ni, nayi maka laifin ba, me yasa zaka huce akaina, namaka alƙawari ka gaya min inda take, zanje har can ingargaɗe ta koma me kake so inyi mata zanyi maka,
Banza yayi da ita ya zaro muƙulli a aljihun sa yaje wajen fridge ya buɗe ruwa ya ɗauko ya sake rufewa ya nufi hanyar waje da sauri ta kuma binsa, tana daf da zata fita yasa ƙafa ya harbota yaja ƙofar ya ƙulle tare da saka muƙulli ya ƙulle, cikin fushi yake tafiya,yana zuwa aka buɗe masa mota daman tun yana ciki ya sanar dasu su shirya zasu fita, shiga kawai yayi suka ja motar me gadi ya buɗe musu suka fice yana gaba motoci biyu a bayan sa, direct gidan su Barazana suka dosa.
Hajiya Aunty Babba kam daga gurin da yabar ta bata iya motsawa ba, abun yayi mugun bata mamaki, ita yasa ƙafa ya ture, me tayi masa har haka kode tayi masa laifi ne bata sani ba, to kode matar da tazo ta kawo magana akanta ne, ta daɗe agun tana tunane tunanen meye mafita ga yunwa da taci gaba da addabar ta, gashi bata taho da wayar ta ba, tana cikin motar su tunda suka dawo ɗinan tabatar ta a ciki, gashi ya ƙulle ta bare ta fita ta nemi wani abun.
Tashi tayi ta nufi ɗakin sa suka sauka, tana murɗawa taji ƙofar a ƙulle, sosai ta shiga tunani da wannan lamarin nasa, dawowa tayi falon ta zabga tagumi tana jiran dawowar sa...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*Hajiya Dannar*
Tana zaune akan kujera da systema cikin wani ɗaki gefen ta da mug ɗin tea, sai gaban ta da system tana dannawa tana ɗan shan in, idon ta ɗauke da wani farin glass kanta ba ɗan kwali, sai ɗaure gashinta da tayi, wayarta ce, ta shiga ringing da sauri ta ɗauka tana ɗagawa tasata a handsfree yayin da take ci gaba da daddana system ɗin.
Hello Hajiya antashi lafiya?
"Lafiya" ta amsa a taƙaice,
"Yauwa daman aikin da kika bayar ne, wallahi mun kasa gano komai, munyi iya binciken mu bamuga inda ya shiga, kuma har yanzu bai dawo gidan ba, saidai zamuci gana da saka ido, kar kiji mu shiru.
"Tom Hamza, ita kuma Rabin fa ta dawo ne?
"A'a wlh, bata shigo garin ba har yanzu tun safe muke zuba ido.
"Okay sai anjima.
Ana kashewa ta ɗau wayar ta shiga daddanawa, ana ɗagawa tace "Maryam ya kuke kun tashi lafiya dai ko ba wata matsala?
Daga can Maryam tace wallahi lafiyar nan dai da sauƙi Hajiya, dan yanzu hakama ɗaya daga cikin su bata da lafiya saboda abun da yafaru jiya bayan tafiyar ku, sojoji suka kuma dawowa suka ɗauke su, can cikin dare kuma suka dawo dasu, saidai har yanzu basu gayan me ya faru ba, sundai dawo duk ba daɗin rai, har yanzu kuma basu da walwala har gwanda Ameela da Babyn baby amma Beenish da Barazana basa cikin walwala, banaso kuma in ta kira musu da tambaya.
"Sauke ajiyar zuciya Dannar tayi sannan tace "ok zanmusu magana inji, daman wannan maganar ce da mukayi zamu tura su, aikin soja, to yanzu nake samun labarin za'a ɗauki mutane zasu fara tarainin a Lagos to amma kinsan basu da wani karatu akan harkar saidai kawai idan da hanya zamu samu dama, shiyasa nake son ki taɓo mana wanda kika ce kin sani ko nawa zamu biya a saka su a ciki, amma banda Babyn baby su ukun dai zasuje tunda ita waccen yarinyar ta tafi,
"Amma tun yanzu bakya ganin loƙacin yayi kusa kuma zasu amince su tafi a gobe gobenna bafa ayi musu bayanin komai ba, amma ya kike gani.
"Zanyi musu bayani, anjima zan shigo gidan kar ki damu.
"Tom shikenan Allah ya kaimu jimawar, sai kinzo.
