x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - SU WAYE SU

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 150

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
hayyacin su, a kusan tare suka ƙara maimaita SIR SURAJ..!suka faɗi sunan sa cike da al'ajabi,

Ai basu tsaya ƙara jin komai ba daga haka, a kusan tare suka ɗau hanya saboda daman sun san inda yake, yarinyar kuka ta saka musu tana roƙonsu dan Allah kar suje amma idan ƙasa tana magana suma zasuyi mata magana, saboda ba wanda yake jin me take cewa, a haka tai ta binsu tana roƙon su, amma babu wanda ya tsaya bare ya saurare ta,

Inda suka san yana ciki suka shiga daman su Beenish shine zai musu lecture yanzu har garin sauri suka haɗu da yarinyar dan haka yanzu already ya riga da ya shiga, ko sallama babu suka shiga kansu tsaye, yarinyar ganin shi yasa tayi saurin juyawa baya, zata gudu, Barazana ta cafko ta, tare da dawo da ita baya,

Beenish ce ta fara shiga da farko baisan da shigowar su ba, saida yaga Beenish a gaban sa, cikin shouting yace mata "How dare you? Get out of here.!! cikin ɓacin rai da masifar sa da ya saba yiwa duk wanda yayi ƙoƙarin shigowa bayan ya shigo, bare kuma har ka shigo masa kai tsaye without his permission zakaga yanda zaiyi disgracing ɗin ka a gaban mutane,

"Stop shouting at her!

Juyowa yayi ya kalli Babyn baby da tayi masa magana cikin ɗaga murya itama, bai gama fita daga mamakin taba, saida yaga sun haɗu su dukan su a gaban sa, suna jefa masa wani irin mugun kallo me cike da tsantsar tsana, zaro ido yayi tare da jin wata mahaukaciyar bugawar zuciyar sa, ba komai ya haddasa masa jin hakan ba, sai inda idanun sa suka sauka akan yarinyar dake tsakiyar su, ba ƙarya bai taɓa jin faɗuwar gaba irin na yau ba, ya tsorata sosai dan ko na agaya masa ba yasan asirin sa ne zai tonu, rasa inda zaisa ransa yayi duk da bai bari tsoron yayi tasiri akan fuskar sa ba, yana dai danƙare a zuciyar sa fal, amma a fuska baza ka gane hakan ba saboda mazewar da yayi,

"Meye haɗin ka da wannan yarinyar?

Jin tambayar yayi bazata dan bai kawo haka ba, baisan kuma mai zai ce musu ba,

"Get out of here I said, don't let me repeat it again, ya faɗa yana nuna musu hanya da yatsan sa,

Ameela ce ta tako zuwa gaban sa daf da shi, tana masa kallon up and down, ta haɗe hannayen ta a ƙirjin ta tana binsa da kallo, a hankali tace; "If not? what u will do? Eh why not ka ɗauke mu ka fitar damu tunda sana'ar kace, ɗaukan ƴan mata ba komai bane agun ka, kai da kake nema ta ƙarfi da yaji, to ga banza ta samu gamu nan mu biyar ras ka zaɓi wacce tayi maka, idan kuma duka zaka haɗa ba matsala bazan ga laifin ka, tunda kai bunsuru ne, nasan uwarka ma ba ɗaga mata zakai ba bare kuma dan ya da ƙanwa sun kasance guri ɗaya kowacce ma binta zakayi....

Beenish ce tayi saurin karɓar ta da cewa; "Bunsuru ai ba ruwansa da tantancewa indai har yabi uwar sa da ƴar cikin sa wace ma bazai bi ba, nan da za'a haɗa masa mu gaba ɗaya munyi masa kaɗan.

