x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 27 - CUTARWA

  • 78001 words
  • 81000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 543

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
mace ne faɗa za ayi da ni"

Mami ta ce "Kai,tashi ka je mini aike na uban tsari".

"To ɗaukko kayan, ki haɗo da kuɗin shan mai".

"Duk kuɗin da babanka yake baka, sai ka damfareni dan zan aikeka, to ba zan bayar ba".

Ya kashingiɗa ya ce "Mami idan kina son aiken nan a kan lokaci, ki bayar da cin hanci " tashi mamin tayi tana hararsa.

Hakan yayi dai-dai da fitowar ummi, fuskarta a jiƙe da ruwa, gaban gashinta duk a kwance, gashin girarta ma tamkar za su haɗe.
Fararen idanuwanta suka bawa brown ɗin ƙwayar idonta fitowa sosai da sosai.
Ƙwayar idonta yake son kalla, domin tabattar da kalarta, sai dai bata bashi damar hakan ba, dan mayar da niƙabin ta rufe fuskarta, ta tayar da salla.

Mami ta dawo falon da ATM ɗinta, tana yi wa Raihan kashedin ya je ya dawo da wuri.

Ya karɓi ATM ɗin yaƙi tashi, ummi ta idar da sallar, tayi Addu'a ta cewa mami za ta tafi, tashi yayi ya riga ummi fita.

Mami ta ce sai ta tsaya ta ci abinci, amma ummi ta ce sauri take yi.

Ta ajiye wa mami kyautar kwalbar turaren humra.

Kuɗin motar da ta bawa ummi ma, ƙin karɓa ta yi, kuma da ganinta ka san tana buƙata amma mursisi taƙi karɓa ta tafi.

A babban falo ta tarar da shi, yana taje sumar kansa.

Har zata fita ya ce "Ki tsaya mu tafi tare na ajiyeki ko a titi ne"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai, zan ƙarasa" bai kuma ce mata komai ba ta fito daga falon.

Ta fita harabar gidan, hakan yayi dai-dai da fitowar wata babbar mace, ta sha ado da lace blue, hannunta da wuyanta duk gold.

Wani matashi yana biye da ita, kai da ganinsa ka ga ɗan shaye-shaye.

Da sauri ummi ta ƙarasa in da matar take, ta ɗaga niƙabinta ta durƙusa ta gaisheta.

Matar ta faɗaɗaɗa murmushinta ta ce "Ummi yau kece a gidan, ba dan Allah yasa na fito ba tafiya zaki yi bamu gaisa ba?"

"Ba haka bane hajiya, a gurguje na shigo ne, kusan kullum ta hanyar nan nake bi, shiyasa na ce yau dai bari na shigo"

"Eh amma zaki tafi bamu gaisa ba ummi, ya gida ya makaranta?"

Ummi ta amsa da Alhamdilillah.

Hajiya ita ce uwar gidan mami, tun lokacin maryam na nan, tana son mu'amala da ummi saboda nutsuwarta, amma ummi ta janye jikinta ta daina zuwa gidan ma, saboda ba a ga maciji, tsakanin mami da Hajiya.

Ummi ta gaida Salim da suke tare da hajiya, ya amsa mata sama-sama.

Hajiya ta ce "Ummi kin yi aure ne?" Ummi ta girgiza mata kai.

"Ai da kin yi aure ban sani ba, sai mun yi faɗa".

Kamar an jefo shi, ya dafo kafaɗar hajiya yayi ƙasa da murya ya ce "Ku daina yi wa mutum irin wannan tambayar babu daɗi"

Hajiya ta yi murmushi ta ce "To babban mutum".

"Biki zaki je kenan?"

Ta ce "Eh, ƴar set ɗinmu ke auran ɗa"

Raihan ya ce "Shiyasa ki ka sha kwalliya, kamar ƙawar amarya mu ga jakar" ya karɓi jakar hajiya ya zuge.

Ya girgiza kai ya ce "Allah sarki Alhaji, an ɗebi kuɗinsa za aje ayi liƙi, to nima bari na ɗebi rabona" ya zura hannunsa ya ɗebo kuɗi ya zura a aljihunsa.

