"A ƙofar ɗakinsu na ganta, wai mamanta take jira, a wannan sanyin, maimakon ta shigo nan ta jira ta".
Iya ta ce "Ka ji munafuka, an tsotso a nono, amma a gaban idonki ai uwar taki ta tafi barki ko?".
Hashim ya ce "Kamar yaya ina ta tafi?"
Iya ta ce "Mhmm, ai mariya daga ita har ƴan uwanta ba su da mutunci, zuwa suka yi za su tafi da ita, shi ne zasu haɗa da ummi, na ce ba zai yiwu ba, in rasa ɗa na sannan ita ma su tafi da ita ba, na ƙwace ta"
Yayi shiru yana kallon iya ya ce "Amma iya meyasa? Kin san bata shaƙu da kowa ba sai babarta, ga mahaifinta Allah ya karɓe shi".
"Ba ka san rayuwa ba magajin malam, mariya sam ba ta da tarbiyya, ba zan rasa ɗa na kuma ta tafi da ƴar sa ba, ta koya mata mugun hali. Tashi ki miƙo mini kwanon can, ki zo in zuba miki tuwo".
Ummi ta kawo kwano, iya ta zuba nata tuwon masara miyar karkashi, sai dai ummi ba ta son miyar karkashi. Ta jagwalgwala tuwon, ta cinye samansa, ta bar guntun cikin tsoro ta ce "Na ƙoshi".
Iya ta kalleta ta, ta kalli kwanon tuwon ta ce "Ni zan cinye miki sauran da ki ka bari?" Ummi ta girgiza kai.
"To maza cinye shi" duk ƙoƙarin da ummi tayi, ta kasa cin abincin nan.
Iya ta din ga zaginta, ta ce ta rufe ta ajiye, zata yi maganin wannan sangartar da aka yi mata.
Mariya ƴan uwa na ta tausaya mata abun da ya faru, da alhinin rashin mijinta ga muguntar uwar miji, da kuma rabata da ƴar ta.
Dan sai da mahaifinsu ya so yayi faɗa, yayanta yayi masa bayanin abubuwan da suka faru, da ƙyar ya fahimta, duk da haka dan mariya tana cikin yaran da yake matuƙar so ne, tana da matuƙar haƙuri da biyayya.
Ya ce in dai ƴa ce, tun da sun ƙwace ta, su ƙarata suma ba zasu sake bibiyar a basu ba, idan sun ga dama su din ga kawota, idan ba su ga dama ba su je su ƙarata, dan babban abun da ya baƙanta masa rai, bai wuce yadda aka ce Iya tayi iƙirarin mariya ce ta kashe mata ɗa ba, karo na farko a kan mariya, aka goyi bayan mace ko dan ba ƙara ta kawo ba, zahiri suka gani, dan maryam ta labarta musu komai, har da yadda ake muzanta ummi, da cewar da iya tayi, wataƙila ɗan ta ma baya haihuwa, saboda su kaf danginsu babu kalar ƴar, daga baya kuma ta ce ita zata riƙe ta.
"Ai ban san mutanen kawai bane na basu ƴa ta, dattakun yaron da nutsuwarsa ce ta sanya haka, ina da yaƙinin zuriyata babu lalatacce, kar wanda ya kuma bi ta kan yarinyar, ku ƙyale su da ita, ke kuma idan kin gama takaba, Allah ya kawo miki miji nagari".
A ɓangaren mariya ba ta ji daɗin wannan goyon baya da aka yi mata ba, mussaman yadda ƴan uwa suka goya masa baya, a kan yanke alƙarsu da in da ummi take, ita a ganinta hakan ba masalaha ba ce, ita da ummi meye nasu a ciki.
Babu bakin magana, haka tayi shiru sai bin su da ido, ta ƙare ta shige uwar ɗaka, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta din ga rusa kuka, ita ma meya rage mata na bashir da za ta kalla ta ji daɗi ban da ummin? Ta din ga kuka, zuciyarta na wani irin zafi, ji take kamar duniya babu wani abu da ya tage mata da zai sanyata farinciki, mahaifiyarsu ta rasu, yayyenta duk sun yi aure, sai ƙananan ƙannenta da matar babansu, dan ma mutuniyar kirki ce.