Daga haka sukayi sallama, ta ajiye wayar, maida hankalinta tayi kan system ɗin tana ta daddanawa, can saiga video gidan Rabi, shiga daga waje ta fara bi da kallo, babu kowa gashidai masu aiki na ta zirga zirgarsu, tana ta kalla, har Hajiya Rabi ta fito, cikin sauri ta shiga mota ta bar gidan, can kuma sai ga Khalifa ya fito shima cikin sauri, nan dai duk taga yanda ya fito da Fateema, saidai bata san wacece ba tunda bata santa a fuska ba, kashe system ɗin kawai tayi ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki, ba jimawa ta fito ta shirya kamar yanda ta saba shirin ta na gayu, tana gamawa ta fito tabar gidan......
$$$$$$$$$$$$$$$$$
*Five star ⭐*
___Da safe ma da ƙyar suka tashi saidai duk wani iri babu walwala, su Beenish dai babu wani ciwo da take ji sai haushin RK da yaƙi barinta har yanzu, Barazana kam jikin ta duk ciwo yake mata da ƙyar ta iyayin sallar asuba ma.
Duk suna falo Barazana na kwance kan kujera, Babyn baby ce tace "wai me ya sami mutuniyar ne tun ɗazu nake tambayar ku duk kunyi min banza,
Beenish ce ta kalli Ameela, Ameela kuma ta kalli Barazana suna haɗa ido ta wani zabga mata harara irin meye kike kallo na, kar kice komai, hakan da tayi sai yaso bawa Ameela dariya amma tayi saurin mayar da abarta.
"Wai meye naga kuna kallon kallo.
Ameela ce tace "kedai ki kwantar da hankalin ki zaki sha labari idan me bada labarin ta tashi yanzu kiɗan bata loƙaci, kafin ta huce da yanzu da zafi take, in kuma kina so ki ƙone to abaki labari.
"Nima daman ina ta son inji me yake faruwa? Cewar Maryam da taba falon batace komai ba sai yanzu,
Ameela ce ta gyara zama tace "hmmm in ana sallah ai ba'a magana, todai yanzu Abu sallah take dan haka bazatayi magana ba ko na baku labari, wallahi dai jiya tsautsayi ya afka mata kunsan daman ance baki shike yanka wuya tode yau bakin Abulle ya yanka mata duka jiki ma ba wuya ba, yau sunyi babbar ganawa da Sojan Beenish,
Da sauri Beenish ta haɗe rai tare da jifanta da kofin dake hannun ta, tace "wai ke har abun burgewa ne a wannan labarin da kike shirin bada shi, to wallahi baki isaba ke bakyama jin haushin abun zaki iya zama ki bada labarin abun da ya faru, to wallahi baki isa ba, saidai idan bama gurin.
Dariya Ameela tayi ganin bilhaƙƙi da gaske Beenish take yanda ta haɗe rai take masifa, sai kace ita aka jibga.
"Allah me hanani labarin nan ban gansaba, mutum ɗayane zai hanani, uwar gayyar ta buɗi baki taban haƙuri tace dan Allah kar na faɗa to naji bazan bayar ba amma muddin ba'ayi haka ba to fa sai na faɗa, Babyn baby kina so kiji ko?
Da sauri Babyn baby ta ɗaga kai tana murmushi.
"Ameela zamu sami matsala dake wallahi kar ki sake ki kuma magana anan gurin, cewar Beenish.
"Allah sai na yi kuwa, Zee Barazana Zee Fashion ko ba kuɗi akwai iya taku me baƙin, waini ji nake jiya kince baza kiyi shiru da bakin ki ba, Allah yabaki baki a hanaki magana, yanzu kuma da muke son kiyi shine bazaki yi ba, rabona da jin muryar ki fa tunjiya da kina ihu, Baby ɗan ɗauko min waccen wayar wutar in baki labarin abun da ya faru da ita.
Allah sarki Barazana duk yanda taso ta tanka ma Ameela kasawa tayi saboda tana magana zata iya yin kuka, dan haka sai kawai ta miƙe zata bar wajen sukaji anbuga musu ƙofa, dakatawa tayi da tafiyar.
Maryam ce taje ta buɗe dan daman tun ɗazu take zuba idon ganin ta.
"Sannu da zuwa.
"Yauw" Hajiya Dannar tace tare da ƙarasa shigowa cikin falon, tana ta faman sakin murmushi abun ta,
Ameela na ganin ta ta haɗe rai kamar bata taɓa yin dariya ba, tashi taso niyar yi Beenish tayi saurin riƙe hannun ta, hakan yasa ta zauna tana kawar da kai gefe.
