"Kedai ki faɗan kawai sauri idan kin dawo zan baki labari.
"Okay, sunana zaka rubuta, amma da Capital letter A ɗin ƙarshe kuma da small letter kuma A ɗin guda biyu zaka saka....
Da sauri ya kashe wayar yana ƙoƙarin sakawa wayar ta faɗi a ƙasa, da sauri ya ɗauka yana ɗauka yajiyo muryar ta tana cewe" saude baki ganshi bane har yanzu? Daga can ɗin dai akace gashi nan naganshi.
Karkarwa kawai hannun sa yake, cikin sauri ya fara saka password ɗin saidai kuma yana buɗuwa yaji an fara buɗe ƙofar da ɗan muƙulli babu yanda ya iya gashi ya buɗe ɗin amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa baiga fuskar komai ba yayi saurin fita ya share komai na wayar ya cilla ta inda ta ajiye ta kan kujera, shi kuma ya samu wata ya kwanta ya kifa kansa yana ta faman sauke ajiyar zuciya, zuciyar sa sai dukan tara tara take amma saboda tsoron kar ta gane yanayin da yake ciki har ɗauke numfashi sa yake, yana ƙara arowa kansa jarumta cikin dauriya.
Da sauri ta turo ƙofar tana shigowa ta gansa kwance, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da cewa; "au ashe bacci kake, banda abun Khalid ai da sai kabar falon a buɗe, yanzu da baƙi nayi ma haka zanta faman bugu baka ɗauka ba?
Sai magana take ita kaɗai, shi kam yana jin ta, wayar ta ɗauka kawai ta fita daga falon.
Tana fita ya tashi da sauri yana sauke ajiyar zuciya harda dafe ƙirjin sa... yana sake jin daɗi da bata gane ba, amma kuma yaso ganin hotunan yade gansu da yawa kuma kamar ma ba iya hotunan mutane ne ba a cikin folder.... gaba sa ne ya ƙara faɗuwa loƙacin da ga tuna abun da ya karanta yanzu tana gida na, tunanin yanda zai lalubo matar yake ta ina zai tunkari gurin batare da kowa ya ganshi ba, dan yana matuƙar tsoron a kamasa....
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*GHAMBURJ*
*HAJJA MAMA*
Har sun shigo tsakiyar falon gida wani ɗaki dake kusa da na su Bilal ta kai Faheema, shi kuma Sergeant major of the Army guda duk girman aikin sa de sai yaci sa'a ba a kaishi ɗakin sauran ba wani ɗaki aka kaisa na daban aka ajiye sa shima da gado a ciki, duk kwantar da su tasa akayi saboda har yanzu basu dawo cikin hayyacin su ba, bacci suke tayi abun su,
Rataya jakunkunan tayi guda biyu a bayan ta ɗayar kuma ta ɗauka a hannu wannan ɗakin kayan ta'addancin nata ta kaisu, zubar dasu tayi a ƙasa tare da zama a ƙasa tana sauke numfashi saboda jakunkunan da nauyi, saida ta ɗan huta sannan daga zaunan da take ta jawo jaka ɗaya gaban ta sannan ta zuge ta, wasu shegun kayan aiki da bana ƙasar nan ba bundugune masu kyau da tsada, harda bomamai a ciki, tana zarowa tana faman murmushi da girgiza kai irin sunyi ɗinnan, ɗayar ta kuma jawowa ita kuma systems ne da wasu Camerori harda abun zooming ɗin nesan nan, da wasu baƙaƙen abubuwa da Ni kaina bansan sunan su ba, ɗayar kuma kuɗaɗe ne a ciki da wasu hulunan sojoji da kayan da takalma wajen ƙafa biyar manya manya masu tudu.
Ɗaga rigar ta tayi ta zaro wata ƙaramar waya, sannan ta danna kira ana ɗagawa tace; to kazo kayi aikin ka kaya sun iso, baka gansu ba, ka turo min Guddu ya taya ni saita su.... Shiru na ƴan sakanni sannan ta kuma cewa; "Hhhh to shikenan ku shigo ɗin ashe kunga shigowa ta shine baku zo kun taya ni ɗauka ba, shikenan dai ku shigo....
