x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - SU WAYE SU

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 166

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tazo bai kamata kiyi saurin dakatar da ita ba, cewar Beenish.

Kallon Beeenish take da idanun ta da suka sauya kala zuwa tsantsan ɓacin rai da take jinsa tundaga ƙasan ranta,

"Uwa fa kika ce Beenish!

Jinjina mata kai Beenish tayi tana ɗan lumshe ido a hankali ta furta, "Eh Ameela uwa ce ba'a canza mata suna kije, ta faɗa tana ɗan bubbuga kafaɗar ta, tare da alamun ta kwantar da hankalin ta taje kawai.

Numfasawa ta ƙara yi zatayi magana...

Beenish tace; "kiyi abun da nace miki, zamu samu matsala dake wallahi, tana faɗar haka ta juya gurin Hajiya Dannar da kamar ma abun da ƴar ta-ta take mata bai dame ta ba, fuskar ta tana nan yanda take bata sauya ba da murmushin da take,

"Sannu da zuwa Ammu!

"Sauran ma duk gaida ita suka yi, amma Ameela ko inda take bata kalla ba, hasali ma kawar da kanta gefe tayi,

"Sannu ku ƴaƴa na, ya ku ke? Ya karatu? Ya haƙuri da jama'a?

"Duk lafiya lau alahamdulillah, Ammu ya hanya? "Cewar Beenish"

"Hanya lafiya lau.

"Ma sha Allah" suka bata amsa.

"To yanzu Ameela sai kuje ke da Barazana ku sauke ta,a gidan, kafin mu gama mu ƙaraso zamuyi test yanzu, muna gamawa muma zamu zo,

"Cikin turo baki tace; Nifa babu inda zani tafa cikin haɗe rai tana tura kanta gefe,

"Baki ji me na ce miki ba koh, ki tsaya gardama da taurin kai, wallahi wannan karon ranki zai ɓaci dan kinga ana miki abun da kike so, bana son shirme fa.

Saroro Ameela tayi tana kallon Beenish da take mata magana kamar ta haife ta, irin itace babbar nan, "Rufe ni zaki da duka sai in san bakya son shirme kinji ni da mata, babu inda zanje nace in kuma da kwai wanda ya isa yayi min dole sai in gani, tana kai wa nan ta juya zata bar wajen.... Taji anyi mata damƙar da saida hannun ta yayi ƙara, kuma tasan wace, amma duk da haka ƙin juyowa tayi.

Ganin taƙi juyowa yasa Aunty Babba fusgota kamar ta fusgo ƙalle haka ta fusgo da ita ta dawo gaban su, duk da haka kuma ƙin sakar mata hannu tayi, tana watsa mata kallo da idanun ta dake ciki tana tsuke baki, ta ce; "Wallahi Ameela ki kiyaye mu in ba so kike muyi gunduwa gunduwa da ƙasusuwan ki ba anan.

Ita ma cikin ɓacin ran tace; Aunty Babba ki sake ni tun muna shaida juna, kar rai yazo yana ɓaci, nace babu inda zani wai dola me ku rabu da ni mana haba kunsan bansan irin wannan abun ko!? Ta ƙarasa maganar cike da ɗaga murya.

Murmushi Ammu tayi me ciwo da har saida taji kamar anzare mata wasu ƙasusuwan dake ƙafar ta, ji tayi ƙafar ta ta saki gaba ɗaya, "ku rabu da ita, zan tafi kar nazo na shiga tsakanin ku...

"Haba yaya ta ta kaina, kije mana, duk girman abun da tayi ki godewa Allah tunda de tana raye, da a ce ta mutu bakya ganin ta ko baki taɓa ganin ta ba, bare har tazo inda kike duk inda kika shiga ta lalubo ki baki taɓa sha'awar zuwa inda take ba, dan kanki, amma duk da haka ta daure take zuwa, kisani tana son ki ne yasa take miki haka, baza ki gane daɗin hakan ba da gatan hakan sai loƙacin da kika wayi gari ki ka tuna ke kaɗai ce fa, a duniyar baki da wanda zaizo wajen ki ya nemeki a matsayin mahaifiya, ke baki san rashin daɗin hakan ba, amma ni da na taso...... Kuka ta fashe dashi hakan yasa ta kasa ƙara sa maganar da take....,

Duk suka ji jikin su yayi sanyi, Beenish kam idon ta ya cicciko da ƙwalla tayi saurin tare sa ta juya gefe ta goge saboda bata so kowa ya fahimce ta.

