x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - SU WAYE SU

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 143

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
sa mudai mun barsa a ciki kumma ace an sace shi taya hakan ta faru,

Aunty Babba tace "To meye namu aciki can ta manne musu dasu da wanda yayi kidnapping ɗin nasa, ai gwanda ma da akayi hakan shegen yaro da fata kamar an soya ƙosai,

Sauran ma duk tsaki suka saboda maganar ko a kwalar rigar su hakan bai ɗaga musu hankali ba ko kaɗan bama su sakasa aransu ba bare ya dame su saima hirar su da suka ci gaba dayi hankalin su kwance.....,

Suna shan wata kwana motar Bodyguard na danno kai gaba da gaba sukayi, cikin jin haushi Beenish ta taka burki tana kallon motar da take shirin bugar tasu, rivers ta taka zatayi baya saboda sun gane motar saidai kuma babu inda taje taga wasu motocin a bayan ta,.

Dubawar da zasuyi sukaga ma ashe duk motacinne suka zagaye su kafin daga bisani kuma sai kawai suka fara jin jiniyar ƴansan da,

Tofa ƴar kallo kallo aka shiga tsakanin su, suna tunanin meye mafita gashi basu da damar guduwa saboda an zagaye su ta ko ina....

Ameela ce tace "akwai matsala fa, Beenish tace Allah ya rabamu da ita, yanzu meye mafita,

Barazana tace indai bamaso aka mamu saidai mu bar musu motar nan, inyaso mu fece dan kar mubari suga fuskokin mu ta daman nasan za'a iya kamamu ta motar nan,

Aunty Babba tace wannan ba mafita nace yaza'ayi mubar musu motar nan impossible wallahi kudai yi wani tunanin bamu da loƙaci kar ƴan sandan cen su riske mu bamu da mafita ......

Wai to duk meye nayin kwana kwana muje kawai mu gaya musu gaskiya mana uban me zasuyi mana , Ameela ta faɗa tana niyar buɗe ƙofar, da sauri Beenish tace "Wait Ameela kar ki fita.......

Bodyguard ɗin ne suka fara firfitowa daga tasu motocin, wannan karan hardashi kansa Alhaji Mas'ud Ɗan Ijje shina na agaba, sai ƴan sanda,

Wani ɗan sanda ne yace kana da tabbacin dai motar ce wannan ko,

"Eh wallahi itace kuma muje indai ba mata bane to basu bane amma indai matane to wallahi sune, nidai na manta ko su nawane,

Gurin motar suka tunkara gadan gadan tare da saita bundigin su kan motar su, wasu kuma suka zagaye su.......

_*Ƴan WhatsApp me son group yayi min magana in saka sa dan bazan ringa share ɗin sa tare da link ba saboda bana son mutane su ringayi join batare da karantawa zasu yi ba, gwanda duk wanda yasan karantawa zai yi sai yayi magana ta number ta 08124226526*_

*Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin Su waye su group ku shiga anan zan ringayi kullum, dan gaskiya ba kullum zan ringa posting group group ba sai lkcn da na samu free time.*

Commen and share saboda Allah.

My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 11:28 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 4💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧


Bissmillah.....✍️


"No way...mu miƙa wuya kawai mufita ayita ta ƙare ko mu ko su, cewar Ameela.

Babyn baby tace "Impossible bazai yiyu ba, ba zamu iya dasu ba bindugune fa a hannun su bazamu taɓa tsere musu ba.

"We can...! Mu shirya ba gudu ba ja da baya alƙawari muka ɗaukarwa kanmu dan haka ba zamu taɓa karaya ba a kan kowa kuma a kan komai dan haka kima daina wannan maganar abun da ya kawo zamu ringa tunawa idan muka karaya tun yanzu kuna gannin burin mu zai cika tun ba aje ko ina ba zamuyi asarar zuwan mu garin......ƙwankwasa glass ɗin motar tasu da akayi ne ya dakatar da Beenish maganar da take.....

Hannun ta ta miƙa tsakiyar su alamun wanda ke tare da ita ya ɗora nasa, Ameela dake gefen ta itace ta fara ɗora nata akai cike da ƙwarin gwiwar da ta kumaji yazo mata.

