a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau" ta ƙarasa maganar cikin zolaya.
Mariya dai ta rausayar da kai ta ce "Wallahi mama ba na ƙaunar abun da zai sake haɗa ni da iya, auren nan ya sake mayar da ni jikin su"
Mama ta girgiza mata kai ta ce "Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri ɗaya zaku zauna ba" mama tayi ta lallaɓata tana kwantar mata da hankali.
Can gidan dr. Kuwa Farida kamar za ta kama dr. Ta daka, saboda azabar kishi da bala'i, sai dai fafur ya mayar da ita kamar mahaukaciya ya ƙi saurarenta.
Yanzu da safe Abdul ya kawo kai zai shigo falo, ya ji yo muryarta tana ta ɓaɓatu, tare da amfani da kausasan malamai wurin ci masa mutunci.
Dr. Ya fito ya fice, ba tare da ya ce mata uffan ba, Kausar na ta ba ta haƙuri, Abdul ya shigo rai a ɓace ya kalli farida ya ce "Maama wannan abun da ki ke yi ba mutuncinki bane ba, duk maƙwabta na jinki, wannan zubar mana da mutunci ki ke yi"
"Haba yaya Abdul, ka san menene kishiya kuwa? Kuma kishiya da mahaukaciya ku baku san komai a kan wannan lamarin ba"
Farida ta ce "Rabu da shi, baƙin ciki ya kasheni, sai su ci duniya da tsinke da ubansa, bands butulci da zalunci irin na ɗan Adam, duk halaccin da na yi masa ya rasa da mai zai saka mini sai wannan rashin mutuncin, maimakon ya auro cikakkiyar mace da zan yi kishin na gaske da ita, sai ya ƙare a mahaukaciya, ai da ƴar tata ya aura shi ne ƙarshen soyayya"
Abdul ya ce "Koma wa ya auro, hakan dai zaki yi maama, wallahi Abba ba ma bin sa bashi, shi ne yake bin mu, menene bai yi mana ba na kulawa a rayuwar nan, shekara sama da ashirin yana ƙarar da ƙarfin sa saboda mu, kuma lokaci ɗaya duk sai mu haɗu mu goya miki baya mu rabu da shi? Bamu yi masa adalci ba, kuma wataƙila da baki kori ummi ba, da bai ce zai ƙara auren ba".
Muguwar ashariyar da ta luluƙa masa ya sanya shi waro ido, ba shiri ya fice ya bar su da kausar.
Ta kalli kausari ta ce "Ki shirya ki je gidan ta, ki dawo mini da ƴa ta, idan ta ƙi ki ci uban noor ɗin, tun da ba mahaukaciyar uwarta ce ta haifeta ba, sannan ki tabattar kin ci mata mutunci da sai ta zubar da hawaye"
Kausar ta ce "Zan yi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga fa yadda ki ke haki" gaba ɗaya farida sai ta fi kama da mahaukaciyar tuburan.
Noor kuwa ta miƙe abun ta a gidan ummi, ummi ta fara samun sauƙin wasu abubuwan saboda noor, ita take bata kuɗin motar zuwa makaranta boko da islamiyya.
Ummi ta ce mata yakamata ta biya gida, su gaisa da su farida, amma ta ce ita ba ta son ta je gidan ta tarar da su Abba suna faɗa.
Ɓangaren mami ma abubuwa sun yi mata zafi sosai, dan haryanzu Alhaji fushi yake yi da ita, ga ɓangaren su safiyya sun hura mata wuta, dan zuba ido suke yi, a danƙaro musu kayan lefe.
Sai dai zancen nema yake yi ya shiririce, dan Alhaji ma ya ce kar ta sake yi masa maganar auren raihan, shi na fari da ya yi masa, shi ne hurumin sa.
Kuma sanin halinta ya sanya yayi mata gargaɗi na gaske, a kan gidan da raihan ya saya wa ummi.
Kausar kuwa da ta je gidan ummi, hankali kwance ta tarar da su har da raihan suna kallo, babu abun da ya dame su.
Sai duk ta kasa sakewa ta yi rashin mutuncin da ta ƙullo, duba da yadda raihan yake muzurai.
Hankali kwance ummi ta karɓeta, ta karrama ta.
Ta ce "Dama maama ce ta ce noor ta koma gida"
Raihan ya ce "Saboda me?"
