x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - SU WAYE SU

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 162

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ta fashe musu fuska da abun da suka saba faɗa dashi, basu san ya akai ba duk basuga sauran ba da suka duba guda ɗaya ne a ciki shima na hannun Babyn baby.

Ameela kuma kawai ɗaukar jakar tayi sai kawai ta kunce mayafin jikin ta da tayi rolling dashi, ta ƙulle jakar aciki sannan ta nannaɗe ragowar mayafin a hannun ta tana ja da baya, tuni kowa ya fara nasa shirin ganin yanda hankalin mutane duk ya dawo kansu ga ƴan sandan da suke ƙara mamaye su, ana cewa su bada jakar a duba.

Tuni Aunty Babba ta tsige abayar dake jikin daga ita sai wando da riga singlet, dunƙulle hannu tayi wara ƙafafun ta yanda zata ji daɗin kaiwa mutum naushi,

Sojoji ma ba'a barsu ba ganin ƴan sanda agun yasa suma duk sukayi gurin duk da yawancin su sun fita waje wasu kuma suna cikin gidan,

Barazana kuma hill shoe ɗin ta da ta saka itama ta cire daga ƙafar ta, ta ware mayafin ta ta jere daidai tsinin ta ɗaure a mayafin Allah ya taimake ta ma daman ba matsatsun kaya tasaka ba doguwar rigace, sai kawai da wando a ciki sai kawai ta naɗe ta ta kawo ta ƙugunta ta ɗaure tana saita wani ɗan sanda da mayafin hannun ta da ta ɗaure takalman ta masu tsini.

Beenish ce ta fusgo mayafin Babyn baby da aka cire mata, ta shinfiɗa sa a ƙasa, sannan ta buɗe jakar ta kawai ta ɗaga ta ta fara zazzago ta, sai ga duwatsu na faɗowa manya wajen guda shida, da sauri ta ɗaure su, itama ta riƙe a hannun ta,

Sude mutane na ganin ikon Allah dan ƴan sandan ma duk tsayawa sukayi suna kallon su so suke suga iya gudun ruwan su, sannan su far musu.

Faheema gigicewa tayi sai ɓuya take a bayan su jikin ya na ɓari, so take ta bar gurin amma takasa, dan ƙafar ta sai karkarwa take,

Magana ɗaya ne yayi wani murmushi dan shi duk abun da suke shirme ya ɗauke sa, cikin zafin nama tunkan kowa ya tunkare su yayi kansu gadan gadan, ta ɓarin da Babyn baby take yabi, ita kuma loƙacin ta juya zatayiwa Faheema magana kawai saiji tayi an kuma funcuko ta yana juyo da ita yasa iya ƙarfin sa ya wanka mata wani mahaukacin mari da har saida ta tafi luu kamar zata faɗi Faheema ta taro ta jikin ta tana fashewa da kuka, dan spray ɗin hannun ta ma faɗuwa yayi a ƙasa take ganin ta ya ɗauke ta fara ganin duhu saboda tsabar shigar ta da marin yayi,

Tun bai gama sauke hannun sa ba shima kuwa yaji rubdugu akan sa, dan a kusan tare duk suka sauke masa mayafen hannun sa, Zee ta zabga masa a baya, Beenshi ya buga masa ƙullin duwatsun a gefen fuskar sa, Ameela ta buga masa ta ɗayan ɓarin, Aunty Babba kam ƙafa tasaka ta daki gaban sa ta ƙasan wando tana sauke ƙafar kuma ta tura sa da ɗayar ƙafar take ya faɗi agun gefen kunnen sa na fidda jini, ga azabar da yake ji a gaban sa.

Ƴan sanda tuni suna suka fara ƙoƙarin kai musu duka, amma suna karewa, kuma suna gurin sunƙi su matsa saboda Babyn baby da bata dawo daidai ba bazata ita ƙwatar kanta ba, ai ƙananun mahaukata suka zama agun, kawai juyi suke suna saukewa duk wanda ya matso kusa da su, wani sojane ya harba bindiga sama, aikwa sai ihu guri ya kuma hargitsewa, ana daidai haka kuma saiga shi an wangale gate ɗin harbin ya ƙara ƙaruwa saidai har yanzu bullet ko ɗaya bai shigo harabar wajen ba.