Tana ɗorawa Barazana ma ta ɗora nata sai Babyn baby sannan Aunty Babba, suna ɗorawa cikin haɗa baki sunka ce "Ba gudu ba ja da baya sai inda ƙarfin mu ya ƙare koda hakan zai zama komawar ga Allah.....

Ƙara buga ƙofar akai hakan yasa suka damƙe hannunwan su tare da sakin su,

Suna sakin hannuwansu Ameela ta jawo wata jaka tare da zuge zif ɗin hijabai ne aciki masu niƙab ƙananu irin waɗanda suka saka jiya, miƙawa kowa tayi cikin sauri duk suka sassaka tare da ɗaurewa sai turarukan me yaji (spray) wanda duk inda zasu da shirin su suka tafe saboda irin haka har takalma aciki sau ciki (cover shoe) duk cure na ƙafar tasu sukayi musamman Zee da ta saka me tsini tuni ta cire sa, me makon ta ajiye sa sai tasa mayafi ta saƙalo sa, Aunty babbace ta karɓi ɗayan itama tayi yanda tayi da nata mayafin, duk wannan shirin da sukayi sunyi sa a ɗan ƙanƙanin loƙaci cikin sauri,

AER YOU READY..!?? Beenish ta tambaye su,

YAP... suka bata amsa,

Zare lock ɗin motar tayi tare, su suna kallon na wajen saboda motar tinted ce (me baƙin glass) shiyasa babu wanda yake ganin su bare yasan me suke yi....,

Go....!!!!

A tare suka buɗe murafen motar da ƙarfi hakan kwa yasa suka buge mutanen da suke wajen ƙofofin su, daga ciki kuma harda ƴan sanda, suna turo ƙofar kowacce ta zuro nata ƙafafun cikin sauri suka fito atare babu wata wata kawai duk da wanda yayo kansu suke fesheshi da turare Zee da Aunty Babba kam takalman nan suke ƙwalawa duk wanda sukayi karo dashi, daga ƙarshe ma Aunty Babba jifa tayi da takalmin tare da dunƙulle hannun wanta tana tala ƙafa alamun idan mutum ya cika shegene to ya matso kusa da ita.....,

Cikin ɓacin rai wani ɗan sanda yayo kan Aunty Babba tana ganin ya tunkaro ta itama tayi kansa cikin sauri tana zuwa takai masa wani kykkyawan naushi akan idon sa, tuni yayi baya yana dafe idon sa bugun da tayi masa wataƙil ma idon ya daina aiki,

Yau ƴan sanda sunga ta kansu gashi duk wannan kurin da nuna bunduga ashe babu bullet acikin su, bare su harbe su, nan guri ya kacame kowa na ƙoƙarin ganin sunci nasara akan su,

Ina ƴan matan nan kamar ƙara ingiza su ake gaba ɗaya sun burkice musu babu wacce tayi sanya ta bari wani ya raɓe ta idon su ya rufe kawai duka suke kaimu su ta ko ina, daman kuma ba wani yawane da su ba, daga Bodyguard ɗinnan sai ƴan sanda guda shida, kuma Bodyguard ɗin da suka ga haka duk hanyar ɓuya suka fara nema, dan basu manta da abun da sukayi musu ba shiyasa suka fara jin tsoron su suka fara ja da baya...,

Alhaji ɗan Ijje kam tun farkon fitowar su wani ɗan sanda yace ya shige mota su zasuji da komai, dan haka duk wannan fafatawar da suke yana ciki yana kallon ikon Allah so yake yaga iya gudun ruwan ƴan mata, ya yabawa ƙwazan su matuƙa amma hakan bazai hanashi ya hukun tasu ba, murmushi ya saki tare da jawo gaban motar sa saiga wata ƙaramar bindiga hannu yasa ya ɗauko ta tare da buɗeta babu komai a cikin harsashin cikin ta sun ƙare,

Saman motar ya kuma jawo abu saiga alburuse da yawa ɗiban yayi ya irgi guda goma ya sakasu a cikin bundugar sannan ya ɗaga rigar sa ya zurata, inda ya ɗauko bindigar ya kuma ɗauko wuƙa itama ya ɗaga riga ya zurata itama tare da ɗaukar face mask ya rufe fuskar sa, harda saka safar hannu sannan ya buɗe motar ta ɗayan barin sannan ya fita daga ciki babu wanda yasan da fitar sa daga cikin motar, kuma babu wanda ya ankara dashi har yayi nesa dasu gefen wani dogon gini dake kusa da gurin ya tsaya ta yanda babu wanda zai gansa amma shi yana kallon kowa saboda ba wani nisa ne ba sosai kawai dai su hankalin su baya gurin shiyasa baza su gansa ba,

