x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 55 - SU WAYE SU

  • 162001 words
  • 165000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 155

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
maida shi kan jikarta kinsan kwa wannan ai ba ƙaramin so bane kuma babu abun da bazai iyayi ba tunda har ya ɗau wannan tsawon loƙacin akan ƙudirin abu ɗaya.

"Gaskiya ne babu abun da bazai iya ba, saidai mu roƙi Allah yayi mana tsari da shi sannan Allah ya kawo ƙarshen sa.

Maryam tace "Ameen dai"

Nan suka ci gaba da tattaunawa har Babyn baby ta shirya ta fito da ƴar akwatin ta,

Kallon ta Amma tayi tace "ina zaki da uban kaya haka so kike a zargi da wani abu da wuri kenan ai ai bakko zaki nema ki saka kamar kalar biyar ko ki bawa Maryama ta haɗa da baki ta ƙulle muku a ɗan kwali ku da zaku a matsayin ƴan aiki, ina ke ina shiga irin haka.

Waro ido tayi jin me akace mata, da sauri ta ce "Ammu to makaranta ta fa?

"Kar ki damu zakici gaba da yi amma sainan da kamar wata ɗaya sai a roƙi matar gidan akan karatun naki, sai ace mata saboda haka kuma fara neman aikin ana biyun ku tana biya miki kuɗin makarantar kingane?

Jagwab Babyn baby ta zauna kan kujera cike da tunanin taya hakan zata faru, ba ƙaramin bayani su Ammu suka shaba kafin su fahimtar da ita ta gane, har ta yarda.

Sai wajen ƙarfe huɗu sannan suka fito daga gidan tare da motar Amma suka shiga, Saida ta kaisu bakin unguwar, sannan ta sauke su tana ta kuma yi musu bayani sosai da ƙara bawa Babyn baby haƙuri sannan ta juya su kuma suka nufi cikin unguwar saida suka sha tafiya sosai sannan suka ƙarasa cikin layin tundaga bakin layin gidan sa ya fara, haka sukai ta tafiya har suka isa bakin gate ɗin, Babyn baby sai cika take kamar zata fashe haka take jinta ansata ta saka riga da zanin ga wani uban mayafi da aka bata ta yafa shima na Maryam ne, sannan suka siya mata silifas a hanya, jinta take gaba ɗaya kamar zata nitsi dan ta ƙaici.

Saida me gadi yayi musu sallama da cikin gidan suka faɗi gurin wanda suka zo sannan aka barsu suka shiga.

Tunda ga waje suke ta bin gidan da kallo har suka ƙarasa shiga har cikin falon, Maryam ce ta iya yin sallama mutum biyu ne a falon samari guda biyu, amma yanda tayi sallama sai kawai suka ɗago suka kalle su suka juya suka ci gaba da game ɗin su ko amsawa basuyi ba.

Jinjina kai Maryam tayi sai ta kuma ɗaga murya ta kuma yin wata sallamar duk da tasan sunji, da sauri Hajiya Khatume ta fito tana amsawa tace "ku kuna ji ana ta yin sallama babu wanda zai amsa ko baza ku daina wannan halin naku ba ko, to kuci gaba duniya ba uwa bace da zata ɗaga muku ƙafa, zata koya muku hankali wataran.

Saida ta gama da su sannan ta juyo tace "kuyi haƙuri dan Allah basu da kirki wallahi yaron zamani sai haƙuri, ku shigo ciki dan Allah.

Murmushi Maryam tayi tace ah babu komai wallahi, fatan kin gane mu dai ko mune aka turo da zamuyi aiki.

Da sauri tace "nasani ai Hajiya ta sanar sani tunda kuka taho, nan suka ƙarasa shiga cikin falon, Babyn ce tayi ɗaraf zata zauna akan kujera, wani daga cikin samarin yace "ke baki da hankali kin taɓa ganin ɗan aiki ya zauna akan kujerar masu gida?

Mamaki ne ya kusan kashe Babyn baby, sai kawai ta ƙame ita bata zauna ba ita bata miƙe ba, gudun kar tayi musu katoɓara yasa Maryam tayi saurin riƙo hannun ta tace kuyi haƙuri yarinya ce dake wannan ne farkon fara aikin ta bata sani ba, ke kuma ba haka ake ba, ki zauna a ƙasa ki gaishe su.

Shiru kawai tayi tana zama a ƙasa amma aranta ta rantse bazata gaida su ba, har gwanda matar taga tana da kirki, amma sude babu wanda zata gaisar...

