mamakin abun da ta faɗa, itama Zee ɗin baki sake take binta da kallo irin wacece wannan kuma?
Tun kan kowa ma yayi magana, Maryam ta damƙi hannun Rabi tace "sakar ta, babu inda zakije da ita!
"Idan ƴarki ce sai ki gaya min, dalla malama sakar ni ko kinga na kulaki tunda nazo wajen nan, idan na bar kasuwa ko sauti banayi mata, na riga da na gama dake, bani da loƙacin yanzu kema duk abun da sakije kiyi kiyi, dan babu uban da ya isa ya hanani tafiya da jikata, ko kema kinzo ki ɗau fansa ne akan su, in ba hakaba me ya kawo ki.....
"Ni na kawo ta! Sukaji an bata amsa ta baya,
Duk juyawa sukayi suna kallon ta, ko wanne fuskar sa ɗauke da mamaki,
Musamman Rabi tafi kowa tsorata da ganin ta, batasan loƙacin da ta saki hannun Barazana ba.
Barka da zuwa Hajiya gaskiya kinji saurin ƙarasowa, to kinga dai abun dake faruwa gasu nan duk sunzo su tarwatsa mana yara...
Ƙayataccen murmushin nan nata ta saki tana binsu da kallo tare da sauke idon ta akan Bulama, suna haɗa ido yayi saurin kawar da kansa gefe, shima ba ƙaramin mamaki yayi ba da ganin ta..
Saida ta gama kallon kowa sannan tace "Zainab ko? Ta kalli Barazana, kai kawai Barazana ta ɗaga mata, shima dan yasan ta.
To ga kakarki nan zaki iya binta idan kina so, amma ki sani zaki zauna da muguwar mata ne maci amana, Ke kuma Beenish nasan antaɓa baki labarin me aikin mahaifiyar ki to gata nan itace ne aikin nata kuma kakar ƙawar ki, wanann kuma da kuke gani a gaban ku duk kusan shine maƙasudin faruwar komai shi yajawo kuka tsinci rayuwar ku a haka kamar yanda naji labari babban makashi ne ya kashe rayuka da dama..
A fusace Aunty Babba tayo kanta kamar zata kwashe ta da mari tana huci tace "Ƙarya kike wallahi kuma ki iya bakin ki kisan a inda kike wallahi duk wanda ya kuma gayawa Uncle ɗina wata maganar banza yana dangantashi da mugaye laifuka to wallahi sai nayi ƙasa ƙasa da mutum agurin nan na rantse da me busan lumfashi...
"Tunda ta fara maganar Ameela ta damƙe idon ta tana ƙanƙame hannun ta, ji tayi ta kasa jurewa har sai da itama ta dakawa Aunty Babba tsawa, tace "Aunty Babba kema ki iya bakin ki uwa uwa ce kuma mahaifiy.....da sauri tayi shiru tana ƙara damƙe idon ta tana kawar da kanta gefe,
Sosai Hajiya Dannar taji daɗi da yanda Ameela ta nuna jin haushin ta akan angaya mata magana, har da cewa Uwa uwa ce bayan kuma tace bazata taɓa kiran ta da hakan ba sai gashi yau ta kira hakan ya mata daɗi...
Aunty Babba tayi nisa bata jin kira indai akan Uncle ɗin ta ne, itama cikin hayayyakowar tace "an faɗa ɗin ke bakiji abin da suke ce masa ba....
Bulamane yayi saurin riƙe ta sai kawai ya fara hawayen ƙarya yace "Sweetheart kar ki kuma cewa komai dan zasu iya kashe mu anan gurin, hakan da akayi sai ya tuna min da loƙacin da na gansu a cikin gidan ku, sune fa suka kashe mana Dadyn mu bawan Allah baiji ba bai gani ba, kema dan na ɗauke nine shiyasa basu san kina raye ba da tuni sun kashe ki sai ranar da nazo ina ta neman ki anan suka gano ke ƴar Olowasun ce shina sukai ta bibbiyata saida suka ga shigowa ta gidan nan sannan suka biyo ni, da baki zo bama da tuni sun kashe ni kinga dai yanda ta shaƙe ni mugaye ne su duka ukunnan duk bakin su ɗaya akwai uban gidan su da yake saka su yana basu kuɗi bakuga yanda suke tara kuɗi ba kuma duk basu da mazajen aure zaman kansu suke kawai, sweetheart kiyi abun da zakiyi mubar gurin nan bana so su kashe min ke ke nake ta jira banyi aure ba har yanzu saboda alƙawarin da na ɗaukar wa Dady nakasa karyawa, yana faɗar haka ya rungume ta, kallon ɓangaren da su Rabi suke yayi tare da ƙifta musu ido ɗaya..,✍️✍️
More comment more typing 🤗
No comment No typing 😎
Gaskiya ba ƙarya ina godiya sosai da comments ɗinku naji daɗin na jiya ta kowane fanni ambiyani, daga WhatsApp har facebook ba laifi ansamu comment sosai, haka ake so dan Allah aƙara dagewa dayin hakan na Kuma ƙara min ƙwarin gwiwa, dande yau na fita ne amma da nayi yafi haka Wlh...
