x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - SU WAYE SU

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 149

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mutane dayawa suna shiga aure da intention din Ayita soyayya ayita caring amman suna mantawa da gyara wanda zai iya saka marriage ya zama burden rather than blessing,

"If Kinason Aurenki yayi Quality, try and no the importance of looking after yourself, so that you can give your best to the marriage baka bari ka zama kaman wani banza,ko wani wanda bashida mafadi,dan gaskiya was rashin mafadi ne yaka saka mata zama haka babu gyara babu gyarawa wanda ko kai a matsayinka na mace bazaka iya rayuwa dasu ba..

My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 11:30 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 6💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

___Duk saranda sukayi kowa yana tunanin what is the solution, whait is going to happen to them like this, who wants to come into their lives like this......????a

Gaban motar suka nufa inda sukayi karo da wani rubutu a jikin farar takardar da aka manna a gaban motar ta ciki,

Ameela ce tayi ƙarfin halin buɗe motar ta zaro takardar me ɗan faɗi, fara karanta musu tayi da ɗan ƙarfi yanda kowa zaiji.

_"ku kwantar da hankalin ku shiga wannan motar nayi muku canji ne saboda neman ku da akeyi akan abun laifin da baku kuka aikata ba, ku shiga kuci gaba da uzurin gaban ku kar ku nuna kunsan wani abu game da tuhumar ku da akeyi kuma ku dena rufe fuskokin ku ina fatan zaku kiyaye?_
_Bislama......._
_Saƙo daga kidnaper....._

Tana gama karantawa ta maida kallon ta garesu da duk sukayi tsurutsuru suna sauraron ta har saida takai aya,

Suma duk itan suka zubawa a kusan suka haɗa baki wajen faɗin _"SAƘO DAGA KIDNAPER??_ Suka faɗa suna tsatstsareta da idanu kamar itace kidnaper ɗin,

Jinjina musu kai tayi alamar tabbatar wa,

Ɗan shiru sukayi na wani ɗan loƙaci kafin daga bisani Beenish ta ɗan numfasa tare da furzar da iska me zafi daga bakin ta sannan tace "bamu da isasshen loƙaci gurin ɓata loƙacin mu da tunani tunda hakan ta faru kawai mushiga mu tafi daga baya mayi tunanin gano ko waye ke shirin yi mana haka dole mu gano ko su waye su,

"Maganar ki gaskiya ce dan idan muka zauna tabbas we are in trouble dan be kamata mu barshi haka ba, yana sace ƴaƴan mutane sannan yana amfani damu" 'cewar Barazana.'

"Dole sata ta saci sata...!

"Kai Beenish banajin fa wanann karan sata zata iya satar sata, domin wannan babbar sata ce bazata saci ba, tunda kika ga haka baƙaramin shiri ne da shi ba kafin ma mu gano ko waye ba abunne me sauƙi ba bare har mu iya sace shi mudai ina ganin kamar tunda har baiyi mana komai ba, ba na jin zai yi mana, gaskiya ba ƙaramin me lissafi bane tunda kinga ƴaƴan manyan masu kuɗi yake ɗaukewa to babban kaine, nidai a nawa ganin mutattara batun sa mu watsar mu ciga ba da rayuwar mu kamar da mu manta da babun sa, amma fa a tawa shawara, amma ku ya kuke gani?

Shiru sukayi kowa yana nazarin maganar da Ameela tayi, a kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya tare da ɗan numfasawa, kafin daga bisani... Fashion ta furzar da iska daga bakin ta sannan tace; A gaskiya maganar ki da abun duba a ciki nima lamarin mutumin ya ɗan ban tsoro wallahi kuma abun mamakin ma duk yanda akai me kuɗi ne saboda ko wannan abun da yayi amfani dashi loƙacin da aka kamamu (tiya gas) ɗin nan ba ƙaramin tsada ne da shi ba, gashi kuma yanzu ya siya mana sabuwar mota, kuma ina da tabbacin tabbas bazai taɓa bari a kama mu ba, duk yanda akai idon sa yana kan mu bana tunani zamu iya gano shi ma bare har mu kama sa, mudai bari kawai muga iya gudun ruwan sa indai bazai hana mu aikin gaban mu... Shiru tayi tana kallon fuskar Beenish da tayi shiru tana jinjina kai tare da ƙara nazarin maganganu su gaba ɗaya,

Almost 1 minute babu wanda ya kuma magana, Beenish ce ta ɗan gyara tsayuwar ta ta kalli Barazana tare da dafa kafaɗar ta tace; kunyi tunani me kyau babu yanda bazai kasance ba amma fa kusa a ranku ko badaɗe ko bajima zamu gano sa ko waye koda ba'a ƙasar nan yake zaune muddin ya cigaba da bibbiyar mu nima bazan ƙyalesa zamu gano sa tabbas zamu gano sa tafaɗa tana jinjina kai cike da confidence.

