gaba ɗayan ku, sannan ku kula sosai dannan san bazamu ƙara haɗuwa ba, tana faɗa ta nufi hanyar fita, da sauri Ruƙayya tace "a'a Mama kar kije dan Allah kizo ke ki fita gwanda mu ki bar mu, ƙwace hannun ta tayi tace Ruƙayya bana son sha shanci kije ku tafi kar ku bari su kama ku kashe ku zasuyi, ni na yarda in mutu ku ku rayu, zanje na same su, ƙin matsawa tayi tana ƙara girgiza mata kai ita babu inda zata, shima kabeer sai jikin sa yayi sanyi ya kasa haurawa, gaba ɗaya ma jikin sa ne ya ɗauki ɓari, yace "Mama kar kije ki zo ki fita dan Allah, mu ki barmu na fasa fita nima, bubbuga ƙofar aka farayi nan suka kuma ruɗewa sun tsaya jayayya tace su fita sunce saidai iya ta fita kowa ya kasa fita daga ciki,
Suna cikin ɗakin kawai suka ga ruwan abun na shigowa ta ƙasan kofar a hankali mama ta tsugunna ta taɓa nan taga ruwan fetur ne yake gangarowa ciki, da sauri ta miƙe ta fashe da kuka cikin masifa tace "fetur ne ƙone mu zasuyi saida nace ku fita ku fita da tuni kun fita amma kunƙu fita, dukan su tsorata suka kuma yi, jikin su sai karkarwa yake...
Shu'aibu da duk suna jin abun da suke cewa suma hankalin su a tashe yake wasu bululluka da suke bayan gidan ya ringa ɗebowa yana jere su dan gurin yayi tsawo yana kaiwa kuma da ya leƙa yana ganin su suna ta kuka gashi bai ɗauki jakar ba tana gurin Kabeer yazo tsallakowa da ita Mama ta fara wannan maganar ya sake ta ya koma cikin ɗakin,
Ko da ya leƙo leƙen inda zaiga jakar yake amma baigan taba, magana ya fara yi musu su fito su fito amma su tsaya ƙoƙarin maida kansa ciki yayi, amma sai kawai ya fara ganin wuta, baisan loƙacin da ya saki ƙarfen da ya riƙe ba ya koma da baya ya faɗin ƙasa....
"Kabeer wuta ce ku tashi mu fita wuta ta fara shigowa, sai loƙacin hankalin su yakai maƙurar tashi, gashi wutar har tazo rabin ɗakin, Maman suka fara ƙoƙarin ɗagawa ta fita amma yanda suka tsure ya zamana jikin su duk babu ƙwari itama garin karkarwa ta suɓuce daga hannun su ta dawo da baya ta faɗi ƙasa, da sauri sukayi kanta suna shirin ƙara ɗagota ta ɗaga musu hannu tana girgiza kai yayin da hawaye yake gangarowa ta gefen idon ta, ƙashin tane ya bugu a faɗowar da tayi, dan har ƙarar sa taji, batajin zata iya tashi...
"Cikin matsanancin hali tace "Ruƙayya ku fita ni tawa ta ƙare har yanzu kuna da sauran loƙaci ku fita ku fita dan Allah kar ku bari ku mutu, suma duk kukan suke sun kasa ta ɓuka komai, Kabeer ne ya kamo hannun Ruƙayya yace muje ki fita ke girgiza kai tayi saboda ƙasan ta hana mata ciwo na ɗinkin da akayi mata da ta haihu bazata ita ɗaga ƙafar ta ba bai gama warkewa, kuma gashi bazata iya tafiya tabar Maman taba, a cikin wannan halin..
Tsawa ya daka mata yace "ki muje ki fita so kike kema ki mutu bakya tsoron mutuwane!
