kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
P10
Saminu ya numfasa ya ce "To shikenan, Allah ya sanya alkhairi"
Iya ta ce "Yauwwa ka turo mini shi, ko kuma ya jira ni a ɗakinsu, zan same shi"
"To shikenan, bari na je na nemo shi"
Hashim kuwa dariya yake yi wa ummi, yana cewa ta tafi a hankali, saboda yadda ta kwasa da gudu cikin tsoro.
Da Iya tayi karo, iya ta kalleta ta ce "Daga ina ki ke?"
A tsorace ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, huwaila ce ba ta yi mini lallen da wuri ba"
"Yenyenyen da an yi magana, dan Allah ki yi haƙuri, ki wuce ki nemi wuri ki zauna kar ki sake fita". Ummi ta ce "to" dan ba ta yi zaton Iya ba zata yi mata tijara ba.
Iya duk ta bi ƴaƴanta da ta haifa da na riƙonta, ta sanar musu da halin da ake ciki.
Ilyas ya ce "Amma Iya naga yarinya ce ƙarama sosai, girman jiki ne kawai ba zata iya jure ɗawainiyar aure ba"
"Yarinya kuma? Ni ma shekarata sha uku aka yi mini aure, uwarta ba sha huɗu aka auro ta ba? Da ta shiga bulunbuƙui za ta yi, yaran yanzu da sun san komai, to idan ba haka ba ya zamu yi?"
Sagir ya ce "To ai Iya ba a shirya ba, da wani kayan ɗakin za ta tare?"
"Wani shirin za ayi? A sayo mata katifa a gidan dillalai, tsohuwa ba sabuwa ba, mai biyar mai goma ku yi karo-karo, ku haɗa a saya mata buta, murhu tukunya da ƴar tabarma, ina da tsofaffin labulaye, da abun da ba a rasa ba, a saka mata kowa da haka yake farawa ai, rufin asirin ɗan uwanta ai na ta ne"
Gaba ɗaya suka amince a kan haka, baiwar Allah ummi sam ba ta san wainar da ake toyawa ba, tamkar ba mace mai ƙananan shekaru ba, ita take ta ɗawainiyar aike da girkin abincin gidan bikin, ko nauyin jikinta ba ta ji, saboda tsabar sabo da wahala, ba ta san zama wuri ɗaya bata aikin komai ba.
Idiris kuwa tun da aka gaya masa, hukuncin da Iya ta yanke, wanda da kanta ta gaya masa, ya kada baki ya ce "Allah ya kiyaye, uban ne zan ci da wannan baƙar yarinyar mummuna ragowa, ni wallahi bana son ta".
Mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na mangare ka, shashasha mara hankali, kai ka isa ka yi jayayya da maganar Iya? Ba kai ka janyo koma menene ba, aure ne babu fashi sai an yi shi wallahi, dan ba zamu ji kunya a idon mutane ba"
Iya cewa take "Bi shi a hankali saminu, na sani ba son ta ka ke yi ba, muni kam akwai shi amma ka yi haƙuri, tun da kai ka janyo komai, mun riga mun tara mutane, idan muka ce an fasa dole za a so jin ba'asin abun da ya faru uban me zamu ce musu? Ko kuma gaya musu abun da ka aikata zamu yi?".
Cike da iskanci, da rashin ɗa'a ya ke kumbura baki yana masifar, shi fa baya son ummi, hindu yake so.
Iya ta fusata ta ce "Uwar hindu ka ke so ba hindu ba, ɗan iska mara mutunci, ba gata aka yi maka ba? Ka je ka yi abun da ka ke ganin zai fishsheka"
Suka tafi suka bar shi, yana wani irin huci da takaici, yarinyar da aka gama lalubewa, wanda yana da tabbacin ba shikaɗai yake yi mata ba, ga baƙi ga muni, ace ita zai aura dan an raina masa hankali, ga hindunsa ƴar fara mai kyau, ace wai ya auri ummi, za ta ci ubanta kuwa, da ƙafarta zata gudu.
Magaji ne ya shiga ɗakin su da kayansa da ya karɓo daga guga, ya kalli idiris ya cika yayi fam, yake ta tsaki da ƙanan maganganu.
"Gunagunin me ka ke yi haka ne?"
