ba zaka san ummi na magana ba, sai ka zauna da ita, a haka kamar ba ta magana.
Sai kuma ta sake cewa "Kawu, kaga da ka san in da mama take ita ma zaka ɗaukkota ka dawo da ita nan? Sai mu zauna ni da ita a gidan nan sai ku koma sabon gida"
Tausayin ummi ya kama shi, ya ce "Ki na kewarta ko?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"In sha Allah zan nemo in da take, zan haɗa ki da ita, sai dai ba zan so na kawo ta nan ita ma ta din ga shan wahala kamar yadda ki ke sha ba"
"To ai ba zan bari ta sha wahala ba, ni zan din ga yin duk wani aiki, idan na iya sana'a na din ga saya mata abubuwa, idan ka gano ta dan Allah kar ka kai ta wurin Iya, Iya ta ce ba ta son ta, wai mama mayya ce..."
"Ummi ya isa haka, ki daina tuna abubuwan da suka shuɗe wanda za su dinga ɓata miki rai, ki yi karatu sosai yadda maman idan ta gan ki za ta yi alfahari da ke"
Ta gyaɗa masa kai ta ce "In sha Allah" kai da ganin yadda ta ɗan kwaɓe fuska, ka san akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta da take burin amayar da su, sai dai babu wanda zai tsaya ya saurareta, to wa ma ya damu da ya zauna da ita balle aji matsalarta.
Cikin son kawar mata da wancan tunanin, ya yi murmushi ya ce "Ki na buƙatar wani abu ne ummana?"
"A'a bana son komai"
Ya ajiye mata ɗari bibbiyu guda biyar, ya ce "Gashi idan kina buƙatar wani abun ki yi amfani da shi".
Kallon kuɗin ummi take yi dan da yawa a wurinta, kan tayi magana ya tashi ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi.
Ɗakin farida ya wuce kai tsaye, ya tarar da ita tana saka kaya a gaban mudubi, ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ya dai?"
A take ya nemi karsashinsa da zafin zuciyar da ya zo da ita ya rasa, duk yadda ya so yi mata magana a kan ummi, sai ya kasa kawai ya tsaya yana kallonta.
"Kana buƙatar wani abu ne?" Kawai ya girgiza mata kai ya juya ya fice, yana jin baƙin cikin kasa yi mata magana a kan cin zarafin da ta yi wa ummi.
Duk da ƙonuwar cikin ummi, haka ta cigaba da yin aikace-aikacen gidan, kuma muddin ta fito ƴan uwan farida suka ganta, sai sun ci zalinta, ko sun aibata ta.
Hatta makarantar boko, kawu ya hanata zuwa, ya ce sai ta samu sauƙi tukuna.
Dan haka, a hakan take naɗe rigar ta, ta bar wurin ƙunar a waje tana shan iska, tana aikinta.
Abdul ne kawai yake tausaya mata yake yi mata sannu, dan shi har ga Allah yake jin matuƙar tausayinta.
Mopping kuwa a rana a gidan nan, sai tayi sama da sau sha biyar, wanke-wanke kamar gidan da ake rabon sadaka, banda ɗorawa da saukewa da kula da yaran baƙi, tana yi ana zaginta.
Wani lokacin haka zata fama ƙunar tayi ta kuka.
Kawu yahaya ya din ga kai ta dressing, Allah ya taimake ta ƙuna ta fara warkewa. Tana matuƙar son ta ɗauki jaririyar da antyn ta haifa, sai dai an ƙi bata damar hakan, daga nesa take hangen ƴar, zuciyarta har raya mata take ta ce a bata ta ɗauketa, amma da ta tuna hakan na iya haifar mata da cin mutunci, sai ta haƙura.
Farida ta je ta tarar da mijinta a bedroom ɗin sa, yana ta aikin takardu.
Ta zauna tana cika tana batsewa ta ce "Dr. Wurinka na zo"
Ba tare da ya ɗago ba ya ce "Ina jin ki"
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Jibi in Allah ya kaimu ne fa suna, haryanzu baka ce mini komai ba, baka bayar da kuɗin hidimar suna ba, kuma wuri nake so a kama ka sani, amma ka ƙi magana".
"A wannan karon babu suna, sauran ukun da aka yi Allah ya amfana, idan Allah ya kawo wata a gaba ayi".
