x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 58 - SU WAYE SU

  • 171001 words
  • 174000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 188

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ta ce gaskiya maganar kubai kamata ba tunda dai har basu cutar daku ba to baku san me yake faruwa dasu ba kuma baku san dalilin da yasa sukai hakan ba nima dai ina goyon bayan ka wannan bai kamata ba gaskiya ace an watsar musu da komai, koma meye tunda har suka bukata toh zunubi yana kansu in ma wata mugun abun suke shiryawa Allah ya fisu Allah yana kallon su tunda dai ku sun gama muku komai sun fito da ku ba tare da sun cutar da kowa ba to kawai kuyi musu haka, yanzu abinda zamu yi shine tunda wuri kar yamma tayi muje kawai a nemi inda yiwuwar siyan gidan to in ma ba zai siyu ba ina ganin kawai mu tafi da su insha Allahu babu abinda zai faru har lokacin da zasu nema ko da daya daga cikin ku ne sai wani ya tafi dasu gida, ko kuma a nemi wani wajen a can a adana musu.

Jin abun tace ya sa su Salama yin shiru suna tunanin maganganun su,

Cike da gamsuwa zai da girgiza kai shima hakan yake so ganin ta goya mishi baya yace gaskiya wannan maganar gaskiya ce dan nima gaskiya matar da ta dauke mu bata nuna alamar cutar damu ko kidnapping din mu ta yi ba kawai dai ban ma dai san wani irin tunani zanyi a kanta bane shi yasa amma idan muka je da su duk daren dadewa koma menene zai fito daga baya, ni na ma yadda zan tafi da abubuwan gidan mu.

Tunda Zaid yace haka suka yi shiru, tunda ba gidansu za'a kai ba shiyasa babu wanda ya kara magana a cikinsu,

faheema ca ta fara mikewa ta ce toh hakan ma yayi yanzu kunga gashi nan karfe biyu na rana har ta kusa ya kamata mu hanzarta muyi abin da zamuyi ko, kar lokaci ya qurai mana tunda dai nan bamu san ma wani gari bane ba ne.

Zaid ma miƙewa yayi tare da cewa "nima dai abinda na gani kenan kawai mun kwana a garin ma fa kawai dai muje mu tambaya, sai a dora mi a hanya, Allah ya sa ma dai babu nisa da nan da inda zamu je,

Duk miƙewa suka shiga yi shi dai zan bai ci musu kara ba don bashi da wani magana a kan su, da a basu da azubar shi babu abinda ya dame shi da su, shi dai kawai ya ganshi a gida shine burin shi.

Fateema ce tayi saurin dakata da su da cewa "amma wani hanzari ba gudu ba, kamata yayi yanzu mu fara buɗewa a san kudin da za a diba sannan a san abu mai mahimmancin da ya kamata a dauka, idain jakunkunan ma za su cinye a rage wasu a barsu saboda tsaro ba don tsoro ba, saboda da in aka ga kowa da jaka irin wannan gashin ku ba in makaranta ba dole wani zai iya zargin wani abun a ganmu da jaka niki niki kowa da jaka a baya,

Nan suka yi na'am da shawarar da ta kawo musu budewa suka hawwi sai dai kudaden daban sai kuma wasu da an ku kulle su sai takaddu haka dai abubuwa tarkace su dai ba komai suka fahimta ba hakan yasa suka san yanda zasuyi suka rage jaka guda daya suka ajiye ta agun ɗata suka saka kuɗaɗen da zasuyi amfani da dasu dan kuɗine bana wasa ba har basu san ma me zasuyi da su ba, uku kuma suka bar ta da kayayyakin a ciki.