"Ba dole in yi gunaguni ba, saboda an tsane ni, za a cuce ni a kassara rayuwata da ta yaran da zan haifa"
"Wai ka da waye ne? Me kuma aka yi maka?"
"Iya mana" ya faɗa a fusace.
"Too iya kuma? Duk kusancin naku, yau a ganku a rana?"
"Ba wani kusanci, za a zalunce ni, wai dan an fasa aurena da hindu, wai sai an ɗaura mini aure da wannan buranyar yarinyar, mummuna wai ni za a aurawa ummi, wai ba zasu ji kunya ba, wannan jakar yarinya mai kama da mayu, ita fa iyan da kanta take faɗar baƙin halin uwarta, kuma za a liƙa mini"
Sakin kayan hashim yayi, bakinsa na rawa ya ce "Wace ummin?"
Idiris yayi masa mugun kallo ya ce "Wace ummin ban da wannan baƙar yarinya, da goshi kamar tsinin jirgi, mummuna ido kamar na kyanwa wallahi ni an cuce ni, kuma wallahi ko an yi auren sakinta zan yi"
Bai bi ta kan kayan ba, ya fita da sauri, ya nufi sashin mahaifiyar su, wanda nan ma ya ɗau harama da mutane, uwar ɗakin mahaifiyarsu ya shiga, ya tarar da ita tana ƙirga kuɗi.
'yaya" ya kira sunanta.
Ta kalleshi ta ce "Ya aka yi?"
"Wai da gaske Idris ummi, za a aura masa?".
Ta ce "Mhmm nima haka na ji"
"Amma yaya meyasa?"
"Kafi kowa sanin ai abun da ya aikata, Iya ce ta kawo wannan shawarar, mu ma rufin asirinmu ne ai"
Kamar Hashim zai yi kuka ya ce "Amma yaya kin san yadda Idris yake da yarinyar nan, gata yarinya ƙarama,a haka zaku bari ayi auren nan?"
"To ni na isa in hana ne? Kai ka san babu mai ja da maganar Iya ai ko?"
Bai sake cewa komai ba ya fita, ya nufi sashin iya, a ƙofar ɗakinta ta hange shi, yana tsaye yana kallonta, fuskarsa babu walwala.
Cikin azama ta fito, dan kar magajin ya faɗi wata maganar banzar, a cikin mutane ya tona musu asiri.
Ta ce "Menene?"
"Iya wai kin ce a aurawa idiris ummi, saboda an fasa auren sa?"
"Eh sai yaya?"
"Amma Iya kin san ba son ummi yake yi ba...
Ta katse shi ta hanyar cewa "To ina ruwanka, ku yaran zamani ku kuka san wata soyyaya, mu duk bamu santa ba, idan ya aureta ko daga baya ya saketa, ba shikenan ba in dai asirin ya rufu, ai ba ana nufin yayi ta zama da ita bane ba din-din"
Galala yake kallon Iya, idan dai-dai ya ji, kamar ta ce ko daga baya ya saketa, wato rufin asirin kawai suke nema, ko da hakan yana nufin tarwatsa rayuwar marainiyar.
"Amma iya"
"Kai rufe mini baki, bana son ƙauli da ba'adin banza, sai in ci maka mutunci yanzun nan, fice ka bani wuri" zuciyarsa na wani irin tafasa ya bar sashin na iya.
Shikenan saboda ummi bata da gata kowa ya goyi bayan Idris, ummi ko ƴar tsintuwa ce, ya ci ta ci albarkacin ita ma ɗan adam ce a kula rayuwarta, balle ita ma cikakkiyar ƴa ce a gidan, yadda idiris yake cika yana batsewa yana masifa, ka sam babu Allah a ransa kuma babu abun da ba zai iya yi ba.
Suka cigaba da shiri, sai washegari da safe, Iya ta kira ummi, da ta sha uban wanke-wanke.
Ta hura wutar kunu, ƙanwar Iya nata yabonta tana cewa taje ta huta.