A fusace ta ce "Ban fahimta ba?"
"To ki jira daga lokacin da ki ka fahimta, sai ki tashi ki bani wuri"
Ta miƙe tsaye ta ce "Yahaya ni zaka wulaƙant, na gama gaya wa mutane da taron suna ka ce ba za ayi ba"
"Hakika kawai zan yi, za a kawo raguna biyu manya, ayi hakika na sanyawa yarinya mariya, sai ki koma ki gaya wa mutanen babu suna"
"Mariya kuma? Wace irin mariya ana zaune ƙalau, sunan uwar waye mariyar da zaka sanya wa ƴa ta, haka muka yi da kai? To ba gara Salman da na ce bana so ba, a kan wata mariya, kamar dattijuwa"
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "To ki koma ki bibiyi tarihin fiyayyen halitta, zaki gane suna ne mai daraja da ma'ana".
Aikuwa ta hau ta din ga surfa bala'i, duk yadda ya yi ƙoƙarin sanar masa da cewa, hukuncin zaluncin da ta yi wa ummi ne, ya sanya ya hukunta da haka ya kasa, saboda tuni ta kai sunansa wurin malamai, a kan ko ya mayar da ummi, ko kuma duk izayar da zata yi mata ba zai iya magana ba, yarinyar ta gaji ta bar gidan.
Tun a haihuwar inteesar, ya so saka mata sunan mahaifiyarsa Salma, farida ta ce ba ta san zancen ba, ba ta so, aka saka sunan ta ta uwar, haihuwar khausar ma, ta ce sunan yayarta da ta rasu za a saka, wannan ma suna ta kai ruwa rana a kan ita gaskiya ya bari sai wani lokacin a saka Salman, tun da sanyan wa ƴaƴa sunan iyaye ba wajibi bane ba, wai Jidda za a sakawa yarinyar, tana son sunan.
Shi kuma ya sanyawa yarinyar mariya, sunan mahaifiyar ummi, wanda ita Farida sam hankalinta bai kai kan cewa sunan babar ummi bane ba.
Ya fice daga ɗakin ya bar ta tana ta sababi da kumfar baki, ya zo falo ya tarar da ƴan uwan farida na ta cin abinci da lemuka da nama zuƙu-zuƙu.
Ga ummi da ɗagaggiyar riga, tana ta mopping, tare da haɗa kwanukan da suka ɓata, sai ta kwashe zata tafi, sai a kirata a jefa mata wani kwanon.
Gyaran muryar da yayi ne ya sanya duk suka juya, mai neman gyale nayi su rufe jikinsu, masu gyara zama na yi.
"Yauwwa, ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala, da kyautar haihuwar mace da ya bani, ina kuma godiya a gareku wurin tsayawa tsayin daka, wurin kula da ƴar uwakku, duk da hakkina ne. Ina godiya sosai, dan Allah idan kun gama cin abincin, zaku iya tafiya gida, rahama zata iya cigaba da kula da ita. Ba za a yi taron suna ba, ga yanayin rayuwa, gara a tattala kuɗin tayi jego mai kyau, kuna iya tafiya idan kun gama kan magariba dan Allah, sunan jaririya mariya, za a dinga kiranta da noor"
Gaba ɗaya turus suka yi suna kallonsa, tun da suke zuwa gidan, su yi duk hauka da rashin hankalin da suke so, bai taɓa yi musu magana ba, sai yau, dan maganar tasa ta wani fannin kamar cin fuska.
Ummi kuwa washe baki tayi, jin an sakawa jaririyar mariya, duk da ba ta san dan sunan mahaifiyarta ya saka sunan ba, amma wani irin daɗi da farinciki ya ratsa ta.
A hankali ta ce "Allah ya raya noor takwarar mama"
Daga in da yake ya hango farinciki a kan fuskar ummi, yayi murmushi ya fice, yana tawasalli da farincikin da ya sanyata yana neman biyan buƙatunsa a wurin Allah.
Farida ta sha kuka, da yin alwashi kala-kala a kan yahaya, saboda yadda ya wulaƙanta ta, ya tozarta ta a gaban ƴan uwanta.
Suka din ga rarrashinta, tare da bata shawarwari daban-daban.
