da kallo duk da ba wannan ne loƙacin da ya fara shigowa falon ba, saidai kuma duk shigowa sai ka samu abun da aka sauya a cikin falon,
"Ahh wata sabon gani ashe talaka na ganinka, Mas'ud baka da kirki wallahi mutuncin ka kaɗanne"
Dariya Alhaji ɗan Ijje yake yi irin tasu ta manya ta masu kuɗi, yana jinjina halin sa da irin waɗannan maganganun nasa, shi dai a kwai sa zolaya...,
Mutumin shima fuskar sa ɗauke da murmushi a kan kyakkyawar fuskar sa ya ƙaraso inda yake zaune yana miƙa masa hannun alamar suyi musabaha da sauri Alhaji ɗan Ijje shima ya miƙe yana miƙa masa sukayi musabaha, sannan Alhaji ɗan Ijje ya koma ya zauna shima mutumin kujera ya samu ya zauna yana fuskantar sa.
Alhajin Allah kana nan abunka ka manta damu kaci mutuncin abota wallahi duk da bansan dalilin ka na juya mana baya ba,
Alhaji ɗan Ijje ya ɗan sosa kai sannan yace; "Hmm ai kune Alhazai wane mu muna gefe, siyasa ta ɓoye ku, ya shirye-shiryen zaɓe kuma?
Saida ya ɗanyi jim kamar bazai ce masa komai ba, sai kuma can yace;zaɓe alahamdulillah, tunda kai ka guje mu me zai hana yanzu ka ƙara fitowa takarar ina tunanin yanzu baza a kuma samun matsala ba kamar da, saboda ada ɗinma laifin kane amma da tuni kasan kai zaka ci amma ka juya mana baya amma......
Hannu Alhaji ɗan Ijje ya ɗaga masa tare da cewa; dan Allah mubar wannan maganar tunda de komai ya wuce, yanzun ma ɗan wani abune ya kawo ni idan zai samu fa amma ba takura idan kuma da matsala shima abarsa.
Shiru yayi kamar yanda ya buƙata amma aransa baiji daɗin hakan da yayi masa ba, ko ba komai yakai wani matsayi da shi bai kai ba duk girman abotar da ke tsakanin su bai kamata ya ɗaga masa hannu ba a loƙacin da yake magana, amma duk da haka me makon ya nuna masa ɓacin ransa saima murmushin girma irin nasu na masu kuɗi da ya sakar masa yana me ɗaukar glass cups ɗin da aka kifesu akan plate juyo dasu yayi sannan ya ɗauki flaks ɗin tea ya tsiyaya a ciki sannan ya ɗauka ya miƙa masa, ba musu ya amsa,
Shima ya ɗauka yayi saida ya ɗan sha sannan ya ajiye, ya ƙara maida hankalin sa gare sa, sai yaga ya riƙe cup ɗin kawai bakai bakin sa ba,
Murmushi ya kuma yi har haƙoran sa na fitowa ya ɗan jinjina kai, sai kawai ya ce; "Ɗan Ijje inajin ka me yake tafe dakai kasan babban abune tunda har aka iya neman alfarma ta nasan ba ƙaramin abu bane,
Ajiye cup ɗin yayi sannan ya ɗago yana kallon sa ido cikin ido ya ce; "ALHAJI KAMAL" banaso wannan abubuwan su ringa faruwa na fahimci kamar kana min magana me harshen damo to ni bada wata manufa nazo gurin ka ba, akan ɓatan ɗana ne da akayi kidnaping shi da ɗan gidan Commisiona, shiyasa nazo inji ko kana da wata hanyar da zamu bi gurin gano inda suke ko kuma kasa ɗan wajen ka cikin lamarin tunda ku kuna faɗa aji, ba kamar mu ba.