Runtse idon sa yayi jin munanan maganganun da suke faɗa suna dangan tasa da ɗan akuya,

Beenish ce ta jawo hannun yarinyar ta matso da ita gaban sa, jikin ta sai kyarma yake ji take kamar zai kuma kamata da kokawa a gaban su,

Wani irin mugun tsanar yarinyar ce ta kamasa dan gani yake duk ita taja masa wannan abun, zuciya ce ta ɗebe sa kawai ya kwashe yarinya da mari, kafin ya ɗauke hannun sa Beenish ta kwashe shi da nata, tana ɗaukewa Ameela ta taro sa da nata ta ɗayan ɓarin, marika huɗu suka sauke masa idan wannan ya mare sa ta ɓarin dama sai wannan yayi masa ta ɓarin hagu, kan kace me fuskar sa tayi shatin sahun hannun su abunka da farar fata,hular kansa har saida ta faɗi ƙasa santalelen kansa da yasha ƙwalƙwal yana sheƙi,

Gaba ɗaya gurin miƙewa sukayi masu ɗaukar hoto nayi masu ɗaukar video nayi, wasu kuma suna tafawa suna yi musu sawa, wasu kuma abun bai musu daɗin kalla ba saboda basu san me ya aikata ba,

Kunaya ce ta kamasa yana kasa ɗagowa baisan wane irin mataki zai ɗauka akan su ba, dan tunda yazo dunayi babu wanda ya taɓa ci masa zarafi da mutunci irin na yau,

"Beenish ce ta sa hannu ta ɗago da fuskar sa, tace; "Dan Allah kar ka fasa abun da kakeyi ka ciga ba, kuma kar ka barta da rai daga yau kar ka bari ta kuma kwana ɗaya a duniyar nan, wallahi sai mun saka dangin ka gaba ɗaya cikin hatsari sai kayi na damar zuwan ka duniya, kuma daga yanzu babu kai babu a cikin makarantar ka rubuta ka ajiye ka gama aiki a duk wata jami'a tunda kai burin ka ka tozarta wani to wallahi kai zaka tozar bazamu taɓa ƙyale duk wani macuci dake zalintar mutane sai inda ƙarfin mu ya ƙare, wawa wanda baisan ciwon kansa ba, kalle ka kamar mutumin kirki nan kwa jahilci ne ke ɗawainiya dakai, kana tunanin duk abun da kayi kasha banza,

Wata mahaukaciyar dariya ya saki kai bakace shine ya shiga wani yanayi ba yanzu, zagaye su ya fara yi yana cewa; kunyi babban kuskure jakar ƙwaƙwalwar ku ta tsara muku shirme, su waye ku da har kuka isa kusa inrasa aiki na, kunsan hukuncin da akeyiwa duk wanda yayiwa lectura rashin kunya ma bare har yasaka hannu ya dake sa, a yau zaku bar makarantar kun tafka babban kuskure a rayuwar ku da bazaku taɓa wanke kanku ba, sai nasa kunyi asarar duka shekarun da kukayi kuna karatu, kuma babu wata makaranta da zakuji kuyi karatu a ƙasar nan. ya ƙarasa maganar yana ƙara kwashe musu da dariyar mugun ta,

Mtsawww, Beenish ta saki wani dogon tsaki tana hararar sa, sannan ta juya ta kalli Aunty Babba, "Aunty Babba fitar mana dashi daga cikin gurin nan, dan bazan juri jin wannan banzar muryar tasa, yazo yana mana haushi a kunne, dan gwanda naji haushin asalin karen da naji ta jakin kare...

Dariyar da yake ce ta ɓace ɓat ta koma baƙin ciki fuskar nan tasa tayi murtuƙ kamar kunun kanwa ya kwana.