Gaisawa suka shiga yi, kowannen su na gaishe da ita amma banda Ameela da ta kawar da kai gefe, Zee ma dai da ƙyar ta iya gaida ta.
Bayan sun gama gaisawar ne, Hajiya Dannar ta ce "to sauri nake wallahi yanzu zan sanar daku abun da ya kawo ni ina fatan zaku ban haɗin kai domin akwai abun da na hango muku wanda ku baza ku gane hakan ba, sai nan gaba, to yanzu dai batare da ɓata loƙaci ba, ina son neman wata alfarma agunku ba daɗewa zakuyi acan ɗin ba, kawaidai zakuyi na zuwa wani loƙacin, komai ma daidai ta in sha Allah zaku bar aikin, shiru tayi tana nazarin su da kallon kowanne su, su kuma sun matsu suji me zata ce mu su.
"Ba komai bane daman jiya naji labarin za'afara training a Lagos za'a ɗauki mutum ɗari kawai zasuyi gasa acikin su kuma za'a ware mutum hamsin suma hamsin ɗin mutum ashirin ake buƙata abunde mataki mataki ne idan kunje zakuji ƙarashen labarin, duk wannan abun bata gaya musu meye ba,
Duk zaro ido sukayi cike da mamaki suke kallon ta, wannan karon hatta Ameela saida ta juyo ta kalle ta batare da tasan tayi ba, Abu kuwa bata san loƙacin da ta miƙe zaune ba,
"Soja fa kika ce Ammu? Cewar Beenish dan itace me bakin bada amsa.
Girgiza mata kai tayi, tace dan Allah kar ku tambaye ni dalili amma dai muddin kuna so wasu burukan naku su cika to sai kunbi ta wannan hanyar,
Tana cewa buruka Beenish ta tafi tunanin, take wani tunani ya faɗo mata, tabbas Ammu tayi gaskiya dole sai sunbi ta hanayar zasu samu cikar wasu burukan nasu, itama kuwa tana da wannan burin dole ta hanyar ce zata iya samun damar yin ramuwarta, daman tun jiya take ta tunanin ta yanda zata cika wannan burin mata to ga dama ta samu ai zama ta amince ko su sauran baza su Amimce ba...✍️✍️
*Da banyi niyar gaya muku abun da ya faru ba, amma dai kwada kuji, yau nayi abun da na daɗe banyi ba, saida na gama typing kaɗan ya rage na kammala na yau, kawai ya goge gaba ɗaya 😭 shiyasa kukaga nayi dare sai bayan sallar magriba nayi muku wannan da ƙyar dan wallahi da cewa nayi ma na fasa sai gobe kuma banaso inyi muku fashi wallahi 😭😭*
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/19, 10:28 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
_______*08124226526*_______
*_episode 41💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
Bismillah..✍️
____Tana cewa buruka Beenish ta tafi tunanin, take wani tunani ya faɗo mata, tabbas Ammu tayi gaskiya dole sai sunbi ta hanayar zasu samu cikar wasu burukan nasu, itama kuwa tana da wannan burin dole ta hanyar ce zata iya samun damar yin ramuwarta, daman tun jiya take ta tunanin ta yanda zata cika wannan burin mata to ga dama ta samu ai zama ta amince ko su sauran baza su amince ba...
"Amma ya kuka gani idan bakwa so bazanyi muku dole ba.
Da sauri Beenish tace "mun amince Ammu, ai duk abun da kika ce daidai ne, zamuyi.
Daɗi Hajiya Dannar taji marar misaltuwa bata taɓa tunanin batare da ta gaya musu dalili zasu amince ba, ba ita kaɗai ba, Maryam taji daɗin jin hakan.
Ameela kuwa bata san loƙacin da ta miƙe tsaye ba, cike da masifa tace "me kika ce, kinsan kwa me kike faɗa Beenish, akan wane dalili zamu amince mu da ko makaranta ma bamu gama ba, to kima canza tunani ko kuma kije ke kaɗai dannidai babu inda zani,
Barazana ma ta samu damar magana yanzu cikin muryar ta da bata fita sosai tace "nima gaskiya Ammu kiyi haƙuri amma bazan iya zuwa ba, ko kayan ma banason ganin sa bare masu sakashi bare kuma ace ni zan saka gaskiya bazan iya, kuma kema da kike cewa kin amince to babu ni babu ke daga ranar da kika fara saka kayan mun raba gari dake dan Allah duk sanda ma kika san zan iya kasancewa agu to kar kizo nima kuma bazan zo inda kike ba dan Allah kar ki amince, in kuma kema so kike ki koma muguwa marar imani da tausayi to nidai ba ni ba ke.