Matar gidan kawai ta kalla ta ce "ina wuni.

Da fara'ar ta tace "lafiya lau ƴan mata, sai kinyi haƙuri da yaran namu kinji.

Ɗaga mata kai kawai Babyn baby tayi hakannan taji duk haushin su ya cika mata ciki, shiru tayi ta shiga kalle kalle a falon, su kuma su Maryam suka ci gaba da gaisawa, Khatumme tana yi mata bayanin tsare tsaren gidan.

Babyn baby na kalle kallen ta idon td ya sauka kan hoton Bilal, ɗan waro ido tayi dan bata mance sa ba, mamaki ne ya kamata daman gidan su sukazo, yin aikin yanzu idan ya ganta fa ya tona musu asiri fa ya zasuyi shikenan burin su bazai cika ba, wata zuciyar ce tace mata ai ba lalle ya gane ki ba, wata ƙilma ya manta fuskar ki, da sauri ta shiga girgiza kai a fili ta ce "kai a'a wallahi zai gane ni.

Da sauri Maryam ta kalle ta tare da cewa "me kika ce Baby?

Sai yanzu abun da tayi ya faɗo mata sai tayi saurin cewa "uhmm daman kawai kawai bamma san me na faɗa ba zancen zuci ne kawai.

"Bata kuma ce mata komai ba ta juya suka ci gaba zancen su da Khattume...✍️





*Ina me sanar daku Free ya kusan ƙarewa in sha Allah ina tunanin indai nakai inda nake son kaiwa a page 50 zan dakata Free pages zasu ƙare sai ku fara shirin payment 500*


*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*

_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)


________* 08124226526*_______


*_episode 47💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧



*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*



_Bismillah..✍️_



*SOKOTO*


_____*BULAMA*

Tun yana kan hanya ya fara kiraye kirayen mutanen sa yana sanar dasu abun dake faruwa tsakanin sa da Rabi, nan yasaka yaran sa dake cikin garin Sokoton, yace su isa gidan nata kafin ya ƙaraso, shi kaɗai yake tuƙin sa babu ɗan rakiya yana tafiya kuma yana shirya abubuwan da zaiyi.

Yana shiga garin Sokoto ya dira a gidan Rabi, a waje ya tsaya sannan ya zaro wayarsa ya kira yaran nasa yace suna ina, duk fitowa suka shiga yi daman suna kusa da gidan sun rarraba kansu gudun kar a zargi wani abun a kansu.

Gaba ɗayan su ko wane da makami a hannun sa wajen su goma take suka doshi cikin gidan tare da yiwa gate ɗin wani irin mugun bugu, da sauri me gadi ya baɗe ƙofar yana sako kansa dan ganin su waye masu bugun hauka haka, yan leƙowa ɗaya daga cikin yaran ya mareshi ta gaba tare da tura fuskar sa gaba ya tura sa sannan suka danna kai ciki su duka.

Saidai suna shiga sukaji an saki harbin bindiga da sauri suka fara shirin juyawa amma Bulama ya hana su, tunda basuga me harbin ba kawai ƙarar bindigar suka ji, nan su kaga ƴan sanda na fitowa daga cikin falon gidan su huɗu ne, ga bindugu a hannun su.

Yaran Bulama tsorata su yi dan sun san kafin suyi wani yunƙuri zasu iya harbin su daga inda suke hakan yasa suka fara juyawa da gudu wasu ma basu san sun ture Bulama ba wajen guduwa su fita daga cikin gidan, shikam Bulama ƙyam yayi ya tsaya batare da ko motsi ba.

Me gadin ma tashi yayi yabi bayan yaran Bulama dan yama rasa inda zaiyi, saboda baiga shigar ƴan sandan ba, sai fitowar su kuma yasan matar gidan bata nan hakanne yasa shi binsu shima.

Gaba ɗaya kansa sukayo suka zagaye sa, suna saita shi da bindiga, tare da cewa "you are under arrest kada ka motsa zamu harbe ka.

Wani shu'umin murmushi Balama ya saki tare da cewa "naga alamar baku san ko ni waye ba, to ku hanzarta sauke bindugun ku kafin kusan da wa kuke tare, wa ya baku lasisin yin harbi acikin gida, kuma aikin ta kuke ko aikin hukuma, me yasa bakuyi bincike ba kafin ku fara yanke hukunci yana da kyau ku fara binciken ita kanta matar gidan kuga wace ce ita indai baku kamata ba da ko wane irin laifi ba to na yarda kuzo kuyi arresting ɗina da babu inda zani, yana da kyau ku muje ciki gaba ɗayan mu.