'Daman Aunty Babba ƙiris ake jira, nan taja babbar malin malin ɗin ta naɗe sa tare da hannayen sa, tayi masa riƙon maza (itafa indai ƙarfi ne idan kazo gurin Aunty Babba har da na siyarwa da akwai😂) dan saida yayi ƙoƙarin ƙwacewa amma sai yaji ƙam ta riƙesa, cicciɓar sa tayi tayi waje dashi me makon ta sake sa da taga wajen ba mutane sai kawai tasa ƙafa ta harbasa gaba, ya faɗi a gun, ko ta kansa bata bi ba ta koma ciki abun ta,

'Barazana ce ta kalli ƴan wajen cikin ɗaga murya tace wayoyin ku ƙasa kada wanda ya kuma ɗaukar wani abu anan,

Da sauri kuwa duk suka sauke wayoyin su,

"Beenish ce ta juya ta kalle su itama, cikin sanyin murya tace; "Nasan ba kowa bane ya gane me ke faruwa to zanyi muku bayani dalla dalla yanda kowa zai fahimta, kuna ganin wannan baiwar Allahr ta nuna musu yarinyar, sannan ta ɗora da basu labarin abun tundaga farko har ƙarshe, sannan tace muna buƙatar haɗin kanku domin wata ɓarnar ba a kashe ta saida wata ɓarnan, a cikin ku tsakanin ku da Allah wacce macen ce ta taɓa fuskantar haka daga cikin ɗaya daga lecturorin dake cikin makarantar nan kada wacce taji tsoro ku faɗa, ina so mu kawo ƙarshen wannan abun koda kuwa zai zama silar rufe wannan makarantar a shirye muke da mutsayawa kowa tare da haɗin kuwa,

Tafi kawai suka saka musu dan sunji daɗin wannan maganar tata, bayan gama tafin su, nan matan suka shiga fitowa abun mamaki saida a kasamu mata wajen goma sha biyar da abun ya faru dasu, waya suka saka da kansu suna yiwa ɗaya bayan ɗaya video suna faɗar abun da ya faru dasu da kuma sunayen lecturas ɗin, wannan tace ai yana yi lalatar da ita wanann tace itama bibbiyar rayuwar ta ake, wata kuma tace wani yayi mata barazanar idan bata yarda ba sai tazo fita zai dawo da ita baya, ko wacce dai da kalar abun da take fuskanta, a ƙala dai saida aka lissafo lecturori wajen guda huɗu da duk halayyar su ce, acikin su saida aka kuma samun wacce Sir Suraj yake yi mata irin yanda yakeyiwa ɗayar.

Bayan sun gama ne suka ce kowa zai iya tafiya, sannan kowa ya zauna cikin shiri zasu iya neman wasu, sannan yanzu zasu ajiye batun sauran malaman, yanzu iya akan Sir Suraj zasuyi,

Bayan fitar kowa daga gurin suka samu guri suma suka zauna, zasuyi tunanin ta inda zasu fara taro masa aiki, su saka a kore sa daga cikin makarantar kafin shi yasa a kore su dole suyi gaggawar yin wani abun.

'Wayar barazana ce tayi ring hakan yasa suka dakata da tattaunawar tasu,

Da sauri ta zaro wayar daga side bag ɗin ta, ganin me kiran yasata saurin amsawa, "tana ɗagawa tayi shiru tana ta sauraron abun da ake ce mata, can kuma sukaji tace; "Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un" Ta faɗa tana shirin faɗuwa da sauri Ameela ta taro ta cike da tashin hankali suka shiga tambayar ta me ya faru, amma takasa basu amsa, sai hawaye kawai da ya fara gangaro mata, suma gaba ɗayan su sun ruɗe ganin ƴar uwar su cikin wannan yanayin,

Cikin kuka tace; "Sun kashe shi wallahi sun kashe shi saida sukaga yabar duniyar hankalin su zai kwanta, cikin garin mu yana cikin tashin hankali, akwai matsala, dole sai naje,

"Su waye su? waye aka kashe, me yake faruwa a garin? Sai tambayar ta suke amma takasa basu amsa sai sunbatu take musu,

Tsayawa tayi da ƙafarta tana maida wayar jaka, tace zan tafi, ku kula da kanku kar ku bari wani abu yasame ku, kar ku bari yayi galaba akan ku, ni zanje akwai wata matsalar acan dole sai naje, tana maganar tana goge hawaye, kuma a hakan so yake ta ƙarfafawa kanta ƙwarin gwiwa, tana gama maganar ta juya zata tafi, Beenish ta tari gaban ta tace;daman akwai abun da zai sameki da har zaki iya tsallakewa ki tafi ke kaɗai batare damu, mu kuma mu zuba miki ido ki tafi ke kaɗai, ba'a taɓa ba kuma baza'a taɓa ba, damuwar ɗaya daga cikin mu damuwar kowannen muce, dan haka tare zamu tafi babu inda zaki ke kaɗai.

