x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - SU WAYE SU

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 196

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
su na dama tare da sara masa kowa hannun sa a saitin kansa yanda de akeyi idan za'ayi salute ɗin wani ne muƙamin, a tare suka sake sauke wa tare da ƙamewa ƙam baki suka sake haɗawa su ka ce; "Sorry Sir!!!

Wani irin kallo yake binsu dashi, hullar kansa dake ɗauke da tambarin sunan sa sai ƙasan tambarin da akayi star biyar ta ban girma, hannu yasa ya janye ta gefe ta dawo saitin kunne sa, facemask ɗin sa ya cire ya jefar dashi gefe, ainahin fuskar sa ta bayyana hmmm abun zan fara cewa shine Masha Allah domin Allah yayi halitta anan gurin fa, kana kallon sa zakace balarabe ne domin yanayin hasken sa da kuma gashin dake kwance a gefen fuskar sa hatta girar sa sun kusa haɗewa saboda yawan gashin gata baƙa ta wani lanƙwasa, yana da manyan ido ga gashin idon sa zara-zara da alama yana da baiwar gashi ga gemun sa da yasha gyara sai ya ƙarawa fuskar kyau sosai sannan hasken sa ya ƙara fitowa tubarkallah masha Allah de kawai zamu ce, amma yanayin halin da yake ciki na rashin annuri akan fuskar yanda ya haɗe ta tamau kamar baisan wani abu sakin fuska ba bare akai ga murmushi uwa uba kuma dariya,

Cikin ƙara ɗaure fuska idon sa har ya fara sauya launi dan tsatstsan baƙin cikin da yake ji, murya a dake ya ce" every body get ready to go and find out the solution, If not I will shoot you one by one,

"Okay Sir! Suka sake haɗa baki.

"kuma ku tabbatar kun dawo min da motar nan, akwai kaya da yawa a ciki, don't let missing the car and all about abun da duk yake cikin ta, duk wata boarder asaka matakan tsaro, da titina da gaɓar ruwa, duk inda akasan mota zatabi ku kira ku sanar da masu gurin su saka ido sosai idan akayi sake aka fita da Sir SMA daga cikin garin nan, ko ƙasar nan you are in trouble gaba ɗayan ku, sannan abi unguwa unguwa a fara checking duk inda ba yarda dashi ba ashiga ayi bincike sannan a rufe duk wasu kasunni da ma'aikatu daga yau zuwa gobe duk wanda ya fito a harbesa did you understanding what I'm saying right?

"Yes Sir"

"Good dividing your self in to four and go to work.

Nan suka fara raba kansu kamar yanda ya faɗa,

"Sergeant! Moohad! Daghfal! Gahyoor! Ya kira sunayen su da sauri.

Suma cikin sauri suka amsa da "Yes sir!!

"Sergeant, ka ɗau mutanen ka kubi duk wata madakatar ruwa.

"Moohad duk wajen da iyakar manyan tituna.

"Dhagfal, cikin unguwanni da bincika tashar jiragen ƙasa. And you Ghayoor a shiga duk wani dajika dake zagaye da nan., Sauran tawaga kuma ku kula da kasuwanni kada abari kowa ya buɗe shago duk wanda kuma ya fito a harbesa....

Ƙara sara masa sukayi suna na'am da duk umarnin da yayi, a take me kiran waya ya ɗauko wayar sa ya fara sanar da duk wata sanarwa da ta dace ayi, suma sauran duk wanda tawagar sa basu cika ba haka suka ringa kira suna sanar da duk wanda baya nan,

Fita suka farayi daga cikin gidan, anan akayi karo da su Beenish suna gurin da aka barsu su kaɗai basu kwa motsa ba suna gurin.

Wanine ya daka musu tsawa tare da cewa ku tashi muje...,

Miƙewa sukayi duk da babu walwala a tattare da su amma baza kace kuma a tsorace suke ba, duk tsayawa sukayi daga bayan su suna tura su da bundugun hannun su har sun kusa fita suna daf da fita dasu wani sojan ya ƙaraso da gudu ya ce; "Sir GA yana son ganin su.