Ɗaya ne daga cikin ku yace babu ruwan mu sa wace ita abun da idon mu ya gane mana da shi zamu yi aiki mun kamaka ka shigo da ƴan daba gidan matar aure wanda hakan kaɗai ya ishe mu shaida kana mata barazana, gashi kuma mun gani da idon da haka ka wuce kawai duk wani sauran bayanai kayi su a police, we are under our permission, saka mu akai dan haka dole ka juya nutafi, "Sani arrest him!

Da sauri wanda aka kira da Sani yayi kansa zaisaka masa ankwa tura sa gefe tare da zaro tasa bindigar dake ƙugun sa, yaja wuyan wani ɗan sanda yana saitawa akan sa, yace duk wanda bai ajiye ba shima sai ya harbe shi.

Duk ajiye bindugun sukayi suna faman rarraba ido.

"Yanzu ku zan sa a ƙulle sakamakon shigar da kukayi kuna shirin kama mutane batare da anbaku izini ba, ku gaya min daga wane station aka aiko ku, yanzu in kira insanar dasu.

Babu wanda ya tanka masa dan basu san me zasu ce masa ba kar suje yajawo musu ruwa dan ba wanda ya sa su yin hakan inba Rabi ba komai na bogi ne daidai da bindigar ba ta gaskiya bace, babu ko bullet ɗaya a ciki.

Ganin duk sun ajiye bindugun yasa Bulama ya saki wanda ya riƙe yace "nawa ta biya ku zan ninka muku su sai huɗu, ku dawo yi min aiki, amma kada ku taɓa nuna kuna bayana ku kasance tare da ita ɗin ni kuma zan gaya muku me zakuyi mata, kun yarda.

Ai da sauri suka shiga ɗaga kai, jin yace zai ninka musu sau huɗu, murya ƙasa ƙasa wani yace "oga ai angama ko mai kake so zamuyi maka saidai gaskiya yanzu bata gidan tace daman in kazo mu kamaka musaka amota sai mu shaƙa maka abu ka suma, daga nan sai mu kira ta mu sanar da ita.

Murmushi kawai Bulama yayi yace "da muatane a cikin gidan?

Girgiza masa kai sukayi, sai ya jinjina kai tare da cewa ina zuwa ku jirani, cikin gidan ya nufa, babu kowa a falon da ya shiga, ganin hanyar kitchen ya dosa, yana shiga ya nufi wajen gas ɗin dake kitchen ɗin silindar gas biyu ne a ciki, buɗe su yayi gaba ɗaya suka fara fita, dan da nan warin sa ya cika kitchen ɗin, fita yayi daga ciki ya doshi wasu gurare dake falon amma ko wace ƙofa a rufe take, har sama yayi hau saida ya ɗan daɗe sannan ya fito daga ciki, yana ta murmushin abun sa, leƙawa yayi ta waje ya hango ƴan sandan suna nan yanda ya barsu, ƙwala musu kira yayi suka amsa tare da tahowa cikin sauri duk batare da sunyi ko wani tunani ba suka shiga, saida ya bari suka shiga sannan shi kuma ya fita tare da ƙullo su ta waje, daga wajen yace "ku maciya amana ne da har kuka yarda zakuyi min aiki akan kuɗi nima idan wani ya baku abun da ya fishi zaku iya yaudarata, na tsani munafiki maci amana, dan haka barin ku a duniya babban haɗari ne gwanda a dinga kawar da irin ku.

Cikin tashin hankali ƴan sandan nan suka shiga roƙar sa suna dukan ƙofar ya buɗe su dan sunji warin gas ɗin har ya cika falon.

Dariyar mugun ta Bulama ya saki da ita, sannan ya zagaya ta bayan kitchen ɗin ya zaro leta ya samu wani ɗan ƙyalle ya kunna wuta ajiki sai ya ajiye sa daga gefen windown cikin sauri yabar gurin yana ta dariya har ya fice daga gidan cikin sauri ya shiga motar sa ya bar ƙofar gidan, tare da datse gidan ta waje, can nesa da gidan ya tsaya saida yaga wuta ta fara tashi sannan ya ƙara gaba, cikin murmushin gefen baki yace "Saura ɗaukan my world, dan ina ɗaukar ki zan bar ƙasar nan dake duniya ta I love you! Yana maganar yana kwarara gudu akan titin dan so yake ya isa da wuri yana zuwa ya wuce gidan ya ɗauko ta subar ƙasar, dan ya matso yaga ya angonce...



