x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 71 - CUTARWA

  • 210001 words
  • 213000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 491

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kula da ita sosai.

Inteesar ta shigo falon gidan, fuska duk a kumbure, idanunta sun yi jawur.

"Ke inteesar lafiya meyafaru?" Ta miƙa wa farida takarda, tana kuka ta ce "Hajiyar sa ta saka ya sakeni, wai sun gaji da ciyar da ni sai dai na yi kashi babu haihuwa, alhalin ɗanta ne silar komai!"

*Ina baku haƙuri, na san ina laifi rashin posting, ayyuka da bukukuwa ne suka yi yawa, ayi haƙuri dan Allah ina godiya da kulawa jama'ata ko in ce na ummi😡*

Ayshercool
08081012143
CUTARWA!




AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g




50

Jikin farida na tsuma, ta karɓi takardar ta duba, ga saki nan rangaɗa-rangaɗa guda biyu.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu ɗaya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai baƙin hali. Ɗaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa hawa-hawa" ta kira wayar dr. Amma bai ɗaga ba.

Ta dungurar da wayar ta ce "Ai na sani, ba zai ɗaga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida".

Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce "ƙamshin abincin kawai ya sa na ji na ƙoshi" tayi murmushi ta ce "Ka dai fara ci tukuna"

Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce "Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi aure ba ta iya girki ba"

"Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor ɗina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta koya"

Dr. Ya ce "Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daɗi"

"Son kai, saboda ƴar ka ce ko?" Yayi dariya yana kashe mata ido ɗaya.

"Yauwwa ga wayarka, an kira ban ɗaga ba"

Ba tare da ya karɓa ba ya ce "Ki na tsoron kar ki ɗaga ki ji budurwa ta ce ko?"

Tayi dariya ta ce "Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana buƙatar wani abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta" ya ɗan ƙura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta riƙe mata ummi, daga baya ta haƙura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta.

Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ƙafa ya lumshe idonsa.

Ta ce "Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri"

"A'a" ya faɗa a taƙaice.

Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa.

Ya ɗago haɓarta ya ce "Kin yi fushi ne?"

"A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?"

Ya ce "A'a sai kin faɗa"

"Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da alaƙa, ba tare da mun san mu ƴan uwa ba ne, dan Allah baban ummi"

Ya ɗan yi murmushi ya ce "Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina da juna biyu kar ki wahala"

"Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a" yanayin yadda ta kwantar da kai take lallaɓa shi ya sanya shi jin daɗi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. Saɓanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani.

"Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah"

Faɗaɗa murmushinta ta yi tana yi masa godiya.

Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su.

Sai dai ta fara da yi masa ƙorafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta miƙa masa takardar da inteesar ta zo da ita.

Ya karɓa ya karanta, sannan ya kalleta ya ce "Na gani, me zan ce?"

"Kamar yaya me zaka ce? Ba zaka kira shi ba a kan abun da ya aikata, ya wulakanta ƴar ka"

Dr. Ya ce "Ƴar ki dai, ki nema mata wani uban da zai tsaya mata, ni da ban isheku kallo ba ke da su, ai na yi zaton wani uban ki ka canza musu, kuma ba wani abu da zan kira mijinta na ce masa, tun da ya riga ya saketa, in dai irin halin da ki ke yi, ta je tana yi dole a korota, yayi haƙuri ma. Idan baki riƙe tawa ƴar bazawara karo biyu ba, ga zaurawa biyu nan har da ƙarin budurwa Allah ya haɗa miki, kuma dolenki ki riƙe" ya fice ya bar mata gidan.

Inteesar ta ɗora hannu a ka ta din ga rusa kuka, can gefe ma rahama kuka take yi, dan an saki mijinta, ya ƙwace mata sauran yaran, bayan aiko mata da tata takardar sakinta.

Farida ta koma kamar mahaukaciya, ta rasa in da zata saka ranta.