Juya ƙyar su akayi aka juyo dasu sannan wanda ya sanar da saƙon ya saka su a gaba suka nufi inda yake, su kuma suka ƙarasa fita cikin sauri.

A cikin minti talatin sukayi duk wani shiri da zasuyi, tuni gari ya fara cika da sojoji ta ko ina, wasu motacin duk sunzo inda suka fita wasu suka fara barin gidan, haka can bakunan titi ma tuni an fara rufe hanyoyi masu gaɓar ruwa ma ansanar da su sun fara aiwatar da nasu aikin, duk yaji labarin wanda aka ɗauke sai ya jijjiga da mamaki,

Cikin farfajiyar gurin duk ta doɗe babu kowa duk sun fita yawan cin mutanen gidan kuma tuni ansaka sun koma cikin gidan gurin ya rage daga shi sai wasu mutum huɗu dake take masa baya sai kuma ƴan tsirarun sojoji suma kuma daman masu tsaron gidanne, sai kuma su frBeenish da akasa suka zube a ƙasa suka tsugunna a gaban RK.

Tunda ya sallame su ya samu kujera ya zauna tare da ɗora ƙafafun sa akan wata kujerar yana dudduba wayar da ya karɓa ta SMA.

Da hannu yayi wa mutanen da suke bayan sa alamar da su basa guri, matsawa sukayi na gefen sa kuma ya kalle sa ya kuma kallon wani guri sannan ya nuna masa cikin gidan, nan ya fahimci me yake nufi, cikin gidan ya shiga, suna zaune agun babu wanda yace uffan, ba jimawa ya kuma fitowa hannun sa ɗauke da leda me ɗan girma, a gaban sa ya ajiye jakar, batare da ya kalle su ba, yace; "Basu"

Buɗe ledar yayi, ya zaro wani yadi sai ya miƙawa Aunty Babba dake gaban sa haka yaringa zaro wa yana miƙa musu, duk karɓa sukayi saidai babu wanda yayi yunƙurin ware sa,

Miƙewa yayi daga kujerar ba tare da ya kalli inda suke ba, "ka kai su inda suke.. yana kaiwa nan yayi gaba.

Yana tafiya, yace ku saka mana, ku tashi mu tafi.

Sai loƙacin suka ware duk da sun san meye amma suka ƙi buɗewa sai yanzu, hijabai ne kala kala kowa da kalar tasa, miƙewa sukayi suka saka a jikin su duk kuwa yayi musu kyau sai suka canza kamanni kamar basu ba,

Har yanzu babu wanda ya ce komai a cikin su, saida suka miƙe ma sannan Ameela tace Babyn baby ɗauko mana jakunkunan mu, gurin da suka hango mayafen nasu ta nufa taje ta kwaso musu duk wani abun su amma bata ɗauko mayafen ba jakunkunan kawai ta ɗauko sai spray ɗin ta da hango ƙasan kujerar, har ta ɗauko zata miƙe ta hangi wani ɗan kunnen gold ware ɗaya ɗauko sa tayi dan kallo ɗaya tayi masa ta gane ta gansa a kunnen Faheema riƙewa tayi a hannun ta sannan ta juya tabi bayan su dan har sun ɗanyi gaba ma,

A cikin wata mota aka ɗauke su tasu kuma akasa wani yabi su da ita abaya, Saida suka hau titi sannan sojan yace musu wacce unguwar ne?

"Sambas road, Barazana ta faɗa masa.

Da kwatan ce suka ƙarasa gidan ya sauke su, a bakin gate ɗin, duk a gajiye suka fito daga motar, zuge gate ɗin sukayi, wanda ke binsu da motar su ya shigar musu da ita compound ɗin gidan baida girma dan haka yana shiga yayi musu parking ɗin ta, sannan ya fito, loƙacin da ya fito kuma suma duk sun shigo suna shirin shigewa ma, bayan su yabi da kallo yana kallon bombom ɗin su duk da a hijabai suke amma hakan bai hanasa ƙura musu ido ba,

Barazana ce ta juyo jin kamar bataji fitar sa ba, tursu tayi ta tsaya ganin yanda ya zubawa sauran ido ko ƙiftawa ma bayayi.