Kanta yayi da ƙarfi ya ɗagata dan wani irin ƙarfi yaji yazo masa, saidai yana ɗaga ta aka turo ƙofar ɗakin amma duk da haka bai dakata ba, yaci gaba da ƙoƙarin turata, yaf sukaji an watso musu abu jikin su suka bi da kallo kansu tantace meye ma warin sa ya dake su, suɓucewa tayi daga hannun sa, shima sai jikin sa yayi sanyi baisan loƙacin da yayi zaman dirshen a ƙasa ba jinsa da motsin sa na neman ɗaukewa gaba ɗaya, idon sane ya sauka akan mayafin Mama da ya fara ci da wuta a sukwani yayi gurin zai cire mata mayafin saidai yana zuwa shima wuta ta lasoshi sakamakon fetur ɗin dake jikin sa, nan wuta ta fara cin hannun, kuka ya fara yi yana sakin ƙara yana bugeta da ɗayan hannun shima sai ya kama, Mama ido kawai dan ta gama daskarewa agun, da ƙyar ta iya kamo hannun sa dake ci da wuta, tureta ya shiga yi, ihun Ruƙayya suka jiyo kawai itama daga inda take ashe suka jefa mata ashana, ta fara ci da wuta, faɗowa tayi daga kan gadon da ta faɗi tun ɗazu gurin su ta gangaro saida kafin ta taɓasu wutar ta cika duka ɗakin, ihun su kawai kake ji, su kuma suna daga bakin ƙofa suna ganin haka suka fita daman sun gama saka fetur a ko ina suna fita kawai suka sakawa duka gidan wuta....
Loƙacin da Shu'aibu ya faɗin nan duk da yaji azaba amma a haka ya miƙe cikin sauri ya karɓi jaririyar da take ta kuka ya kama hannun Fateema yace "yi sauri kiyi gudu, gudun take amma tambayar sa take Su Mama fa, amma janta yake kawai suna gudu daman bayan gurin yayi kama da bayan mutane sai gonake da shukoki sun farayin tsawo, saida ya san da sunyi nisa da gurin, sannan ya samu wani guri da yayi duhu sosai, sannan yace "ku zauna anan yanzu zanje gurin su zamu taho tare kinji kar kitaɓa tashi daga nan koda kinga bandawo da wuri ba sannan kiyi addu'a kar kiji tsoron komai yanzu zamu taho tare da su...
A nan ya barta sannan ya kuma kwasa a mugun guje ya nufi gidan, yayi mata hakane dan ta denajiyo muryoyin su hankalin ta yana kuma tashi.
Gudu yake sosai iya ƙarfin sa, saidai tun daga nesa ya hango wuta na tashi daga gidan daman yasan za'a rina, daman tunanin sa yabasa kafin ya dawo zasu iya ƙona su, gashi ma gaba ɗaya gidan suka ƙona, zubewa yayi awajen yana sakin wani marayen kuka, danji yake duk laifin sane dan shi ya sakasu a cikin wannan laifin da baikai musu ƴar ba da tuni duk wannan abun bai same su, kuka yake sosai yana bubbuga ƙasa kamar ƙaramin yaro haka ya dawo, yanzu gashi ya ja musu duk sun mutu gashi kuma abun da suke yi dan samun hujja suma suna ciki sun ƙone,
Ya daɗe agun yana kuka yana saƙa da warwara, da ƙyar ya iya miƙewa daga gun ya tashi gwiwayin sa duk a sake, yana tafiya hawaye na zubo masa, a haka yaje ya same su suna inda ya barsu ko kallon ta bai iyayi ba, ya kamo hannun ta kawai ya riƙe yarinyar tana ta tambayar sa amma ya kasa bata amsa, hakan yasa ta fahimci abun da yake nufi kuka kawai take yana janta bai hanata ba dan shima kukan yake haka suka ringa tafiya da su kansu basu san inda suke dosa ba...
A gurguje....