Tashi tayi ta fara shirshiya wasu kayan tana cikin haka sai ga wasu ƙarti uku sun shigo, suna shigowa suka saki ihu ganin kayayyakin,
"Oh Hajja Mama kinyi fa aiki anan gurin irin waɗannan kaya haka, kice an kusa fara aikin gaske dan har yanzu wasa ake,
"Ai daman zuwan su kawai nake jira amma kafin nan muna buƙatar ƙarin wasu mutanen da zamu tura wancen garin ni bazan shiga ba, kuma kuma nasan baza ku iya ba, to dole zan samo mana wasu mutanen, Amma dai zan tuntuɓi GEE muji yanda ya tsara.
"Eh gaskiya dai bakuyi waya ba kenan, ni idan na kirasa baya ɗagawa... Wani daga cikin su ya faɗa.
Ɗaya yace; "Kai ai BOSS lamarin sa sai shi ina ganin ƙoƙarin sa....
"Yauwa Hajja Mama yaushe zai shigo nan ɗin,
Tsayawa tayi da shirya kayan da take, ta ɗora hannun ta a kafaɗar ta tana kallon su, tace; "kuma ai kun sani baya faɗa saidai a gansa dan haka sai ku zauna cikin shiri tundade yace in mun ɗauko kayan zaizo ya gani, so any time ma zamu iya ganin sa, sai ku kiyaye sannan waɗannan yaran ku tabbatar da sun samu lafiya kar yazo ya gan su a haka, dan naje part ɗin ku naga sai a hankali wallahi ku sake dubawa sosai, nidai banda matsala da ɓarina komai normal ko yanzu ma ya shigo.
Ɗaya yace "Gaskiya nima dai banda matsala ko yanzu yazo,
Ɗan hararar sa tayi tace "Kai Guddu ka tabbata kuwa ko da yake nasan kai da ɗan sauƙi akan su O'O da hum hum.
Dariya sukayi sauran, sannan suka ce; "Hajja Mama tamu, kema da bakiyi nasara ba a wannan karon ai da kin ɓatawa Boss shiri wallahi, wai har yanzu basu farfaɗo bane, so nake inga reaction ɗin SMA.
Sosai Hajja Mama ta dara sannan tace; "Deen Allah ya gyara ka, me kuwa ya isa yayi saidai yagama abun sa, yanzu ai yayi sanyi shiyasa ma muka iya ɗauko sa amma da bazai ɗauku ba, yanzu ma saida ya gwada mana wai shi tsohon soja ne, mu kuma muka nuna masa tsohon ƙashin me ƙarko, ya tashi nima ai tashin nashi nake jira zanyi magana da shi idan fa yama bada haɗin kai Gee yace sakin sa za'ayi, in kuma yayi taurin kai zaiga namu kan dutse ne baya dannuwa.
Guddu ne yace; "Eh hakan ma yayi amma banajin zai bada haɗin kannan da wuri bari dai ya farka ɗin muga ni, waccen yarinyar fa?
Taɓe baki tayi tace; "tana part ɗin su Zaid yace tare zasu zauna a bata kulawa itama, juyawa tayi taci gaba da aikin suma suna tayata, sunayi suna hirar su.
*Gidan tsohon governor*
Har yanzu basu dawo daidai saboda rashin Faheema, sojoji har yanzu basu daina bincike ba kuma babu wani labari da suka samu, sai wajen yamma ne ma sannan aka samu labarin ganin motar da akayi, amma babu komai a ciki, koda RK yaji labarin haka sai yace su maida motar inda take sannan a buɗe hanya a ci gaba da bincike a ko ina, abun da suke tayi kenan har dare babu labarin da suka samu abun har ya fara basu mamaki ganin an rasa su,
*Five star ⭐*
A ɓangaren su kuma yau wunin gida su kayi babu inda suka fita,
Suna zazzaune a madaidaicin falon su, sunci abin cin rana sun bar kwanu kan agun ko wacce da waya a hannun ta, jikin su sanye da ƙananun kaya, daga me ƙaramin wando da riga sai wacce ta saka riga iya gwiwa, Babyn baby kuma ƴar bes ce a jikin ta sai gajeran wando, Barazana kuma doguwar riga ce a jikin ta marar hannu, taci kwalliya kamar zata fita, ita kuma ɗabi"ar ta ce tana son kwaliya ko da yaushe cikin kwalliya take saboda yanda take ji da kyan ta, ita kaɗai ma yaban kanta take to yanzu zaman da sukayi sai hoto take ɗauka tana tatso kyaunn ta..