Kwanan ummi arba'in da biyar, ita da raihan da noor suka tafi yawon arba'in, a motar da Alhaji ya bata.

Suka fara da zuwa gidansu raihan, da suka je gwiwa a ƙasa ummi ta durƙusa ta din ga yi wa Alhaji godiyar mota da ya bata.

Yara sun cika hannu, sun ƙara kyau sosai, babu yadda za ayi ace yaran hausawa ne a yadda.

Alhaji ya ce "Su wannan larabawan ba su fara dariya ba ne? Ko ni ɗin ne ba su gane ba" yayi maganar yana yi musu wasa.

Har wurin mami suka je, sai dai Nihal ce kawai ta ɗauki yaran, tana hangen yaran abun ka da jini, zuciyarta na son ɗaukarsu, amma sharrin zuciya da ƙiyayyar ummi ta saka ta share su.

Ana ta shirin bikin Nihal, saboda an kusa kawo kayan lefe, da an kawo kuma ba za a saka da yawa ba, za ayi bikin.

Daga nan kuma ta ce su tafi can gidan farida, daga nan ma ta duba jikin rahama, tun da an ce a gidan take jinya.

Raihan ya ajiye su, ya ce awa uku ya basu, zai dawo ya ɗauke su, su tafi gidan mama.

A falo suka tarar da inteesar, kamar aljana ta rame, hasken nan babu shi, duk ta fita hayyacinta.

Ummi ta zauna tana faɗin "Anty intee kwana da yawa, ya ki ke ya gida?"

"Lafiya lau" ta amsa jiki a sanyaye, tana ƙarewa ummi kallo, da shigowarsu kawai ƙamshin kabbasar kayanta, ta gauraye ɗakin. Wata irin danƙareriyar lafaya ce a jikinta mai tsada, hannunta yatsu uku duk gold ne, haka kunnenta, har da chain na gwal a ƙafarta. Kai ba sai an gaya maka ba ka san ummi a hutu take.

Noor ta ce "Anty intee baki da lafiya ne? Duk kin rame" inteesar ta girgiza kai.

"Ina su Antyn su ke da rahama?" Da hannu kawai ta nuna musu ɗaki.

Ummi ta kwantar da iman, a kan kujera noor ta ajiye aiman suka shiga ɗakin da sallama.

Ɗakin sai warin gyambo yake, sai ɗan zani aka yafawa rahama, duk ta ƙone.

A gigice ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Anty rahama sannu ya jiki" rahama ta sunkuyar da kai sannan ta amsa.

Ta kalli farida ta ce "Anty ina wuni, ya mai jiki?".

"Dalla rufe mini baki, kin zo munafunci ki ga a wani hali nake ciki, ko na haukace na fara bin bola kamar babarki, to ina nan daram. Dangin maita bakin da ki ka yi mata ya kama ta.

Jiki a sanyaye ta ce "Astagfirullah, ƙaddara ce daga Allah, kuma ke ki ka hasala ni, ɓacin rai ya sanya na yi wannan furucin. Sannu Anty rahama, yadda Allah ya jarabce ki da wuta a duniya, Allah ya haramta mata namanki a lahira, Allah ya baki lafiya da akwai wani abu a raina ba zan zo duba ki ba, Allah ya baki lafiya"

Rahama ta riƙo hannun ummi ta ce "Ummi ba zan musa ba, idan aka ce alhakinki ne ya kamani, na san mun azabtar da ke, wallahi tun da na yi aure ko amarci ban gama ci ba, na fara shan wahala har yau ban samu kwanciyar hankali a gidan aure ba. Dan Allah ki yafe mini"

Ummi ta shafa hannun rahama ta ce "Na yafe miki wallahi, Allah ya yafe mana baki ɗaya, Allah ya baki lafiya bari na je falon na ji kamar kukan aiman" ta miƙe ta fita.