Bayan shekara bakwai, acikin shekarun abubuwa sun faru da dama, saida suka samu nutsuwa daga inda suka baro take basa ƴar ƙaramar jakar tarkacen sa da yayi tunanin ta ƙone, ashe loƙacin da Kabeer ya sake ta ita kuma ta ɗauka, dake babu nutsuwa a tattare dashi yasa baiga jakar ba, saida suka sauka a wani gari yagani, a cikin shekaru bakwanan ya samu aiki a wani gari basu daɗe tare ba ya auri Fateema inda suka samu gidan su madaidai ci suke rayuwar su ga kuma cikin mutunta juna suna bawa jaririyar kulawa iya bakin ƙoƙarin su har ta girma, makaranta babu wacce batayi, duk wani nauyi da za'a saukewa yaro sunayi mata, babu abun da suka rage ta da shi, suna zaman kwanciyar hankali dan inba zama sukayi bama basa tuna rayuwar su ta da, sun tattara komai sun barwa Allah, saidai duk daɗewar nan Fateema bata haihu ba sai a wajen shekara shida ta samu ciki....
Watarana kwatsam saiga mutanen nan sun gano inda yake inda suka fara bibbiyar sa, saidai wannan karan ta ruwan sanyi suka biyo masa suna so ya basu, amma shima saboda yayi musu barazanar ko sun kashe shi abun yana hannun mutane da yawa kuma kashe shi ne zaisa asirin su ya ƙara tonuwa hakanne yasa suke binsu a hankali ba kamar shekarun baya ba,
Saida daga baya dai da sukaga bashida niyar bayar da shi watarana yazo ya same shi a gida shi maɗai saida ya fara dukan sa sannan ya ɗaure sa yana tambayar tambayar sa ya basu yana zaune akan kujera a ƙulle.
Fateema kuma da tsohon ciki ajikin ta, haka ta fito daga ɗaki da gudu,
"Dan Allah...! Dan Allah,Dan Annabi ku taimaka kuyi haƙuri kar ku kashe shi na roƙeku, kada kuyi haka, ku rabu damu namuku alƙawari zan sashi yabaku duk abun da kuke nema amma dan Allah ku rabu dashi ko inhelar ce ku taimaka ku bari ya sha idan numfashin nashi ya daidai ta sai kuyi magana, sai roƙonsu take ga tsohon ciki ajikin ta amma duk ta fita a hayyacin ta ganin me gidan nata yana shirin barin duniyar.
Da haka ta kuma rarrafawa taje gaban su tare da dafa ƙarfar mutum da taga yana shirin kunna sigari, kallon ta yayi ta ƙasan ido tare da ɗaga ƙafar sa saida ya saita daidai cikin ta sannan ya turata ta faɗi ta bayan tare da sakin wata mahaukaciyar ƙara saboda azabar da taji ta a ƙasan marar ta,
Hankalin sa ya mayar kan mutumin dake ɗaure ajikin kujera yana ta fusge fusgen yanda zai kwace daga ɗauren musamman da yaga yanda yayiwa matar sa, hawaye ne kawai yake gangaro masa daga cikin idanun sa, idan ya yunƙura yaga ya kasa sai ga koma tare da ci gaba da kuka me ciwo, ga numfashi sa da ya dawo ƙirji yana shirin ɗaukewa idanun sa sun kaɗa sunyi ja shi kaɗai yasan halin da yake ciki,
Gashin kansa yakamo ya ɗago dashi, sigarin da ya kunna ga zuƙa tare da hura masa hayaƙin a daidai saitin hancin sa, nan da nan kwa yayi wata ɗauke gaba ɗaya sannan ya kuma kawowa cikin mawuyacin hali,
Da sauri ta kuma yunƙurawa zata tashi tana sakin kuka me ƙarfi amma bata kai ga ƙarasawa ba ya kuma turata baya ta faɗi tare da bugewa da jikin kujera nan itama ta ɗauke bata kuma motsawa ba, ko kallon inda take beyi ba, ya ci gaba da abun da yake yana zuƙu sigarin sa yana busawa Shu'aibu duk dauriyar sa dole yakasa komai yanaji yana gani babu ƙarfin ƙwatar kansa, tun yana gani bibbiyu ya dawo ganin dishi dishi kansa yana lanƙwashewa sai ya kuma yin ƙarfin hali ya buɗe su amma sai su ƙara rufewa saboda sunyi masa nauyi ga numfashin sa saura ƙiris ya ɗauke, girgiza wa ƴar su kai yake alamun kar ta fito daga inda take a ɓoye, sai kuka take a hankali dan tunda yaji sune yace ta tsaya ko me zata gani kar tayi kuka kuma kar ta fito in ba hakaba kuwa zasu kashe ta, hakan yasa taji tsoro taƙi fitowa daga gurin.....