Ƙoƙari ake tayi a kama su ma amma sunƙi bada dama idan suka kama wannan sai su zulle musu ko kuma su haɗarwa wanda yayi ƙoƙarin riƙe wata, Babyn baby tuni ta miƙe ta ɗauki spray ɗin ta tana aiki dashi hakan nema yasa wasu basa zuwa inda suke saboda koya suka feso shi sai kaji raɗaɗin sa, ba komai yake kawo suji hakan ba sai barkonon da suke sakawa wataran su saka a cikin spray ɗin shiyasa idan suka fesawa mutum yake daɗewa bai dawo hayyacin sa ba.

Nan fa guri ya fara hayaƙi kawai sai gani akai hayaƙi na tasowa ta ƙasa anrasa daga ina yake, sosai hankulan wasu ya sake dugun zama da tsoro, daga waje sojoji kawai harbi suke suna harbin duk wanda sukaga alamun baida gaskiya, saboda shigowar wasu gurin masu baƙaken kaya anata ƙoƙarin a tare su amma saida suka shigo, saboda yawan su, har sun so sufi ƙarfin sojojin, dan suma da tasu bindigar shiaysa suka samu ƙarfin shigowa,

A gurin su Zee ma babu abun da aka tsaya dashi faɗan sukaci gaba dayi, da kaɗan da kaɗan hayaƙin yaci gaba da ƙaruwa agun har ya mamaye gurin tun kana ganin na gaban ka har ka dena ganin komai, dan hasken dake gurin ma kashe shi akayi tsayawa akayi da harbin saboda kar aje a harbi wanda bashi da laifi, amma ba'a daina doke doke ba, duk wanda kaji a kisa dakai duk kake kaimasa sannan kana ƙoƙarin kare kan ka kar a dake ka baka ankara ba, sude sun haɗe guri guda sun haɗa baya kowa na kai duka da hannun sa..

Magana ɗaya ne yayi ƙarfin halin miƙewa da ƙyar, yana miƙewa yaji an kuma maka masa wani abu komawa yayi ya zauna yana dafe kansa, amma duk da haka bai daddara ba sai ya lallaɓa inda yake da tabbacin suna nan, ta ƙasa ya kamo ƙafar ɗaya daga cikin su kawai yafara ja, tare da zaro wayar sa ya shiga haska gaba, fashewa tayi da kuka tana kiran wayyo Allah na na shiga uku kasake ni, sautin muryar ta kawai suke ji, Faheema ce take ta wannan ìhun ashe ita ya kamo.

Fitulun wayo da na mota duk aka shiga kunnawa da haske amma ba ko ina ba sai kana daf da hasken zaka ringa ganin komai shima ba ras ba, a haka akayi dabara sojojin suka ringa shiga da mutane cikin guarding ɗin gida dan cikin fako yayi musu kaɗan, manyan baƙi da ƴan gida ne kawai aka shigar da su falo.

A nan su Beenish suka rabu tabi bayan Faheema dada gudu inda take jiyo muryar ta tana ta kurma ihun a sake ta,

Yaude kowa yaga tashin hankalin da bai taɓa gani ba, duk da yawanci kowa mamakin abun da ya faru yake, duk da basa wajen gurin amma hankalin su a tashe yake.

RK kam duk da haka bai tashi daga inda yake ba, sai dai sojojin gurin da duk sukayi masa runfa suna kare sa, sai daga baya de da yaga abun yaƙi ƙarewa sannan yace su matsa masa miƙewa yayi daga inda yake ya tunkari tsakiyar gurin, zasu bishi duk ya dakatar da su, duk da ba haske sosai amma ana iya ganin na kusa dakai.