Da sauri Ameela ta jawo ta ta rungume ta tana bubbuga bayan ta tace; "Haba Babyn baby meye hakan kuma, duk me ya kawo wannan maganar da har zaki sa kanki cikin damuwa haka, duk dan saboda naƙi zuwa zaki na wannan maganar....

Ƙoƙarin janye jikin ta tayi cikin kukan tana cewa; "dole inyi me yasa za'ace kike kina cewa bazaki ba, ki sake ni kawai mun rabu dake amma kema sai ki rabu damu... tana maganar tana ci gaba da ƙoƙarin janye jikin ta daga riƙon da take mata.

Ƙara riƙe ta Ameela tayi, cikin sanyi murya tace; "shikenan naji zanje ki daina kuka Auta Please.!

Ɗan janye ta tayi daga jikin ta, ta shiga share mata hawayen tana ɗan ƙaƙaro murmushin yaƙi tace; "komai ya wuce kar ki ƙara yin tunanin komai, kuje kuyi test ɗin kar ki bar komai a ranki da zaisa ki faɗi a test ɗin ki maida hankalin ki kai, me kike son ci idan munje gida in dafa miki?

Jikin ta a sanyaye tace; "komai ma ki dafa zan ci.

"Tom shikenan zan miki favourite food ɗin ki, kiyi ƙoƙari sosai kinji?

Kai ta kaɗa mata kawai amma duk da haka hankalin ta ba'a gun yake ba.

Sakin ta tayi tana juyawa tace "Zee muje...
tana faɗar haka tayi gaba bata kalli kowa ba.

Bayan ta Ammu tabi da kallo tana ɗan girgiza kai a hankali ta ce; "She is never change!

Ɗan murmushi Barazana tayi tana kuma jinjina wannan lamarin nasu, kallon ta tayi ta ce; "Kiyi haƙuri zata canza watarana"

"Hmm Ameela kenan halin ta sai ita, Allah ya shirye ki. cewar Aunty Babba.

"Aikam dai, Ammu mu tafi kar ta fusata ta canza hanya, ba kamuwa take ba.

"Hmmm muje to, naga har ta shiga mota, gaba tayi barazana tabi bayan ta, har sun ɗanyi gaba tayi saurin juyowa ta ce; "oh Faheema koh? Ga su Beenish nan sai kiyi musu bayanin abun da yake tafe dake, Beenish ga Faheema nan.... Tana faɗar haka ta juya cikin sauri tabi bayan Hajiya Dannar.

Beenish ce ta kalli Faheema ta ce; "muna sauraron ki, zamu shiga test.

Murmushi ta ɗan yi sannan ta ce; "ah ba wani abu bane naga kawai kuna burge ni nazo mu gaisa, gashi kuma kuna sauri ma haɗu gobe bari inje nima,

Ita ma mmurmushin tayi mata "ayya to shikenan Allah ya kaimu, mun gode sai anjima... Daga nan ta riƙo hannun Babyn baby sukayi gaba, a gun suka barta tsaye tana ta faman bin su da kallo, daga ƙarshe ma sai ta koma gurin ta zauna kawai ta rafka ta gumi tana tunanin a bun da ya faru yanzu a tsakanin su, duk maganganun da suke kawai bin kowa take da kallo ta rasa wane irin tunani ma zatayi a kansu, yanda suke gudanar da rayuwar su, sai taji sun bata tausayi kuma sun ƙara shiga ranta.... Ta daɗe a gun tana tunani kafin daga bisani ta tashi ta nufi office ɗin Dr. Aveed...

