x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - SU WAYE SU

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 128

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[3/5, 11:27 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________

_💧SEASON ONE💧"
*_episode 1💧_*


💧💦محمدالرسوالله💦💧

Bismillah..✍️

.......'Kan titin cike yake da go-slow. Muatane sai horn suke dan son a basu hanyar wucewa, Kowa ka gani a gun fuskar shi cike take da gajiyawar tsayiwar da suke a wajen, wasu sai zufa suke sakamakon ranar da a ke tsalawa,

"Wallahi wannan yaron baida mutunci ko kaɗan har yaso yafi ƙanin nasa wulaƙanci, daga dawowarsa yabi ya addabi al'umma, kuma rashin tausayin nasa ma ace ya wuce unguwa sai kazo titi wajen wucewar al'umma, wannan ai zalinci ne, 'Wani ɗan tsoho dake kan agwagwar mashin ɗinsa yake wannan maganar cike da taƙaici.

Wanda ke gefen sa ya ɗora da cewa; "Wallahi ni banma sanshi ba, na dai ji ƙishin ƙishin ɗin labarin sa, Amma na ɗauka duk zancen mutanene danni bansan shi da wani ɗan ba, bayan wance yaron.

'Wanda yayi maganar ɗazu, yace "Wallahi da gaske ne, ɗan sane ai kasan yana da wata matar da ta rasu, To ina jin ƴaƴan tane kode ƴaƴan waye oho, amma dai ƴaƴan sane, ai dan bakaga ranar da yadawo ba ai baka isa ka biyo titin nan ba aranar, Kaga uban mutane, kuma a ka hana kowa wucewa,

"Mtsww ɗayan yaja tsaki yace; "Allah ya kyauta, Allah yasaka mana abun da suke mana, gashi sauri nake idan nace kuma zan koma babu hanya, Allah de ya kyauta ya kawo mana sauƙi,

"Ameen, ɗayan ya amsa masa dashi, Kafin ya kuma cewa; "Bansan ma me ya faru ba, ya rufewa mutane hanya, Munkusa awa ɗaya a gurin nan fa.....

"Kutumar babbar bura'ubannan, Wane ɗan isakan ne haka, Yo Allah na tuba ko ɗan gidan uban waye bana ci uban sa ba, BARAZANA...! Kunji wai wannan uban jiran da muke a kan mutum ɗaya ne, 'tayi maganar tana huhhura hanci ta kalli wacce ke gefen ta,

Sauran dake bayan motar duk suka leƙo kai, suma suna kallon ta cike da rashin fahimta,

Juyawa tayi tana kallon su tare da maimaita musu abun da taji mutanen nan na faɗa,

Gaba ɗayan su sukayo caaa kowa da abun da yake faɗa, "Wai daman duk wannan loƙacin da muka ɓata ba go-slow bane wanine ya haddasa mana shi, aikawa zaici ƙaniyar sa yau ko ɗan shugaban ƙasa ne.

Da sauri ita ta gaban motar wacce tayi musu bayani, tace wai me kuke jira, yanzu fa saura 15 minutes wannan ɗan isakan ya shiga kunsan kuma idan ya shiga, ba mushiga ba, sunan mu ƴan zaman wajen...

Ai kan ta rufe baki ma tuni ɗaya ta ɓalle murfin motar ta fice suma duk buɗewa sukayi suka fita tsabar bala'i na cinsu ko murfin motar basu gama ƙullewa ba.

Ɗaya ce ta tsaya ta tambayi wanda sukaji suna zancen tace; "Baba dan Allah a wajen ina yake?

Kallon ta yayi da mamakin tambayar da take masa, Memakon yabata amsa sai yace "ke kwa yarinya me zakiyi masa ai kawai ki koma kici gaba da jira wataƙli nan da wata awa ɗayar idan yagama abun da yake ya matsa mana hanya, kuyi haƙuri ku kom...

Tuni tayi gaba bata jira ma yakai ƙarshe ba, daman dan tasan inda zasu dosa tunda sauran ba suma tsaya tambayar ba, tuni sukayi gaba abun su,

Itama cikin sauri tabi bayan su...