"Raihan abun har da gori, sai ka gayawa duniya kuɗin babanka ne"

Yayi dariya, ya ce "A dawo lafiya"

Ummi ma ta ce "Hajiya bari na tafi, a dawo lafiya "

Hajiya ta ce "A'a ummi, shigo mu fara aniyeki, sai mu ƙarasa wurin bikin"

Ummi ba za ta iya jayayya da hajiya ba, dan haka ta ce "To na gode"

Har ummi ta juya zata bi su ya ce "Eh ba shakka, ba zaki hau babur ba sai mota shikenan ai".

Lokacin suna Islamiyya, Maryam bata da aiki sai bayar da labarin Muhammad Raihan, barkwancinsa da kuma tsokana, tsokanar ma irin mai cika cikin nan.
Dan haka ummi ba ta waiwayo ba, tayi murmushi ta bi bayan su Hajiya.

Ayshercool
08081012143
Whats app only please 🙏
    *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P22

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

22

Raihan ya nufi in da babur ɗin sa yake, ya ɗauka ya fita daga gidan.

Suna tafe suna taɓa hira da ita da Hajiya, duk da ta kasa sakin jiki da hajiyar sosai, saboda yadda take matuƙar jin nauyinta.

Har kan layinsu suka kai ta, ummi ta yi ta musu godiya, sannan ta sauka ta nufi gida.

A harabar gidan ta tarar da Abdul hannunsa riƙe da waya. Yana ganinta ya tsaya yana jiran ƙarasowarta.

"Yaya ummi ina ki ka shiga ne?".

"Na ɗan biya wani wuri ne, meyafaru?"

Maama sai faɗa take yi, intee ce aka dawo da ita,  wai ta kuma yin ɓari, zasu tafi asibiti zata bar miki sallahu baki dawo ba.

Ummi a ranta ta ce 'Ga kausar a gidan, ita ba za a bar mata sallahun ba'

A zahiri ta ce "Subhanallah, ubangiji Allah ya bata lafiya".

Ya amsa da "Amin, Allah ya taimake ki sun tafi, yanzu na dawo daga kaisu, kafin su dawo na san ta huce ba za ta yi miki faɗa ba".

Ummi ta ce "Haka ne, bari na yi sauri na shiga ciki"

Ta ƙarasa ɗakinta, ta yi wanka a gurguje, ta canza kaya ta saka hijjabinta na zaman gida, ta nufi kitchen.

Ta tarar da noor tana wanke-wanke a kitchen.

"Mama aiki ki ke yi haka?"

Noor ta ce "Eh, rage miki aikin nake yi, na san a gajiye zaki dawo, na ɓoye miki abincinki a ƙarƙashin dining, kar a cinye ba ki ci ba" tayi maganar cikin iyayi.

Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai mama, bari na je na ci abincin, in zo mu ɗora abincin dare"

Noor ta ce "Kije ki yi bacci ma ki huta, zan yi miki greating kayan miya, na yi miki mopping"

Murmushi ummi kawai take tana kallon noor, soyayyarta da noor gamon jini ce.

Bayan magariba Rayhan ya dawo yana zaune a falon mami, yana ta bawa ƙannensa umarni, duk barkwancinsa idan yana nan basa wani sakewa saboda akwai dealing.

Mami na zaune a gefe tana cin abinci, tana kallon citruss.

Ya kalleta ya ce "Mami kin san ina ta yi wa baƙuwar ɗazu kallon sani, sai daga baya na tuna a wurin saukar su Maryam na san muryarta, dan ban ga fuskarta ba ranar"

Mami ta ce "Auu wai ummi, yarinyar kirki".

Ya ce "Tana da tarbiyya sosai tun ranar da na ganta a wurin saukar nan, tubarkallah idonta mai kyau, ban taɓa ganin irin idonta ba".