Babyn baby ce murya cike da sanyi tace amma Aunty Beenish bakya ganin....

Hannu Beenish ta ɗaga mata tare da saka yatsar ta ɗaya a baki tana cewa; Shhhhh alamun yi shiru tana faɗin haka ta buɗe gaban motar wajen driver seat ta shiga,

Babu yanda suka iya suma babu wanda ya samu damar yin wata magana dole suka shiga bubbuɗe murfin motar suka shiga suna shiga ta tayar da motar ta nufi wajen gate ɗin saida taje daf da gurin taja burki ta tsaya, da sauri Aunty Babba ta buɗe motar ta fita tare da zuge musu gate ɗin suka fita sannan ta rufe ta buɗe ƙaramar ƙofar ta fita, tana zuwa ta buɗe motar ta shiga, Beenish taja su suka ɗauki hanya babu wanda ya kuma magana acikin ɗif kamar babu kowa aciki, duk sunyi shiru kowa da abun da yake saƙawa a cikin ransa......

*$$$$$$$$$$$$$$$$$*

"Dan Allah...! Dan Allah,Dan Annabi ku taimaka kuyi haƙuri kar ku kashe shi na roƙeku, kada kuyi haka, ku rabu damu namuku alƙawari zan sashi yabaku duk abun da kuke nema amma dan Allah ku rabu dashi ko inhelar ce ku taimaka ku bari ya sha idan numfashin nashi ya daidai ta sai kuyi magana, sai roƙonsu take ga tsohon ciki ajikin ta amma duk ta fita a hayyacin ta ganin me gidan nata yana shirin barin duniyar.

Da haka ta kuma rarrafawa taje gaban su tare da dafa ƙarfar mutum da taga yana shirin kunna sigari, kallon ta yayi ta ƙasan ido tare da ɗaga ƙafar sa saida ya saita daidai cikin ta sannan ya turata ta faɗi ta bayan tare da sakin wata mahaukaciyar ƙara saboda azabar da taji ta a ƙasan marar ta,

Hankalin sa ya mayar kan mutumin dake ɗaure ajikin kujera yana ta fusge fusgen yanda zai kwace daga ɗauren musamman da yaga yanda yayiwa matar sa, hawaye ne kawai yake gangaro masa daga cikin idanun sa, idan ya yunƙura yaga ya kasa sai ga koma tare da ci gaba da kuka me ciwo, ga numfashi sa da ya dawo ƙirji yana shirin ɗaukewa idanun sa sun kaɗa sunyi ja shi kaɗai yasan halin da yake ciki,

Gashin kansa yakamo ya ɗago dashi, sigarin da ya kunna ga zuƙa tare da hura masa hayaƙin a daidai saitin hancin sa, nan da nan kwa yayi wata ɗauke gaba ɗaya sannan ya kuma kawowa cikin mawuyacin hali,

Da sauri matar ta kuma yunƙurawa zata tashi tana sakin kuka me ƙarfi amma bata kai ga ƙarasawa ba ya kuma turata baya ta faɗi tare da bugewa da jikin kujera nan itama ta ɗauke bata kuma motsawa ba, ko kallon inda take beyi ba, ya ci gaba da abun da yake yana zuƙu sigarin sa yana busawa bawan Allah nan duk dauriyar sa dole yakasa yanaji yana gani babu ƙarfin ƙwatar kansa, tun yana gani bibbiyu ya dawo ganin dishi dishi kansa yana lanƙwashewa sai ya kuma yin ƙarfin hali ya buɗe su amma sai su ƙara rufewa saboda sunyi masa nauyi ga numfashin sa saura ƙiris ya ɗauke....

"A'ah...! A'ah..! Baba..!!Baba...!! Muryar ta ce ta karaɗe duka Hole ɗin dake ciki da mutane almost 200 suna ɗaukar lecture, gaba ɗaya mutane hankalin su ya koma kanta, kowa ya zuba mata ido, da gudu Babyn baby ta ƙarasa kusa da ita tana zuwa ta faɗa kanta ta rungume ta sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara ƙanƙame ta, cikin sanyi jiki Aunty Babba ta ƙaraso kusa dasu itama idon ta ya canza kala dan har ƙwalla ta tarar mata ta cika idon, tayi saurin gogewa bata bari ya sauko mata,

Kowa na gurin duk da basu san ne ya faru ba amma saida suka tausaya musu yanda suka riƙe juna suna kuka dole su baka tausayi.