Iya ta kira Ummi, ta kalleta ta ce "Ki je ki duba a tsummokaranki masu kyau ki wanke su, an fasa auren Idris da ke za a ɗaura, ki wanke kayan da zaki tafi da su, idan ya so daga baya a ɗinka wasu daga kayan auren da aka dawo da su a kai miki, atamfarki da na saya miki ki sakata gobe ɗaurin aure"
Sai da numfashin ummi ya kusa ɗaukewa, na wucin gadi, ta haɗiye wani irin yawu da taji tamkar tana haɗiye wuta ta ce "Iy..Iya aure kuma?"
"Kurma ce ke ba ki ji me na ce ba?"
Karon farko da ummi tayi yinƙurin yin musu da Iya ta ce "Iya makarantar fa? Kuma yaya idiris dukana yake yi, dan Allah kar ayi mini aure da shi, ko da wa aka yi mini auren na yarda amma dan Allah ban da yaya Idris, wallahi dukana zai yi"
"Ke dalla rufawa mutane baki, ba taimakonki ma za ayi ba, da wannan munin uban wa ye zai aureki ya zauna da ke? Ai idiris taimaka miki zai yi, kamata yayi ki yi mana godiya, idan ma bai zauna da ke ba, ai an samu asiri ya rufu, da mu da ku baki ɗaya, ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta, ki je ki tsami kayanki ki wanke"
Kuka ne ya ƙwacewa ummi, ta juya ta tafi ɗakinta, ta kalli viva da take zuba kaya a ciki, ina wasu kaya ma suka banda tarkacen tsummokara, kuka kawai take tare da tabattarwa da kanta kashinta ya bushe.
Karo na farko da ba ta taɓa neman taimakon kowa, wurin gaya wa wani matsalar ta ko damuwarta ba, amma ta fito cikin tashin hankali, ta tunkari sashin su Hashim tana nemansa, da ta rasa shi a gidan, ta fita waje a can ta samo shi wata majalissa da suke zama, ba kowa a wurin sai shi.
Ya miƙe tsaye ya taro ta, jikinsa ya bashi wataƙila ummi ta samu labari, cikin dakiya ya ce "Ummi lafiya?"
"Yaya magaji"
"Na'am Ummi"
"Yaya magaji, wai iya ta ce ni yaya Idris zai aura?" ta riƙo hannunsa ta ce "Dan Allah mu je ka bata haƙuri, dukana zai din ga yi, ya ce ya tsane ni a rayuwarsa dan Allah mu je ka bawa iya haƙuri, dan Allah kar a aura mini shi".
Hawaye take tsiyayarwa daga idonta, kamar an kunna famfo.
"Ummi ki yi haƙuri, ƙaddararki ce a haka, na yi iya yi na, sun ƙi fahimta ta, ki yi haƙuri"
Ummi ta ɗora hannu a ka ta ce "Shikenan na shiga uku, wallahi kasheni zai yi da duka, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku" tayi maganar jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali da kiɗimewa.
"Ki yi haƙuri ummi, ki cigaba da addu'a, babu abun da ya gagari Allah, idiris bai isa yayi miki abun da Allah bai yi miki ba"
Kasa magana tayi, sai kuka tana jin yadda fargaba da tsoron idiris ke ƙara shigar ta.
Muryar Hashim ta ji ya na cewa "Ki tafi gida, kar ki su yi ta nemanki, ki ja wa kan ki matsala"
Ummi ta jinjina kai, ta tafi hannunta a tana zubar da hawaye, gaba ta yi ta bar cikin gari, ta samu wani wuri tayi zamanta, ta din ga kuka, idanuwanta suka haye suka kumbura sosai da sosai.
Har azahar ta yi bata da niyyar tashi, sai da rana ta take sosai da sosai, sannan ta tashi ta tafi gida, daga nesa take hangen gidan, gabanta ya sake faɗuwa, tayi kwana ta tafi gidansu na'ima.
Maman na'ima ta tarar a tsakar gida tana girki, ta na yi mata magana, amma ba ta iya tankawa ba, kawai ta shige cikin ɗaki ta kwanta.
"Ummi ko ba lafiya ne?"
Ummi ta girgiza mata kai, kanta na yi mata wani irin ciwo, ta hau bacci.
Ƴan biki suka din ga tambayar Iya, ba za aje gidan su amarya kamu da suaran al'adu ba?
Iya ta ce musu ba sai an je ba, gidan su amaryar malamai ne, ba sa gabatar da al'adun aure, sai ɗaurin aure da tariya kawai.