Mami tayi dariya ta ce "Kaga iskancin da su maryam suka din ga yi mata suna Islamiyya, saboda fatarta da idonta, duk in da maryam ta zauna sai ta bayar da labarin baƙin ummi. Gashi uwar riƙonta na azabtar da ita, ai ainihin ƙawancensu ma, maryam ce ta ture ta, ta faɗi ashe ƙonuwa ce a cikin ta, ta dinga zubar da jini, uwar riƙon ta ƙonata da dutsen guga a ciki, shima da ƙyar ta gayawa malaman ƙunar duk ta jagwale"

A razane raihan ya tashi zaune, ya ce "Ta ƙonata da dutsen guga fa ki ka ce?"

"Wallahi kuwa, maryam ta ce kusan kullum cikin kuka ummin take, kuma bata magana sai ta ga dama, duk yadda za ayi da ita, ba zata faɗi ga abun da yake damunta ba, sai kuka".

Ya murza goshinsa a hankali ya ce "Mami kuma babu wani abu da ki ka yi, ki taimaka mata a wannan lokacin?"

"Rufa mini asiri, ai yanzu ba a wannan shishshigin, na so dai na din ga taimaka mata financially, amma yarinyar nan ba a bata kyauta ta karɓa, halint sai ita"

Ya dinga kaɗa ƙafarsa a hankali yana tunani, gaba ɗaya kalar ummi ba mai hayaniya bace, hasali ma fuskarta kalar tausayi ce.
To wani laifi za ta yi wa mutum, har a ƙonata da iron a ciki, ita kuwa wannan wace irin azzaluma ce.

Labarin da mami ta bashi tana dariya, bai ga abun dariya ba a ciki, na cewa yara na tsokanarta saboda tana da duhu da kuma ƙwayar idonta, meye a baƙar fata duk halittar Allah ce, kuma idanunta meye aibunsu, ai abun a hukunta su ne a wancan lokacin, ga child abuse a gida, makaranta ga takura daga abokan karatunta, Allah ka ɗai ya san the hardship she goes through.
Dan bai manta yadda Maryam ke bashi labarin abun da ake yi wa ummi ba, da yadda take kwatanta masa baƙinta, sai duk iya ƙoƙarin sa wurin gano muninta shi bai gani ba.

Fuskarta kawai yake hangowa, ko ɗazu da suka yi faɗa kan ya shigo bashi da gaskiya, amma ta bashi haƙuri, komai nata simple ne.

Ya miƙe tsaye ya ce "Mami sai da safe, bacci nake ji" yana gama maganar ya fita.

***
Ko da farida ta dawo sai da ta ci wa ummi mutunci, duk da ta san ummin wurin aiki take zuwa, domin kuwa bautar ƙasa take a lokacin a wani gidan jarida, daily news.

"Maama dan Allah ki daina yi wa anty ummi faɗa, ba gashi nan duk mun gama yi miki aikin gidan ba".

Cikin tsawa ta ce "Idan ina magana ki na saka mini baki sai na yi ball dake" tayi maganar tana nuna noor da yatsa.

Ta mayar da idonta kan ummi ta ce "Dan kan ki, gaba ɗaya kin mayar mini da yarinya fitsararriya mara ɗa'a kamar ke, zaki haifa ne kema. Sakwara zaki daka, da jar miya, kije Abdul ya kai ki asibiti ki kai wa inteesar ki kwana da ita asibiti, kausar ta dawo gida".

Daga auren inteesar zuwa yanzu, tayi ɓari ba adadi, dan kamar har mijin nata ya fara ƙosawa da hakan.

Ummi ta je kwana da ita, ta tarar ana yi mata ƙarin jini, duk ta rame, ƙannen mijin suna zazzaune, suna ta hirarsu ko a jikinsu da halin da take ciki, kausar ce a kusa da ita a zaune, ita ma kuma danna wayarta take yi.

Ko da ta ga ummi ta wani haɗe rai ta yatsine fuska ta ce "Dan wulaƙanci, tun kan mu taho asibitin nan ake jiranki, amma ki ka ƙi dawowa kin bar mutane da yunwa, kuma kin san dai ba iya cin abincin sayarwa muke ba"

Ummi ta ja wuri ta zauna ba tare da ta kulata ba, suka gaisa da ƙannen mijin inteesar.

