙewa matar tayi tana sakin ƙayatacen murmushin ta da ya zama kamar ɗabi'arta saidai yasha bambam da sauran saboda yanda take yi, wannan cike yake da ma'anoni ba marar ma'ana bane.

Ƙaraso mana ko kinyi mamakin gani na ne?

Wani yawu ta haɗiya da ya tsaya mata a maƙogaro, cikin sauya kalar fuskar ta tace "Hajiya Dannar me ya kawo ki guri na jinake mun gama magana dake tun ba yanzu ba me koma yasa ki ƙara dawowa?

"Tambaya ta a kullum" ta bata amsa.

Shiru tayi mata tana sauke nauyayyir ajiyar zuciya, sannan ta ƙarasa shiga ciki.

Gaban ta taje suka shiga kallon kallon, kafin tace "Dannar ki fitar min daga gida tun kafin nasa a fita dake, sau nawa zan gaya miki bansan komai ba akai babu ruwa na a ciki kije ki lalubo su duk inda suke amma ni bansan ma inda suke ba a yanzu.

Hhhhh "Hajiya Dannar tayi dariya tace "Rabi! Rabi! Rabi ikon Allah yanzu ni kike tsatstsarewa da ido haka har kike cewa za'a fitar dani daga wannan ƙazamin gidan naki me cike da dukiyar ƙyamata lalle duniya juyi juyi ce, ko da yake ba abun mamaki bane dan shugaban ƙasa ya zama shoe shaina ikon Allah ne,

To in baki sa an fita dani ba baki haifu ba uwarki shegiya ta haife ki, har ni zaki faɗawa wannan maganar to, ba abun da yakawo ni ba kenan, ina son in sanar dake na baki nan da wata ɗaya duk wani abu da kika san kin mallake shi ta hanyar ta ki gaggauta dawo dashi, sannan ki gaggauta sanar dani duk abun da ya faru da abun da kuka ƙulla, kuma ki gaya min ko SU WAYE SU, in ba haka ƙaramin zaki zai nuna miki shima zaki ne, kuma kar kiyi tunanin guduwa ko kimin barazana ko kisa a kai min farmaki to lalle zaki gane kiɗa da karatu da bambanci, sannnan yarinyar da kika turo ta kije ki ɗauke a barki kafin inyi mata illa da ido huɗu nake kwana ba da biyu ba, duk wani shige da ficen ki a kan ido na kike yin sa dan haka ki tabbatar da kin kiyaye kafin ki kuma jefa kanki ga halaka bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane ma ci amana kawai.., tana faɗa mata haka tasa kai ta fice daga falon ta barta tsaye a gun takasa ko motsi.....

Ji tayi tana shirin faɗuwa da sauri ta lalibi kujera ta zauna tana dafe kanta, "Rabi ina son ki wallahi jinki nake kamar ƴar uwata saboda biyayyar da kike min duk da nasan kin girme nima, wallahi Rabi tsoron haihuwar nan nake ji nake kamar mutuwa zanyi,

"A'a bazaki mutu ba Hajiya in sha Allah haihuwa ai ba mutu wa bace, da ana mutuwa muma ai duk da ba a haife muba, dan haka ki cire wannan a ranka ma.

"Nasan da hakan amma wallahi duk da haka sai nake jin kamar ma ba zan iya haihuwar ba ko kuma idan na haihu mutuwa zanyi,

"Nafa ce miki ki dena faɗa dan Allah kiyi shiru,

"Mumushi kyakkyawar matar tayi tana shafa cikin ta, tace "to shikenan Rabi na dena faɗa, amma bari in faɗi na ƙarshe idan na mutu kice a baki ƴar na bar miki ita halak malak nadan zaki kula da ita kamar yanda kula dani, koda ƴan uwana sunce ki basu kice ni na faɗa miki haka zan rubuta ma in ajiye saboda sheda wasiya ce zan bari wallahi har zuciya ta nake faɗa....