Ɗaga rigar yayi ya zaro Gun ɗin tare da saita su, jira yake kawai ya tsayar da ita akan ɗaya saboda baya so ya samu ɗaya daga cikin ƴan sandan,

A dai-dai saitin Beenish ya saita ta saboda yaga kamar tafisu iyawa gwanda ya fara kawar da ita, bai saki bindigar ba sakamakon ƙarar jinyi da yaji hakanne yasashi ɗan dakatawa...

Suna cikin haka saiga wata motar ƴan sandannan ta ƙaraso gurin tun kan ta tsaya mutane suka fara firfitowa da tsallen su a ƙalla zasu kai wajen mutum ashirin koma fi,

Yanzu kam sun ɗan tsorata da ganin kallon kallo suka farayi a tsakanin su ko wacce tana tunanin me kuma zai faru dan turarukan ma da suke amfani dasu duk sun ƙarar dasu kuma sunyi nasara akan su dan gaba ɗaya ƴan sandan babu wanda yake iya buɗe idon sa,

Ganin dai da gaske sun tunkaro su yasa suka haɗe guri ɗaya suna tare da niyar su gudu sai kawai sukaji tushhhh an saki harbin bindiga kallon junan su suka shigayi ganin babu wanda aka harba,

Cikin ɗaga murya wani ɗan sanda yace "kada wacce ta ƙara ɗaga ƙafarta daga nan idan kuma kukayi ƙoƙarin barin wajen nan to zaku rasa rayukan ku, nagaya muku kada wacce ta ƙara motsawa U are under arrest, hand's Up...!!! yayi maganar yana ƙara harbin ƙasa....

Yau de ta ƙare musu dan babu wacce cikin ta be ɗuru ruwa ba, tsayawa sukayi cak tare da ɗaga hannun su sama, suka sunkuyar da kai dan sun gama saduda sun miƙa wuya basu da mafita da tafi wannan, gashi gabasu sai faɗuwa yake da tsoron hukuncin da za'ayi musu dan sunsan ko ba'a kashesu ba sai sun shiga gidan yari kodan abun da sukayiwa ƴan sanda nasu hukuncin ma kaɗai da banne bare kuma a haɗa da wance binciken yaron akansu, dan haka komai ma za'a iya yi musu muddun aka kamasu,

Gaba ɗaya ƴan sandan suka zagaye ta ko ina yanda babu damar guduwa me bindiga a hannun sane ya zagayo gaban, yana tsayawa zai fara yi musu magana kenan, Alhaji ɗan Ijje ya fito daga gurin sa yana cewa "Wait.....

Gurin yaƙaraso shima ta gabansu saida ya gama ƙare musu kallo sannan tundaga sama har ƙasa, shi abunma da yazo ransa da ban tunda ya tsaya ya kafe ƙirjin Beenish da kallo aransa yana ayyana abubuwa da dama da kalmar irin wulaƙan tasun da zai yi idan sukazo hannun sa,

"Ku buɗe fuskokin ku, ina son sanin ko su waye ku, Kafin ku karɓi hukuncin ku,

Daga cikin su babu wacce tayi yunƙurin buɗewa, dan tunanin su ɗaya ta yanda zasu gudu su bar wajen,


"Uhmhum uhmhum.... Ɗaya daga cikin tayi gyaran murya hakan kuma da tayi duk sun gane me take nufi, atare suka tsugunna ƙasa suna niyar bi ta gefe gefen su su guda amma ina tuni sauran ƴan sandan sukayi kansu tare da ruƙosu babu wacce ba a riƙe ba acikin su, hakan kuma da sukayi ba ƙaramin fusata shugaban su yayi ba badan an hanasu harbi ba a irin wannan wajen da babu abun da zai hanasa ya harbe,

Alhaji Ɗan Ijje kam cikin tsantsar ɓacin rai da gajiya rainin hankalin yaran ya zaro bindigar sa ya shiga saita ɗagawa yayi zai harbe su baikai ga sakin ta ba,