"Haka dai ta ce"
Raihan ya ce "To ai ni mun yi magana da dr. Ya ce tayi zamanta, ta din ga zuwa makaranta daga nan, amma noor kin ji abun da mamanki ta ce"
Noor ta tura baki ta ce "Ni na tambayi Abba ya ce na zauna, zan koma amma ba yau ba" juyin duniya, noor ta ce ba in da za ta je, ita fa maama ba son ta take yi ba, dan kullum cikin yi mata faɗa take da zaginta.
GAGARWA.
"Kai auwalu, daga kai har Alhassan kun kashe zuciyarku, kalli yadda rana ta take, sai baccin asara ka ke yi ba zaka tashi ba?" Tayi maganar tana dukan ƙofar ɗakinsa.
Amma ya ƙi tashi, ta gama ɓaɓatunta yayi burus da ita, ta ƙyale shi, ta koma sashinta, ta ɗebi ruwa tana alwala.
Ta ɗago za ta tashi, ta ji an yi ball da ita gaba, ta dungura.
Cikin tangaɗi da maye, ya ce "Ke banzar tsohuwa, ban gaya miki babu ruwanki da ni ba? Ko in tashi ko kar in tashi ban hana ki shiga harkata ba"
Iya da ƙyar ta motsa, wani irin jiri ya din ga ɗibar ta, taga gari yana jujjuya mata.
Kan ta ankara, ya sake surarta yayi jifa da ita kamar tsummokara.
Ta kurma uban ihu, amma ba kowa, ya din ga jifa da ita, tun tana ihu, ta koma kakari, jini ya fara zuba daga hancinta.
Ya sake surarta yana tangaɗi ya nufi wawakekiyar rijiyar da ke tsakar gidan.
Ayshercool
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
47
Gadan-gadan ya nufi rijiyar yana tangaɗi.
Amaryar kawu Ilyasu ta ƙwala ihu da salati, bayan ta shigo daga cefane.
Bai kai ga rijiyar ba, ya sake yin jifa da ita. Ta tafi da gudu tana kiran sunan iya, sai dai jini sai zuba yake daga hancinta.
Auwwalu kuwa cikin maye yake ta masifa "Sai da na gaya mata ba ruwanta da ni, amma taƙi ji, dama a ƙule nake da ita ta zagi babarmu jiya, duk ta tsane ni saboda bana ba ta kuɗi, ina kallo har kazata ta mara dan tana jin haushina, wallahi wiwina ta fiye mini wannan tsohuwar banzar" yana gama maganar ya juya yana tangaɗi ya fice.
Da gudu amarya ta fita tana kururwar neman agaji, mutanen gidan suka fara shigowa, Iya na kwance ko motsi ba ta iya yi.
Da ƙyar aka samo abun hawa, aka tafi da ita asibiti, daga can asibitin suka ce sai dai su je babban asibiti, ba zasu iya dubata ba.
***
Can garin kanon dabo kuwa, ummi kamar ta taka rawa, saboda ranar dr. Zai ɗaukko mata mama daga Maiduguri, ita da noor sai aiki suke yi, ummi cikinta ya fito sosai ganin tudunsa a rigarta.
Dr. Kuwa tun sassafe ya tafi maiduguri, domin ɗaukko mariya, da shi da abokinsa.
Can Maidugurin ma, an shirya musu kayan abinci, an yi wa mariya lalle, ta sha gyaran jiki kai ba ka ce ta haifi ummi ba, ana gobe dr. Zai je suka ɗan gayyaci mutane da ƴan uwa aka yi walima a can maidugurin.
Anty maryam ta kalli mariya ta ce "Wai duk murnar ganin angon ce haka? Bakinki ya ƙi rufuwa"
Ta ce "Haba Anty Maryam, kin saka na ji kunya, kawai zan ga ummina ne, nake ta jin daɗi"
"Kai mariya, ke sam ba ki da alkunya, ƴar fari ce fa"
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shekarar mu nawa ba ma tare, sai in din ga jin tamkar ta koma ƴar karamarta, ƴar baƙar ƴa ta mai kyau, na gyara duk wasu abubuwa marasa kyau da suka faru da rayuwar ƴa ta, wallahi anty maryam haryanzu ina jin tausayin ummi, rayuwar da ta yi ya kasa zama tarihi a wurina, kuma zuwan da ta yi na ƙarshen nan, kamar akwai wata damuwa da take ɓoyewa, fatana Allah ya sa ba wata matsalar ce a gidan auren nata ba, Allah ya sa ta daina shan wahala" kan ta kai maganar gaba ɗaya hawaye ya wanke mata fuska.
Mama ta ce "Mariya, ba zaki daina ɗorawa ranki damuwar abun da ya wuce ba ko? Ga bawan Allahn nam sun zo, ai sai su zata ko son shi ne ba kya yi"
Sallama dr. Yayi tare da abokinsa, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa.