Ameela ce ta shiga driver seat a motar su, Hajiya Dannar tana ƙarasawa ta buɗe motar da kanta ta shiga gefen ta, Barazana kuma ta shiga baya, sannan taja motar suka bar cikin makarantar.....

Maimakon ta doshi gidan su sai kawai tayi doshi wani waje dasu, saida sukaje wajen ma sannan Barazana da hankalin ta ke waya ta ɗago taga gurin sannan tace; "Ameela meye hakan ba gida zaki kaita ba naga munzo nan wajen?

Eh ai ba daɗewa zatayi ba, yanzu zamu rabu zansiyiwa baby abu ne a waccen plaza ɗin ta faɗa tana nuna ɗan nesa dasu,

"Hmm kawai tace mata bata ce komai ba, tasa kai ta fita daga motar tare da rufo musu ƙofar,

"Ina jin ki... Ameela ta faɗa idon ta na gefen window tana kallon waje.

Kallon ta kawai take amma ta kasa magana, saida taja loƙaci me tsawo tana ta faman thinking....

"Mama na wai har yaushe wannan ƙiyayye zata ƙare ne, me yasa baza ki haƙura ki dawo wajena ba, ko ki yafe min, har yanzu kina min kallon me laifi, amma ina so ki ƙara ban loƙaci zan gaya miki duk abun da kike so, ko ban faɗa miki da kaina ba loƙaci zai gaya miki, ki ƙara ban loƙaci kinji...

"Eh naji zaki iya tafiya idan shi kaɗai ne ya kawo ki"

Dafe goshin ta tayi tana jin wani iri aran ta, amma da haka ta ƙara daurewa, ta ci gaba da cewa; "babu abun da ya kawo ni da ya wuce inzo ingan ki, saboda nayi missing ɗin ki, kusan kullum sai naje inda kuma baro bana samun ki, yanzu nazo na ganki kuma naji daɗi. Sannan ina me ƙara baki haƙuri ki ajiye komai zuwa wani loƙaci, ki bani haɗin zamuyi wani aiki, amma ta waya zan turo miki da komai ki cire Ni daga Blocking ɗina da kikayi, zamuyi magana kuma tana da mahimman ci, idan kina son abun da kike nema to sai kin ban haɗin kai idan kuma ba haka ba, to bai zama lalle ki samu abun da kike so ba, very soon,

Hannu ta zura cikin jakar hannun ta, ta zaro sarƙa da ɗan kunne na gold tare da wannan dollars ɗin da ta karɓo bandir uku ta ajiye mata, a gefen ta.

"Ki ɗauke a bunki bana buƙatar su ko kinga nayi kama da me buƙatar kuɗi ko ta wacce irin hanya, ki kwashe abun ki, waɗanda naci ma a baya har yanzu bandai na danasani ba, duk da arashin sanine, ina danasani, bare kuma yanzu ina sane da komai zan ɗau kuɗin hannun ki inci, bazan iya ba.

"Idan kinga dama in kin tafi ki jefar dasu a hanya, kuma abun da kike tunani basu bane, waɗannan kuɗaɗen da halak ɗina na ciwo su, kuma saboda ke na samo su, dan na baki idan kuma baki yarda ba ga waya ta nan zaki iya dubawa, ki bar saka zuciyar ki cikin kokwanto ki ci su hankalin ki, kwance, da irin kuɗin da kike tunanine, da transfer ɗin su zan yi miki baza ki taɓa ganin su a haka ba, daga London na taho miki da su...

Sai loƙacin Ameela ta juyo tayi mata wani irin kallo sannan ta kuma juyawa, "Hmmm ko menene nace bana buƙatar komai daga gare ki, hakan ma ya ishe ni.

"Ya kamata ki nutsu kiyi tunani me kyau akaina kinfi kowa sanin halina, bana tsoron uban kowa bare ke da kika fito daga ciki na, dan haka baki kai matsayin da zanyi miki ƙarya ba, tunda nace miki haka to yarda ta rage taki ki yarda ko kar ki yarda ki kashe ko kar ki kashe damuwar ki ce...