"Jinjina kai yayi bayan jin abun da yafaɗa duk da yasan maganar amma tunda har yazo da kansa dole zai taimaka masa"
"To abokina nima komai na faɗa da wasa nake ma, daman naji maganar tun aranar amma yanzu gaskiya ni bazan iya cewa komai ba game da inda za'a same su, saidai ku ƙara haƙuri a cigaba da addu'a da neman inda ake tunanin zasu kasance daga nan zuwa nan da sati biyu ranar da za'a fara taron ƴan majalissu ranar MAHEER zai dawo Nigeria idan ya dawo sai a miƙa masa case ɗin nasan duk wanda ya ɗauke suma idan sukaji labari zasu dawo dasu in sha Allah.
Ajiyar zuciya ya sauke duk da baya tunanin zai iya jura har zuwa sati biyu besaka ɗansa a idon sa ba baisan halin da yake ciki ba dan yana jin kamar kafin loƙacin zasu iya cutar dashi, "Allah ya yarda dan wallahi abun yaban tsoro kuma da wasu mata ake zargi saboda sunɗan samu saɓani tsakanin su dashi a danger to shine ake zargin ko su suka ɗauke su to amma commissionana ya kirani yace ya kamasu kuma basu bane dan yana da tabbaci akansu yayi duk binciken da zaiye har ƙulle su yayi a sale amma ya gane basu ɗin bane kawai dai sun taka sahun ɓarawo ne,
"Ƴan mata kuma daman banda abunku ku rasa wazaku zarga sai mata me mata zasuyi dashi dan kawai wannan ɗan abun da ya faru a tsakanin su, nima naji labarin su bandai gansu ba, amma tunda naji labarin nasan baza su aikata ba, kawai dai yanzu abun ayi haƙuri a jira kiran su dan nasan dole zasu kira suce suna buƙatar wani abun mukuma tanan za'a samu damar cafke su.
"Nima abun da nake taso kenan naso su kira inji me suke so, amma shiru shiru har yanzu basu kira ba"
"Abokina kar ka wani damu babu abun da zasuyi musu, kunsan ku masu kuɗi daman sai kunyi haƙuri da irin waɗannan abubuwan da ƴan baƙin ciki zasuyi muku...
Ɗan hararar wasa yayi masa ya ce; "Idan mu masu kuɗi ne ku kuma sai akiraku dame, ai irin ku zasu farayiwa kafin mu koh ya ƙarasa maganar yana ɗan yin ƙaramar wasa ta alamun zolaya.
"Shima murmushin yayi sannan yace; mu da ko rabun ku bamuyi ba ina wasu kuɗi anan..... Nan dai sukai ta tsokanar junan su kamar kananun yara saboda abotace tun ta yarinta, shiyasa idan suka haɗu suna mantawa da sun girma, a haka suka ɗau loƙaci ne ɗan tsawo suna tattaunawa cike da tsokana har suka gama yayo masa rakiya bakin ƙofa sannan suka rabu.......
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*R, K, D, UNIVERSITY KANO*
Kamar yanda suka saba haɗuwa idan sun fito daga lecture yanzu haka duk sun haɗu su duka biyar ɗin amma ba gida zasu ba zasu wuce su farayin lunch saboda a cikin su akwai masu lecture ɗin yamma dan haka sai sun jira su zasu haɗu su tafi gida gaba ɗayan su, suna daf da shiga gurin suka hango wata yarin daga can gefe ta kifa kai tana ta kuka, da ɗan tazara tsakanin su amma ba sosai ba suna sai iya jiyo sautin kukan ta, duk tsayawa sukayi tare da kallon junan su. sai kawai suka wuce basu ce komai, har suka shiga sukayi order ɗin abun da suke son ci sannan sukaci agun sun ma daɗe suna ƴar hirar su sama sama dan a ƙalla sunkai kusan minti ashirin a gun, kafin Beenish ta kalli agogon dake hannun ta ta miƙe da sauri tace kai Aunty Babba wlh munyi late muyi sauri Allah yasa SIR SURAJ bai shiga ba, kar ya hana mu shiga.