Iya bata farga Ummi ba ta nan ba sai la'asar, hankalinta ya tashi aka shiga nemanta, nan da nan Iya ta kawowa ranta ko guduwa ummi ta yi, to ta gudu ta je ina?
Aka din ga nemanta, har tasha aka je, amma aka ce ba a ga ummi ba.
Hashim hankalinsa ya tashi sosai da sosai, saboda shi ya yi wa ummi ganin ƙarshe, dan sai da iya ta rutsa shi tana tuhumarsa a kan ko shi ne yayi wani abu, ya ɓoye ummi ko makamancin haka.
Ummi kuwa bayan ta tashi, tayi salla, maman na'ima ta bata abinci, ta ci kaɗan kanta na cigaba da sara mata.
Sai dai ƙememe ta ƙi yi wa maman su na'ima magana, balle ta gaya mata abun da yake faruwa.
Har aka yi sallar magariba tana gidan, tayi sallar magariba, sannan ta cewa maman ta tafi.
Ko da ta shiga gida, da yawan an watse, an tafi yawon nemanta, dan haka kai tsaye ta tafi ɗakinta, duk an baje itace a ɗakin, ta tutture su ta kwanta a kan buhunta.
Iya ta dawo afujajan, saboda tashin hankali, ta din ga tsinewa ummi, da mariya tare da aibata mariya da cewa duk baƙin halinta ne yake gudanawa a jinin Ummi.
Ummi na jiyo ta, tana jin wani abu mai ɗaci ya tsaya mata a ƙirjinta, da ta kasa haɗiyewa, ta sake ƙudindinewa tana kuka, tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.
"Laaa, ummi, nan ki ka zo ki ka kwanta ana ta neman ki?" Matar tayi maganar tana haske ummi da fitila.
Iya ta ce "Wace ummin? A ina?"
"Gata a nan a kwance"
Iya ta ƙarasa ta leƙa, ta ga ummi ta dunƙule wuri guda.
"Shegiya matsiyaciyar yarinya, ina ki ka tafi ki ka tayar mini da hankali?"
Ummi ta tashi zaune, amma ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Ba magana nake yi miki ba, sai na zo na hau ruwan cikinki? Wurin wani ɗan iskan ki ka je? Wurin maza ki ka tafi ko?"
Ummi ta yi shiru tana tunanin ta je wurin maza tayi me?.
"Dan ubanki tun safe, da yake ba mutunci ne da ke ba, ki ka saka ƙafa ki ka fice, ba zaki gaya mini in da ki ka tafi ba, tsinanniya ƴar matsiyata" salati wasu suka din ga yi, suna hana Iya tsinewa Ummi.
"Ku rabu da ni, ba ku san mugun halin yarinyar nan ba, riƙonta kawai nake yi, baƙin cikinta ya kusa kasheni, ku kalli ina yi mata magana ta yi mini banza, balle in san in da ta tafi, kuna ji ina tambayarta tayi shiru".
Hawaye wani na bin wani a fuskar ummi, amma ta kasa magana, kawai iya ta rarumi itace, ta sauke mata shi a kafaɗarta, gantsarewa tayi saboda zafi da ciwo, amma ta kasa guduwa, aikuwa ta cigaba da kwaɗa mata duk in da ta samu, da ƙyar ƴan biki aka hanata.
Wata ƴar yayar Iya ta ce "Haba Iya, yanzu wannan ƴar yarinyar da baki ki goya ba a bayanki, ki ke rafkawa wannan itacen, wannan ai mugunta ce. Ni tun da na zo gidan nan, wallahi ban ga yarinyar nan tayi wani abun ashsha ba".
"Bar ni marka da hatsabibiyar yarinyar nan, baƙin cikin uwarta bai kasheni ba, na ta zai kasheni, ni na fara tunanin ko dai ba jinina ba ce, dan kaf zuriyarmu babu wannan munin kamar baƙar buranya".
Aka yi ta bawa Iya haƙuri, ummi kuwa tayi mursisi ta kwanta, ta cigaba da kuka, tana jin kamar bayanta ya karye.
Ƙaiƙayin nan ne ya cigaba ta taso mata, duk yadda ta so ta daure, kasawa tayi, ta din ga soshe-soshe, kamar za ta zaee.