Babu kunya suka ja kwanon sakwarar nan suka buɗe, suka ci abin su, suka gama suka ƙara gaba.

Sai da inteesar ta yi sati a asibiti, ummi ce ke sintirin kai abinci da ɗawainiyar kwana da ita, amma duk basa gani sai rashin mutunci da hantara, gashi idan ta kwana kan wani yazo daga gida ta koma ta shirya ta tafi in da take SIWES, sai ta makara sosai da sosai.

Idan ta je wurin aiki, shima ayi ta yi mata faɗa a kan makara.

Farida ta cewa sageer ya bata inteesar su tafi gida, ta ɗan kwana biyu ta huta.

Inteesar ta ji daɗin hakan, dan kuwa azabar ƙannen mijinta sun isheta, mijin suna zaune lafiya sai abun da ba a rasa ba, amma fa ƙannensa ba sa laifi, dan akan su har zaginta yake yi, ya ci mata mutunci tayi ta musu bauta.

***

A ƙalla ummi ta shafe mintuna goma sha biyar a tsaye a bakin titi, tana ƙoƙarin tsallakawa, amma ta kasa saboda tarin ababen hawa da ke kaiwa suna komowa. Ga rana gashi ta gaji matuƙa, ta gaji da tsayuwa.

"Tsallaka titin ma sai kin yi masa yanga Yaya?" Sai da gabanta ya faɗi, dan kuwa ta tsorata sosai.

A hankali ta waiwaya tana kallon fuskar sa.

Idon da yake son gani ya samu yana kallo, dan yau ba niƙab ta saka ba, facemask ne.

Sai dai bai kalla yadda yake so ba ta janye idonta, tana ajiyar zuciya.

"Na tsorata ki ne?"

Ta ce "Na tsorata ne, ina wuni?"

Ya dawo gefenta ya tsaya ya ce "Yini yana gidan biki, Ai mami ta ce ki daina gaisheni, ni ƙaninki ne, dama kin ce girma ya riga hankali zuwa"

Murmushi ta yi ta sake cewa "Ya mamin da kowa da kowa?"

Raihan ya ce "Suna nan ƙalau, ke na hango na tsaya a tsallake, morethan 20minutes, kin kasa tsallaka titi ki na yanga"

A ɗan marairaice ta ce "Eyya ba yanga nake yi ba, kasa tsallakawa na yi ne"

Ya jinjina kai ya ce "I see"

Ya ce "Taho mu tsallaka" Gaba ya fara yi, tabi bayansa a hankali, sai da suka je tsakiyar titi, ta juya zata koma da gudu saboda motar da ta taho da gudu. Hanata hakan yayi, ta hanyar danƙo hannunta yayi suka yi gaba suka tsallaka.

Ƙoƙarin cire hannunta take daga nasa, amma ya riƙe gam ya ce "Ke haka ki ke tsallaka titi? Gaba ɗaya kin tsorata kanki? Nutsuwa ake yi idan za a tsallaka titi"

Ta sunkuyar da kai, tana cigaba da ƙoƙarin cire hannunta daga nasa.

Ya kalli hannayensu nasa fari tas, na ummi mai duhu, sai dai nata hannun yafi nasa kyau sosai da sosai, nasa da gani kaga hannun namiji, duk a murɗe ga uban jijiyoyi, nata kuma ɗan madaidaici, ɗauke da dogayen yatsu, tafin hannunta fari tas, haka faratanta farare ƙal dogwaye gwanin sha'awa, ga hannunta tamkar auduga dan taushi.

Ya zare nasa ya basar ya ce "Mu je na ajiye ki a gida"

Ta ce "A'a kar ka damu, wannan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"

Raihan ya ce "Ai ba babur bane, yau mota ce, tun da ba kya hawa babur sai mota".

"A'a ba haka bane wallahi, kar ka damu, yanzu zan tafi na gode sosai".