A hankali DR. JAVEED ya shiga takawa zuwa gaban su yana zuwa ya naɗe hannuwan sa a kan chest ɗin shi yana me binsu da kallo gaba ɗayan su,

'Aunty Babba ce ta shiga rarrashin su tana ɗan bubbuga bayan su amma basu bar kukan ba saida sukayi me isar su, sannan Babyn baby ta ɗago daga jikin ta cikin sanyi jiki, sai ta ɗora hannun ta a kan fuskar ta tana girgiza mata kai, Muryar ta har ta fara fashewa ta ce; Yaya me yasa? Me yasa zakiyi haka? Ke da kike share min hawaye na ke kike kwantar min da hankali a koda yaushe kina yawon gaya min indaina tunanin komai inba abun dake gabana ba kina yawon gaya min kar inbari tunani yasani kuka, kina yawon gayan kar nasake na ringa bari hawaye na yaringa zuba a kan tunani amma ke me yasa kikayi kina tunanin zan iya daurewa zan iya hakan bayan nasa kema kina cikin damuwa yaya nasan da ciwo amma kar ki bari raunin ki ya ringa bayyana idan ina gurin, a duk loƙacin da naga haka ina iya kaiwa sati ban dawo daidai ba ko so kike nim.....

Da saura ta ɗora hannun ta a kan bakin ta ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai tana ƙaƙaro mmurmushin dole tanayi, fuskar ta cike da murmushin dole da ta aro sa itama ta shiga goge mata nata hawayen tana ce wa; Babyna babu fa komai ni ba a bun dake damuna bakiga ma mmurmushi nake miki ba kawai wani a abu na ɗan tuna kuma kukan da nayi ai dannaga kina yi ne amma ni babu abun dake damuna ki kwantar da hankalin ki duk abun da nake gaya miki gaskiya kar kiyi tunanin komai kinji...

'Duk wannan maganar da take tanayi tana mmurmushi saidai kuma bata sani hawaye har rige rigen fitowa suke daga idon ta tana ta ƙoƙarin ta ɓoye damuwar ta amma ba hali, duk wanda ya kalle ta sai yaji tausayin gashi magana take tana mmurmushi yayin da kuma idanun ta suke ta faman tsiyayar da ruwa, zubar hawaye da kuma mmurmushi duk a loƙaci ɗaya.

Babyn baby da ta fahimci halin da take ciki sai taji ta ƙara bata tausayi dan haka cikin sanyi murya tace; Yaya......

Bata kai ga ƙarasa faɗar abun da zata faɗa ba, Dr.Aveed yayi gyaran murya dukkan su ɗagowa sukayi suna kallon sa dan su sun ma manta a inda suke, suna kallon sa kuma, Bineesh tayi saurin sunkuyar da kanta murya ƙasa ƙasa tace sorry Sir dan tasan halin sa baida mutunci ga wani kuka da take jin yana taso mata, amma tana dannewa, gudun kar ta ƙara rikita ƙanwar ta ta,

Ƙara taku ɗaya yayi zuwa inda suke yayi gaf da su, Bineesh da kanta ke ƙasa sai kawai taji anriƙo mata hannu da sauri ta ɗago ta kalle sa a ɗan tsira ce sai kuma ta ƙara maida kallon ta ga kan hannun su da nata ke cikin nasa.

Jikin ta ne yafara kyarma cikin harhaɗa magana ta ce; S.ss.ir.. yana jin ta kira sunan sa, a hankali yace; Shiiiiit, yana faɗin haka kuma yajuya baya tare da jan hannun ta yanda yayi ɗin bata da zaɓi dole ta shiga binsa a baya fuskar ta kuma har yanzu bata bar zubar da hawayen da take yi ba, fita yayi da ita daga cikin gurin...

Suna fita daga gurin Babyn baby ta kuma fashewa da wani kukan tana toshe bakin saboda bata so sautin kukan ga fito, Aunty Babba ce tayi saurin riƙota ta rungume ta tana bubbuga bayan ta.

Tafiya suke amma kawai jefa ƙafarta take dan hankalin ta yafara barin jikin ta, a hanya mutane sai kallon su suke masu gulma nayi saboda mamakin ganin hakan ansan dai Dr.Aveed bashi da mutunci kuma duk a bun da zaiyi maka a gaban mutane zaiyi maka, to me yake faruwa da har ya riƙo hannun ta kuma bisa ga dukkan alamu office ɗin sa yake shirin shiga da ita, saɓanin ko da yaushe shi bai yarda da kowa ya shigar masa office ba, hakannan kuma har maza bare kuma mata da in banda tsana babu a bun da yake nunawa matan makarantar.