Cikin sauri suke tafiyar suna tafiya suna zazzaga bala'i, Mutane na kallon su da mamaki wasu na tausaya musu dan furucin da sukaji sunayi shi yabasu tabbacin abun da suke shirin yi, Kowa dai da ido yake binsu, Yayin da waɗanda suka san su kuma suke ƙananin maganganu ak ansu,

Tafiya kawai suke saida suka kusan zuwa ƙarshen titin ganin wasu shegun motoci wajen guda biyar da sukayi layi akan titin sai kuma guda ɗaya da ta bambanta da sauran, gashi wasu mutane masu baƙaƙen kaya su wajen goma duk sun zagaye motar, Alamun dai suna guarding ɗin ta,

Burki suka ja daga inda suke suna bin mutane da motocin da wani irin kallo yayin da zuciyoyin su sukeyi musu ƙuna, Ta gaban ce ta ɗago ta kalle su, Sai suka shiga ƴar kallon kallo, kafin daga bisani suka fara takawa zuwa gaban motar.

Tunkan su ƙarasa daga cikin masu tsaron motar wani yayi saurin tarar gabansu...Yana zuwa gaban su yace "Where are you going? From where to where?

"Daga gidan uwar ka zuwa gidan uban ka...Wata tabasa amsa...

Kasaƙe yayi ya tsaya yana kallon su. Bisa ga dukkan alamu baiji me suka ce ba,

Ƙara tamke fuska yayi duk da besan me suka ce ba, sai ya kuma cewa "Go back, you are not needed here.

"Kai ƙaton banza marar aikin yi ajawo kawai. Saida ta gama aika masa harara sannan ta matsa kusa dashi tace "Hey Oya, move over there and let's hurry up,

"Where are you going? I told you to move from here before your body is destroyed."

Wata mahaukaciyar dariya suka sanya gaba ɗayan su har da tafawa, Dariyar su kuma ta jawo hankalin sauran da basu san meke faruwa ba,

Wajen mutane biyar ne suka yo kansu,

"Jay.! What's going on, Who are they? What are they looking for? Wani yake tambayar sa,

Zaiyi magana kenan, sukayi saurin tarar bakin sa, da cewa..., "Uwarka muke dalla can kubamu guri mu wuce gurin wancen na cikin motar muka zo ba gurin ku ba,

Cikin zaro ido wani daga cikin su yace "What...! Uwa mu? ya faɗa cike da rashin iya hausar sosai, yaji me sukace, mayarwar ce take basa wahala amma yanaji.

"Yesssss, ɗaya ta basa amsa,

Ganin suna ɓata loƙacin su, yasa me ɗan dama dama ta cikin su, tace "Kutsaya guys, we want to find a way to pass. We have been waiting for a long time, please... Tell your Boss we need way yabamu waje mu wace

Wanine ya watsa musu wani kallon banza tare da cewa, Oh, that's what you came to do? is this what you want?

Sun ɗauka da gaske yayi maganar dan haka sukayi saurin cewa "Eh.

Wanda yake jin hausa, yace "ba'a matsa ba,

"Kai naci kutumar ubanku dan ma ana binku ta lallami "Ṣe iṣẹ ti o mu wa..!(muyi aikin da ya kawo mu) tayi maganar cikin yaren ta na yarabanci,

Riƙe hannuwan su sukayi, tare da yin layi. ɗaya ta kalli wannan ɗaya ta kalli wannan sannan suka haɗa baki atare cikin ƴar waƙa su kace; "GARI BAMBAM ALLAH ƊAYA WAYYO DUNIYA, DUNIYA DAƊI INDA RANKA KA SHA KALLOH MUJE...!!! suka faɗa tare da buga ƙafafun su a ƙasa...

Suna faɗar haka, suka sa iya ƙarfin su da Allah yabasu, suka ja da baya sannan suka taka da ƙarfi sukayi kan mazan nan dake tsaye, 'su da basu san me suke shirin yiba suka saki jiki suna kallon su, kan su ankara sai ji sukayi anyi ciki dasu, gaba ɗayan su babu wanda be faɗi ba dan su tsorata ma sukai, Saboda ihun da matan suka saka sannnan suka bi ta kansu,

Bayan sun zubar da su a ƙasa sai suka kuma dawo wa suka shiga take su da takalman ƙafar su, babu ruwan su fuska ko ƙafa ko hannu ko ina ma takawa suke, tare da fesa musu wani abu a fuska hakan yasa duk suka rufe idanun su ko gani basa yi,

Sauran ne sukayo kansu a sukwane kowannen su na ɗaga hanci sama.