Shima gurin da yake jiyo muryar ƙanwar sa ya nufa dake sauri yake yi ma sai ya riga Beenish ƙarasawa yana zuwa kuwa shi kuma Magana ɗaya yana shinrin sakata a motar ƴan sandan, wata uwar damƙa yakaiwa damtsen hannun sa da a take ƙashin sa yayi ƙara wulli yayi dashi gefe guda baiyi duba sa kayan ƴan sandan dake jikin sa ba, kamota yayi ya fito da ita, duk da baya gani sosai amma yasan itace, wani waje ya kuma nufa da ita,

Suna juyawa ita kuma Beenish na ƙaraso ganin dishi dashin juyawar su yasa tayi tunanin ko duk wanda yake son ɗauke ta ne, sai ta kuma bin su, da gudu har tana karo da muta ne ta faɗi ƙasa ɗagowar da zatayi taga babu su, tashi tayi ta ci gaba da tafiya zata wuce wani guri kenan taga kamar wasu mutane suna jan wani mutumi sun saka masa ƙyalle a fuskar sa,

A kalar ta ta juya zuwa gurin, da sauri wani ya sha gaban ta, har tana karo dashi, hannun ta ya riƙe ita kuwa ta kai masa duka gefen fuskar sa, tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, shi kuma yana janta, ji tayi an ƙara riƙe ɗayan hannun, nan hankalin ta ya fara tashi saboda duk babu komai da zata iya ceton kanta, gashi ita kaɗai ce hannun ta kuma da zata dake su dashi sun rirriƙe mata shi, janta kawai suke amma duk da haka tana ƙoƙarin turjewa da ƙafar ta a haka har takalman ta suka cire,

"Ku sake ni nace, ku sake ni kafin na kashe ku, wallahi zanyi muku illa, basu fasa ba sukaci gaba da tafiya da ita, bakin wata mota suka kawo ta, tana zuwa tajiyo sautin muryar Babyn baby tana cewa "dan Allah ku sake mu wai me mukayi muku, Aunty Babba kiyi wani abu mana.

"Babyn baby kiyi shiru haka surutun ya isa haka" cewar Ameela.

Da ƙarfi Beenish tace "ya akai haka kuna nufin kun tsaya an kamaku ina Barazana?

"Gani" kinji ki da wani Abu zasuyi mana abun da Allah baiyi mana bane muga gudun ruwan su, in sun sha yanzu ai bazasu sha gobe, na rantse da Allah sai mun gutsun uwar commissioner dan durun uwar sa mu zaisa ayiwa wannna izayar....

Bata gama faɗa ba wani ya make mata baki tare da wanka mata mari, amma duk da haka bakin ta bai mutu ba, tace "kaima bana gane kaba zaka ci kutumar uban ka shegu guntun sigari....

Marin ta ya kuma yi, ku saka su acikin mota mu yafi dasu, basai muga a inda zaku ramaba idan kun rayu kenan ai yauce ranar mutuwar ku.....

Aunty Babba sai ƙwace ƙwace take dan ita maza biyar ne suka riƙe ta, sauran kuma maza bibbiyu ne suka riƙe ko wancen su riƙon da bazasu iya ƙwace wa ba, duk wannan abun da ake fa acikin duhu ne dan hasken gurin kaɗanne.

Buɗe ƙatuwar motar akai zasu fara saka su a cikin motar kawai na gaba yaji an yankar masa hannu da sauri ya sake ta yana riƙe hannun, ba zato ba tsammani saiji sukayi ana ta yankar su da wuƙa wani a wuya wani a hannu wani a ciki, kuma sun rasa wanda yake musu daga sun juya sai suga babu kowa, masu taurin kai duk da haka sunƙi sakin Beenish da Aunty Babba, duk da haka ƙoƙari suke su saka su a cikin motar,

Fitt kakeji an cirewa wani hannu ba shiri kuwa ya faɗi yana sakin ƙara, haske ne ya ɗan kawo wal ya ɗauke nan sukaga kamar macece take musu wannan ta'asar,