Babyn baby zo muyi kinga yanda wannan fitar take da kyau, woo wallahi ni kyakkyawa ce zo muyi in haska ki, ki shafi kyawu na, yanda baby inyaganki sai ya rikice yace gida zai dawo.
"Haba Zee Zee ai kin san na fiki kyau sai dai in haska ki, tana maganar hankalin ta akan waya da take ta faman buga game, tana cikin yi ta faɗi sai tace "kashh kinga kin sa na faɗi, bari dai inzo muyi kar kiji badaɗi dan bakiyi hoto da sele ba,
Miƙewa tayi tana ƙarasa kusa da inda take tana wani turo ɗan ƙaramin bakin ta da karne ido ta saka kanta cikin wayar yanda zata fito da kyau.
Zee ce ta kalle ta ta harare ta tana cewa "Banza dalla can meye haka matsa min ma na fasa yi dake ma, bari inje muyi da ƴar sukuta ta alhaji babba taci tuwo tanai mana yanga,
"Babbar yaya ta gaban mota ɗaura ɗan kwalin ki kar kisa wayata ta tsorata da ganin wannan kitson naki irin na ƴan garin ku me kama da ƙahon saniya..
Wata uwar harara Aunty Babba ta wurga mata tana girgiza kai tace; "Allah Abu zanyi maganin ki kaf ɗin ku babu wanda yamin rainin da kika yi min, duk kinbi kin cika mana kunne da surutu ni wallahi shiyasa ma bana son zaman gida idan muka zauna baki da aiki sai na tsokanar mutane wallahi taron dangi zamuyi miki.
"He he he nan gani nan bari ɗumaman uwar mayya ba ƙatuwar bace, wai dan Allah bakyajin nauyin jikin ki zankaki wani guri da ake ragewa mutum ƙiba ko zaki daina kama da mazan garin mu...
Fillon gefen ta Aunty Babba ta ɗauka ta jefa mata, tayi saurin gocewa sai ya faɗa kan wayar Ameela da ta duƙufa kan wayar ko ɗagowa ma batayi, wayar ce ta faɗi da sauri ta miƙe tayi kan barazana ta kai mata duka ta kare da hannun ta, sai kawai ta fashe da dariya tana cewa yee mun tafa wani ta ƙara kai mata ta kuma tarewa da tafin hannun ta,
Girgiza kai kawai Ameela tayi tana komawa ta ɗau wayar ta tana cewa; "aikin banza mutum shi ko da yaushe baya son zaman lafiya ke ko gajiya ma bakya yi da faɗa...
"Kin manta nice ma Hajja mama gurin rashin gajiya da dambe.
Da sauri Beenish ta tashi zaune da rigar ta iya gwiwa sai gashin ta da ta ɗaure a tsakiyar kai sweet ɗin hannun ta ta ƙarasa shanye wa sannan tace; "Ni sai yanzu ma da kika faɗi sunan ta na tuna, anfa ɗauke wannan yarinyar ya sunan tane ma?
Ameela tace "Faheema ba, Allah sarki, amma ai ba lalle ba ta cutar da ita wataƙil ta riƙe ta kamar yanda tayi mana, amma dai wallahi banji daɗi ba da ta ɗauke ta naga yarinyar tana yin mu sosai..
"Eh wallahi nima banso ba, kodan mu samu damar shiga gidan naso munci gaba da mu'amalla da ita, abun ta ƙaici gashi mun shiga gidan ma bamu samu wani news ba, naso mun shiga cikin gidan wallahi" cewar Barazana.