Farida ta kalli noor ta ce "Sannu sallalamammiya, ashe kin canza uwa ko?"

Noor ta ce "Idan na yi miki laifi fa ce wa ki ke yi na nemi wata uwar, dama ke ba uwata ba ce, ki yi ta hantarata da zagina, ni kuma bana jin daɗi ni ki ka tsana ban san me na yi miki ba" sai jikin Farida yayi sanyi, ta tuna maganar ummi, ba ta taɓa zaton abun da tayi zai yi tasiri a zuciyar noor ba.

Ta basar ta ce "Da uban wa aka saka miki rana ban sani ba?"

"Yayan yaya raihan ne, yaya salim"
Kausar da ke gefe tana danna waya ta ce "kutt wannan gandamemen mutumin, me yayi miki zafi?"

"Ni kar ki yi mini hassada, haka kurum in tsufa a gida, ke da ki ke kyau ma baki yi aure ba, balle ni ba zaki zigani ba" suka hau faɗa kasancewar kwana biyu ba su haɗu ba.

Farida ta tsawatar musu, sannan ta koma kan rahama da masifar, uban me suka yi wa ummi da take neman yafiyarta.

"Ashsha! Yaya ki farga kema kan lokaci ya ƙure. Kin san mun azabtar da ita, ke ki ka gaya mini halin da Iya take ciki, ni dube ni wallahi hakki ne"

"A'a ni ban ɗauki hakkin kowa ba, dan haka ba wata yafiya da zan nema, ta daɗe ba ta yafe ba".

Ummi kuwa na komawa falo, ta tarar da inteesar tana zaune ta zuba wa yaran ido, ta saka hannu ta ɗauki aiman da ya tashi ya fara kuka.

Tana ɗaga kai ta ga ummi ta ajiye shi, tana basarwa. Ummi ta yi murmushi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ajiye mata shi a cinyarta ta ce "Haba ɗan gidan babban mutum, mamanka ce da ba ka santa ba, ka buɗe ido ka kalleta" Inteesar ta saka hannu ta rungume shi, ta fashe da kuka.

Ummi ta san kukan me take yi, ta dafa ta ta ce "Haba Anty intee, Allah ya baki rai da lafiya, kar ki yi masa butulci, rashin haihuwa jarabta ce, ki gode masa ki yi addu'a idan ki na da rabo, Allah ya baki naki kema. Zan taya ki Addu'a in sha Allah zaki ga ɗanki, Allah ya baki rabo a satin nan, ni na yi biyu ke ki yi uku, mu tarawa kawu abokan wasa"

Cikin kuka ta ce "Aurena ya mutu ummi, uwar mijina ta saka ya sakeni, wai bana haihuwa sai ci da kashi. Sun wulaƙanta ni, sun tozarta ni, Abba ya ce babu ruwansa na ƙarata na nemi wani uban. Zuciyata za ta fashe ummi, gashi tun da na dawo kausar ta mayar da ni kamar maƙiyiyarta sai raini da wulaƙanci ita kanta maama tayi ta hantarata, wallahi ji nake kamar na sha guba na mutu"

Da sauri ummi ta toshe mata baki, fuskar ummi ɗauke da hawaye ta ce "Haba anty inteesar, mutuwar aure ba kan ki aka fara ba, ba kuma yana nufin ƙarshen rayuwarki bane ba. Abba kuma kun yi masa laifi yana gaya mini, kun tafka kuskure da kuka daina kula shi, ko gaishe shi ku ka daina yi, dan ya auri mamana. Ku ka manta da duk ɗawainiya da hidima da ya yi mana a rayuwa.
Ki kwantar da hankalinki, ki nemi afuwarsa nima zan taya ki roƙonsa, na san zai yafe miki. Abu na gaba kuma, ki yi ta addu'a da miƙa wa Allah lamuranki, idan ki ka gama idda, ki roƙi Abba ya bar ki, ki koma karatu, ko ki fita ki koyi wata sana'ar hakan zai rage miki lokacin da ki ke spending a cikin gida da su Anty farida, amma dan Allah kar ki sake cewa zaki kashe kanki"