Tunanin su kuwa daidai office ɗin sa ya buɗe ya shiga da ita amma sai yabar ƙofar a buɗe saboda duk yana ankare da masu kallon su da suna tahowa kuma yasan babu a bun da mutane bazasu faɗa ba a kan hakan dan wannan a bun sabon a bune a gun sa

Zaunar da ita yayi a kan kujera sannan ya wuce ya je wajen fridge ya ɗauko gorar ruwa ya dawo inda take zaune da take ta faman share hawaye da hannun ta amma hawayen yaƙi tsayawa, jin hannu a kusa da ita yasaka ta ɗagowa a hankali ta sauke rinannun idanunta da suka sauya kala, ganin yana miƙa mata yasa ta miƙa hannun ta a hankali ta karɓa tare da kafa robar a bakin ta bata sauke ba saida ta shanye ta tass sannan ta sauke tana maida ajiyar zuciya tare da lumshe idanun ta na ɗan sakanni sannan ta kuma ware su, yanda tasha ruwan sanyin nan haka taji zuciyar ta ta ɗan yi mata sanyi, daga nan kuma sai ta shiga sauke ajiyar zuciya akai-akai.

Duk abun da take a kan idon sa amma daga nesa kuma dan zaka iya cewa ma ba ita yake kallo ba, sun kai wajen 5 minutes babu wanda yayi magana a cikin su, zaman gurinne ya gundureta, zumbur ta miƙe tsaye kamar wacce aka tsikara haka ta tashi, tana tashi ta nufi hanyar waje, bata kalli inda yake ba bare kuma tayi masa godiya,

"Su waye ku.!?

Tambayar da taji ya jefo mata kenan a loƙacin da take ƙoƙarin fita daga cikin office ɗin, cak taja ta tsaya amma sai ta kasa juyowa saboda koda ta juyo bata amsar tambayar sa bare ta basa dan haka juyowar ta a yanzu bazata amfane sa da komai ba, dan haka bata wani tsaya dogon tunani ba kawai tasa kai ta ƙarasa fita daga ciki.

Bayan ta yabi da kallo tare da jinjina kai, watakon ko godiya baza tai masa ba kuma ya tambaye ta tabawa iska ajiyar sa, jinjina kai ya kuma yi a karo na biyu kafin a hankali ya furta "SU WAYE SU? Me ya sa shiga irin wannan halin me take tunani, can wata zuciyar tace masa to kai ina ruwan ka me yasa kake son sanin SU WAYE SU, kafadun sa ya ɗaga tare da ɗan taɓe baki ya kuma cewa kuma fa hakane ko ma me yasa na jawo ta gashi yanzu ta watsa min ƙasa a ido, shiru yayi yana sakin tsaki sannan ya kuma cewa amma kuma ina san sanin ko "Ko SU WAYE SU. ko ba komai cikin makarantar nan suke dole ingano ko SU WAYE SU a yau ɗin nan, 'To a kan me wata zuciyar ta kuma tambayar sa shiru ya kuma yi loƙaci guda kuma tunanin a bun da ya faru loƙacin da suke kuka su duka da loƙaci da take hawaye tana mmurmushi sai yaji a bun ya kuma dukan zuciyar sa.

*Hmmmmm ya sauke nauyayyen numfashi tare da furzar da iska daga bakin sa, a hankali ya sake ce wa; tausayi, kuka me hakan ke nufi? shi kaɗai sai kunta da warwara yake yakasa tsaida a bun da ya kamata yayi, kira ne ya shigo wayar sa hakan yasa ya katse tunanin da yake yayi saurin ɗaukar wayar duba screen ɗin yayi take annurun dake fuskar sa ya ɗauke cikin tsananin damuwa da ɓacin rai ya ɗaga wayar yana cika yana batsewa..,

"HAMMAD dan Allah kar ka kuma kirana na gaya maka, indai akan wannan harkar ce bazan taɓa amince maka ba, kuma wallahi idan bakayi wasa ba Allah sai nasa an ɗaure ka wallahi wallahi wallahi, wai yaushe ne zaka barni inyi rayuwata cikin salama, daga ɗan abu ƙanƙane kullum sai ka ɗaga min hankali, kasani idan kasa martabar mahaifina ta zube ko wani abun ya taɓa masa jam'iyya to kasni bamu kaɗai zata shafa ba har da ku, matsaya ci kawai wallahi nagaji da kai kuma idan ka kaini ƙarshe wallahi sai na haɗaka da RK idan ina tsoron wani yaji to shi bana tsoron sa nasan zai fahimce ni, dan haka yana kan hanyar sa ta dawowa inbaka rabu dani ba case ɗin zai koma hannun sa wallahi mtsww banza me zuciyar mata sha shasha, marar kishin ɗan uwansa mtsawww.

Yana gama faɗar haka ya kashe wayar gaba ɗaya ma tare da yin jifa da ita yana dukan table ɗin dake gaban sa daga inda yake ya zame ya yayi zaman dirshen ɗago kan da zaiyi yaga ƙofar
End Ads