Cikin marairaicewa tace "A'a kada kuyi haka idan muka tafi tare wannan matsalar kuma ya zakuyi da ita, akwai matsala idan muka tafi gaba ɗayan mu rayuwar mu zata kuma shiga garari bama mune abun ji ba, ita wannan yarinyar da kuma sauran yaran komai zai iya faruwa damu da su, gwanda ku tsaya kuyi solving ɗin wannan matsala, ni kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin komai bai faru ba koda zan rasa raina, zan taimakawa wasu, dole sai naje,

"Zainab kar ki kuma magana anan gurin ki wuce muje zamuji da komai, nadan halin garin nan, basai kin ban labari ba, dan basu da imani muje kawai, babu abun da zai faru danan har muje mu dawo, cewar Ameela.

Babu yanda Barazana batayi da su ba akan su barta ta tafi ita kaɗai amma sunƙi yarda, dole ta amince su tafi taren......✍️✍️✍️

"Tofa wata sabuwa, ba'a kashe wata matsalar ba ga wata ta ɓullo, yanzu idan suka tafi to ya zasuyi, ga ƙudirin Sir Suraj akansu nasawa a kore su daga makaranta a yau.....
[3/5, 11:47 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 12💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

____Da sauri suka fito daga gurin suka nufi wajen da sukayi parking ɗin motar su, duk wanda yagan su yasan babu kwanciyar hankali a tattare da su, dan gaba ɗaya fuskar su ɗauke take da damuwa,

Har zasu shiga, Beenish tace su ɗan jirata tana zuwa, babu wanda ya tambaye ta me zatayi ko ina zata, haka ta juya tabar wajen, su kuma suka bubbuɗe murfin motar Ameela ce ta shiga driver seat sai Babyn baby ta shiga gefen ta, su kuma ragowar suka shiga baya, bata dawo da wuri dan har saida suka kira wayar ta suna tunanin ina ta shiga?

Can dai bayan wani ɗan loƙaci, sai gata ta dawo gurin da sauri, sai faman zufa take kamar tana sharewa da hannun ta, babu wanda ya tambaye ta inda taje, kawai Ameela ta tayar da motar.

A guje taja motar suka fice daga cikin makarantar, basu tsaya a ko ina ba saida suka zo gida, nan ma da suka shiga gidan babu wani ɓata loƙaci kowa jakar sa ya ɗauka ya zuba kayan da zai buƙata, sannan suka je suka zubasu amota suka kuma ɗaukar hanyar garin su Barazana.., gudu kawai Ameela take shararawa a hanya, yanayin halin da suke ciki yasa basu wata hira me tsayi sai ɗan jefi jefi, Barazana kam ko ƙala batace musu ba, duk da janta da suke sa hira amma takasa sakin jiki, hakan yasa suma jikin su duk ba walwala.

Sunci rabin tafiya, dan sun ma kusan ƙarasawa ga yamma tayi sosai ana daf da kiran sallar magriba, Beenish ta ɗauki wayarta ta dannawa wata number kira ba a jima ba, aka ɗauka, "Ya ake ciki ne, kun gama komai? Shiru tayi tana sauraron abun da akece mata.

"What....!!!" Haydar me kake so kace min ban fahimci maganar kaba, okay turo min maza turo min, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un, ya Allah! Kashhh...! Ta ƙarasa maganar tana dafe goshin ta tare da dafe kanta cikin matsananciyar damuwa.

