Ɗan taɓe baki tayi tace da sauƙi yanzu ma na sha magani da zan fito, dan inajin kana cikin garinnan naji na warke.
"Uhmm, sorry dear.
Kamo damtsen hannun sa tayi tana kwantar da kanta akan kafaɗar sa, cike da shagwaɓa tace "Sweetheart wai har yaushe ne zaka amince da auren mu nifa na matsu inganni a ɗakinka kaji please my dear kodan wannan rashin lafiyar tawa, indai ina tare da kai banfiya yi ba, shiyasa nake son muyi auren ko ciwon nan ya daina yawan tayar min.
Hannu ɗaya ya ɗaga yaɗan shafa kanta tare da cewa "very soon we have to be together don't worry your self right?
Jin jina masa kai tayi sannan ta kuma miƙewa zaune tana kallon sa tace "what about her?
"Who?
"Malikha mana nasan tana sonka kuma gashi kullum kuna aiki tare bana son kuna yawan mu'amala wallahi sai naji kamar zaka so ta, kuma wallahi idan kaso Sweetheart Allah zan iya mutuwa, yanda nake son ka kai kaɗai haka nake so kaima na zama I'm the only one in your heart, my heart it's for you, then I hope you too kamar yanda tawa take.
Haɗe rai yayi yana kallon ta yace " I hate this silly talk, bana son irin wannan you know me very well, so keep dis matter a side.
Matsawa tayi daga gefen sa fuskar sa kamar zata yi kuka, ta kawar da kai gefe, shi wai ba dama tayi magana akan waccen sai ya haɗe rai alamuma kenan yana sonta tunda baya son ana maganar,
Bai kula taba ya mayar da kansa ya cigaba da aikin sa, haushi ne ya ishe ta sai kawai ta miƙe fuuu tayi waje ita wai tayi fushi kuma jira take sai ya dakatar da ita ya bata haƙuri, shi kam ko ɗagowa baiyi ba duk da yana sane da duk abun da take har ta fice.
Tana fita ya ɗauko wayar sa ya ɗanyi typing ɗin abu ya tura ta, mata sannan ya ajiye wayar a gefen sa.
Tana fita taji wayar ta tayi ƙara da kamar bazata duba ba saidai ta tsaya ta ɗauko ta ajaka tana buɗewa taga message daga shi da sauri ta buɗe ta shiga karantawa _Take care your self _
Murmushi tayi kawai ta mayar da wayar sannan ta yi part ɗin Moohad, a rufe taji ƙofar saida ta ƙwanƙwasa ta tsaya sannan yazo ya buɗe mata, murmushi ta sakar masa shima ya mayar mata yana bata hanya ta shiga cikin falon, saida ta zauna sannan suka gaisa, tashi yayi dan ya ɗibo mata abun sha tace a'a ya barshi kawai yazo wajen mutumin ne, kuma sunyi faɗa dan haka ita baza ta tafi ba anan zata zauna har sai yazo nan ya bata haƙuri.
Jin abun da tace yasa Moohad girgiza kai tare da cewa "to taya zaisan kina nan ai sa acan ɗin kika zauna yafi baki, kinsan wannan tsakanin ku ne, ba'a shiga tsakanin masoya duk wanda ma ya shiga shi zaiji kunya.
Dariya ta ɗanyi tana miƙewa tsaye tace zanyi yanda zai zo ne, yanzu dai bari inyi fitsari, ta faɗa tana nufar inda Beenish take, shi yama sha'afa da Beenish na ciki shiyasa bai hanata ba, saida ta shiga ma ta fito tana cewa "Moo kamar mutum magani kan gadon ka wace ce?
Rasa me zaice mata yayi yama manta me yasa bai rufe mata ɗakin ba da yagama bata maganin, ɗan sosa kai kawai yayi cike da basarwa yace "ba damuwa ki shiga kawai ki fito Madam ɗina ce bata ɗan jin daɗi ne shine ta kwanta zuwa safiya.
Dawowa tayi falon fuskar ta ɗauke da murmushi tace "really? Are you serious Moo!
Kaɗan mata kai kawai yayi yana tunanin me kuma ya kamata yayi yanzu.