Loƙaci ɗaya kawai sukaji ƙarar tiya gas kan kace me tuni gurin ya kauraye da hayaƙi babu abun da kake gani basu,

Hakan kuwa yabawa su damar kaiwa duk wanda ya riƙe su duka suka shiga ƙwace kansu, a haka acikin hayaƙin suka ƙwaci kansu tare da nufar motarsu, Saida suka tabbatar da kowa ya shiga sukaja motar su suka bar wajen,

Sunkai wajen 10 minutes agun hayaƙin nan bai bajeba saboda sakar musu shi aka ringayi, duk tsugunnawa sukayi suka rurrufe idanun su saboda yajin sa, kar ya shigar musu ido,

A hankali hayaƙin yafara bajewa har yagama bajewa gaba ɗaya suna buɗe idon su sukaga wayam babu ƴan matan,

Da sauri Alhaji Ɗan ijje ya miƙe yana rarraba ido cikin matsanancin tashin hankali yace "Ina suke....?Ina suke...?Ina suke....? yana maganar yana tsatstsare su da ido sai faman jujjuya kai yake yana tambayar su yana kallon gefe da gefe kamar zai hango su a wani wajen,

Ƴallaɓai dan Allah ka kwantar da hankalin ka zamu nemo su duk ma inda suka shiga a faɗin garinnan,

Caƙumo wuyan sa yayi yace me yasa ka barsu suka tafi me yasa? me yasa? Eh ina magana kana cewa a kwantar da hankali bazan kwantar da hankalin ba ku ne momin su meye amfanin ku waye kawo mana abun? Sai surutai yake gaba ɗaya yagama fita daga hayyacin sa,

Sakin ɗan sandan yayi yana futar da iskar baki me zafi tare da kama ƙugu yana jin jina kai yana ciccije baki, saboda abun yana ƙara ci masa rai,

Haƙuri suka shiga bashi suna so su kwantar masa da hankali amma hakan ya gagara ya burkice musu sai surutai yake musu, da zuba musu sharaɗai kala kala akan anemoma sa ɗansa a yau sannan akamo masa yaran nan,

Da ƙyar dai suka samu ya bar wajen ya tafi wajen motar sa yana ƙara zazzaga masifa da zage zage da faɗar banzayen kalamai akan su, harda su furta sai ya kashe su gaba ɗayan su inda ya haɗu da su,

Yana shiga ya finciki motar da mahaukacin gudun shikaɗai yasan yanda zuciyar sa take tafarfasa, saboda ba ƙin cikin dake cinsa, ya daɗe baiyi irin wannan ɓacin ranba, amma wasu banzaye sunzo sun haddasa masa shi a rana ɗaya kuma abun taƙaicin ma mata ne sukeyi masa wannan rainin hankalin,

Ƴan sanda de babu wanda ya ƙara tanka masa, bayan tafiyar sa suma suka haɗa ina su ina su suka bar wajen da tunanin kuma ta inda zasu fara binciken nan da yake shirin burkita musu ƙwaƙwalwa...

***********************

Sosai suke kwarara gudu kamar zasu tashi sama basu tsaya ko ina ba, saida suka gansu a cikin gidan su, sannan suka tsaya, a galabaice suka fito daga motar gaba ɗayan su kowa ya gaji, sai maida numfashi suke....,

Ciki suka shige suna shiga falo duk suka zube akan kujeru wasu kuma suka zauna akan capet, har yanzu babu wacce tayi magana shiru sukayi kowa na harhaɗo nutsuwar sa,

Kawai ji sukayi Babyn baby ta kwashe da dariya, duk kallon ta sukayi suna jiran jin me zatace, amma har yanzu bata dena ba...

Barazana ce tace "ƙawa meye ya faru me kika tuna haka,

Cikin dariyar da har yanzu takasa yin shiru tace "hhhh wallahi kawai hasko mu nayi ɗazu, loƙacin da muka ɗaga hannun mu, hhhhhh kunji yanda cikin Ameela yanda ya ringa ƙugi na tsoro harda tusa tasaki ina jin da anci gaba da zama sai ta saki gudawa.. wallahi saura kaɗan dariya ta ƙwace min ɗa zunnan wallahi... Ta ƙarasa maganar tana cigaba da yi mata dariya, suma sauran na taya ta,

"Kai kai Babyn baby kiji tsoron Allah ki tuna zaki mutu yaushe kika cikin na yayi ƙara da ƙarya.....