Suka shiga ɗakin da aka saba saukarsu, ya kalli maman ummi, ya tuna maganar Farida, ta yi shar da ita, sai dai yayi mamaki ganin tana kuka.
Ya kalli mama ya ce "Mama lafiya kuwa take kuka?"
Anty maryam ta ce "Daga yin zancen ummi, ta hau kuka ta ƙi ta bar abu ya wuce, kullum ta tuna rayuwar ummi sai ta yi kuka, abu ya riga ya zama tarihi"
Mariya ta ce "Anty Maryam, tun tana kan cinya fa, aka ƙwace mini ita, kuma fa itakaɗai ce da ni"
Mama ta ce "To da mutuwa ta yi ya zaki yi?"
Da sauri ta ce "A'a ummi ba zata mutu ba, babanta ya mutu, ƙaninta ya mutu, idan ta mutu ya zan yi?"
Dr. Ya fuskanci jikinta haryanzu da saura, kuma tuna rayuwar ummi, ke saka jikin ya motsa mafi akasari, dan haka ya ce "Shikenan ya isa haka, ke da zaki koma kano ma, duk lokacin da ki ke so zaki ganta, ku koma kusa da juna"
Kamar ƙaramar yarinya take goge hawayenta ta ce "Ni sonake ta koma ƴar ƙarama kamar lokacin da iya ta ƙwace mini ita, in din ga goyata, idan na yi mata wanka na yi mata kwalliya, amma kawai iya ta ƙwace mini ita, ga zafin mutuwar mijina"
Ya ɗan ƙura mata ido, ba a ƙasa ummi ta ɗaukko shagwaɓa ba, duk da ummi ta ninka mariya shagwaɓa nesa ba kusa ba.
Ya kalli su Anty Maryam ya ce su ɗan basu wuri.
Bayan sun fita ya matsa gabanta ya ce "Haba maman ummi, idan mijinki ya mutu yanzu ba gani ba".
Ta kalleshi ta ce "Kai ba bashir bane, yaya yahaya ne, ba na so kai ma iya ta ce na kashe ka, wai iya ta ce ni na kashe baban ummi, ya za ayi na kashe shi?" Tayi maganar hawaye na cigaba da zuba.
"Ki manta da maganar iya, yakamata ace memorynki, yana tuna abubuwa masu daɗi, idan baby ki ke so ki yi addu'a Allah ya kawo miki ƙannen ummi, ki yi ta goyawa ita yanzu ummi tana da mai goyata"
Ta ɗan yi shiru kamar wadda ta farka daga bacci ta ce "Kai, ummi fa ta yi aure, kuma nima sai na haihu?"
Yayi murmushi, ganin kamar tunaninta ya dawo.
Ya ce "Idan ki ka cigaba da kuka, da tuna abun da ya wuce, ba zan tafi da ke ki ganta ba".
Haka yayi ta rarrashin ta, dama tuni su mama sun haɗa mata kayanta, suka raka su har mota, suka kama hanyar kano.
Gidan ummi, bayan sun gama aiki, noor ta ɗauki wayar ummi ta tafi ɗaki tana game.
Ummi kuma na falo tana kallo, sai ga Farida ta zo gidan, gidan da tun da ummi tayi aure, kusan shekara ba ta taɓa takowa ba.
Sai dai duk yadda ake kwatanta mata haɗuwar gidan ummi, sai yanzu ta tabattar da idonta ya gane mata.
Kamar babu komai ummi ta tashi cikin fara'a, kamar babu wani abu a ƙasa tana "Oyoyo, yau na yi babbar baƙuwa, sannu da zuwa anty" wani irin mugun kallo take yi wa ummi, da mamakin iskanci ne ko rainin hankali ya sa take wannan washe mata bakin.
"Ke saurara bana son karuwanci da iskanci, ni zaki yi wa bariki kina wani washe baki kamar bakin buhu?"
Ummi ta shafa bakinta, a iya saninta dai ba ta da ƙaton baki, ji ta yi kamar ta yi dariya amma ta maze ta ce "Ai baƙonka annabinka anty, kuma akwai hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da yake cewa wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya girmama baƙonsa. Ki zauna bari na kawo miki ruwa".