Nan suka dauki hanya zuwa cikin kauyen suna zuwa suka fara tambayar nan dan Allah wa ne gari ne nan ake gaya musu suna cikin katsina ne sai suka kuma tambaya dan Allah ina zasu samu motar da za ta kai su kano, wani babban mutum ne yace musu sai dai su hau mashina daga nan sai a kaisu can tasha in yaso a nan zasu samu motar da zata kai su har cikin garin kano,

Ba tare da bata lokaci ba suka hau mashinan da zai kai su tasha, kowa mashin ɗaya ya hau sannan aka dau hanyar tashar dasu, sai da aka yi tafiya sosai sannan suka karaso bakin titin dake kusa da tashar garin, sai dai kuma suna isa bakin tashar aka ce motar da zata tafi kano ta cika sai dai sujira ta karfe hudu, nan suka zauna suna cigaba da tattaunawa, anan gurin ma dai sai da suka yi musu wanda zai tafi da fateema kowa na shi zai zafe da ita kowa na shi zai tafi da ita suna tambayar ta wa za ta bi ita dai kawai dariya take musu har yanzu bata dauki ko daya daga cikinsu ba saboda wallahi ta kasa bata san ya zatayi ba sai dai su sasanta a tsakanin su wani ya hakura dan ita ko'ina ma zata iya zama....


$$$$$$$$$$$$$$

*BARACK*

Saida Beenish tayi sati guda a part ɗin Moohad, sosai ta warware hannunta ya warke babu inda yake mata ciwo don karayar ma, ta warke, kamar ma ba ta kareye ba babu abinda bata iya yi da kanta sai dai har yanzu Moohad ya hana ta fita ya tsare ta a cikin gidan kullum kuma part dinshi a garkame, sannan duk wani horo da za'a basu yasan tsarin sai yazo ya koya mata itama, daidai yanda zata gane, kafinma wani loƙacin a koyawa ƴan wajen shi ya koya mata, saboda a abun da ake koyawa duk a tsare yake daga wannan sai wannan haka abun yake a rubucen tsarin gurin, wani abun mamaki kuma RK bai ƙara shigowa ba, tun lokacin da yazo yayi mishi magana har kawo kwanakin nan bai kuma waiwayan shi ba, saboda haushin shi yake ji dan ganin yake ma da haɗin bakin sa tabar cikin Barack ɗin.

Ɓangarn RK kuwa zuwa loƙacin tun yana neman ta har ya daina ya watsar da lamarin ta a fili amma aransa indai zai zauna sai yayi tunanin yanda akai ya rasa ta, amma abun da ya barwa kansa shine kawai wani ne ya taimaka mata ta tafi gida, shiyasa ya daina neman ta yaci gaba da harkar gaban sa,

Bangaren su Barazana kam sun kwantar da hankalin su sakamakon kwanan ta daya washegari Moohad ya same su aboye ya sanar dasu abin da ke faruwa tare da cewa sai taji sauki zata fito sun nemi ma da ya barsu suje su ganta amma ya hana su saboda tsaro yasan duk inda sukayi RK yana kallon su, idan ya gansu a part ɗin sa, zai iya gano wani abun shiyasa ya hana su zuwa, sannan kuma ya sanar da su cewa su daina nuna tsoro a kan RK babu ruwansu da shi suyi abin da ya kawo su kawai, idan kuma suka ci gaba da nuna jin tsoro akansa zai musu abin da basa tunani don haka duk wani abu da zai ce su yi to suyi kar sununa gazawar su, indai suna so su zauna lafiya dashi to su jajirce sosai akan abun da yake koya musu, dan shi mutum ne me son ganin mutum ya jajirce akan abu musamman idan shi zai koya maka, sannan kar su ringayi masa shishshigi ko yawan kallon sa, duk abubuwa ne da suke cikin abun da baya so, tun daga nan suka maida hankalin su akan abin da ya kawo su yanzu sosai suka saki jiki duk wani training da za'a koya suna yin shi sosai suke karɓar training.


Kamar ko da yaushe a inda suka saba yin training ɗin, suna gurin yayin da kowannensu riƙe da bindiga 1 by 1 suke saitawa gurin da zasu harba, wani RK da sojan da suke basu horon suna bayan su, duk wanda ya harba sau ɗaya bai harbi cikin tsakiyar layi ba, gefe zai koma, haka suka dinga yi kowa na harbawa amma basa harbawa daidai tsakiyar cycle din da ake so su harba, duk yadda aka so a nuna musu yanda zasu yi amma duk sun kasa sai dai kowa ya harbi gefe, sun gama ƙular da RK dnn ya nuna musu ya nuna musu yanda za su yi amma ina sun kasa har hannun wasu ya riƙe yana saita musu amma daga ya matsa sai su harbi wani gurin daban haka suka dinga yi sun daɗe suna abu ɗaya amma har yanzu babu wanda yayi nasara ya harbi daidai tsakiyar gurin.