"Haba Hajiya faɗe dai kike amma ina ni ina riƙe yarinyar ki duk yawan ƴan uwanki kinsan ma baza su taɓa bani ba.....,

"Wallahi Rabi zasu baki dade mahaifiyar mu na raye shine nasan baza ta yarda ba amma yanzu nasan zasu yarda, suna son abun da nake so indai suka ga rubutu na haka zasu yarda suma ai suna sonki kamar yanda nake son ki saboda kulawar da kike bani nasan ko wacce muka fito ciki ɗata iyakar abun da zatayi mun kenan,

"Hajiya nidai na gaji da wannan labarin ƙanzon kuregen bari kiga inje in haɗo miki abu me ɗan ruwa ruwa ki sha naga Babyn naki kamar yunwa yake ji tun ɗazu baki ci komai ba, har ta miƙe zata tafi matar ta kamo hannun ta tana dariya tace taɓa kiji motsi yake wallahi tana murmushi,

Ɗora hannun nata tayi akan cikin, sai tayi saurin janyewa itama tana dariya tace "yarintar ki tayi miki yawa wallahi nidai bari inje tayi gaba tana dariya itama,

Itama matar dariya tayi sosai tana cewa wayyo wayyo ciki na Rabi wasa yake da ƴaƴan hanji na fa kar naje ya cire min ƙoda...

Tana daga kitchen ɗin tana jiyo shirmen da take yi babu abun abun da take sai dariya.....

Da sauri tasa hannu ta toshe kunnen ta amma duk da haka dariyar tata take ji kamar ta cika falon ma.....✍️✍️✍️✍️

*Godiya ne tarin yawa mutanena masu yi min comments*

Ina jin daɗin comments ɗin ku kodan ku dole inyi typing me yawa.

Aunty fauzyyy🌹

Aunty fauzyyy 2🌹

Ummu Aysha🌹

Zaraty kanuri🌹

Maryama Hamza facebook🌹

Amina me kuɗi🌹

Hauwa'u ISAH🌹

Ƴar gatah🌹

Aishatu Hassan Tata🌹

Asma'u🌹

Rabi'ah, Orsting (lambuuu)🌹

Wacce take sa Z nace ki faɗan sunanki baki faɗa ba to kema ga🌹 Z🌹 ɗin kiman

Ƴan amana bazan manta da ku ba wallahi much luv wujiga wujiga iya wuya muna tare🥰🥰😍🥰🥰🥰

Ragowar masu comments ɗin stickers da masu mun gode da masu Allah ƙara basira to Ameen kuma duk ina miƙo muku jinjina ta musamman🙏🥰🥰

Masu karantawa kuma suna yin likimo Nagode da rashin m😏😏😏 Allah ya shirye ku kuringa yi😤😤
[3/5, 12:00 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*

(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)

______________________________


*_episode 24💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

____Da sauri tasa hannu ta toshe kunnen ta amma duk da haka dariyar tata take ji kamar ta cika falon ma, miƙewa tayi tsaye tana damdamƙe ido tana girgiza kai wai duk don ta dena jin sautin muryar ta.

Ta daɗe tana zagaye a tsakiyar falon kafin daga bisani ta tafi wajen jakar ta da ta ajiye kan kujera da sauri ta saka hannun ta a jakar ta zaro wayar ta buɗewa tayi ta ɗanyi danne dannen ta, ta dannawa wata number kira....

Zagaye ta fara yi a falon tana kara wayar a kunnen ta tana jiran a ɗaga, ba jimawa kuwa aka ɗaga ana ɗagawa bata jira amsa sallamar da akayi mata ba ta ce; "Hello Alhaji Saleem merah! Dannar ta ƙara dawowa kuma wallahi kamar a shirye take wannan karon dan naga alama a idon ta, ka gayawa su Bulama su sake shiri, inma kashe ta za'ayi ayi ko kuma a ɓatar da ita dan tana shirin tona mana asiri tazo har cikin gidana ta cimin mutunci, ni kaɗai ta sani kuma sai bibbiyata take duk wani motsina akan idon ta bazata barni in huta ba wallahi kuyi gaggawar yin wani abun, gi kuma yarinyar da muka tura mata ta gane wace ce bamu da wani abu kuma dole sai kunyi maganin abun tun yanzu kar ta ɓallo mana ruwa...