"Wait..!

Duk tsayawa sukayi suna kallon ta, tare da kallon inda sukaga tana kallo, suna kallon sa yayi saurin janye idon sa cike da kwaɗaituwa da su ji yake kamar yaje ya rungume su.

"Me ya faru? Beenish ta tambayi Zee.

Batare da ta basu amsa ba tayi gaba Saida tayi taku kamar uku sannan tace"ɗan iska ne kunga kallon da yake faman binmu dashi..

"Aunty Babba kuji da shi wallahi nagaji da yawa bari in shiga daga ciki, inji Beenish..

Aunty Babba ce tace ba matsala kuma kuje bari inje ni, ta faɗa tana kallon su Ameela da Babyn baby, bayan Beenish suka bi, ita kuma tabi bayan barazana da har taje gurin sa.

"Kai me kake kallo? Wani kallo ya watsawa Barazana, yana kawar da kai yace; kaya mana.

Bai ankara ba kawai yaji ta wanke sa da mari, Aunty Babba ma na ƙarasowa ta sauke masa nata, dafe fuska yayi ransa a ɓace ya ɗago zai rama Aunty Babba ta damƙi hannun sa, tace kar ka kuskura malam tun da kyan ganin ka ka kama hanya ka bar wajen nan kafin mu canza maka kamanni wawa kawai... Tana fadar haka saki hannun sa,

Barazana tace "ko ba kaya ba zakaci kutumar uban ka ne waɗannan kayayyakin sunfi ƙarfin uban ka ma baranta na kai, daman iskan ci aka ce kazo kayi mana, wallahi kaci sa'a amma da saina tsiyayar maka da idanu anan gurin wawa kawai a jawo, na mamajo kwarton banza kwarton wofi....

Kawai kallon su yake amma ya kasa taɓuka komai saboda tunawa da yanda yaga suna faɗa ɗazu yasan yanzu shi kaɗaine kuma bashi da komai da zai tsorata su shi kar yaje su illata sa, shiyasa ya yafawa kansa ruwan sanyi cikin salama ba tare da yace musu komai ba, sum sum yabi gefen su yana girgiza kai, abun da ya iyayi kenan ya wuce ya fita daga gidan.

Saida suka ga fitar sa sannan suka juya suka shiga ciki, suna tafiya suna ci gaba da surfa masa masifa sai kace yana gurin har yanzu.


*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*Hajja Mama*

Gudu kawai take shararawa akan hanyar ta sai motoci uku da suke bin bayan ta, motar da aka kawo RK ita take tuƙawa, gudu suke sosai kai kace zasu kife saboda tsabar gudu,

Basu tsaya ko ina ba, saida suka zo inda zasu zo loƙacin da suka zo gari ya ɗan fara washewa dan sallar asuba ma a hanya sukayi ta, duk fitowa sukayi daga motocin buɗe, bayan motar taje ta buɗe, saiga wani babban mutum a ciki sai kuma budurwa duk a kwance alamun de kamar a sume suke, macen ta fara ɗagowa sai loƙacin naga ashe Faheema ce, ɗayan kuma de SMA ne.

Kamasu sukayi duk suka sakasu a cikin jirgin ruwan, sannan ta buɗe booth ɗin motar saga wasu manyan jakunkuna guda uku da ƙyar ma suka iya ɗagosu suka saka a cikin jirgin ruwan, saida suka tabbatar da sun ɗauki duk wani abun da suka san zasu ɗauka, sannan Hajja mama tace suyi gaba zata biyo su su tsaya a bakin ruwan furjaj haka kuwa sukayi suka tuƙa sukayi gaba saida da taga sunyi nisa ma sannan ta kuma shiga motar ita sa sauran ta wagar suka kuma juyawa hanyar da suka biyo ta cikin dajika suka ringa bi, saida sukayi nisa su masu motocin sukayi wata hanyar daban ita kuma taci gada da tafiya, saida tayi nisa sosai ta saita wata hanya sannan ta tsayar da motar cikin sauri ta fito daga ciki wata igiya me ƙwari ta ɗauko a ciki, sai taje ta ɗauro bayan motar dashi sannan taje jikin wata bishiya ta ɗaure ajiki, dawowa tayi ta shiga motar ta tayar da ita sannan ta kuma fitowa ta samu wani ƙaton dutse me nauyi ta ɗora sa akan total ɗin motar sai ta kunna giya motar na ta ƙara, da sauri ta fita ta rufe motar sannan taje wajen bishiyar ta kunce ɗaurin da tayi nan kwa mota ta tafi da gudu kamar da mutum a ciki daman hanaya ce street dan haka tafiya kawai take.