Suna cikin yin haka kawai suka ga wani bullet ya taho shuuuuu ta gefen kunnen RK ya wuce bai sauka ko'ina ba sai daidai tsakiyar inda ake so a harba, haka aka dinga harbo bullet ba a daina harbun gurin ba sai da aka harba sau wajen biyar sannan aka daka ta,

Ba RK ba kaɗai gabaki dayan su cike da mamaki, dan a kusan tare duk suka juyo suna duban daga inda bullet ɗin yake fitowa, a wani irin slow RK ya juyar da kanshi yana duban gurin, Beenish fi ya gani da bindiga a hannunta jikinta sanye da kayan sojoji tun daga kafarta ya fara bi da kallo da ke sanya cikin wani arnan takalmi na sojoji, sai wando rigar kuma ba ta sa ta zo zan ba sai ta saka fara rigar sojojin kuma ta daura ta a ƙugunta, sai hannunta cikin wata farar safar hannu,, gashin ta kuma ta daure shi ya ɗan sauko yana lilo, kanta kuma sai ta ɗaura p_cap akai ta dan tura ta gefe kadan yadda za a ga fuskarta sosai, wata irin tafiya ta shiga yi tana wulwula bindigar hannun ta har ta ƙaraso inda yake, sannan tayi wata irin juya bindigar ta totse ta a ƙugun ta, ɗagowa tayi tana kallon sa ido cikin ido ta sakar mishi da wani arnar murmushi tar da daga hannunta ta buga masa wani uban salute da yatsu biyu tana ɗaga masa gira ɗaya sai ta ɗan duƙar da kai batare da ta cire hannun ta daga saitin kanta ba tace "Sir I'm back! Tana faɗar haka ta ɗago tare da ƙamewa tana sakin murmushin gefen baki sannan ta raɓa gefen sa ta wuce gurin su Ameela.....



*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*

_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba, sannan akwai wasu da suka buɗe group irin nawa amma bashi bane, nawa zaku gansa da dpn su waye su ɗin da kuma ɗan rubutu a gefe_
[4/25, 8:28 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)


________* 08124226526*_______


*_episode 50 💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*

_Bismillah..✍️_


Kowa baki sake yake kallon Beenish, tunda loƙacin da suka juyo idon ƙyan akan ta komai tayi a kan idon su, suna binta da kallon mamaki, dan ko motsawa ma wasu basa yi.

RK kam ya kame ya daskare ya manne a tsaye yama kasa motsawa duk wani ruwa dake lungu da saƙon na jikinsa a daidai lokacin nan dai to saida yaɗan dakata, wadna shi kansa bai san dalilin hakan ba dan yama rasa wani kalar irin tunani zaiyi akai, saboda tunanin nashi ma tsayawa na wucin gadi, ya kai wajen minti 3 a tsaye ba tare da ya motsa ba, sannan hankalin shi ya dawo jikin shi a hankali ya juya yana kallon bayanta inda ta tsaya gabansu Barazana.

Beenish na zuwa gabansu Ameela ta kuma faɗaɗa murmushin ta tare da watsa musu harara ganin yanda suka saki baki sun kallon ta kamar yau suka fara ganinta kowa ya kafeta da ido babu mai magana domin ta gama narkar da su agun da mamaki.

Sai da tasa hannu a saitin fuskarsu tana wavin dinsu da hannunta tare da cewa "yade kuke kallo na kamar baku taba ganina ba,

Ameela bata san lokacin da itama tayi saurin dawowa hayyacinta ba, ta ke ta rungume Beenish tana sakin ta sannan ta shiga kallon ta tundaga sama har ƙasa sannan washe baki kawai saita ta ɗaga hannun ta ta hau sara mata dan taji daɗi ganin ta a haka sosai, itama Barazana nan take ta ɗaga hannun tana sara mata tare da sakar mata murmushi, ganin abin da sukai sai ya burge sauran take suma dukansu suka ɗaga hannun su kayi mata salute tare da saukewa suna ƙamewa.