Washegari da asuba, iya ta idar da sallar asuba, ummi na ƙasa a duƙunƙune a cikin hijjabinta a ƙasa, ko zani ba a shimfiɗa mata ba, ba wanda ya kai ta tayi fitsrai, ta saba sai mariya ta kai ta tayi fitsari, kan ta kwanta, dan haka ta yi wa iya fitsarin kwance.
Kamar zata daki sa'anta, haka iya ta taƙarƙare ta ɗalawa ummi duka, a gigice ta tashi tana sosa wurin, saboda zafi.
"Dan ubanki fitsarin kwance ki ka yi mini saboda sangarta?" Dubawa ummi tayi ta ga fitsarin tayi, ta yi shiru ta kasa magana, sai hawaye.
"Au kuka ma ki ke yi mini, saboda sangarta da iskanci, zan yi maganinki, fita ki ɗebo ruwa a randa ki zo ki zuba"
Da sauran duhun asuba, dan haka ummi tsoro take ji, ta fito waje ta tsaya tana kuka.
"Ba zaki wuce ba, sai na zo" ta jiyo muryar iya. Cikin sauri ta je ta ɗebo ruwa, garin sauri ta koma ɗakin, ta faɗi sassanyar ruwan randar nan ya sheƙe mata a jiki.
A gigice ta yi wata irin ajiyar zuciya, tana kyarma. Ta tashi da guntun ruwan a moɗa, ta shiga ta zuba a wurin, kamar yadda iya tayi mata umarni, ta dawo ɗakin ta tsaya.
Iya ta kalleta ta ce "Munafuka, shi ne ki ka zuba ruwan a jikinki, sai ki cire kayan ki saka wasu, ga tsummokaranki can".
Cikin rashin wayo, ta kwance kayan, ta saka uniform ɗin ta, dan ta san ranar monday ce, ta tattara kayan fitsarin, ta haɗa su a cikin masu kyan ta ɗaure, dan kuwa mama ta hanata zubar da kaya ko ina.
Ta juya ta kalli gabas tayi salla, ba tare da tayi alwala ba, dan da ruwan ɗumi take alwala da mama tana nan, dan haka ta zata idan ba ruwan ɗumi, ba sai ka yi alwala ba.
Gari yayi haske, ta je gaban murhu, ta saka hannunta ta dangwalo toka, ta cuccuɗa bakinta, ta kuskure ta koma ɗakin iya, tana jiran iya ta bata abinci.
Aka kawo wa Iyan kunu mai zafi, amma ta kalli ummi, ya ce ta ɗauki tuwon jiya ya cinye, dan ba za a zubar ba.
Miyar karkashin ce ba ta so, dan haka ta sake jagwalgwalawa, ta ajiye ta fito tsakar gida, tayi ta kallon ƙofar ɗakin su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin tana ƙwanƙwasawa, wai ko mama zata buɗe, sai da ta gaji, kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaɗata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita.
"Ke daga ina?" Malamar da take ajin su ta tambaye ta.
"Gida" ta faɗa a taƙaice.
"Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?"
Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce "Mama ce bata nan, ba ta dawo ba"
"To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda zata aikatau ba makaranta ba" ƴan ajin suka kwashe da dariya.
"Silent" malamar ta tsawatar tana kallon ƙafar ummi, da kamar an ciro ta daga haƙa rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ƙasan farin hijjabinta, tana goge hawaye.
"Wuce ki je ki zauna"
Ta nufi wurin zamanta, can wuri ɗaya, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ƙasa² yana cewa "Baƙar tukunya, yau an shafeta da toka"
Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa tana nemanta.
Ummi kuwa da ƙyar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu'a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke ɗora girki, shi ma babu komai a wurin, ta kalli ƙofar ɗakin su, ɗakin dai a rufe.
Ɗakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba.
Bacci ya ɗauke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, "Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya.
"Makaranta na je"
"Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?" Ummi ta girgiza kai.
"Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai ɗaga mini hankali ba, balle ke" ummi dai tayi shiru ba ta ce komai ba.
Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci.
Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na'ima, ta zo tafiya da ita, Naima ƴar ɗakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ƙwace ummi. Ta tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye.
"Iya na zo tafiya da ummi makaranta"
"Gata nan, sai kun dawo" iya tayi maganar tana nuna ummi a wulaƙance.
Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga jiƙaƙƙun kaya a ciki.
Ta ce "Ummi, na ji kayan ki a jiƙe?"
"Fitsarin kwance na yi ban sani ba"
"To ki daina haɗa su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu"
Ummi ta saka mata kuka ta ce "Yaushe mama zata dawo?"
"Ki yi haƙuri, nima ban sani ba, amma za ta dawo" ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta.
Kwana ɗaya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ƙafa, ta koma gagarawa, ta ɗaukko ƴar ta, duk sallar da tayi, bata iya addu'ar komai, sai roƙon Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta.
A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki.
Da suka koma gida, aka din ga yi mata faɗa, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun nan.
Watanni huɗu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma tafi samun sauƙi da sassauci, a lokacin da mariya tana nan.
Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ƙyar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform ɗin nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi taƙi yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta.
Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata ɓarnar mai.
Wanki kuwa, sai idan na'ima za ta yi nata, sannan ya ta haɗa da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa, sai dai tayi ta yawo cikin dauɗa.
A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta haƙura.
Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta ɗauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta jiƙa jikinta da ruwa buta ɗaya.
Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ƙoshi da wanda iya take bata.
Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuɓe ummi, ta ce ya zane mata ita.
Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya ɗauke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya ce idan ta sayo ta kai masa ɗakin su.
Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raɓe-raɓe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciɓis da ummi a soro ta ce "Ummi, tun ɗazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara, amma shi ne baki taho ba".
"Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa ɗakin su".
"Ɗakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa ɗakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki" ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karɓi omon ta ce "Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma"
Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci.
Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa ɗakinsa a samarin gidan.
Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala'i.
"Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?"
Naima ta ce "kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara"
"Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini saƙona?"
"Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka ɗakin ka" nan da nan bala'i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya.
Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris.
Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuɓe tana kuka.
Naima ta ce "Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza kawai" iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima.
Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya shaƙo ummi tare da luƙa mata wata irin ashar. Ƙara tayi tana kakari.
"Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai na kashe ki" ya jefar da ita a wurin, ta riƙe wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata.
Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga ɗaki, tana ƙoƙarin fita, mama wadda take matar babansu, ta riƙe ta, ta ce "Mariya lafiya ina zaki?"
"Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ƙofar gida fa"
"Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?"
"Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji"
Mama ta ce "Iya kuma, nice fa mariya"
Mariya ta yi ƙuri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba ɗaya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata.
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya ɗauke ni na ga ummi"
Mama ta ce "Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa"
Mariya ta amsa da "To"
"Ki din ga yi mata addu'a, Allah zai tsare miki ita" gyaɗa mata kai kawai ta yi, ta koma ɗaki.
Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin shaƙar da ta sha.
Iya ta ritsuta a ɗaki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na'ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai, tana tsoron kar ta dake ta.
Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daɗi, ta yi wanka, ta sanya cukurkuɗaɗɗun uniform ɗin ta, dan ma an yi sa'a a wanke suke, dama na'ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi.
Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta ɗau kofinta, ta je sashin sa'adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta.
Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji.
"Baki tafi makarantar ba ne?" Ta jinjina masa kai.
Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki.
"Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?" Ta jinjina masa kai.
Ya karɓi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya miƙa mata kunun cikin kofi.
Har ƙasa ta tsuguna ta karɓa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji.
Ta shanye ya karɓi kofin, ya bata naira ashirin, ta karɓa ta ce "An gode"
"Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki" ta ce "To"
Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ƙoshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaɗi.
Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ƙazanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta.
Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala.
Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buɗe jakarta da yanzu a baƙar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace, fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama ɗan mitsitsi da ƙyar take iya riƙe shi ta yi rubutu.
Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna.
Ya dubi malamarsu ya ce "Malama, yara biyar zaki zaɓo mini masu ƙoƙari, zamu tafi