Da aka yi sallar magariba, ta tafi banɗaki tayi fitsari, ba tare da wurin ya tsane ba, ta tashi ta fito da jiƙaƙƙen wando, aikuwa ƙaiƙayi ya sake tasowa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin wurin da duhu, ya sanya ta kai hannu ta fara sosawa, wanda har ta shagala saboda azabar zafi da ƙaiƙayi.
"Ai dama na faɗa, na faɗa wurin maza ki ke zuwa ko ummi, wurin maza ki ka je tun safe ba kya nan" zabura ummi tayi, ta girgiza mata kai, saboda yadda Iya ta haske ta da fitila.
"Uban me ya kai hannunki gabanki, ki na soshe-soshe a duhuwa? Na faɗa wurin maza ki ke zuwa, kina sakarci, an ƙi yadda, na ce ayi miki aure, sun ce kin yi ƙanƙanta, yanzu meye Wannan?" rasa amsar da zata bata tayi, Iya ta din ga yi mata kwarmato, a cikin mutane da duk wasu kalaman cin mutunci da muzantawa, kunya baƙin ciki duk suka cika zuciyar ummi.
Saboda azaba a zaune ta yi salla, da ta motsa sai ta ji kamar ana yayyanka naman gabanta da reza, saboda wurin duk ya kwailaye.
Ummi haka tayi kwanan baƙin ciki, ta rasa yadda za ta yi, saboda abubuwa kashi-kashi, da wasu ma ko sanin kan su ma ba ta yi ba, da yawa wasu daga maganganun Iyan ba ta san in da suka dosa ba, amma abun da ta fahimta kawai shi ne, ta san cin mutunci ne maganganun Iyan, uwa uba kamata da ta yi tana susa take yi mata kwarmato, da cewa tana zuwa wurin maza, to ta je ta yi me?.
Hashim kasa bacci yayi, tsananin tausayin ummi na cin zuciyarsa, mussaman yadda ya ji Idiris ya na alwashin cin mutuncin ummi, da kuma azabtar da ita, da duk iya ƙarfin sa.
Duk yadda ya so yi wa idiris nasiha, yayi mursisi yaƙi ganewa, ya din ga kumfar baki tare da muzantar halittar ummi.
Bayan sallar asuba, Ummi ba ta fito ba, sai da Iya ta zo ta sakata a gaba, aka ce tayi wanka, da yawa sai a lokacin suka san cewa wai Ummi ce amarya.
Da yawa akwai magana a bakin mutane, sai da ana jin tsoron Iya, babu wanda zai iya tofawa.
Sai a lokacin Iya ta bata sabon kaya ta saka, ta nemi wuri ta zauna kamar gunki, kan nan a ƙasa tana aikin kuka.
Ƴan uwan Iya suka din ga tambayar, ina dangin mariya, duk ba su zo ba?Iya ta ce "Ai auren ne ba shiri, wancan Yarinyar iyayenta sun raina ƙoƙarin idris, shiyasa aka fasa auren na ce ya auri ummi, ƙara zumunci, dan haka daga baya zasu zo".
Ƙanwar babar idiris ta ce "Amma idiris yayi jihadi, na ji kin ce yarinyar ba ta ji, kina iƙirarin tana zuwa wurin maza".
Kowa ya din ga faɗar albarkacin bakinsa, a kan auren, wasu suka din ga cewa idiris ya samu yarinya ƙarama mai nutsuwa da ƙoƙarin aiki, wasu kuma sun hau maganar Iya sun zauna, suna yi wa ummi hukunci da shi.
Da azahar aka ɗaurawa ummi aure da Idris, a kan sadaki naira dubu takwas, mutane aka din ga yi wa ummi nasiha, ana ta cewa ta yi haƙuri, aure ɗan haƙuri ne.
Abun da ummi ta kawo a ranta shi ne, ashe sun san halinsa dukanta zai din ga yi, amma aka aura mata shi.
Cikin matsanancin tashin hankali, babar na'ima ta shigo gidan, dan tabattar idan da gaske ummi aka yi wa aure, aikuwa ta samu dahir, an riga an ɗaura aure ma.
Galibi maƙwabtan su, sun girgiza da jin wai ummi aka