Wani saurayi ne dake jikin su yayi saurin matsowa kusa da ita tare jinjina mata babban yatsan sa,

Daɗi ne ya kama Beenish ta ƙara wage baki da murmushi, itama sai ta sara musu tana dan sunkuyar da kanta ƙasa alamun gaisuwa, gaisawa suka shiga yi tsananin ta da su Ameela da sauran ƴan matan, sai surutu suke suna tambayar ta ina ta shiga like basu san komai ba, sun ma manta a ina suke,

Iya shaƙa RK ya shaƙa da ganin abun da sukayi mata, hakannan yaji ransa yayi mugun ɓaci, cikin ɓacin rai da ɗaga murya yace "Ke!

Gaba ɗayan su saida suka firgita dajin yanda ya kira sunan da ƙarfe cikin tsawa, ita kanta Beenish saida hantar cikin ta ta kaɗa dan daman suna zancenne kawai amma hankalin ta yana kansa, jira take kawai taji hukuncin da zai yanke mata, amma tunawa da abun da ya kawota da kuma wasu maganganun da Moohad ya gaya mata akan halinshi, sai kawai ta maze a fuska bazaka taɓa cewa da ɗigon tsoro ba amma cikin ranta dukan uku uku yake,

Mamakine ya kamasa ganin duk sauran sun nutsu sun maida hankalinsu kansa amma ita ko juyowa batayi ba bayan yasan kuma tasan da ita yake, cikin fusata yayi kanta gadan gadan yana zuwa ya juyo da ita da ƙarfi tare da ɗaga hannun sa zai mare ta saidai yaji caraf ta riƙe hannun sa tare da ɗaga idanun wanta tana sauke su acikin nasa, da bakin ta tayi wani abu yana ɗan fitar da ƙara kaɗan kaɗan kamar dai tsaki tare da rage yanayin kallon ta tana girgiza masa kai, hannun sa da ta riƙe sai ta juya nata ta zura a tafin hannun sa tana shigar da yatsun ta tsakankanin nasa yatsun ta damƙe, sannan ta wani kashe murya tana turo baki ta ce "My hus nagaji da zaman laɗaicinne ni kaɗai, naga kuma kaƙi ka dawo kasan kasabar min da kanka a tsawan satinnan ji nake kamar mun shekara dakai wallahi shiyasa na fito amma kayi haƙuri idan muka gama sai mu koma, ko kuma kazo mu tafi yanzu I need you now my husss.... Ta ƙarasa maganar tare da janta sai kuma ta zaro bindigar dake gefen ƙugun ta ta shiga yi masa yawo da ita akan ƙirjin sa, sannan ta sauya kalar kallon da take masa zuwa kallon tsana a daidai zuciyar sa ta tsayar da bindigar tana ɗage masa gira sannnan tayi ƙasa da murya wanda shi kaɗai ne zai iya jin me tace, tace "inajin yanda na ɗora ta nan badan ina tsoron Allah ba saina harbeka saboda na tsaneka na tsaneka na tsaneka ji nake kamar na kashe ka, tana maganar tana kuma goga masa bindigar a wajen zuciyar sa sannan ta watsa masa banzo kallo me cike da tsana,

Ƙoƙarin cire hannun ta tayi daga nasa amma sai ta ji su gam ya mugun damƙe shi kamar zai karya mata yatsun dan da ya lanƙwasa su babu abun da zai hana su karyewa, ita kaɗai tasan azabar da take ji amma haka ta kuma daurewa ta ƙaƙalo murmushin yaƙe, tare da kuma sakin jikin ta kamar zata faɗa kansa tace "auch ash tana kuma riƙe nasa kamar irin bata jin zafi nan sai tace Husss muje ciki dan Allah nagaya maka I need u then I know u too.

Kawai kafeta yayi da ido dan tagama kaishi ƙarshe har ya rasa ma wane irin ɗanyen hukunci zaiyi mata dan gani yake duk abunma da zai mata yayi kaɗan, sako sako yayi da riƙon hannun nata yana zare ya tsunsa daga tsakankanin nata, ta ɗauka sakin ta zai yi sai kawai ta ji ya ce
End Ads