[3/5, 12:32 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 33💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah..✍️
___Cike da ɗumbin mamaki duk suke bin sa da kallon jin ƙaryar da yake kwararowa,
Cikin matsanancin ɓacin rai Aunty Babba ta ƙwace jikin ta daga gurin sa, kallon sa tayi murayar ta kamar zatayi kuka tace "Uncle abun da kake gaya min da gaske ne waɗannan ne suka kashe min Dady? Nima kuma so suke su kashe ni? Kaima kuma haka? Ta jero masa waɗannan tambayoyin"
Cike da ƙara basarwa yace "na taɓa yi miki ƙarya ne ko zan faɗa miki abun da bahaka bane,
"Ƙarya yake munafiki shi yakashe shi ba wani ba" cewar Maryama"
Da gudu Aunty Babba tayi kanta zata rufe ta da duka, Su Beenish sukayi saurin rirriƙarts ko da inda ya riƙe, amma sai fisge fisge takeyi tana musu ihu da ƙatuwar muryar ta "Ku sake ni sai na kashe su wallahi sai na kashe su da hannun ku sake kuma zan kashe ku idan baku sake ni ba.
Babu wacce tayi yunƙurin sakin ta saima ƙara riƙeta da sukayi gam duk yanda taso taƙwace kasawa tayi,
Ci gaba tayi da ihun ta da hauka, tana cikin haka Barazana ta kwashe ta da mari cikin faɗa tace "wai ke meye hakanne baza ki tsaya ki saurari mutane ba sai faman hauka kikeyi wa mutane, ya kamata ai ki fara bincike bawai kawai daga gaya miki magana ki hau ki zauna ba, duk a cikin su waye yayi miki kana da makashi shi da aka faɗi abun da yake meyasa baki yarda sai shi da yagaya miki zaki yarda, a wannan maganar tasa akwai rashin gaskiya a ciki, ki bari zamu bi komai a sannu koda ace suɗinne zamu lalubo su mu da kanmu zamu ɗaukar miki fansar da duk wani abu da ya dace ayi, ya kamata ki nutsu ki dawo cikin hayyacin ki...
Duk wannan maganar da Zee take mata batayi tasirin a zuciyar ta ba sai ma ci gaba da abun da take tayi tana zazzagawa Zee bala'i da take yi harda su zagi.
Cikin fara jin haushin abun da take musu yasa suka sake ta, cikin ɓacin rai Ameela tace gaki ga su inbaki fasa kashe su baki haifu ba mtsww dan kinga ana ta bako haƙuri mtsww ta kuma daka mata tsaki tana hararar ta.
Still bata daddara ba ta kuma yin kansu zata damƙo Dannar, Dannar ta kwashe ta da mari tana sauke wa Ameela ma ta turata gefe tace "Rameca ya ishe ki haka bama son hauka wai ina hankalin ki ya tafi dafe fuskar ta tana me jin wani irin abu na taso mata daga ƙasan ranta...
Bulama ransa fari ƙal yanda suke wannan dramar abun sai ya ƙayatar dashi, saida yaga de dagaske yarinyar baya da hankali ya yarda da abun da yaga mata, shima kuma yana son tafiya batare da wani abu ya faru ba.
Dan haka sai ya riƙo hannun ta yana janyo ta gaba ɗayan ta, cikin sigar rarrashi yace ki kwantar da hankalin ki tundade gani nazo kizo mutafi muyi auren mu inbaki kulawa da kariya babu wanda ya isa yazo ya taɓa ki, mutafi..