Harara wasa Beenish ta jefa mata tana cewa "Ammu kar rabu dasu duk zasu je kar kibi takan su, su yara ne har yanzu basu san rayuwa ba ne.
"To sannu masaniya ke ai sai kije amma ni kinga tafiya ta ma, Ameela na faɗar haka ta nufi ɗakin su fuuuu kamar zata tashi sama, dan ita maganar ma haushi take bata.
Sosai Hajiya Dannar ta nuna jin daɗin ta a fili sannan tace "to shikenan nagode nagode my daughter, amma fa sai ku fara shiru tun yau dan gobe da safe zaku tafi inaso kubi jirgin ƙarfe goma dan naji da wuri zasu fara taron kafin a ɗibe ku.
"Adai ɗebe ta dan wallahi babu inda zani saidai ko idan su tafi da Babyn baby daman tare muka gansu amma wallahi inason lafiyata bazanje a sauya min siffar jiki ba, a koya min baƙin hali da mugunta, da rashin tausayi.
Tunda suka fara maganar Babyn baby ta saki baki tana kallon su, sai yanzu da Barazana ta yi wannan maganar yasa tayi saurin cewa "gaskiya nima bazan iya zuwa ba kuma bazan iya zama babu yaya ba a kusa dani ba, Ammu dan Allah kubar wannan maganar kowa fa da burin abun da yake son zama idan mun kammala karatun mu amma kuma akawo wannan zancen da ko daɗin ji babu.
Ammu zatayi magana kenan Beenish ta rigata da cewa "daman ai ba dake zamu ba ke zaki zauna anan tare da wannan matar kici gaba da karatunki ki zama babbar likita, kuma fa nima ba wani daɗewa zanyi ba, bakiji me tace ba, na zuwa wani loƙaci domin cikar wasu burukan namu da zarar ya cika fa zamu dawo muci gaba da yanda muke,
Ai duk wannan bayanin nata Babyn baby bataji sa ba take idanun ta har sunciko da ƙwalla dan itafa bazata yarda da wannan maganar ba, taya zata zauna babu ita taya ma gidan zai yi mata daɗi,
Cike da shagwaɓa saura kaɗan hawayen ya gangaro kana jin muryar ta kasan kuka take shirin yi tace "Dan Allah yaya kar ki min haka kisan bazan iya zama a ko ina ba idan bakyanan, kuma ni wallahi bazan iya zuwa ba, saidai ke ki haƙura mu zauna tare.
Barazana da taji zancen bana kwance bane yasa ta tashi zaune tana cewa "Ke dalla wai kike wani saka jam'u mu ba gamu ba, ko ance miki zuwa zamuyi, nida Ameela muna nan babu inda zamu kibari taje idan jikin ta ya gaya mata zata dawo ƙafarta.
Kuka kawai Babyn baby ta saki sai kace yanzu yanzu za'ayi tafiyar.
Haƙuri suka shiga bata gaba ɗayan banda Barazana, Ammu, Maryam, Beenish.
Amma kamar an ƙara mata ma volume ta koma jikin Beenish ɗin taci gaba da kuka banza Beenish tayi da ita daga baya dan tasan idan taci gaba da rarrashin ta zata sa taji ko ta fasa tafiya, amma batajin zata haƙura zata yakice kowa dan cikar burinta.
Daga haka Dannar tayi musu sallama tare da kuma jadda musu su shirya, saidai tana faɗa Barazana na kuma cewa bata ba, bata kulata ba tunda Beenish tace ta rabu dasu shiyasa ta rabu da su ɗin, bayan fitar ta, Beenish ta miƙe tsaye Babyn baby ma ta sharar hawaye amma taƙi kulata, saima maida dubanta da tayi ga Barazana tace "ku fara shiri fa dan zuwa babu fashi,
"Kidai shirya, Malama ki daina lissafi da ni fa, daman ai duk ke kika ja min wannan abun da baki buɗe ƙofar ba tun farko ai da duk hakan bata faru ba, amma yanzu ga abun da kika ja min nan, ke wallahi ma Allah ya isa ke yakamata ma in tayiwa Allah ya isa kafin shi, dan gaba ɗayan ku ne kuka cuce ni, kuma wuta bal-bal daga ke har