"To tusar fa ki rantse bakiyi ba,

Harara ta watsa mata itama tana dariyar tace "Ke yo ba dole inyi tusa ba ai ko kashi ne yazo min yinsa zanyi bundiga wasa ce, wallahi har ga Allah na gama tsorata da harbin nan da yayi nayi zaton ma ni aka harba da naji ƙarsr farko saida na buɗe ido na ganni aduniya, sai nayi zaton ko wata aka samu ai yau wallahi sun hargitsa min ciki....

Zee fashion ta kaɓeta da cewa "Wai kai mutanan nan fa yau sunyi mana bura'uba aini tuni nafara karanto kalmar shahada ai nazata kuma nidaku saidai muhaɗu a lahira idan da rabon haɗuwar mu, ai ba ke kaɗai ba nima nan nakusa sakin fitsari agunnan ammafa ni zagaye mun da sukayi naga bamu da fita idan suka kamamu tun yanzu ai munkaɗai har ganyen mu wallahi, kema fa Babyn baby da na riƙe hannun ki naji yana kerma,

Beenish tace"Hmm in ana sallah ba'a magana Allah ya kyauta dai amma akwai ƙurafa tunda muka haɗu da wannan ɗan iskan yaron sai munyi da gaske muncanza taku tukunna,

Aunty Babba tace "Ƙwarai kuwa dan bisa ga dukkan alamu wannan mutumin mahaifin yaronne, kuma ina kallon sa nasan shegen kansane bazaiyi mutunci ba,

""kai wai ku duk ba wannan ba kunma manta taya akai wannan tiya gas ɗin yazo waye ya turo mana shi, badan shi ba da tuni yanzu muna bayan kanta ko cikin Sele, cewar Babyn baby.

"Kinga zancen da nake taso inyi nima, ai gaskiya koma waye ba ƙaramin taimakon yayi ba, amma dai kamata yayi musan waye kar muje wani na bibiyar mu bayan barin mu daga unguwar cen, cewar Beenish,

"Haba dai gaskiya bana tunanin haka wataƙil dai kawai Allah ne ya aiko mana shi dan ya taimake mu.......

Sun daɗe suna tattaunawa akan lamarin kowa na faɗar tasa maganar kafin daga bisani suka tashi daga gurin suka koma ɗaki tare da fara canjin takun da zasu kumayi, gashi indai suna so kar a kuma kamasu saidai su daina fita da motar su inkwa ba hakaba dole a ringa kamasu ta hanyar ta, har yanzu dai basu gama tsaida magana ba ɗaya ba,......

Bayan sallar magriba suka ƙara taruwa a falon tare da kunna TV, amma yawancin suma hankalin su yana kan wayoyin su,

"Kan bala'i munshiga uku jama'a zuwanmu garinanna kuwa alkhari ne anƙara kidnapping ɗin ɗan gidan minista, kuma mu ake zargi....

Tsalle Babyn baby tayi ta koma kusa Ameela dake basu labarin, wayar ta fusge itama tana ƙara karantawa.

Wallahi kuwa, amma anraina mana hankali mu da bamusan shi bama taya zamu sacesa ko wancen ɗin ma shi yajawa kansa kuma munsake sa,

Beenish ce tace "Kunsan me tunanina yabani kuwa?

Har suna haɗa baki wajen cewa "A'a sai kin faɗa, suna maida hankalin su gare ta,

Miƙewa tsaye tayi tana jinjina kai sannan tace "ina tunanin duk yanda akai wanime yake aikata hakan kuma yana so ya ringa amfani damu yana yin nasa aikin kuma shine ya taimake mu da tiya gas ɗinnan yasan damu duk yanda akai tambayar itace "Waye shi ko wace ita? amma sanin hakan abune me wahala agare mu, duk da dole ne mugano hakan in ba hakaba bazamu taɓa iya zaman garin nan ba cikin kwanciyar hankali bare har mucika burukan mu, kuna ganin jiya da yau duk bamu samu damar zuwa makaranta ba, me zai faru idan yaci gaba da yin hakan mukuma muna fita ana tsananta bincike akan mu, indan mun kuɓuta wataran wataran bazamu kuɓuta tunda ƴaƴan masu kuɗi hakama dole agano
End Ads