"Cikin kuka tace "kana nufin haka zan barsu ba wallahi sai na ramawa mahaifina abun da sukayi masa, nima babu wanda zan bari da ransa tunda suka rabasa da ransa,
"Eh naji zaki rama amma ki bari ba yanzu zamu san abunyi daga baya bayan munyi auren mu sai mu shigar da case ɗin koto sai hukuma ta yanke musu hukunci da ya dace da su, haka yai tayi mata huɗubar ƙarya harta yarda, ta daina yi musu haukan kuma ta yarda zata bishi.
Hannun ta ya kamo yana kallon su yace baiwa kowa magana ba saida ido da yake binsu, kallon ta ya kumayi sannan yace muje gaba yayi yana ɗan jan hannun ta, nan ta fara binsa a baya....
"Idan kika saka ƙafar ki kika fita daga gidan nan kin fita kenan kuma sai kinyi da nasani ina mai baki shawara da kiyi tunanin kafin ki yanke hukuncin haka, idan kika fita ko me yayi miki kar ki kuma nemansu ko a hanya kika gansu kar ki nuna kin san su nagaya miki wannan, Hajiya Dannar ke yin wannan maganar.
Beenish tayi saurin cewa "Ammu ki barta ta tafi ɗin zata gane kuren ta ne wallahi bantaɓa tunanin haka daga gare ki, koda ace hakan ya faru gaskiya ne meye laifin mu a ciki sune da laifi su zaki tuhuma bakwai mu ba yanda muka taso muke zaune mukaaɗai bai kamata ace a ɗan ƙanƙanan loƙaci wani ya juya miki tunani kin zaɓi ki bishi mu ki barmu to kinyi daidai kiyi yanda kike so, kamar yanda ta faɗa indai kika bisa kin bisa kenan ba mu ba ke ko a hanya kar ki nuna kinsan mu tunda haka kika zaɓa muma zamu watsar dake kamar yanda kikayi.....,
Cak Aunty Babba ta tsaya tana tunani sosai jikin ta yayi sanyi tasan bata kyauta ba abun da take shirin yi, ji tayi kamar ta rabu dashi ta zauna dashi amma kuma idan ta tuna da son da take masa sai taji gwanda ta rabu da kowa ma ta zauna da shi, gashi kuma maganganun su sun ɗan tsaya mata a rai wata zuciyar kuma sai tace indai ma tana tare dashi wane kuma da nasani zatayi da har zata neme su, zai aure ta suma bar ƙasar suje suyi auren su su haifi ƴaƴan su suyi rayuwa cikin farin ciki, ba ta tsaya nan suna dambe da al'umma ba,
Jin tayi shiru yasa Bulama kallon yana kashe mata ido yace "Rameca in tafi ne zaki zauna tare dasu? Kije ni sai intafi kuma idan na tafi kashe kaina zanyi tunda kema kin guje ni, shikenan nagode ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin cire hannun sa daga nata, da sauri ta riƙe sa tana girgiza kai tace "a'a wallahi babu inda zan tsaya babu me rabani dakai na yarda na zaɓeka zan zauna da kai,
Murmushin jin daɗi ya kumayi a ransa sannan yaja hannun ta saida suka kai ga fita sannan ya ɗan juyo idon sa cikin na Maryam ya ɗaga mata gira tare da kashe mata ido yana jinjina kai irin ya kika gani ko zaki dakatar da hakan? Harda ɗaga hannun sa ɗaya ya sara musu sannan yayi gaba ranshi fess.
Basu ɗauke idon su aka Aunty Babba saida sukaga ta fita ji tayi sukayi kamar almara kamar mafarki suke yau ɗaya Aunty Babba ta canza musu ya zaɓi wani akan su..
Rabi ki fice daga gurin nan kema idan kuma tare da ita zaki tafi ga gatanan ki sani itama idan ta tafi kenan.
"Ammu kima daina wannan maganar babu inda zani saboda babu wanda nasani kuma koda na sani ma hakan bazai sa in rabu da ƴan uwana ba, zan zauna tare da su..✍️✍️
Banyi alƙawari ba idan na samu enough time zaku iya ganin update gobe, wallahi yau bansan meke damuna ba nakasa rubutun kwata kwata tun safe nake abu ɗaya amma ɗan wannan nayi har yanzu, nama rasa me zan rubuta 😅 ku tayani da addu'a 🙏🥰
[3/5, 12:33 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 34💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah..✍️
__"Ammu kima daina wannan maganar babu inda zani saboda babu wanda nasani kuma koda na sani ma hakan bazai sa in rabu da ƴan uwana ba, zan zauna tare da su....