Shiru tayi tana sauraran sa danni dai banji me tace ba,

"Yauwa nasan zaka iya duk wani wanda take ma'amala dashi a datse ta, da komai da ta mallaka dan ta hakane kawai zamu iya cin gala ba akan ta idan muka barta a haka da kuɗi zata iya yin komai dole musaka ta cikin talauci kamar yanda muka saka su a baya dole su maimaita irin rayuwar da sukayi a baya ita da ƴan uwan ta... Shirun ta kumayi, sannan tace; "yauwa yauwa to shikenan sai anjima har naji raina yayi sanyi wallahi... Daga haka ta sauke wayar ta komawa kan kujera ta zauna tana sauke numfashi.

Wata number ɗin ce ta shigo wayar ta ganin sabuwar number yasa ta ɗanyi burus kamar bazata ɗaga ba har saida kiran ya kusan yankewa sannan ta ɗaga, koda ta ɗaga saita saka ta a hans free batare da tayi magana ba.

"Hello Mami nice...

Da sauri tace "Salma ya akai naga kin kira ni da wata number daban gashi kuma na dawo gida tun ɗazu baki dawo ba,

"Naje wani party friend ɗina ne sai dare zamu dawo.

"Okay to a dawo lafiya.

"Yauwa Mami daman wata mata ce ta ganni tace ni ƴar kice amma, shine nace mata eh sai tace wai kun daɗe baku haɗu ba in bata number ki ku gaisa gata...

"Assalamu alaikum barkan ki da yamma Rabin Mamman!

Gaban ta ne yayi wata muguwar faɗuwa batasan loƙacin da ta miƙe tsaye ba, take zufa ta zayyo mata hannun ta har karkarwa yake, ko a mafarki bazata taɓa mantawa da wannan me muryar ba.

"Hello kinajina kuwa naji kinyi shiru.

"U..hmmm.. ehhhhh, ta ta amsa mafa da ƙyar.

"Ƴar dariya tayi ta cikin wayar cikin ƙasa da murya tace kinyi mamakin yanda na nemo ki koh, na daɗe da sanin inda kike kawai rabuwa nayi dake, naji ance yanzu kinyi kuɗi koh, ki shirya tarbata zan kawo miki ziyara gobe da yamma....

Da sauri Hajiga Rabi tace "kar kizo min gida bana neman ki kuma wallahi Maryama, kar ki sake ki taɓa min yarinya duk wani abu da zakiyi kiyasa iya kaina, Salma yarinya ce ƙarama bata san komai ba, basai kinbi ta wajen ta ba, zaki samu abun da kike so, ki gaya min inda zan same ki sannan ki gaya min abun da kike so....

"Kai haba dan Allah sai yanzu kika san da wannan, ai wallahi babu abun da zan kuma karɓa yanda kika sa akayiwa ƴar wata wallahi kema sai nakai ƴarki, amma ki kwantar da hankalin ki ba yanzu ba, sai zaɓi ya tashi yace lalle lalle ita yake so dan haka baki da wani choice, in kuma zaki neme sa ku sasan ta zaɓi ya rage naki, ni umarni kawai nake bi, sai anjima kiyi saving ɗin sabuwar number ta....

"Zatayi magana kenan taji ƙitt... Ankashe wayar, sauke wayar tayi tana binta da kallo tare da jifa da ita kan kujera, kamar zararriya haka ta fara maganganu.

"Ƙarya ne!!! Wallahi ƙarya nee me kuke so ku maida ni taɓaɓɓaɓiya ko me, wai ni kaɗai na aikata hakan nace muku bansan komai ba bansan komai ba amma kun takuran me yasa kowa sai ni komai ni nayi, sai yanzu da nake tunanin na samu kwanciyar hankali duk zaku zo kusa kani a gaba to wallahi baku isa ba daidai nake da ku ɗaya bayan ɗaya duk sai nayi maganin ku ko dan kunga nayi sanyi yanzu bana bibbiyar kowa, to yanzu zamu sake sabon shiri yanzu wasan ya fara mu ko ku a shirye nake da ɗaukan ran duk wanda ya ɗauki ran ƴata sai inda ƙarfi na ya ƙare...

Turo ƙofar ɗakin akayi jin ƙarar motar yasa tayi saurin yin shiru.

"Mami ke da waye ne haka, wani matashin saurayi ya ƙarasa shigowa yana tambayar ta tare da tsare ta da ido, dan yaji komai amma sai ya nuna kamar baiji komai ba...