Cike da ƙosawa dan ta fara gajiya da zama tare da ita, kamar za ta yi kuka tace; "Ammu...! Ki fita Please I'm so tired to speak with you. Dan Allah ki ɗauki kayan ki, ki tafi hakan zaifin kwanciyar hankali....,

Hannu ta saka ta talle mata ƙeya, tana jan kunnen ta tace; "Ameela..! Wai ya ku ke so inyi ne, me kuke so inyi muku me zanyi a duniyar nan ku ɗauke ni matsayin mahaifiyar da ta haife ku, ba na jin daɗin wannan a bun da ku ke min ke da ƙanin ki, shin har tsawon yaushe ne a bunnan zai zo ƙarshe? Duk wani abu da uwa takewa ƴayan ta na muku amma bakwa taɓa ganin hakan bakwa yarda dani wannan wace irin rayuwa ce.....

"Me kike mana da kika cancanci zama uwa a gare mu, baza mu taɓa zama ba kuwa muddin zaki ci gaba da kasancewa a haka, har abada bazamu kalle ki matsayin uwa ba, uwar da ta cancanci a bata muƙami na uwa ita ce, uwa ta gari, ba uwa irin ki ba, ki daina kiran kanki da uwa domin baki cika uwa ba.

"Ameela...!"

Hannu ta ɗaga mata Ammu Please and please leave me alone ki tafi inda zaki, in kuma in tafi in bar mi ki motar a nan fine zan fita in bar miki,

Jikin ta a mugun sanyayye ta jijjiga kai muryar cike da rauni sosai da ta daɗe bata yi sa ba, ta ce; "Ameela zan fita zan tafi zan tafi bazan sake dawo ba har sai kinne me ni da kanki bansan ƙiyayyar da kike min ƙaruwa take ba, a koda yaushe bansan duk sanda na haɗu da ke ba kike son ɓatan rai ba, zan tafi, ki kula da kanki ki kare mutunci ki a duk inda kika tsinci kanki a duk halin da kike tsinci kanki...

Aikin kuma da nace zamuyi shawara ta rage taki idan kinga dama ki neme ni idan baki ga dama ba kuma ki barsa nima zan barsa, daman zanyi sane domin ke, amma tunda bakya so to shikenan mu barsa..... Tana faɗar haka ta buɗe ƙofar cikin tsananin ɓacin rai ta fita, daman drivern ta na bibbiye da ita tana fita ta nufi wajen motar ta-ta......

Tana fita Ameela ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, jingina kanta tayi ajikin mota ta ce; "Ammu..! Ammu..! Ammu..!!!! Sai kiran ta take tana kuka......✍️✍️✍️

My WhatsApp number 08124226526

*💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*

_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________

*_episode 18💧_*

💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

___A kusan tare duk suka miƙe tsaye cike da mamaki.

Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki da ta saba yin a mafi yawan cin loƙata tanayi tana tunkaro su cikin takun ta na masu kuɗi.....

A dai-dai gaban su ta tsaya, hannu ta sa ta zare glass ɗin dake idon ta, kyanta ya ƙara fitowa, tana niyar yin magana kenan.

Ta ɗaga mata hannu tare da cewa; "me kika zo yi min kuma, waye ya baki address ɗina, bana son jin ko wacce magana dan Allah ki juya ki tafi inda kika fit......

"A'a hakan ba dai-dai bane bai kamata ba, uwa ce fa, kamata yayi ki fara tsayawa kiji da me tazo bai kamata kiyi saurin dakatar da ita ba, cewar Beenish.

Kallon Beeenish take da idanun ta da suka sauya kala zuwa tsantsan ɓacin rai da take jinsa tundaga ƙasan ranta,

"Uwa fa kika ce Beenish!