"Wow gaskiya nayi farin ciki bantaɓa ganin ka da budurwa ba sai yau ashe ka samo kaga shikenan sai a haɗa bikin mu da naku wow zan so ganin ranar, da sauri ta ɗauki jakar ta tace "bari in koma gurin sweetheart ni har najima na daina fushin, bari inje mu fara shirye shiryen yanda abubuwa zasu kasanece amma dear bai kyauta ba da bai gaya min ba, zan same shine yanzu sai na mishi mita wallahi, tana maganar tana niyar fita, da sauri Moohad ya shiga janta yama rasa ta yanda zai ganar da ita kar taje, sai kame kame yake mata akan ta zauna zai kirasa, amma tana ta dariya tace ya bari kawai bari taje ta faɗa masa da kanta...✍️✍️
[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
________* 08124226526*_______
*_episode 48💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
_Bismillah..✍️_
___Duk yanda Moohad yaso ya hana ta zuwa ƙin dakatawa tayi ta tafi tana ta faman jin daɗi.
Tana fita Moohad ya sawa ƙofar key dan shi kaɗai ne mafitar sa, bayan ya rufe falon yaje itama ya ƙollota sannan ya shiga wani ɗakin, yan tsammanin zuwa RK dan yasan yau sai ta Allah idan tagaya masa dole zaizo ya duba.
Loƙacin da ta ƙarasa part ɗin RK har ya tashi daga falon ya koma ɗaki, ganin bata gansa ba a falon ta nufi ɗakin direct, ba tare da ta ƙwanƙwansa ba, ta tura ƙofar ta shiga, tsayawa tayi tana kallon bayan sa da ya juya waya riƙe a hannun sa alamun dai waya yake.
"Ya kamata ki shigo gobe, I want to see you tomorrow, we discuss something idan kinzo, shiru yayi yana sauraron abun da take cewa kafin daga bisani ya sauke wayar tare da cewa "ok see you bye.
Bata ji farkon maganar ba kuma batasan da wa yake magana ba, hakan yasa zuciyar ta tashiga yi mata wasi wasin da wa yake waya har yana cewa yana son ganin ta, batasan loƙacin da ta saki jakar hannun ta ba, cikin ɗaga murya tace "who is that!
Juyowa yayi yana dauke mata idanun sa akan nata fuskar sa a ɗaure baice mata komai ba kawai ya tsare ta da ido.
Ƙarasawa gaban sa tayi itama fuskar ta a ɗaure tace "I'm asking you? why are you looking at me like dis, ba kallo na nace kayi ba just answering my question, tayi maganar tana harɗe hannun ta a ƙirjinta.
"It's not ur own business, duk da wanda zanyi mu'amala it's necessary ne sai kin sani, I told you na tsani shishshigi bana son takura da tambayar masifa, wai ina ruwanki da rayuwa ta ne ko kin taɓa jin na tsaya ina miki waɗannan abubuwan yanda bana cikin rayuwar ki please leave me alone in saka ta in wala nifa soyayyar nan babu dole kinsanni tun ba yanzu ba, in kinsan bazaki iya ba, ki barshi mana mtsw, banason takura, yana kaiwa nan ya doshi hanyar bathroom.
Da sauri ta sha gaban sa, kamar zata yi kuka tace "why kake faɗa min irin wannan maganar haka, meye problem ɗin son da nake maka ne laifi, Please dear ka daina irin wannan maganar you know I can't never leave you, you are my entire world, I can't live without you in my life, tana maganar tana shirin faɗawa jikin sa da hannu ya tare ta yace "Please go home zamuyi maganar daga baya yanzu I want to be alone.
Kuka tasaka masa, tana riƙe hannun sa, tana cewa me yasa kake min haka kwata kwara baka so na raɓi da jikin ka, sai kai ta wani jajjan baya dani, nifa taka ce komai nawa naka ne ka daina hanani taɓa jikin ka, you and your body all it's my own, ƙara yunƙurin rungumesa tayi amma still ya kuma dakatar da ita, dan shikam abun ma haushi yake basa, amma dan ya samu ta fitar masa daga ɗaki sai yace "stop crying, I won't to see ur tears, hannu ya ɗora akan haɓarta sannan ya ɗago ta suna kallon idon juna muryar sa ba wasa yace just go back to home, zamuyi magana, banason taurin kai.
Share hawayen tayi tana ɗaga masa kai badan ta so ba, zata tafi dan ita so take ma ta kwanta a gidan, amma kullum tayi ƙoƙarin yin hakan sai ya kore ta gida, tama manta me ya dawo da ita haka ta juya ta tafi gida kamar yanda ya buƙa ce ta data ta yi ɗin.