A zabure Hajiya Rabi ta kalle ta jin maganar da tayi, cikin inda inda ta ce; "Zainab kar kice haka, ki zo mu tafi idan kika zauna anan za su cutar da ke, baza su bar ki ba.
Wani kallo barazana ta wurga mata na uku saura kwata tana taɓe baki cike da mamaki, kawar da kai gefe tayi ta ce; "ke nifa bansan ki ba, kima daina kira na da jikarki domin ni na jikar ki bace banda wata kaka a duniyar nan uwa ta da ubana kawai na sani, zaki iya tafiya tana kaiwa nan ta daka tsaki tare da barin wajen ma gaba ɗaya.
Da sauri Rabi tayi kanta zata riƙo ta Dannar ta dakatar da ita tare da cewa; "kar ki kuskura ki kuma zuwa inda take kamar yanda ta faɗa miki ita ɗin ba jikar ki bace dan haka ki gaggauta barin gidan nan yanzu yanzun nan, idan kuma ba haka ba zan miki abun da bakya tunani, kuma ko da wasa kar na sake ganin ƙafar ki a cikin gidan nan dan sai nasaka su sunyi miki dukan dan bazaki ƙara moruwa ba, sannan maganar da nayi miki kwanakin da na baki sun kusa ƙarewa idan bakiyi wani abun akai ba zaki ga abun da zai biyo baya ki fita daga cikin gidan nan, ta ƙarasa maganar tana nuna mata hanyar fita.
Harara Rabi ta watsa mata tare da cewa; "ai daman ko baki faɗa ba zan bar gidan basai kin kore ni ba, amma ki sani nima ki saurari nawa shirin kuma dawowa kamar nayi na gama da dan sai na dawo idan kin isa kar ki bari na fita da rai daga cikin gidan, tana gama faɗa mata haka tayi gaba fuuuu kamar ledar da iska ta kwaso ta..
Babu wanda ya tanka mata kuwa bare a dakatar da ita har ta fita, saida ta fita Dannar ta sauke numfashi tana furzar da iska daga bakin ta, maida duban ta tayi ga Ameela tana shirin yi mata magana ma kawai ta haɗe rai tare da juyawa ita ma ta bar wajen.
Hakan yasa Dannar haɗiye maganar da taso yi, sai kawai ta kalli Maryam ta ce; "Maryama ki kula da su danni juyawa zanyi yanzu akwai gurin da zanje yanzu ana jira na, tana faɗa mata ta kuma ɗorawa da cewa "Beenish ga baƙuwa nan zata zauna daku zuwa wani loƙacin ku girmama ta sannan duk wata shawara da ta dace zaku iya yi da ita ku ɗauke ta kamar uwa kunji ni?
Jinjina mata kai duk sukayi cike da gamsuwa da baya nin da tayi musu, bata kuma ce mu su komai ba sai sallama da ta kuma yi mu su ta tafi, bata bi takan Ameela ba.
Beenish ce ta kalli Maryam sai ta ce "yauwa zaki iya shiga wancen ɗakin extra ne sai ki kai kayan ki can, kafin zuwa da safe dai mu nunnuna miki wasu abubuwan, idan da abun da kike buƙata ga ɗakin mu nan sai kiyi mana magana.
Wani murmushi jin daɗi Maryam tayi jin yanda yarinyar take mata magana ba wani harigido ba rashin dacewa ko nuna rashin sanayya, sai kawai ta ce; "Okay nagode babu abun da nake buƙata, ai da akwai toilet a ciki ko?
"Eh akwai komai a cikin, Babyn baby ta bata amsa.
Murmushi tayi mata tana binta da kallon tausayi sai take ganin ta kamar maman ta duk da ba daɗewa sukayi tare ba amma bata manta kamannin ta ba.
Juyawa tayi ta nufi ɗakin tana kuma yi musu godiya, har zata shiga, Beenish tayi saurin cewa "Me kike son ci a dafa miki?
Ɗan juyowa tayi sai ta girgiza kai tare da cewa "wallahi babu komai kar ki damu naci abinci a hanya, ni yanzu kwanciya kawai nake son yi saboda gajiyar hanya.
Bata takura ta ba akan sai taci daga nan sukayi sallama, ta ƙarasa shigewa ɗakin.
Tana shigewa Beenish ta zauna akan kujerar dake kusa da ita tare da dafe kanta..