Inteesar ta kwanta a jikin ummi ta ce "Ba ki san me nake ji ba"

"Na ɗanɗani fiye da abun da ki ka ɗanɗana, da ko maƙiyina bana fatan ya ɗanɗana. Sai da ta kai a duniya ina jin kamar nikaɗai aka tsana, na sha jin nima kamar na kashe kaina, a lokacin da bani da kafaɗar kashingiɗa na yi kuka, noor ce kawai take tayani kuka, sai zuwan Baban su iman rayuwata, ya nuna mini ita rayuwa yadda ka ɗauke ta, haka take zuwar maka. Dan Allah ki daina wannan kukan".

Ummi ta yi ta rarrashin inteesar, Farida ta fito tana faɗin "Ke Inteesar kukan me ki ka yi mata?"

Inteesar ta share hawayen ta, ta ce "Babu abun da tayi mini, miƙo mini macen na ganta"

Ummi ta miƙa wa inteesar iman, ta haɗa su ta rungume, tana cigaba da zubar da hawaye.

Duk yadda farida ta bugi cikin noor, a kan ta gaya mata shirye-shiryen da ake ciki a kan aurenta, amma tayi mursisi tayi shiru.

Sai da suka yi faɗa, ta ce noor ba za ta bi ummi su tafi ba.

Sai ga inteesar ta sake da ummi, tana ta bata labarin irin zaman da ta yi a gidan aurenta.

Ummi ta ce "Babu auren da ba shi da ƙalubale" nan ita ma ta din ga ba ta labarin irin ƙalubalen da take fuskanta.

Ummi ta din ga jaddada mata, ta nemi yafiyar dr.

Raihan ya kira wayar ummi ya ce yana waje.

Noor ta kwashi takalmanta da gudu, ta yi waje saboda farida ta ce ba zata bar gidan ba.

Ummi ta je ta ajiye wa rahama kuɗi, suka yi waje.

Inteesar ta raka ummi da jariran nan, kamar kar ta bawa ummi su, har ta yi wa ummi alƙawarin zuwa har gida ta yi mata barka.

Daga nan suka wuce gidan mariya, tayi murna sosai da sosai da zuwansu, aka yi sa'a dr. Yana nan, ummi ta yi masa maganar inteesar.

Ya ce "Inteesar tsakanina da su ai sai ido, ni da ban ishe su kallo ba"

Ummi ta ce "Mun yi magana da ita kawu, dan Allah ka yi haƙuri, za ta baka haƙuri ma. Ta fara iƙirarin shan guba ta kashe kanta, dan Allah ka yi haƙuri ka ja ta a jiki dan Allah. Mun yi hira da ita sosai, ta fuskanci ƙalubale sosai a gidan aure, sai dai anty farida ba ta din ga ba ta shawara ta kirki ba"

Ummi ta cigbaa da lallaɓa shi, har ya amince.

Noor tun da aka saka ranar aure, take wani irin jin nauyin Salim, idan ya zo duk surutun ba ta iya yi masa.

Kausar kuma hankalinta ya tashi, noor za ta yi aure ta bar ta, duk samarin nata babu na aure sai ƴan sharholiya.

Mariya kuwa, Abdul ne zai kai ta maiduguri, ummi kuma da ita da noor, raihan ya tafi da su bauchi, daga can idan suka kwana biyu su tafi maiduguri.

Hajiya Aisha ta din ga murna, dan dama raihan bai taɓa kai mata ummi ba.

Ranar da suka sauka da magariba, Hajiya Aisha ta kira wata a waya, ta ce ta shigo yau ga matar raihan su gaisa.

Ummi na zaune a kan sallaya tana lazumi, ta ji muryar da ko a mafarki ba zata manta mai ita ba.