Da sauri duk suka miƙe duk da ba dukan sune zasuyi attending ɗin ba amma atare suka baro wajen har suna ɗan haɗawa da sauri,
Suna fitowa garin sauri suka ci karo da wata yarinya da sauri taja da baya mutyar ta cikin kuka tace dan Allah kuyi haƙuri ban kula ba kanta a ƙasa tayi maganar kamar zata kuma fashewa da sabon kuka, bata jira cewar su na tayi sauri ta bi gefen su, tana shigewa ta kuma fashewa da kuka tana toshe bakin ta dan bata so sautin ya fito,
A kusan tare suka juya suna bin bayan ta da kallo, duk sun kasa ɗauke idon su akan ta.
'Aunty Babba ce tace; "ku wallahi wataran ku kuke jawa kanku raini da shishshiginku yanzu me ya shafe ku a ciki idan ita da mahaifin ta ne fa ko kuma saurayi ko mahaifiya ku zakuzo kuji kunya,
Beenish ce tace ;Aunty Babba..! ta kira sunan ta cikin wata irin murya me kama da fara ta jin haushi, "Wannan wace irin magana ce ita ma mace idan kuma abun da kike zargi ba haka bane idan ma hakane shi mahaifin nata me yasa zai musguna matan da har zata fito waje da baƙin ciki Allah yabasa amanar ta bawai dan ya musgunawa ƴar sa, kinsan duk abun da iyaye zasuyiwa ƴaƴan su da har ya wuce suyi musu hukuncin da zasuyi shi a cikin gida wannan ba daidai bane, domin su ƴaƴa da kike gani amana ce da Allah ya bawa iyaye amma wasu iyayen basa aiki da hakan dan Allah banason kina sawa ranki irin waɗannan tunanin, yanzu da ɗaya daga cikin mu kika gani zakiyi tunanin wani abu, nasan zuwa kawai zakiyi kiyi ƙoƙarin jin damuwar sa, to yanzu ma ki ƙadarta ɗaya daga cikin mune kije kiji damuwar ta damuwar ɗan uwa musulmi damuwar kace domin duk daga abu ɗaya muka fito, kar muga ɗan uwan mu cikin damuwa muyi tunanin ai damuwar sa damuwar sa, yazama dole musa a ranmu taimakon duk wanda muka gani cikin wani hali na damuwa muyi ƙoƙari iya bakin iyawar mu ganin muntayashi warware masa inda hali musanya shi cikin farin ciki, bawai sai abun da ya shafe mu ba indai akan wannan fanninne idan ka taimaki wani kai kuma Allah zai ta make ka ne a duk inda kake kusa wannan aranku ba da ita kaɗai nake ba da gaba ɗayan mu nake.
Jikin Aunty Babba ne yayi sanyi dan tasan gaskiya ta faɗa mata yanzu da ace ɗaya me yake cikin wannan halin har yake fitar da kuka irin wannan da kana ji kasan ba ƙaramar damuwa mutum yake ciki ba, da a cikin sune sai inda ƙarfin ta yaƙare,
Ameela ce tace; maganar ki gaskiya ne Beenish musamman ma irin natannan ki duba fa kigani tun kan mushiga yake kuka kuma har yanzu bata gama ba wayasan ma tun loƙacin da ta farayi.
Allah sarki wallahi nima taban tausayi yaya kinga yanda idon ta yayi ja, cewar Babyn baby.
Zee tace ba tsayawa zamuyi muna kace nace ba, muje gashi kuma ku zaku shiga lecture kuje mu bari muje wajen ta ni da Ameela,
"A'a ku muje tare kawai, babu komai, cewar Beenish,
A tare suka jera suka koma cikin restaurant, hangen idan zasu ganta suka fara, can suka hango ta kuma kifa kanta akan table ɗin ga abinci a gaban ta da tasa aka kawo mata kuma ba iya ci zatai ba,
Da ɗan saurin su suka ƙarasa inda take duk zagaye ta sukayi suna kallon ta na ƴan sakanni, Beenish ce ta jawo kujera ta zauna daf da ita.
"Assalamu alaiki, Ƙawata...