Tana fita yabi bayan ta da harara tare da neman bakin gado ya zauna yana ta faman sakin tsaki, kwata kwata shi fa shiyasa baya soyayya dan bazai iya jurar irin waɗannan abubuwan ba, bazai zauna yai ta rarrashin mace ba, ko ta zauna tana masa maganganu san ranta bazai jura ba, ai ba dole daman dan ta nace ne kuma yana ganin mutuncin ubanta shiyasa yake kula ta amma shi bama sonta yake ba, ai ba dole sai yayi soyayyar ma gaba ɗaya, meye a cikin soyayyar in banda hauka, Indai sai anyi soyayya za'ayi aure to ya gwammace ya zauna a haka dan bazai iya bawa mace loƙacin sa ba saboda ya tsani naci da takura, wani tsakin ya kuma ja da ƙarfi sannan ya miƙe ya shiga yayo wanka, a haka ya kwanta batare da ya saka kaya ba, lumshe idon sa yayi yana tunanin can tunanin ɓatan yarinyar nan ya faɗo masa da sauri ya miƙe zaune yana kuma jan wani tsakin yana miƙewa tsaye sannan yaje ya ɗauki kaya marar sa nauyi na bacci irin na maza, yana sakawa ya kuma bin gadon ya kwanta yana rufe idon sa kamar me bacci saidai ba baccin yake ba, kawai yana buƙatar yajishi a hakan ne, saboda abun da wannan budurwar tayi masa duk sai yaji sa wani iri ransa na ta kuma ɓaci..
Moohad shiru shiru yana ta jiran yaji bugun RK amma baiji ba har ya gaji da jira shima ya kwanta, da safe yana tashi yazo ya tashi Beenish, ko da ta farka ta ɗanji jikin nata da sauƙi hannun ne kawai yake ɗanyi mata zafi shima ba sosai ba, duk wani abu da yasan zata buƙata yaje ya siyo mata kama daga kayan sakawa da abubuwan ci, duk ya kawo ya ajiye mata, ita dai godiya ta ringa yi masa.
$$$$$$$$$$$$$$
*ƊAN IJJE'S HOUSE*
Maryam da Babyn baby, suna cikin ɗakin sa aka sauke su na ma'aikatan gidan, suna ɗaki Babyn baby ta dasa mata kuka tana cewa ita bazata iya ba, ya za'ayi ta zauna a gidan nan a matsayin ƴar aiki gashinan daga zuwan ta yaran gidan sun fara ɗaga mata murya harda hanata zaman kan kujera, ita dai Maryam haƙuri take ta bata tana kuma nusar da ita amfanin zaman nasu a gidan, amma duk da haka ita dai bata jin daɗi, a haka suka kwana tana faman yi mata mita, suna idar da sallar asuba Maryam ta tisa ƙyarta suka shiga cikin gidan dan matar gidan already ta riga tayi mata bayanin komai dan haka farawa kawai zasuyi.
Girki aka basu da kula da kitchen ɗin da gyara shi da wanke wanke, nan Maryam tace tayi wanke wanke, saida tayi kuka sannan ta fara shima tana yi tana hutawa dan ta manta rabon da tayi wanke wanke duk ƙanƙantar sa bare wannan me yawan da ƙyar dai tayi shi, ita kuma Maryam ta ɗora abinci bayan ta gama wanke wanken Maryam ta saka ta gaba suka ci gaba da aikin girkin tare, tana yi tana share hawaye, da tayi tunanin zata tafi sai kuma ta tuna da maganar da Ammu tayi mata, hakanne yake sawa take ɗan ƙara dannar zuciyar ta tana yi.
Sai kusan tara suka gama suka kawo suka jere komai inda aka nuna musu, ɗaya bayan ɗaya mutanen gidan suka shiga fitowa suna halartar kan dinning ɗin kowa in ya zauna sai ya watsa musu banzan kallo, tsautsayi yasa Babyn baby hararar wani saurayi da yayi mata banza kallon ita kuma ta mayar masa da harara, murmushin gefen baki yayi yana ayyana abun da zaiyi mata, dan yaga alamar baƙuwa cc a gidan, fasa zama yayi sai ya juya tare da cewa ke ƙazama ki haɗo min komai da komai dake kan nan gurin ki kawo min ɗakina, yana faɗa ya juya ya nufi wajen wata ƙofa.
Babyn baby nunawa tayi bata ma san yana yi ba, wata budurwa wa ce tace lalle yarinyar nan baki da kunya baki san waye yaya Shuraim ba, yana miki magana amma kikayi banza dashi, to ki hanzarta kiyi abun da yace miki.
Nan ma shiru tayi, da sauri Maryam ta shiga zuzzuba masa tana murmushi tace "bata sani ba tunda jiya muka zo ai sai a hankali zamu wane da kowa, Baby gashi na zuba zo ki kai masa, miƙo mata ganin yanda Baby tayi yasa tayi saurin kwaɓar ta da ido tace "yauwa yi sauri, naga kaman can hanayar ya nufa.