Mutum biyu aka yanke wa hannu fit ya faɗi ƙasa, waɗanda aka yanka kaɗanne suka fara kai duka suma suna zaro nasu wuƙaƙen ashe mutanen ɗan caucau ne suka hallara(magana ɗaya kenan)

Fitilar motar aka kunna gurin ya ɗanyi haske, nan suka fara kai nasu wuƙaƙen kan su Beenish, da ta zaro tata kuwa sai da taci uwar tasu a tsawo da kaifi, duk kawowar da zasuyi sai ta kare sannan takaiwa mutum ta yanke sa a hannu,

Guri ɗaya su Beenish suka haɗe suna kallon ikon Allah tare da mamaki da al'ajabi da yagama kashe su dan ko ƙwaƙƙwaran motsi basayi saboda mamakin yagama kashe su, dan har suna tunanin waye wannan dan a tunanin su ma namiji ne..

Ita kuwa baza baƙar rigar ta kawai take tana kare su, wani ne ya zagayo ta bayan su, cikin hanzari ya ɗaga tasa wuƙar zai sauke ta akan Beenish dake gefe, saidai baikai ga sauke ta ba tayi wani juyi ta kifa kansa suka faɗi ƙasa, itace akan sa shi kuma a ƙasa, wuƙar ya ƙara ɗagawa zai luma mata tayi sauri ta jirkice gefe ya daki ƙasa, sai loƙacin hankalin me baƙar riga ya dawo kansu,

Da sauri ta ƙaraso gurin ta taka hannun sa wuƙar ta faɗi ƙasa ganin Beenish a kwance yasa tayi tunanin ko ya yanke ta, da sauri ta durƙusa ta kamo hannun ta anan glass ɗin idon ta ya faɗi ƙasa nan sukayi ido huɗu da Beenish zaro ido tayi cike da ɗumbin mamaki da ya kusa kashe ta da ranta,

Bakin tane ya shiga yin karkawa tana nuna ta da ɗayan hannu zatayi magana kenan ta girgiza mata kai alamu kar tace komai miƙar da ita tayi tsaye tana ɗan bubbuga kafaɗar ta, tana ɗaga mata gira, tana yin haka, ta juya da sauri ta kuma yankar wani da tagani a kusa da su, tana baza rigar ta ta tsugunna agun tana miƙewa kuwa ta zaro wasu ƙananun wuƙaƙe guda biyar ta zube su a gaban su, cikin sauri tayi gaba tare da ɗan ɗaga muraya tace "take carefully" cikin gudu ta ɓacewa ganin su.....

Mutanen magana ɗaya tuni tsoro yasa suka fara shiga mota waɗanda suke da damar iya shiga ɗin sauran kuwa suna kwance jini na fita ko motsawa sun kasa.

Cikin rawar baki da har haɗa magana kamar masu koyon magana a kusan tare suka haɗa baki su huɗe wajen cewa "Haj...jjj....jjjjja..!!!! kasa ƙarasawa sukayi saboda tsabar mamaki da yagama kashe su....

"Maaamaaa.!!!" Beenish ta ƙarasa musu....

Tsugunnawa Ameela tayi ta ɗauki wuƙaƙen da ta ajiye musu kallon su ta shiga yi tana miƙewa tsaye tace tabbas itace wannan wuƙaƙen ba inda ake samun irin su sai a gun ta...

Beenish ce ta matso kusa da ita tana karɓa itama ta shiga gani ta ƙura musu kamar ance zatagan ta ajikin wuƙaƙen.

"Wai daman tana raye har yanzu wallahi nazaci ta mutu" cewar Babyn baby.

Hannu Aunty Babba ta ɗora akai tana cewa "Oh my God ya Allah he he Hajja Mama na nan a raye?