Jinjina mata kai Beenish tayi tana ɗan lumshe ido a hankali ta furta, "Eh Ameela uwa ce ba'a canza mata suna kije, ta faɗa tana ɗan bubbuga kafaɗar ta, tare da alamun ta kwantar da hankalin ta taje kawai.

Numfasawa ta ƙara yi zatayi magana...

Beenish tace; "kiyi abun da nace miki, zamu samu matsala dake wallahi, tana faɗar haka ta juya gurin Hajiya Dannar da kamar ma abun da ƴar ta-ta take mata bai dame ta ba, fuskar ta tana nan yanda take bata sauya ba da murmushin da take,

"Sannu da zuwa Ammu!

"Sauran ma duk gaida ita suka yi, amma Ameela ko inda take bata kalla ba, hasali ma kawar da kanta gefe tayi,

"Sannu ku ƴaƴa na, ya ku ke? Ya karatu? Ya haƙuri da jama'a?

"Duk lafiya lau alahamdulillah, Ammu ya hanya? "Cewar Beenish"

"Hanya lafiya lau.

"Ma sha Allah" suka bata amsa.

"To yanzu Ameela sai kuje ke da Barazana ku sauke ta,a gidan, kafin mu gama mu ƙaraso zamuyi test yanzu, muna gamawa muma zamu zo,

"Cikin turo baki tace; Nifa babu inda zani tafa cikin haɗe rai tana tura kanta gefe,

"Baki ji me na ce miki ba koh, ki tsaya gardama da taurin kai, wallahi wannan karon ranki zai ɓaci dan kinga ana miki abun da kike so, bana son shirme fa.

Saroro Ameela tayi tana kallon Beenish da take mata magana kamar ta haife ta, irin itace babbar nan, "Rufe ni zaki da duka sai in san bakya son shirme kinji ni da mata, babu inda zanje nace in kuma da kwai wanda ya isa yayi min dole sai in gani, tana kai wa nan ta juya zata bar wajen.... Taji anyi mata damƙar da saida hannun ta yayi ƙara, kuma tasan wace, amma duk da haka ƙin juyowa tayi.

Ganin taƙi juyowa yasa Aunty Babba fusgota kamar ta fusgo ƙalle haka ta fusgo da ita ta dawo gaban su, duk da haka kuma ƙin sakar mata hannu tayi, tana watsa mata kallo da idanun ta dake ciki tana tsuke baki, ta ce; "Wallahi Ameela ki kiyaye mu in ba so kike muyi gunduwa gunduwa da ƙasusuwan ki ba anan.

Ita ma cikin ɓacin ran tace; Aunty Babba ki sake ni tun muna shaida juna, kar rai yazo yana ɓaci, nace babu inda zani wai dola me ku rabu da ni mana haba kunsan bansan irin wannan abun ko!? Ta ƙarasa maganar cike da ɗaga murya.

Murmushi Ammu tayi me ciwo da har saida taji kamar anzare mata wasu ƙasusuwan dake ƙafar ta, ji tayi ƙafar ta ta saki gaba ɗaya, "ku rabu da ita, zan tafi kar nazo na shiga tsakanin ku...

"Haba yaya ta ta kaina, kije mana, duk girman abun da tayi ki godewa Allah tunda de tana raye, da a ce ta mutu bakya ganin ta ko baki taɓa ganin ta ba, bare har tazo inda kike duk inda kika shiga ta lalubo ki baki taɓa sha'awar zuwa inda take ba, dan kanki, amma duk da haka ta daure take zuwa, kisani tana son ki ne yasa take miki haka, baza ki gane daɗin hakan ba da gatan hakan sai loƙacin da kika wayi gari ki ka tuna ke kaɗai ce fa, a duniyar baki da wanda zaizo wajen ki ya nemeki a matsayin mahaifiya, ke baki san rashin daɗin hakan ba, amma ni da na taso...... Kuka ta fashe dashi hakan yasa ta kasa ƙara sa maganar da take....,

Duk suka ji jikin su yayi sanyi, Beenish kam idon ta ya cicciko da ƙwalla tayi saurin tare sa ta
End Ads