Tana ganin tafiyar ta juya da gudun gaske tabi wata hanya, wani rami ta shiga shima saida ta ɗanyi tafiya sannan tazo wajen wani ruwa kamar ɗan ƙaramin kogo haka gurin yake sai kawai tayi tsalle ta faɗa ciki, ashe ruwan me yawa ne, saida tayi kwana saiga shi ya bayyana me yawa, iyo kawai take kamar kifi, ko ɗagowa ma batayi saboda tsabar ƙwarewa, saida tayi tafiya me ɗan nisa sannan ta kawo bakin ruwan da tace musu su haɗu, tana fitowa ko kaya bata sauya ba, ta shiga jirgin suka ci gaba da tafiya.


*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*SOKOTO*

Wani babban gida ne da yafi ko wane gida girma a unguwar, babban layi ne saidai kuma ya haɗa da ƙananun gidaje masu ƙyauraye, unguwar de bazaka ce mata irin ta masu kuɗi ba kuma bazaka ce mata gaba ɗaya talakawa bane, saidai akwai gidajen da kallo ɗaya zakayi musu tunda ga waje zaka fahimci talakawan ne,

Ga cikowar yara da suke ta shige da fice har ma da manyan, ga masu abubuwan siyar wa, irin su me kifi masu mangwaro da masu da kuma shaguna, duk ko inade gashi nan unguwar a cike take da mutane.

Wata zan kaɗeɗiyar budurwa ce ta fito daga cikin gidan cikin takun ta naji da kai ga wata uwar riga da ta matse ta ta fitar mata da shap kamar ajikin aka ɗin ka ta, ta wani tokara ɗan kwalli tayi ture kaga tsiya sai kuma kitson ƙarin gashi da ta zubo da shi gefen fuskar ta, ga wata ɓullar hanci da ta saka abun hanci bakin ta tayi masa ado da baƙin ƙwalli, tunda ta fito daga cikin gidan ake binta da kallo.

Ita kwa ko ajikin ta tafiyar ta kawai take mayafi akan kafaɗa shima kuma a tattare da shi da babu duk ɗaya, sai ƴar site bag ɗin ta da ta saƙala tana wani yaryarfa hannu haka take ta keta mutane hankalin ta kwance, mutanen kirki suyi ala wadarai da ita saboda inda sabo ta saba kullum a haka take fitowa, masu irin halin ta kuma suna ta yabawa aransu dan babu wanda ya isa ya tunkare ta saboda da bala'in ta.

"Sunnu da zuwa!
Wani ya faɗa loƙacin da tazo bakin wani shago.

Ko kallan inda taji anyi maganar batayi ba bare ta kula sa,

Wani gida me ƴar ƙaramar ƙofa naga ta tura ta shiga, nide binta nake kawai dan ban taɓa tunanin a yanayin ta zata iya shiga wannan gida ba,

Tura kofar ƙyauran tayi ta shiga ko sallama babu, zata wuce kenan daga wani ɗaki dake cikin zauran a kace; "Fauziyya!

Shiru tayi kamar bata ji ba taci gaba da tafiyar ta, tana turo baki.

Tsawa ya daka mata yace "baki ji ni bane?

"Na'am" ta amsa ciki-ciki tana ƙara turo baki gaba ta koma da baya ta tsaya a bakin ƙofar...

"Daga ina kike tun safe sai yanzu!

"Gidan su Salma naje fa...