Ƙoƙarin saurin saita kanta tayi, tana kallon tace "babu komai fa ni da wata ne da ta siyi kaya tun ba yanzu ba amma shine wai ta fasa zata dawo da su shine da danna ce ban yarda ba shine take neman ta ɗaga min hankali ni banyi mata masifa ba sai ita ce zatayi min...

Ɗan murmushin taƙaici yayi yana zama a kan kujerar tare da cewa; ai sai haƙuri haka wasu mutanen suke baka iya musu....

"Wallahi kuwa Khalifa sai a hankali ta ɓatan rai da yawa wallahi, daga shigowa ta ko gama hutawa banyi ba sai bala'i wannan wacce rayuwa ce...

"Rayuwar da kika ɗaukar kanki...

"Me kake cewa...

Da sauri yace "ah babu komai haka kawai Rayuwa sai a hankali,

Bari inje in rage kayan jiki na Abban ku ya dawo ne?

"Eh amma ya ƙara fita..

"Okay" kawai tace tana ficewa daga falon ita kaɗai tasan tafarfasar da zuciyar ta take mata...

Bayan ta yabi da kallo yana girgiza kai a hankali yace; "Mami kenan wallahi kin goge min hadda zan ma gani ki ne duk abun da kike shiryawa...

Har ya miƙe zai fita, sai kuma idon sa ya faɗa kan wayar ta da ta jefar kan kujera, da sauri yaje ya ɗauka hamdallah yayi ganin bata shiga lock ba, har ya fara dannawa sai yaji kamar tafiya da sauri yaje ya sakawa ƙofar key sai ya zare sa daga jikin ƙofar ya ajiye sa a gefe kan wani table,
sannan ya dawo ya zauna akan kujerar zaro wayar sa, ya ɗauki nombobi ukun ƙarshe da yaga tayi waya dasu last, da ta wacce ta kirata yanzu da kuma ta Alhaji Saleem merah, sai wata da yaga anyi saving ɗin ta da Baba lawan.

Messages ɗin ta ya shiga, nan yaci karo da rubutun da ta turawa wata number....

_Yauwa naji gurin babu network bari inyi maka text kawai, kar a sake a kashe ta nagaya muku idan ta mutu dole wataran allura sai ta tono garma mu ci gaba da azabtar ta da ita idan ta gaji zata faɗa inda ta ɓoye, amma idan aka kashe ta fa bamu san inda ta ɓoye ba, mubi komai a hankali yanzu nama saka ancanza mata guri su kansu basu san inda take ba, yanzu haka tana cikin gida na na ƙulle ta a store so nake daman muyi maganar daku, ko fitar da ita za'ayi daga ƙasar ma gaba ɗaya nidai sai nafi samun kwanciyar hankali yanzu tana sakani wahalar jigila da ita danna ranar nan ɗiyata ta kusa ganin ta wallahi,
Duk yanda de kuka yanke hukunci sai ku faɗi yanda za'ayi sai najika..._

Take jikin sa ya ɗauki rawa zufa ta shiga tsatstsafo masa, fita yayi daga cikin number baiga reply ɗin da aka turo mata wataƙil ko waya sukayi, nan ya shiga yayi tayi mata bincike, a gaba ɗaya wayar inda saida ya kusan shiɗewa saboda yanda zuciyar sa take bubbugawa da abubuwan da yake cin karo da shi,

Wata folder ya gani ta hotuna da akai hidden ɗin ta kuma aka saka password, gwadawa ya farayi ko zai canki daidai, amma sai wrong yake sakawa, Salma ce ta faɗo masa hakan yasa shi saurin ɗaukar wayar sa ya kirata saidai yana ta kira ba'a ɗaga ba, baikuma fasa kiran ba, yana cikin kiran yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar, rikicewa yayi saboda nutsuwar sa ta fara barin jikin sa,

"Khalifa meye na ƙulle ƙofar kuma buɗe min na manta wayata, ƙwan ƙwan ƙwan sai bugu take da ɗan ƙarfi, can kuma yaji tace; "Saude ɗauko min muƙulli a kan madubi...

Miƙewa yayi da ƙyar yana sake kiran, bugu ɗaya kuwa ta ɗaga, da sauri yace "Salma kina jina, Password ɗin Mami zaki gaya min na waya ranar nan da kika faɗa min na manta,

"Me ya faru, bata
End Ads