Kama hannuwan suka kuma yi tare da yin baya da sauri kamar irin guduwa zasuyi, Saidai sunayin gaba suka saki hannuwan tare da rarrabewa...

kafin mazan suyi wani yunƙuri su cimma su, duk suka tarwatse, Ganin sun tarwatse kuma yasa suka rasa wacce zasu kama sai kawai suka tsaya...

Ƙara haɗewa sukayi guri ɗaya tare da tunakarar su ba tsoro ba fargaba a tattare dasu, suna zuwa gaban su tun kan su sukawo musu nasu dukan su suka fara feshe musu fuska da wani turare me yaji(spray) take duk suka rirriƙe ido kowa na neman hanya, idanuwan su sun rufe, masu ragwanta ma harda sakin ƴar ƙaramr ƙara,

Suna ganin haka suka tunkari waccen motar Suna zuwa suka ƙwanƙwan sa glass ɗin motar ta gaba, ƙin buɗewa akayi,

"Wallahi zan fasa glass ɗin motar nan" cewar wata,

"Bari dai muga iya gudun ruwan sa, ɗaya ta bata amsa, wata ma ta ƙara bata amsa,

Da ƙarfi ta ƙara ɗaga hannu zata sauke akan glass ɗin sai taga anfara sauke sa ƙasa, dakatawa tayi tare da ƙamar da hannun ta, bata janye sa ba daga ɗagawar da tayi,

Ana saukewa sukaga wani tsoho a gaban motar bisa ga dukkan alamu kuma shi driver ne, cike da ɗan tsoron su dan yaga duk abun da yafaru yana tsoron kar shima su fesama sa, har ɗan rufe ido yake yana kakkare fuska zaiyi magana kenan......

Ɗaya tace "buɗe motar nan ka fito, juyawa yayi ya kalli na bayan motar da yake ta bacci abun sa hankali kwance kamar ba a mota yake ba,

Ƙara juyowa yayi ya kalle su cikin rawar murya yace "Dan Allah kuyi haƙuri bacci yake ba'a tashin sa idan yana bacci, kuma wallahi idan muka bar wajen nan ya tashi ya gansa awani wajen gaba ɗayan mu sai ankore mu,

Leƙawa tayi ta gaban ta hango wanda ke cikin motar abaya a kwance, kwantar da murya tayi tace "Kar ka damu Baba, ba tashin sa zamuyi ba, kaidai kawai ka fito, minti biyu yayi yawa mungama abun da zamuyi,

Badam yaso ba, yacire luck ɗin dake jikin motar tun kan ya fito ma suka sa hannu suka buɗe bayan motar da boss ɗin nasu ke bayan motar,

Suna buɗewa suka ga wani sauri kwance a back seat ɗin ya ɗora ƙafar sa akan hannu kujera yayin da ya rufa wani abu akan fuskar sa ya rufeta ya ɗora hannusa awajen goshin sa sai kuma waya dake kan cikin sa, kana ganin sa kasan hankali kwance yake baccin sa,

Driver na fitowa, ɗaya ta shiga ta zauna awajen sa,

Ɗaya tace bari inje gurin motar mu ku kuma sai ku janye waɗannan motocin daga gurin,

Da sauri sauran ukun tare da ɗayan driver ɗin sa, suka shiga sauran motacin suka janye su daga tsakiyar titin, dawowa sukayi gurin sauran dake tsugunne har yanzu azaba suke ji a idanun su,

"Zaku tashi kubar wajen nan ko sai motoci sunbi takanku"
Duk miƙewa sukayi saidai kuma basu san inda zasu dosa ba, saboda basa ganin gaban su,

Da hannu suka ringa jansu suna turarasu gefen titin, wacce ta shiga motar da Boss ɗin ke ciki, ta leƙo tace "BEENISH...! zo muyi gaba,

Wacce aka kira da BEENISH tayi saurin ƙarasawa gurin ta buɗe ɗayan gefen ta shiga, sannan ta tayar da motar tayi gefe inda zata bawa sauran mutane hanya.

Ragowar biyun kuma gefe sukayi suna jiran ƙarasowar ɗayar ƴar uwar tasu, da zata tuƙo tasu motar,

Nan mutane kowa yaji daɗi wasu nata mamakin su, amma dai babu wanda ya tsaya tambayar su, kowa yaja abun hawan sa, wasu kuma nayi musu godiya da kuma jinjinawa ƙoƙarin su a kan abun da sukayi.

