x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - CUTARWA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 487

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake fashewa da kuka.

Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haɗu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taɓa gani ba, dan haka ta ƙudurce a kan balarabe za ta juye.

Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala'i, tamkar ba ita ta haife shi ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi.

Yayi ta bata haƙuri, sannan ya nufi ɗakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci.

Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba.

"Ya jikin ummin?"

"Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ƙasa, ta koma falo kan kujerar da ke ɗakin ta zauna. Da yake ɗakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo.

"Ba sauƙi fa ki ka ce maman ummi?"

"Ina sauƙin yake bashir? An yi wa ƴa ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya riƙe ta da amana, alhalin an binne gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, ɗan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi ɗaukar ƴa ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle ɗan adam" Ta ƙarasa tana sheshsheƙar kuka.

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce "Haba maman ummi, ya zan yi, iya uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni"

Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ƙoƙarin sa a kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali.

Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san ba zasu taɓe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wulaƙanta ba.

Abun ka da mata da miji, haka ya lallaɓata ta janye batun yin yajin, har ya fara ƙoƙarin shiga wani abun daban.

Iya ce ta faɗo ɗakin tana faɗin "Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ƙule a ɗaka da mace" a razane mariya ta yi gefe, tana kare jikinta.

"Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama... Yanzu aka kira sallar"

Ayshercool.
08081012143
    
                       *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)



3

Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya.

"Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba"

Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba.

Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba.

Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi.

Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa "Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani"

Ya ce "Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci.

Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta.

A zahiri kuma ta ce "To Allah ya yassare" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita.

***
Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daɗi wasu marasa daɗi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da ɗaci da raɗaɗin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba.

Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance.

Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.

Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.

Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.

"Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"

"Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.

Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce "Saboda me ummina"

Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata"

Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi"

"Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma"

Ummi ta yi shiru ta ce "To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?"

Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu.

Iya ta ce "Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi"

Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce "Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri" tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci.

Mariya ta ce "Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai" tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki.

"Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?"

Mariya ta goge hawaye, ta ce "Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haɗa kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?"

Ummi ta girgiza kai alamar a'a.

"Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki".

Ummi ta taɓa idonta ta ce "Sai akuya ko?"

"Akuya kuma?"

"Eh, malamarmu ce ta faɗa, ta ce ni da akuya irin idonmu ɗaya, eyes sunan ido da turanci in ji anty"

Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya.

Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ƴan uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuɗi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ƴar ta a gabanta ba.

Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya ɗaliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki.

Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce "Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata"

Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya.

Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba.

Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna.

Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce "Baba kafi mama loma" tayi maganar tana dariya.

"Eh mana, baki ga na fita girma ba?"

Ummi tayi dariya ta ce "To ni kuma gaba ɗaya ƴan gidan nan, na fi su loma"

Mariya ta ce "Ke ɗin, sai ka ce abinci ki ke ci"

"Mama nafi duk ƴan yara girma fa"

Babanta ya ce "Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena"

Ta kama kumatunta ta ce "Iya ta ce bani da kyau ai"

"A'a ke kyakywa ce sosai" miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida.

Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?"

Ya kalle ta ya ce "Meyasa zaki faɗi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ƴarmu ba ta da kyau mummuna ce?"

"Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya"

Jiki a sanyaye ya ce "Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba"

Mariya ta numfasa ta ce "Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne.
Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ƙalubalen da zata fuskanta wataƙila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raɗaɗin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wulaƙanci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karɓi ƙaddarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ƙara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a ɗaki ita ɗaya, an cuce ni" tayi maganar kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata.

Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin ɗaci a zuciyarsa ya ce "Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ƙetare maganar ta na iya shafar mu baki ɗaya, amma in sha Allah, ina sanya ran Allah ba zai wulaƙanta ummi ba, dan Allah kiyi haƙuri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na ɗau matakin abun da aka yi wa ummi".

Ta share hawayen ta, ta ce "Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka ɗau mataki, wannan wani miki ne a zukatanmu da ba zai taɓa warkewa ba".

Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ƙaramin haƙuri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya.

Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu.

Ummi suka tarar da Alhassan ɗan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murɗe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta sun mimmiƙe, duk ta gigice.

A guje mariya ta ƙarasa, ta hankaɗe shi, ta ƙwace ummi da ke kuka.

"Alhassan me ummi tayi maka ka murɗe mata gashi haka?"

Cikin fitsara yaron ya ce "Ɗan magenmu take mana wasa da shi"

A fusace mariya ta ce "Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?"

"To waye ya ce ta taɓa mana magenmu, ana ta nemansa?"

Cikin zafin rai, mariya ta ɗauke Alhassan da mari.

Sai da balarabe ya waro ido.

"Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa ƴa ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar mini ƴa sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba"

"Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido" Alhassan ya wage baki yana kwarmato"

Bakomai ya hana balarabe taɓuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ƙaramar tijara zata yi ba, kuma ƙarshe su zata ɗorawa laifin".

Buje a hannu iya ta fito daga banɗaki tana faɗin "Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?"

Alhassan ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gaya mata.

Ta kuwa hau sababi "Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taɓa ƴar gwal sai tayi yinƙurin cire masa ido. Duk ɗawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin ɗawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ƙashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ƙoƙari ta kashe masa ɗa, wallahi duk matakin da ya ɗauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku"

Cikin takaici mariya ta ce "Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuɗi shi ne ɗa, da idan aka ɗaukar masa mataki ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba ƴa ba? Iya Allah fa" cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin ɗacin zuciya ta koma ɗakinta.

"Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ƙofar arzkin ka ta buɗe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki"

Bai cewa iya komai ba, ya shiga ɗaki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta ɗaga masa hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ƙyaleta ya fice.

Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaɗai ke da hakki a kan sa ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna buƙatar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba.

Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya.
Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe ƴaƴansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne.
Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaɗe ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi ƴar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuɗi.

"In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a
End Ads