Mutumin ne ga kuma busa masa sigarin a hanci sannan yasa hannu ya toshe masa hanci bai saki ba saida yaga ya dai na numfashi,
Wani ƙaton ƙarfe yarinyar ta ɗauko da Shu'aibu yake fita dashi, idan zasuyi aikin saran nama, lallabowa tayi ta dage iya ƙarfin ta ta buga masa akai nan take kuwa shima ya faɗi a ƙasa ya suma,
Hannun ta na karkarwa ta saki abun ta koma kansa ta shiga girgiza sa tana kuka tana kiran sa,
"BEENISH..!
Da sauri ta juya gurin ta ganin ta farfaɗo yasa ta tashi da sauri ta koma kusa da ita tana kuka tace Umma Baba ya mutu kice masa ya tashi, dan Allah kar ya mutu ya barmu, yunƙurawa tayi ta tashi da ƙyar tana dafe kanta da yake mata ciwo, sai loƙacin idon ta ya sauka akan mutumin dake kwance bata san loƙacin da ta tashi ba tana kallon yarinyar tace Beenish me kikayi masa, tashi mu gudu idan ya tashi muma kashe mu zaiyi,
Suna kuka gashi suna kallon sa amma babu yanda suka iya, dole ta shiga ɗaki ta ɗauko duk abun da zata ɗauka cikin sauri ta kamata suka bar gidan..
Mota ta tarar musu suka ma bar garin gaba ɗaya, suna zuwa kuma asibiti kawai ta tambaya dan tana jin cikin ta na muraɗawa kamar naƙuda, suna zuwa kuwa akace mata ai tanama daf da haihuwa, karɓar ta akayi tayi duk wani ciki ciki da zatayi aka shiga labour room da ita,
Bata ɗau loƙaci ba ta haifi santaleliyar ƴarta mace, saida aka kaita ɗakin hutu sannan aka kai mata yarinyar da ta bada ajiya, kwanan su uku aka sallame su saidai basu san inda zasu dosa ba, a cikin garin suka ringa yawo da taga kuɗin gurin ta sun kusa ƙarewa sai kawai ta fara bin gida gida neman aiki, nan kwa ta samu wani gida, ta haɗa su da Allah zata zauna da ƴarta itama sai su bata wani aikin, anan suka ci gaba rayuwa tsawon shekara ɗaya, suna zaman su wani yayi musu sharrin Beenish ta ɗaukar masa kuɗi nan kwa akayi musu cin mutunci a ka kore su daga gidan,
Wajen wata me saida abinci ta kuma samo musu, suka farayi, agurin tana cikin wanke wanke watarana taga wata mota ta tsaya a gaban wajen tare da sauke glass sai taga ana nunata, tashe tayi da sauri ta shiga cikin gurin yaranta da ta bari suna wasa taje, zanin goyon ta ta ɗauka sai tayi sauri tace "Beenish tashi yi sauri maza miƙewa tayi tana tambayar lafiya taga duk ta tsure haka, shiru tayi mata cikin sauri ta ɗauki Haneefa shine sunan yarinyar da ta haifa wacce kuka fi sani da Babyn baby.....