Beenish ce tayi shiru kafin daga bisani yace "Hmm ni daman nasan bata mutu ba, kuma tana sane damu bazata taɓa cire idon ta akan mu ba, duk wani motsin mu zata iya sani mune de bazata taɓa bari mu san inda take ba, kuma maganar gaskiya dole mu nemota ganin ta na da matuƙar muhimmanci a rayuwar mu,

"Gaskiya ne maganar ki, ni abun mamakin ma me ya kawo ta nan dan nayi mamakin ganin ta wallahi, inji Ameela.

Barazana tace "Kema ai kin san halin ta bai kamata ma kiyi mamaki ba, hmmm Hajja Mama ikon Allah tana nan da halin ta ashe..

"Wayyo Mamana Hajja Mama tawa nikwa ta Allah ni wallahi dama ta ɗan saka ni a gefen rigata ta tafi dani, ji nake kamar na bita" cewar Babyn baby

"Ɗan murmushi sukayi gaba ɗayan su, suna cewa "yanzu ma ai da kin bita zaki same ta tana waje inajin....

Gurin ne ya fara washe wa alamun an daina sakin hayaƙin tiya gas ɗin amma fa ba irin namu bane nan kar wasu suji inacewa tiya gas kuma anzauna lafiya ana shaƙar numfashi, irin na ƙasar waje ne kawai hayaƙi ne da shi.

Tushh Tushhh Tushhh kawai kake ji ana harbi a waje sosai ƙarar bindugu suke fita, kanaji kasan musayar alburusai kawai ake.

Ganin hakan yasa Ameela cewa ya kamata mu bar gurin gidan nan kafin a tado da waccen maganar ta koken bamu da hujjar kare kanmu indai aka gani acikin jakar mu, idan aka gani waɗancen masu zubin jaɓoɓin da kayan su kore kamar gansa kuka, zasu iya jiƙa mana aiki,

Beenish tace "To a haka zamu fita kinajin harbin da akeyi ai sai a haɗa damu, ga kuma wuƙaƙen nan a hannu kowa ta karɓi tata, Ameela ta miƙawa Ameela na shirin karɓa kawai idon ta ya sauka akan sunan da aka rubuta ajikin wuƙar, wai Boss, da sauri tace muga sauran ga mamakin su sai su
[3/5, 11:57 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*

(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)

______________________________


*_episode 23💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

___Jinjina kai yayi sai ya kuma cewa "Ina Sir SMA? (sergeant major of the Army), shugaban sojojin gaba ɗayaiwanda shine ƙarshen muƙami sama da kowa da kowa yake. Kuma shine wanda RK ya fara gaisarwa a airport...

Sai loƙacin kowa hankalin sa ya dawo kansa, nan aka shiga neman a amma babu shi babu me kama da shi, a garin laluben sa ne ma akaci karo da wayar sa da ta faɗi, sunji taƙaicin ganin ta saboda da ace tana jikin sa dole zasu iya bibbiyar sa ta hanyar wayar amma yanzu ba su san ma ta inda zasu fara ba,

"Sir mun fa duba ko ina babu shi amma de ga wayar sa, suka miƙa masa.

suna miƙa masa loƙacin yayi daidai da shigowar sauran tawagar sojojin da suka bi motar basu samo ta ba, hakan yasa suka dawo, dan sanar da RK (General of the Army)

Suna ƙarasowa tun kan suce komai ya zare glass ɗin idon sa ya watsa musu wani kallo take duk sukayi ƙasa da kansu dan babu me iya bari ya haɗa ido dashi musamman da suka san abun da sukayi.

Cikin ɗaga murya me tare da amo irin ta zaratan maza kuma a matsayin sa na babban soja da ranshi ya ɓaci yana zazzaro musu ido yace "Prepare to move out and hold the line..!!

Kan kace me kowa ya shiga hankalin sa, waɗanda ma basa gurin da sukaji maganar sa da gudu su ƙaraso gurin suka shiga yin layi, a ɗan ƙanƙanin loƙaci da baifi minti ɗaya ba da ƴan sakanni suka gama saita kan su, a tare suka buga ƙafafun
End Ads