A hankali ƴar matashiyar budurwar ta ɗago da jajayen idon da kumatun ta da suka kukkumbura kallo ɗaya zakai mata kagane ba ƙaramin kuka ta sha ba,
Tana ɗagowa zata buɗi baki kenan Beenish ta toshe mata bakin ta, tana girgiza mata kai alamar kar tayi magana, sannan ta sa hannu ta fara goge mata hawayen da ya gama wanke mata fuska, abincin da ta jawo sai ta fara zuba mata ruwa da kanta ta bata, ba musu yarinyar ta karɓa dan tana buƙatar ruwan amma takasa sha da kanta,
Tana gama shan ruwan ta buɗe plate ɗin abincin priderice sai cabage da aka ɗan zuba a gefe, spoon ɗin ta ɗauka tafara bata a baki da farko haka tace bazata ci ba, saida taga ta haɗe rai sannan karɓa, bata daina bata ba saida taga taci sosai har yafi rabi sannan ta kuma bata ruwa ta sha da kanta,
Har yanzu babu wanda yayi mata magana, saida Beenish ta tabbatar ta ɗan samu nutsuwa sannan ta miƙe tare da dafa kafaɗunta ta ɗago ta tsaye.
"Muje koh.., ta kalli sauran tana kamo hannun yarinyar, jale jale yarinyar ta shiga binta, abun mamaki takasa tanka musu da komai bare tayi musu taurin kai ko ta tambaye su ina zasu, kawai ta bisu, amma har yanzu bata bar sauke ajiyar zuciya ba,
Can wani waje suka nufa da ba mutane, sannan ta zaunar da ita ta zauna agefen ta, suma sauran duk zama sukayi, amma gurin bai ishe su ba, Babyn baby da Barazana a tsaye suka tsaya,
Cikin muryar rarrashi Beenish tace; in badamuwa zamu iya jin damuwar ki, me yasa ki kuka haka,
Take hawaye ya ƙara cicciko mata idon.
"No don't cry my dear, ni fa tambayar ki kawai nayi, ki faɗan kawai in Allah ya yarda zamuyi ƙoƙari gurin share miki wannan hawayen,
Shiru tayi ta kasa cewa komai dan tana tsoron faɗa musu tazo ta ƙara jefa kanta cikin damuwar da tafi wacce take ciki,
"A gida akayi miki, wani abun. Zee ta tambaye ta,
Girgiza kai tayi alamun "a'a"
"Saurayi, ƙawa, ƴan uwa, maƙota, waye daga ciki yasaki zubar da hawaye.
A hankali ta girgiza kai ƴar ƙaramar Muryar ta tace; babu ko ɗaya ta faɗa cikin sanyi jiki.
"Kinga look at me, give me your attention.
Kamar yanda Beenish tace haka tayi ta haɗa hankalin ta guri ɗaya, tana fuskantar ta da kyau,
"Yauwa my lovely sister, ina so kisa aranki zamu magance miki matsalar matuƙar bata fi ƙarfin mu ba, kar kiji tsoro duk wanda yake neman shiga rayuwar ki ki gaya mana, zamu tsaya miki, in kuma matsalar kuɗi ce ki faɗa mana nawa kike so, kar kiji komai nan duk ƴan uwan ki ne da yayyan ki da ƙannen ki, ki ɗauka duk ciki ɗaya muka fito kigaya mana damuwar ki baza mu taɓa cutar dake ba.
Hawayen da take riƙewa ne ya ƙarasa sauko mata, tayi saurin saka hannu ta share, sosai taji zuciyar ta tayi mata sanyi ko basu magance mata damuwar ta ba, tasan ta haɗu da waɗanda suka damu da damuwar ta,
Nagode da kulawar ku, ina cikin babbar matsala amma bana tunanin zaku iya magance min ita amma duk da haka zan faɗa muku, saidai kuyi min alƙawari baza kubari maganar nan ta fita ba, domin zaku ƙara jawo min wani bala'in dan Allah ku rufa min asiri kar ku faɗawa kowa wannan yazama sirri tsakanina daku kumin alƙawari.