$$$$$$$$$$$$$$$$


*LAGOS*


"Kaf cikin barack babu inda RK baisa an duba mana sa ba, amma babu ita babu dalilin ta, Su Fashion tun suna ɗaukan abun wasa har abun ya fara basu tsoro suka fara shiga tashin hankali, gashi RK yace idan basu nemo ta ba, sai yayi maganin su, sojojin ma da suka ce basu ganta ba, bai yarda dasu ba, Saida yayi musu duka akan sai sun faɗi inda tayi da ta fito, su kuma sunyiwa Moohad alƙawari baza su faɗa ba, shiyasa tun farko suka ce masa basu ganta ba, yanzu kuma idan suka dawo suka faɗi gaskiyar me ke faruwa, nan ma ba tsira zasuyi ba tunda suka ɓoye masa tun farko.

Moohad na kallon su suna ta haukan nemanta, daga ƙarshe ma komawa part ɗin nasa yayi sai ya ƙulle sannan ya kira me gyaran a ɓoye yashigar dashi ciki ya kuma duba hannun Beenish ɗin, sosai yake bata kulawa a wunin ranar har dare babu wanda yasan inda suke, dan yau ko training basuyi ba, ana aikin neman ta.

Su Ameela su na komawa inda aka sauke su, tace Barazana ki gwada kira mana Amma ko ta komawa gida ne, hankalin fa ya tashi Allah yasa ba wani abunne ya faru da ita ba.

Cikin damuwa Barazana tace "ni abunne ma yake ban mamaki ya za'ayi ace daga zuwan mu anneme ta an rasa to kode loƙacin da ake harbin ansame ta, to amma idan harbinta ma akayi ai za'aganta koda gawar ta ne, amma yanzu kaf girman gurin ace an duba ba'aganta ba, abun ai da mamaki, wayar ta ta ɗauko tana kallon Ameela tace "to bani number, dubawar da zatayi taga lodin miss call ɗin da Babyn baby tayi mata.

"Wayyo Allah masoyiyya babu wanda ya nemeta kinga kiran da ta jera min, nasan kuma duk ta kira ku, tayi maganar tana kallon Ameela tare da nuna mata wayar, sannan tace bari in fara kiran ta ma kawai sai muji ko tana gida ne.

Da sauri Ameela tace a'a gaskiya kar ma ki kirata idan taji muna neman Beenish kinsan dai akwai matsala ko, gwanda dai kawai ki kira mana waccen matar mu tambayeta.

"Eh kuma fa haka ne kema kince wani abu, bani number, nasan yanzu ina kiranta sai ta nemeta gwanda mu bari sai mun fara sanin inda take, nan Ameela ta bata number ta shiga kiran ta amma har ta katse ba'aɗaga ba, haka suka ringa kira har suka gaji da kira, hankalin su duk ya kasa kwanciya ko abincin ma da aka kawo musu kasa ci sukayi, duk sunyi jigum jigum kamar masu zaman makoki.


*RK*

Shi kansa abun ya basa mamaki ganin yanda suka rasata, tana fitowa fa ya fito amma ace an nemanta anrasa how comes hakan zata faru, anya ba wanine ya fita da ita daga gaba ɗaya gurin ba, kuma babu wanda yake zargi in ba Moohad ba, tun yana tunanin abun ma har ya watsar yaci gaba da uzirin gaban sa.

Yana zaune a falo akan kujera kan cinyarsa da laptop yana daddannawa, turo ƙofar falon akayi bai ɗago ya kalli wajen ba dan atunanin sa Moohad ne, amma jin muryara ce yasa shi ɗagowa ya ɗan kalle ta sai ta kuma kawar dakai yaci gaba da abun da yake, cikin takalmin ta me tsine ta shiga takowa zuwa cikin falon ƙwasƙwas tazo kusa da shi ta zauna.

Cikin ƙwarewa da jan hankalin namiji ta ɗan shafo gemun sa tana ɗan ja kaɗan tace "Hy sweetheart, yanzu dan Allah ka shigo garinnan shine baka sanar dani ba, sai a gurin waccen ballagazar yarinyar wai har yanzu bazata cire ka aranta ba, tunda tasan ka mata nisa kaiɗin nawa ne ni ɗaya ni taka ce kai ɗaya.

"Ba tare da ya kalle
End Ads