Suna gurin ta ƙaraso gabansu ta tsayar da motar duk suka buɗe suka shiga ɗaya ta shiga baya ɗaya ta shiga gaba,

Saida suka shiga ɗaya ta leƙo tana kallon su tace "Ina mukayi?

Wacce take gaban motar tace "Ku da kunsan ƙarshen zancen ai kawai batun makaranta babu shi ayau, tamu makarantar zamuyi,

Dariya sukayi sannan su kace "Mu wuce...!

Da gudu driver ɗin yaje wajen motar yana cewa "Dan Allah ina zaku kaishi, tunda kun janye motar ai sai ku fito,

"Baba kar kaji komai zamu dawo dashi, bacci zamu kaisa yayi, nan ai ya takura, ka kwantar da hankalin ka kamar kayi baƙo ya mutu babu abun da zai sameshi sai alkhairin mu, dan tarbiya zamu basa tunda bashi da ita, tana kaiwa nan kawai taja motar bata jira cewar sa ba,

Nan ma sauran suka kwasa a guje suka bi bayan ta, suka ɗauki wata hanyar daban, suna gaba suna binsu a baya,

Mutumin na kamar ya ɗora hannu aka ya fasa ihu haka yake ji, ga ragowar har yanzu basu dawo cikin hayyacin su ba,

Shima zubewa yayi a wajen su yana me tausayin kansu da kansu,

Wasu daga cikin mutanen wanɗanda suke kan abin hawar su duk tsayawa sukayi saida sukaga barin ƴan matan sannan sukayi gaba, Kowa da irin maganar da take fitowa daga bakinsa,

Bodyguard ɗin kuwa saida wannan tsohon drivern yaje ya samo musu ruwa me sanyi sannan yazo musu dashi da ƙyar aka samu idanun wasu ya ɗan buɗu shima basa ganin sosai sai dishi dishi,

Bayan farfaɗowar su duk zaune sukayi agun cike da taƙaicin abun da waɗannan yaran sukayi musu, tunda suke basu taɓa haɗuwa da irin su ba,

Jigum-jigum sukayi gaba ɗayansu babu wanda ya samu damar furta wani abun, kowa da tunanin abun da zai biyo baya yake, taya zasu tunkari gida ba tare da wannan yaron ba....

Wannan drivern ne wanda ya taimaka musu da ruwa suka wanke fuskar su, dan a fuska zai girmemusu gaba ɗayan su, shine yasamu ƙarfin gwiwar cewa....

"Ku kam ku tashi mu bar gurin nan duk kunyi zaune babu me cewa komai, zaman namu anan ai babu amfani gwanda muje mu sanar dasu abun dake faruwa a gaggauta bincike a kan yaran nan. Yayi maganar yana bin su da kallo duk da yasan ba lalle bane sun fahimci abun da yake cewa saboda yawancin su basa jin hausar ma gaba ɗaya wasu kuma sunajin kaɗan kaɗan.

wani daga cikin su da yake ɗan jin hausar yace "What..!? Me kan kace? Mu tafi gida, Me kanaso ayi mana idan munka koma house batare da shi ba....

Mutumin sai ya kuma cewa....

"To yanzu ya kuke so a yi? zami ta zama ne anan, ko kuma mubi bayansu ko zamugan su tunda nan hanyar sukayi,

"Duk ai laifin kane me yasa ka barsu sunka tafi dashi baka bisu ba,

Cikin ɗan rarraba ido gaba ɗaya hankalin sa ya fara barin gangar jikin sa, yace l; "Naji tsoron sune ni kaɗai bazan iya binsu ba shiyasa na bari idan ku ka tashi sai muje kar naje na bisu su cutar da ni.

"Mtsww wani yaja tsaki tare da tashi daga gurin ya buɗe mota ya shiga. ganin hakan yasa suma sauran babu wanda ya kumayin magana dan abun da yake damun su ma ya ishesu, basu da loƙacin zama kace nace, ga abun ya haɗar musu goma da ashirin taƙaicin su yanda yaran nan suka zo sukayi musu wasa da hankali suka ci galaba a kan su, har suka zubar dasu a ƙasa, babban tashin hankalin kuma inda zasu samu wannan yaron, koda anganshi sun san idan akaji labarin abun
End Ads