"Ina amaryar tamu, yau Allah ya yi zamu haɗu, na ji kunya ni ban je ba su gasu a garinmu"

Raihan da yake bawa yaransa madara ya ce "Aikuwa dai kin ji kunya yasin, kuma na daina uwar ɗakin da ke"

"Amma dai ka san uzurina, bama gari amma tuba nake, dolena na je Kano, Mummy ki taya ni bayar da haƙuri"

Hajiya Aisha ta ce "Kun fi kusa ni babu ruwana".

"Anty Na'ima" ummi ta yi maganar cikin rawar murya.

Na'ima ta waro ido ta ce "Ummi, ummi ke ce" da gudu ummi ta ƙarasa jikin na'ima suka rungume juna, ummi na kuka"

Na'ima ta ɗago ta ce "Ummi, dama zan sake ganinki? Kan rasuwar mama duk lokacin da na je gagarawa sai na tambayeki, ace mini ki na kano, bayan rasuwar mama na daina zuwa, ummi me ki ka zo yi nan, zan sake ganinki dama".

Mummy ta ce "Ikon Allah, ai ita ce matar babban mutum"

Na'ima ta waro ido ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah kai ne abun godiya, ummi na san ba zaki wulaƙanta ba a rayuwa, raihan ummi ƙanwata ce, dan Allah ka ƙara riƙe mini ita da kyau, ta sha wahala a rayuwa"

Raihan dai ya din ga bin su da ido, da ƙyar suka bar kukan. Na'ima yaron mijin Hajiya Aisha take aure, shi ne, shi ne babban yaronsa, dan shi ne babban manager, kuma lokacin da raihan ya zauna a bauchi, gidanta yake zuwa yawon cin ɗan wake, suna zaman mutunci sosai.

Ummi ta fara basu labarin, gudunmawar da take iya tunawa, da Na'ima ta yi mata a gagarawa.

Raihan ya ce "Salma, ku daina tuna abun da ya wuce, anty na'ima in dai ummi ce, ba zan sake barin tayi kukan wahalar rayuwa ba".

Na'ima ta ce "Ummi ina Anty mariya?"

Nan ummi ta bata labarin suna tare, da yadda gagarawa ta koma.

Ai har kusan sha biyun dare, Naima suna tare da ummi, kuma ta yi wa ummi alƙawarin zuwa kano.

Kwanansu biyu a bauchi, suka tafi Maiduguri.

Mariya sai ɓoye-ɓoye take yi, dan kar a ga cikinta, ita kuwa ummi tuni ta gano ta.

Gagarumin taron family aka shirya, ƙaton hall na gaske, da ya haɗa da manyan mutane daga sassan ƙasar nan, wanda suke duk ƴan uwa ne, ba tare da sun san ƴan uwa bane ba.

Riahan ma yana wurin, noor ta ce "Yaya ummi, kin ga har da larabawa a ƴan uwanku".

Aka rarraba musu sovenir, wanda a ciki yake ɗauke da littafi da ya bayar da asalin su.

Asalin mahaifin kakan su mariya ta ɓangaren uba, balaraben ƙasar tunus ne. A yawon fatauci ya auri wata ƴar somalia, ya taho da ita Nigeria, yawon fatauci, jin daɗin zamansa a Nigeria, ya sanya ya cigaba da zamansa a Nigeria, ya auri wasu matan ya hayayyafa.
Bayan rasuwarsa, galibi duk suka kama gabansu, ita ta somalia ta koma ƙasarsu, manyan ƴaƴanta da suka riga suka girma a Nigeria, basu bi ta ba suka yi auratayya a Nigeria, duk suna jin turanci, larabci da wasu yarukan na Nigeria.

A taron har da ire-iren dangin su na tunusiyya, da wasu daga cikin dangin matar nan ta somalia.

Kuma ɓangaren su ummi,
End Ads