"Hmmm gaskiya bazamuyi miki alƙawari ba saboda bamu san abun da zaki faɗa ba, zamu iya jure ko baza mu iya ba, kawai dai ki faɗa ai munsan daidai kuma bazamuyi abun da zai sa ki ƙara cutuwa ba.
Ɗagowa tayi tana kallon Barazana dake mata wannan maganar. Zuciyar ta sai raya mata take ta faɗa musu ko karta faɗa musu,
Hannun ta Beenish ta kamo tasaka cikin nata, tun kan tayi magana ma yarinyar tace; wani lectura ne a makarantar nan ya takurawa rayuwa ta sau uku yana dawo dani baya kuma yana sawa ina ta ƙara asarar kuɗi kuma mahaifana bama su hali bane, yanzu kuma yace idan ban amince dashi ba sai yasa an kore ni daga makarantar gaba ɗaya duk shekarun da nayi a banza, kuma yace idan nasake na faɗa sai ya lalata min suna ya ɓatawa mahaifina suna, yanzu haka daga gurin sa nake ya matse ni da ƙyar na gudu da office ɗin sa, na rasa yanda zanyi dashi har gida yake bina, yai tayi min bazarana da rayuwa ta.... tana kawai nan ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Beenish dake gefen ta,
Gaba ɗayan su ransu in yayi dubu to ya ɓaci ɗaya bayan ɗaya, Beenish kam har idon ta saida ya kaɗa yayi ja saboda tsabar ɓacin rai, Barazana kam jikin ta ɓari kawai yake, Aunty Babba andunƙule hannu jira kawai take ta ɗagasa ta sauke sa akan bil'adama, Ameela kuma sai faman cije baki take ta miƙe tsaye tana zagaye agun, Babyn baby kuka kawai ta fashe da shi tana dan ita lamarin tsoro ma yabata,
A hankali Beenish ta janye ta daga jikin ta, ga mamakin su sai kawai ta kwashe ta da mari tana miƙewa tsaye, kowa saida ya saki baki yana kallon ta, dan basu taɓa kawo haka ba,
Da yatsa ta nunata cikin tsananin jin haushi tace; "kinayin irin wannan rayuwar shine har kika tsaya kika kasa gayawa kowa, kin gwammace aci mutuncin ki da na iyayen ki akan tonuwar asiri wani ƙaton banzan shekara uku kina fama da ƙunci a zuciyar ki, baki sa uwa baki da uba babu hukuma babu shugaban makaranta babu na gaba dashi, zaki zauna kina gani zaki kashe kanki a banza, wannan wane irin shirme ni, shiɗin annabi ne da zakina tsoron sa har haka ya isa yayi miki abun da Allah bai miki, duk da tsoron sa da kike nuna masa ai bai fasa yi miki komai ba, kuma bazai fasa ba, tunda kin maida shi mala'ikan ki, me yasa zaki zaɓi mutuwar ki... Hannu ta kuma kaiwa zata jawo ta, Barazana ta riƙeta tace; "Haba Beenish calm down man yanzu sai ki ƙara rikitata ai,
Huci kawai take zuciyar ta na tafar fasa ta daka mata tsawa tace; "Waye shi ya sunan sa uban waye ubansa acikin garinan, wane ɗan akuyar ne haka, waye...!!!!!
Cikin matsanan cin tashin hankali yarinyar cikin kuka da kiɗimewa, tace; SIR SURAJ NE...!!!!!!✍️✍️
[3/5, 11:47 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 11💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
___Cikin matsanan cin tashin hankali yarinyar cikin kuka da kiɗimewa, tace; SIR SURAJ NE...!!!
Cike da ɗumbin mamaki gaba ɗayan su suka bita da ido, jin sunan wanda ta ambata yasa su mutuwar tsaye dan saida numfashin su yaso ɗaukewa na wucin gadi kafin daga bisani sukayi saurin dawowa