"Dan Allah ko zaki nuna mata gurin bata san ko ina ba, tashi ƴar matashiyar budurwar tayi tace "muje amma kar ki kuma irin wannan yana magana koyi masa banza, tana maganar tana tafiya ita dai Baby binta kawai take a ƙufule, har suka ƙarasa, budurwar ta buɗe ɗakin, tana yin sallama yana bakin gado ya ɗago ya amsa ganin ba wace yaso gani ba yasa ya haɗe mata rai yace "wa yace ki shigo min ɗaki?
Taɓe baki tayi tace "ai ba hakannan na shigo ba, wacce ka kira na rako kuma yanzu zan barmaka ɗaki kayi haƙuri, tana faɗa ta juya ta fita daga ɗakin tana hararar Babyn baby tace ki shiga, fuska a murtuke ta shiga ko sallama batayi ba, tsayawa tayi a bakin ƙofar ita bata shiga ba ita bata zauna ba,
Daga inda yake ya ce "ni kike so nazo na karɓa ne?
Ƙarasawa tayi ta tsugunna ta ajiye masa a gaban sa, tana shirin tashi yace "ina zaki ai zama zakiyi kibani har sai na ƙoshi, bani kika harara ba,
Ɗagowa tayi ta kalle sa cike da rashin fahimtar me take nufi take kallon sa, ɗage mata gira yayi yace "ko bazaki yi bane in sauya da wani?
Ƙin amsa masa tayi saima janye kanta da tayi gefe.
"Hhhhh lallai yarinyar naga taki kalar, ki tashi kiyi abun da anace kafin inyi miki abun da zakiyi ta dole ko kina so ko bakya so, ganin ta kuma yin banza dashi yasa yasaka hannun sa duka biyu ya riƙo fuskar ta yana kallon ta yace "idan baki ban da hannun ki ba, zaki ban baki da baki yanzu nan.
Ƙwace fuskar ta tayi tana miƙewa tsaye zata juya ta fita yayi saurin jawo ta kansa yana miƙewa tsaye tare da rungume ta yana shirin juyo da ita, batasan loƙacin da ta aro wata jarumta ba saboda ya kaita ƙarshe, ture sa tayi ta ƙwace jikin ta tare da zagewa ta wanke masa fuska da mari, cikin ɓacin rai dan har hawaye ya fara zubo mata, ta nuna sa da yatsa tace "kai ɗan iskan ina ne acikin gidan ubanka kake shirin yin iskanci, ko nayi maka kama da irin ka, idiot useless ko iskan ci zanyi kayi min kaɗan wawa kawai mtssww tana kaiwa nan ta juya fuuu ta fice daga ɗakin tana goge hawaye.
Mamaki ne ya gama kashe shi yana dafe da fuskar sa har ta gama zazzaga masa ta fice batare da ya iya taɓuka komai ba, saida ta fita sannan ya dawo cikin hayyacin sa, abincin dake gaban sa yayi ball dashi, cikin tsantsar ɓacin rai ya kuma shafa gurin da ta mare sa, yana jinjina kai a hankali ya shiga cewa "mari this small girl is slapped me, ni, ni zaki mara, sai na nuna miki cikakken iskanci zakiyi bayani sai kin biya marin nan da kikayi min...
Babyn baby na fitowa barayi wajen dinning ɗin ba kawai ta wuce part ɗin su cikin sauri tana ta faman goge hawayen ta, tana shiga kawai ta zauna kan katifar ɗakin tare da fashewa da kuka, can kuma ta shiga laluben wayar ta amma bata ganta ba...
A can ɓangaren kuma Maryam nata jiran ta, shiru bata dawo ba, gashi me gidan ya fito daman so take tazo su gaieda kafin ya fita, saidai bata fito ba har suka fara cin abincin, ita kaɗai ta tsaya duk ta sallami kowa sannan ta koma kitchen ɗin, jin shirun yayi yawa ya sa ta nufi ɗakin su, tana shiga kuwa ta tarar da ita tana aikin kuka, nan hankalin ta ya tashi ta shiga tambayar ta, saidai bata iya ce mata komai ba, rabuwa tayi da ita dan abun nata ya fara ɓata mata rai wallahi ance tayi haƙuri tayi haƙuri amma taƙi tayi shiru salon ta jawowa kanta wata cutar, nan dai ta kuma bata haƙuri ta fito daga ɗakin ta koma can cikin falon dan jiran idan sun gana ta kwashe kayayyakin da