Beenish ta ɗan numfasa tana taune pink lip ɗin ta ɗan ƙarami kamar ta shafa masa janbaki, girgiza kai tayi tace; "nima nayi ta ƙaici amma nasan zamu koma za'a iya neman mu, in ma bamu shiga ba zamu samu wata a cikin gidan da zatayi mana aikin da muke so...
"Ga wata shawara kunsan me.!!!
Duk juyawa sukayi suna kallon Ameela da tayi maganar....
"Indai muna so mu shiga gidan nan koda mu kaɗai ne yanda suke da tsaro sosai ba lalle mu samu haɗin kan su ba, abun da zamuyi anan kawai shine dole sai mun samu kyakkyawar alaƙa da ɗaya daga cikin yaran gidan, mace ko namiji....
"Me zai haɗamu da namiji kuma? Inji Beenish.
Kallon ta Ameela tayi tana ɗan murmushi tace "fake love" mu mata ne kuma suma mazane dan haka dole mu samu labarin adadin mazan da suke cikin mazan gidan, ɗaya daga cikin mu ta ƙulla soyayyar ƙarya,su wayayyu ne nasan dan namijin yakai ta gidan su ba lalle su kalli hakan da rashin dacewa ba, dan haka ina ganin ta haka ne kawai zamu shiga jikin su musamman idan muka samu karɓuwa a wajen, sannan mu ringa nuna damuwar mu akan ɓatan ƴar su, har mu nuna zamu iya nemo musu muma zamu saka ido muyi bincike, ina ganin kamar hakan zaisa mu ƙara shiga jikin su amma ya kuka ce...
Duk shiru sukayi suna nazari kowa ya kasa magana, Babyn baby ce tace eh wallahi idan kuma daga soyayyar wasa ta koma ta gaske ai shikenan sai mushi biki, amma dai saidai a idan Yay........,
Wata uwar harara Beenshi ta watsa mata tana doke mata ƙyeta tace saidai uwar yaya tunda kike kin taɓa ganin na tsaya da namiji me zance masa, kude da kuke so sai ku zaɓi ɗaya tayi, ga abu me sauƙi ma banaji ance Dr. Aveed ɗan gidan bane...
Dariya sukayi gaba ɗayan su, Fashion tace; "Allah kuwa Beenish ke ya dace kinga wannan ba abun da ta iya ta nuna Ameela, ni kuma ina da mawa, Baby tana da babyn ta, to sai kuma.....Hhhhhh dariya ta kwashe da ita harda buga ƙafa, tunkan ta faɗa ma suma suka kwashe da dariya amma duk da haka saida tace; "tom cikin waƙa waƙa tafara cewa "kunsan dai ita wannan baiwar Allahr da kuke gani tammm ga hanci dooogooo ga baki ƙarami ga kai duk gashi ga fuskar ba tsagu ga haske yayi yawa ga siranta tabi jiki ka kalar ta ta mat........,
Daga inda take ta farɗo ta da hannu saida ta dawo gaban tashi tayi ta zauna akan ruwan cikin ta tana cewa wallahi sai nayi maganin ki yau..
"Wayyo Babbar yaya wallahi na tuba basan sake ba, ki ɗaga min ciki Allah numfashina ya kusa ɗauke, wai kuna ganin ta ku janye min wannan buhun kwaki...., Au na ba kwaki ba wallahi Auntyn mu kimin rai...
Ita kuwa ƙara gyara zama take akan ruwan cikin ta ga ta buɗa mata hannuwan ta ta daddane da gwiwar ƙafar ta tana cije baki, su kuwa dariya kawai suke wa Zee Babyn baby kuwa wayar ta ta ɗauka take musu video.....
"Baby wallahi zanci mutuncin ki ku taimake ni amma shine zaku min dariya, wai sai ta kashe ni bazaku ɗauke ta, Aunty Babba wallahi na biki nabi Allah kiwa Allah ki ɗaga ni Allah da gaske nake zan iya mutuwa duk kin haɗe min ƴaƴan cikina da hanji da ƙoda da hunhu duk sun haɗe guri ɗaya Allah zaki kisan kai.....