Sai ka ce ubanta haka ya haɗe rai, ya ce "Mu je in sauke ki, bana satar mutane ai, ki daina haka"

Haka nan ummi tayi tsuru-tsuru, dan da ya haɗe rai sai yayi mata kwarjini, ya nufi tsaleliyar motar da yayi parking ɗin ta a gefen titi, glasanta baƙaƙe wuluk, sai sheƙi yake, da gani ka san ba a daɗe da fara hawanta ba.

Ya buɗe wa ummi gaban motar, gaba ɗaya ji tayi kamar zata aikata zunubi, ko da wasa bata taɓa hawa motar wani ba, idan ba ta kawu yahaya ba.

Wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗin gaske ya baƙunceta a cikin motar.

Ya zagaya ya zauna, ya rufe motar, ya ɗaukko robar ruwa da lemo, ya miƙa mata ya ce "Ga ruwa ki sha, kin daɗe a rana".

Fuskar sa ta kalla, ta karɓa ta ajiye a kan cinyarta.

"Ina zaki yi ne?"

"Gida"

"Gida ina?" Ta kwatanta masa, ya ja motar ya fara tafiya.

Ta gefen idonsa yake kallon yadda duk tayi tsuru-tsuru kamar ba ta da gaskiya, gaba ɗaya a takure take, kamar wadda ke zaune a kan ƙaya.

Tunani yake ta yi a zuciyarsa, this innocent looking lady, ace an azabtar da ita har haka, to wane irin laifi zata yi, da zai saka ayi maka haka?.

Ɗan satar kallon sa tayi, kamar ba shi ta gani wancan lokacin ba, yana barkwanci da wasa da dariya ba.

Ya ɗaukko wayarsa ya nemo lambar Maryam, ya saka a hansfree.

"Ke yane?"

Ta amsa da "Normal, ya aka yi?"

"Guess what?"

Ta ce "I have no idea, menene?"

"Na sake haɗuwa da ƙawar nan taki, da na ce miki tazo gida gaida mami"

Ta ce "Allah sarki, ummi?"

"Eh ita"

"Wallahi bani da numbernta, ban sani ba ko tana da waya ma?"

"Baki da kirki, maybe tun da ki ka yi aure baki sake neman ta ba".

"To a ina zan ganta, ban son zuwa gidansu, antynta ba ta da mutunci"

Ya ce "Ai shikenan, a gaida yaran"

"Za su ji in sha Allah".

Ya ajiye wayar, ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa.

"In da na ɗauko ki aiki ki ke ne a wurin?".

Ummi ta ce "SIWES"

"Me ki ke karanta ne?"

Ummi ta ce "Mass communication"

"Mass communication, ai karatun masu baki ne, ke kuma kamar ba kya magana ma"

Ita dai tayi shiru ba ta ce masa komai ba.

Ya bata wayarsa ya ce "Saka mini lambar ki, sai na turawa maryam, ku dinga gaisawa, zumunci abu ne mai kyau".

Wayar ta sa zuƙeƙiya mai kyan gaske, ta saka masa lambar ta miƙa masa.

Ya ce "Masha Allah, to nima za a din ga zumuncin da ni? Tun da ƙaninki ne ni?"

Ummi ta yi murmushi ta ce "To"

"To yaya ummi na gode sosai, sunana Muhammad Raihan"

Ta ce "Ai na sani"

"Ai tuna miki na sake yi, ranar da muka haɗu mun kusa yin faɗa, ashe kin sanni nine ban gane ki ba"

Tayi murmushi tana sake gyara zaman facemask ɗin ta.

"Ki rage saka niƙabin nan da facemask, idan ba haka tayaya mutum zai gane ki, you are lucky ina da saurin gane mutane ma, da mask ɗin na gane ki"

Ummi dai ba baki, dan dama can ba mai hayaniya ba ce, sai murmushi da take yi.

A bakin titi ta ce masa zata sauka.

Ganin ya takura mata, ya sanya ya ƙyaleta, ta buɗe motar ta waiwayo ta kalle shi ta ce "Na gode sosai"

"Nima na gode ki gaida gida" yana kallonta cikin dabara ta ajiye masa ruwa da
End Ads