"Yanzu ke dan Allah kinyiwa kanki a dalci kullum sai nayi miki faɗa amma a banza na rabaki da wannan gidan amma kinƙi kiji, ki tsaya a matsayin ki amma kin ɗau ƙarya kin ɗorawa kanki ina ke ina yaran gidan nan, wallahi ina jiye miki ranar da zaki zo kina da nasani, ke har abada bakya jin magana, to wallahi zanyi maganin ki......

"A'a a'a me kuma tayi daga dawowar ta zaka tare ta kana mata masifa Ali ka kiyaye ni, kai kullum cikin takurawa yarinyar nan kake me ta tsare maka, to wallahi baza ta daina zuwa, shiga cikin gidan yanzu ta fara ya za'ayi anayi mana abun arziki mutanen nan kullum da arziƙi suke binmu amma kai da sharri kake bin su to wallahi a hir ɗinka baka isa ka hana min yarinya walwala ba, ehe, ke wuce mu tafi.

"Habiba kije kuyi abun da kukaga dama idan yarinyar nan ta lalace ke zaki zo kina kuka da idon ki wallahi kar kice zaki nemi inda, kije ki ci gaba da ɗaure mata gindi tayi abun da take so, kwaɗayi mabuɗin wahala ne, duk wanda ya hau motar kwaɗayi zata kasa tasha ta baro sa.

"Saidai ta baro ka wallahi aniyar ka ta bika, me baƙin baki, kai baka nemo ka kawo mana ba kuma yarinya ta fita tana ɗan samo mana abun lasawa a baki shine kake mana baƙin ciki to agani akan me mugun baki, tana faɗar haka bata jira cewar saba taja ƴar ta suka shige ciki..

"Dattijon mutumin girgiza kai kawai yayi yace rayuwa ce wataran sai labari Allah ya shirya ku gaba ɗayan ku baku san rayuwa bane shiyasa duniyar kuka zo ta ishe ku riga da wando harda zanin ɗaurawa, littafin sa ya jawo yaci gaba da karatun da yake.

"Ke kuma banza da taguwar zuciya meye na kuka zaki zauna ranki na ɓaci, muje ciki kici abinci,

Tsakar gidan kaca kaca yake inajin ma kwanan sa biyu baiga shara ba ƙudaje sai yawo suke ga wanke wanke da aka tare gefen rariya ƙudaje nabi ba'a wanke ba...

Amma ga mamakina sai gani nayi an ɗauko mata gasashshiyar kaza sai coke da yake ta ɗarin sanyi haka tazo ta ajiye mata a gaban ta, tace maza kici, ga wayar ki can naga kamar Sabeer ne ke kiran ki na ɗaga de nace masa kin fita, da farko ma ya ɗauka kece ashe be gane muryar ta ba, kin san har yanzu murya ta kamar ta ƴan mata shiyasa ba'a ganewa indai na ɗaga miki waya (subhanallah wai uwa ce ke faɗar haka, kuma wallahi a gaske na akwai Allah ya shirya)

Dariya yarinyar tayi tace "ai mama dama kince masa banda lafiya, kinsan idan yazo bazai zo hannu rabbana ba zai taho mana da ɗan kayan ciye ciye,

"Eh wlh kuma fa hakane wallahi amma akwai wataran in ba yau.

Da kanta ta tashi take ta ɗauko mata wayar ta ƙirar Iphone me tambarin apple 11 pro ce,

Karɓa tayi tana cewa "nace fa kidaina ɗaukar min wayar nan kar kije ki fasa min tsada ne da ita kinsan dai wuyar da naci kafin a bani ita.

Bakiga riƙon da nayi mata ba, da hannu biyu fa na riƙe...

Shiru tayi tana daddana wayar tana yagar kazar ta, bata gama bama ta miƙe tsaye da sauri, umma bari inje Salma na kirana a waje zamu je wajen wani party bazan dawo da wuri ba, tana kaiwa nan tayi gaba bata jira cewar umman tata ba, amma saboda asara sai itama uwar ta miƙe da sauri tana cewa to a dawo lafiya Allah yasa a yo mana babban kamu, tuni ta fice amma har waje tabita tana
End Ads