Duk surutun ta bata ɗaga taba saida tasan ta galabaita tayi laushi sosai idon ta har ya kaɗa yayi ja, sai loƙacin ta ɗaga ta tace gobe ma ki ƙara ƴar ranin hankali...
"Humm Humm sai wani irin numfashi Zee take saukewa na wahala ba ƙarya taji jiki, hannuwan ta kuwa da ta danne da ƙyar take iya ɗaga su, amma aranta ita kaɗai tasan rashin mutuncin da zatayi musu gaba ɗayan su tunda suna gani tayi mata haka basu dakatar da ita ba.....
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*SOKOTO*
*Gidan Hajiya Rabi*
Saida ya huta sosai sannan ya lallaɓo ya fito daga falon yana fitowa yaga babu kowa a falon waje ya nufa sai yaga babu motar Hajiya, da sauri ya dawo ya shiga kitchen ya tambayi me aikin ko tasan inda taje, tace masa eh tace anyi mata kiran gaggawa sai can cikin dare zata dawo ko kuma ma saida safe.
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓe sa ji yake kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, tunanin da barar da zai yi mata ta fita daga gidan ya farayi,
Juyawa yayi kamar zai fita sai kuma ya dawo yace; "yauwa Saude dan Allah gidan su Kaka zaki kice wai meye suke buƙata zanje kasuwa gobe da safe, kinga duk na kira wayar su bata shiga ba, kuma abokina zaizo bana so yazo bai sameni ba ga kuɗin mota, ya zaro wajen dubu biyar ya bata.
Aikwa hannun ta har yana karkawa wajen karɓa,
Daman da hijabi a jikin ta kuma tagama aikin ta, dan haka kuwa fitowa kawai tayi ta fita,
Yana ganin fitar ta yaji wani daɗi yaƙara mamaye sa,
Kitchen ɗin ya shiga sannan yabi ta ƙofar baranda ya zagaya can baya inda store ɗin yake, saida yaje gurin sai kuma yayi turus ganin akwai kwaɗo a jiki,
Tunanin mafita yafarayi, gidan ya koma yayi ta lalaben abun da zai buge kwaɗon, saida ya sha lalube kafin ya samu wani ƙaton ƙarfe, da sauri yazo yana ta bubbuga shi ajikin ƙwaɗon, inda Allah ya taimake sa ma, duk ma'aikatan gidan basa guraren wajen suna can wajen me gadi kuma da tazara tsakanin su dan haka babu wanda zai kawo me ake bugawa,
Da ƙyar ya samu ya buge ƙwaɗon da sauri ya zare shi ya tura ƙofar, yana shiga kuwa ya hangi baiwar Allah ƙasan kanta zaune ta bakin ta da ƙafafun ta ta a ɗaure sai kwanun kan abinci a gefen ta, da aka ajiye mata bata ci ba saboda bakin ta da aka ɗaure mata ta baya,
Da sauri yaje gurin ya tsugunna ya kunce mata bakin yana ta kallon ta cike da tausayawa babbar macece ma dan ta ɗan manyan ta fara ce amma kana ganin ta zaka san tana tattare da damuwa.
Kallon sa kawai take bata hana sa ba kuma bata ce masa komai ba,
Ruwan da yagani a gefe ya ɗauka ya bata karɓa kuwa tayi ta kafa kai bata sauke ba saida ta shanye gaba ɗaya sannan ta ajiye gorar ruwan,
"Sannu!
Gyaɗa masa kai tayi kawai, tana ɗan lumshe ido.
"Taso muje..
ba shiri ta tashi kuwa tayi ta miƙe tsaye,
Hannun ta ya kamo yace; tsaya anan bari in ɗauko mota, nan jinjina masa kan tayi, da sauri yaje ya ɗauko motar ya kawo ta daf da gurin yanda ba wanda zaiga shigar ta, fitowa yayi ya kuma kamata ya saka ta a gaban motar, sannan ya fita da ita batare da kowa ya gansa ba,
Saidai yayi tafiya me nisa yabar unguwar, wani ɗan madaidaicin gida yakai ta, da taimakon sa ta fito har suka zo kuma babu baice mata komai ba itama kuma bata ce masa ba,