Dukan su zuba mata ido sukayi suna jiran ƙarin bayani amma tayi shiru, wayar ta kawai ta zubawa ido hawaye na shirin zubowa daga idon ta, tayi saurin mayar dashi,

Barazana dake gefen ta ta karɓi wayar hannun ta, itama mutuwar gaske ce kawai batayi ba ta de yi suman zaune, sai taji damuwar da take ciki kamar ma wannan so take ta fita,

Ameela dake gaba tana tuƙi kawai ta samu gefen hanya tayi parking ɗin motar, tana juyowa cikin tsananin damuwa tace; "Wai Kun barmu a duhu ku gaya mana me yake faru mana,

"A hankali Beenish ta buɗi bakin ta da yayi mata nauyi, dan dan bakin tane ma kawai yake magana amma kamar bata hayyacin ta take maganar,

"She is laying to us gaba ɗaya shiri ne, she is his wife, matar sa ce, Why? Why? Me yasa zasuyi mana haka? Me yasa? meye haɗin su damu waye ya turo su SU WAYE SU..!!!!?? Gaba ɗaya ta rikice har dukan goshin ta take,

Suma cikin tashin hankali da basu taɓa yi ba ganin Beenish cikin wannan halin yasa suma nasu hankalin ba ƙaramin tashi yayi, duk da basu gama fahimtar zancen nata ba gaba ɗaya,

Babyn baby dake baya tuni ta fashe da kuka, tana tambayar ta, "Yaya wai suwa kike magana me yake shirin faruwa kin saka mu a ruɗu ki fahimtar da mu,

Ɗago jajayen idon ta da suka sauya kala tayi tana sauke su akan Babyn baby, da take kuka, karkaɗa kai tayi kawai tana kuma lumshe kyawawan eyes ɗinta tana jingina kanta jikin motar tana sauke ajiyar zuciya da ƙyar, cikin wata iriyar murya tace "tayar da mota muje...

"Cike da ɗan shouting Ameela tace "Beenish wai me yake faruwa yaza'ayi kice muje, baki gaya mana real abun da ya faru ba, meye hakanne??

Duk da haka Beenish batace komai ba, Saida ta ɗan ja loƙaci sannnan ta buɗe idon ta tare da tashi zaune tana kallon Ameela na ƴan sakanni sannan "tace duk bayanin nan da nayi muku baku fahimta ba me yafaru yau?

Duk da haka da kallon rashin fahimta suke binta,

Barazana ce tace; "Batun yarinyar da muka taimaka yau tayi mana ƙarya ne ita ɗin matar sa ce, ku kalli nan, ta miƙa musu wayar nan suka shiga kallon hotunan da aka turowa Beenish, wani sunyi tare tana kansa wani kuma suna kitchen suka ɗauka, harda na bikin su ne event da akayi,

"Ya Allah Ameela tafaɗa jikin ta nayi mata sanyi ji tayi kamar an kunce mata notikan gwaiwar ta,

"Na shiga uku mutane me suka zama meye ƙudurin su, akan mu taya suka iya haɗa wannan abun kamar gaske da kuka da yanda suke tsoron junan su gaba ɗaya, taya hakan zata zama ƙarya shiri, shiri akan mu SU WAYE SU to waye ya basu wannan aikin? Babyn baby ta faɗa itama tana dafe kanta dan gaba ɗayan su abun ya mugun ɗaure musu kai har sun rasa wane kalar tunani zasuyi akai.

"You see, koma me ya faru mu muka jawa kaina saida na gaya muku gaskiya amma kuka ƙi fahimta yanzu gashi zata jefa mu cikin matsala, daga taimakon ta, wallahi mutane yanzu basa tsoron Allah kowa abun gudu ne, ɗan haƙƙin da ka raina shi yake tsokane maka ido, yanzu da wacce hujjar zamu kare kanmu akan wanann lamarin?

Duk shiru sukayi mata babu wanda yabata amsa duk da maganar a kwai ƙanshin gaskiya
End Ads