Goya mata ita tayi ta ɗaure ta sosai, sannan ta jawo ta wani lungu tace ku tsaya anan duk abun da zaki gani kar ki sake kiyi magana, kuma kar ki fito nagaya miki....
Tana gama faɗa musu haka ta juya tana fitowa fili kuwa taci karo da mutane a gaban ta daman tun ɗazu suke neman ta suna ganin ta kuwa suka dannan mata farin ƙyalle sukayi gaba da ita tare da danna ta cikin mota..
Kuka me ƙarfi ta fashi dashi tana toshe bakin ta tace tundaga ranar ban kuma ganin su ba ban kuma fita ma waje ba kullum ina ƙulle, anan gurin na barsu bansan wane hali zasu kasance ba da masani bance ta tsaya anan ba, yanzu nasan suma sun kashe su yaran da basuji ba basu gani ba, sosai take kuka tunawa da abubuwa da tayi, shima taya ta yake babu me rarrashin wani..........✍️✍️✍️
Ni zanzo na rarrashe ku🤣😅
[3/5, 12:12 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 28💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah....✍️
*Five star ⭐*
___Suna zaune a falo sukaji anayi musu bugun hauka, kallo kallon suka shiga yiwa suna mamakin wanda keyi musu bugun dan sun san sude basu da wani wanda zai shigo musu gida, Aunty Babba ce tace "waye ne haka, ta faɗa tana miƙewa tsaye, tare da nufar wajen ƙofar,
Leƙawa ta farayi ta wata jikin wata ƴar ƙofa, da saura ta juyo tana kallon su, suma kuma duk sun zuba mata ido suna jiran suji me zatace, a hankali tace "Soldiers!
Duk miƙewa sukayi ko wacce da gudu ta shiga wawuro abun da zata kare kanta wasu suka shiga kitchen suka ɗauko wuƙa, wasu kuma muciya, harda ne fork spoon, a yanda suke da shigar su nan babu wanda ya sauya kaya, zuwa sukayi suka jeru a bakin ƙofar duk suka yi ready jira suke kawai Aunty Babba ta buɗe, tana buɗewa itama taja da baya baya ta dunƙulle hannun ta tana tala ƙafa, turo ƙofar akayi, ana turowa kuwa wanda ya fara sako ƙafar sa duk suka kai masa duka, da sauri akaja shi ta baya aka mayar dashi gefe, ƙafa ɗaya ya ziro da taci uban takalmin sa na sojoji me tudu, shima dukan suka so kai masa, har suna ɗaga zasu sauke masa, sukayi saurin dakatawa, suna janye hannunwan su, ɗayar ƙafar ya ziro tare da saka ƙafa ya tura Beenish dake gaban sa, nan kwa ta faɗi wuƙar hannun ta, ta faɗi gefe, Babyn baby ce ta shiga fesa masa abun hannun ta saidai ko gezau beyi ba saboda ya saka glass itama damƙo ta yayi ya jefata gefe, a tare sauran sukayi kansu, amma tun kan su matso inda yake yasa ƙafa duk ya tura su babu wacce bata faɗi ba kuma babu wacce bataji jiki ba,
Shigowa yayi gaba ɗayan sa sannan ya zare glass ɗin sa ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya, idon sa akan Beenish ya tsaya saidai suna haɗa ido ta galla masa harara tana shirin miƙewa yasa ƙafa ya kuma buga ta saida ta matsa daga inda take, ƙara ta saki bata san loƙacin da bakin ta ya furta Allah ya isa ba, a fusace ya kalle ta zai kuma yin kanta, sai kuma ya tsaya tare da saurin kawar da idon, sakamakon ganin rigar ta ta yaye sai santala santala cinyoyin ta da suka fito saboda daman rigar