"Ki yi mini shiru ko na ɓarar da ke, ba ki da abun da zaki bani, ke da aka kawo mini ke cikin dauɗa da ƙazanta babu ko suturar kirki, har ke ki ke da abin bani, dan kin auri mai kuɗin da uwarsa ba ƙaunarki take yi ba, auren abun kunya, auren yaro ƙarami? Butulallaiya mara mutunci, wato abun da ki ka yi wa wancan ƴan ƙauyen shi ne nima ya biyo ta kaina, ki ka saka dr. Ya auri babarki, mahaukaciya da ba ta san ciwon kanta ba?"
Ummi ta ce "A'a fa, ni ban bayar da shawarar hakan ba, dr. Ya zo mini da maganar na goyi bayansa ɗari bisa ɗari, ko ba komai na yi ramuwar gayya, kuma ba fata ba ko aurena ne ya mutu, ko wani abu ya faru ina da wurin zuwa.
Da ki ke iƙirarin an kawo ni cikin dauɗa da ƙazanta, ai ba ke ki ka kula da ni ba, wan ubana ne, dan haka ke bai kamata a ji wannan gorin daga bakinki ba, ba ki isa ki yi mini gori ba a kan wannan, ko kin manta irin riƙon da ki ka yi mini?" Ummi ta ɗaga rigarta, gefen cibiyarta ya ɗan yi shati, ta ce "Na san wataƙila ke kin manta, kuma an yi sa'a jikina ba ya riƙe tabo, wannan ne kawai yayi saura kuma da shi zan koma ga Allah, har azaba da wuta ku ka yi mini ke da ƙanwar ki, wallahi da ramuwar gayya zan yi a kan ki, sai kin bar gidan dr. Kuma Alhamdilillah a yanzu dai Allah ya yi mini sutura da rufin asirin da ba kwa so, kuma wallahi ni Salma ina da abun da zan baki.
Amma ba wannan ba, na zata bayan na yi aure komai zai wuce, na yafe komai ya wuce, amma na fuskanci hali zanen duste ne, ba zaki canza ba, tun bayan da ki ka yi mini korar kare da na je gida aurena ya samu matsala, dan haka mun saka ƙafar wando ɗaya da ke, za ki ga mahaukaciya ganin idonki, yadda na ke shimfiɗa mulkina ba boka ba malam a gidan mijina, sai uwata mahaukaciya ta shimfiɗa na ta mulkin ba yadda ki ka iya, zaɓi ya rage naki, ko ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ko kuma ki shirya yin fito na fito da ni, tsakanina da ke babu ɗaga ƙafa, kuma ki gaya wa rahama, idan har muna raye sai Allah ya jarabceta da wuta, kamar yadda ku ka yi mini azaba da iata, dan wallahi ban yafe ba! Ko zan yafe muku komai, banda wannan"
Tirƙashi! Ummi ta shayar da farida ruwan mamaki, gani take kamar daga wani wurin maganar ke fitowa ba bakin ummi ba.
Cikin dakiya farida ta ce "Yaushe aka yi daren, da har gari zai waye, ki ke iƙirarin shimfiɗa mulki a gidan miji? Ɗa namiji ne fa da bashi da tabbas".
Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty farida, ai daren yayi tsayi, ke ce ba ki farga ba, sai da garin ya waye. Duk da kina iƙirarin uwata ba ta da hankali, amma a hakan ta din ga yi mini nasihar, jin tsoron Allah, riƙe addu'a da biyayya a aure, idan har tsoron Allah, addu'a da yi wa miji biyayya na saka a ci ribar aure, da yardar Allah ni da uwata mun fi ƙarfin masu bin ƴan tsubbu, kuma zamu zauna dai-dai a gidan miji, namiji ba shi da tabbas, ya danganta da yadda ki ka ɗauke shi ne, nawa yana da tabbas, haka babana dr., Ke ce baki iya tattalinsa ba ki ke ganin ƴan tsubbu sun mallake miki shi, shiyasa ki ka ga bashi da tabbas".
Farida ta saki baki, hangal tana kallon ummi, ba ta gama mamakin ba ummi ta ce "Yauwwa tun da bani da abun baki, zaki iya tafiya, na ga kin yi mini aike noor ta koma, in dai noor ce, sai dr. Ya ɗauke ta ya ba wa mamana, saboda kin raini ƴar ki da ƙiyayyarki, saboda banzan dalilinki, na an saka mata sunan mahaifiyata, duk shaƙuwar ɗa da uwa, ta fi son babanta a kanki, cikin sauƙi zan sanya ya karɓe ta ya bawa mama ita, ba zan so ta tashi da rashin imani irin naki da su kausar ba, masu baƙar zuciya ba, tayi aure tana hali irin naki ba, idan kin fita ki rufe mini ƙofar falo, kar ƙuda ya shigo mini bana son