Babbar yayarsu ta xe "Duk sakacinki ne, waye ya gaya miki ana barin namiji haka, kyakywar mallaka zaki nema, ta mai da ɗan gida bawa, ki juya shi yadda yake so, kar ki yi bori da yawa, ki girgiɗe auren, duk cikinmu babu wanda yake cikin rufin asiri da kwanciyar hankali kamar ke, kar ki yi mana sagegeduwa, amma dole mu zage damtse".
Suka din ga zigata, ƙarshe kan sallar magariba suka watse daga gidan sai rahma, rahama kuma ba wani abun kirki take yi mata ba, saboda shegen son jiki ne da ita.
Bayan watsewar ƴan gidansu, ta ƙuduri aniyar ƙuntatawa dr. Ta hanyar nuna halin ko in kula ga yarinyar, gashi mutum ne mai mugun son yara, baya son ya ga ƙaramin yaro cikin damuwa.
Yarinyar shegen kuka ne da ita, ba ta taɓa ɗa mai kukanta ba, idan tana kukan sai ta yi banza da ita. Yayi ta maganar ta kula da ita amma ta share shi.
Ranar da aka yanka hakika kuwa, ummi ce ta zage ƙwanji, tsaf ta gyara hanjin nan, dan kuwa rahama ƙin fitowa tayi kan naman, ga rana na dukan kayan kitchen.
Abdul ne ma ya kama mata wasu abubuwan, ta kunna murhu ta ɗora sai ka ce babbar mace.
Sai azahar yayenta suka zo da ƙanwar babanta, suka tarar da ummi a akan aikin, suka din ga yi wa rahama da farida faɗa, wai dan me za su bar ummi ta yi aikin naman, sai ta sace ta cinye tukuna.
Abdul ne ya fusata ya ce "Yaya ummi ba ɓarauniya ba ce ba, ba ta taɓa ɗaukar abun da ba nata ba"
"Rufewa mutane baki kan in mareka, mara kunya fitsararren banza"
Ummi da jikinta yayi sanyi ta ƙyale musu aikinsu.
Suka gama aikin nama suka kwashe wanda za su kwashe, suka bar saura suka tafi, dr. Ya dawo ya tarar da farida da yaranta suna ta cin naman, ya leƙa ɗakin ummi tana zaune tana ta tilawar Alqur'ani ga gida ya buɗe da ƙamshi, ya shiga ɗakin farida ya ciko leda da nama, ya kai ya bata.
A gaban yara ta rufe shi da masifa, a kan ko dai ummin nan kishiyarta ce ba ta sani ba.
Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya bar wurin.
Cikin miyagun maganganun da take yi masa, har da gugar zanar ko wani abu ne tsakanin sa da ummi, da ya sanya shi bawa al'amarinta muhimmanci har haka.
Ta dire noor ta tashi ta bar masa falon.
Ummi kuwa da sauri ta wanke hannunta, ta hau naman nan da ci, dan tun ana suyarsa ƙamshin ya cika mata ciki, ranta ya biya.
Sai tayi aikin abinci da nama ba adadi, da ta gama rahama ta shiga ta raba abincin, ta kwashe naman ta hanata, koma ta bar da ɗan kaɗan sai dai ta haɗa da ƙanzo, dan haka nama tana kallo ba za a bata ba.
Ta fito falo, dan samun tsinken sakace, ta tarar da kawunta rungume da jaririya tana ta tsala uban ihu.
Da sauri ta ƙarasa in da yake ta ce "Kawu bani ita, ban taɓa ɗaukarta ba".
Ya miƙa wa ummi ita ya ce "Gata nan mai sunan mamanki, ina fatan ita ta so ki, kuma ta din ga ɗebe miki kewar mamanki"
Da sauri ta ce "Amin ya Allah, Allah yasa" ta karɓi yarinyar ta ce "Mamana ki daina kuka, mama tana da haƙuri, kawu ta zama kakarka kenan? Maman mama ko?"
Sai da ya ɗan dara ya ce "Tsohuwa ce kenan?"
Ummi ta ɗorata a kafaɗarta, tana jin soyayyar yarinyar a ranta, da aka saka mata sunan mamanta.
Haka ummi ta din ga zagaye da ita a falon, tun tana tsala ihun har tayi bacci.
Dr. Ya ce "Lallai ummana kin iya raino, tun da har gashi kakata tayi bacci, kawota ki je ki kwanta"
Ta bashi ita, tana kallon fuskar yarinyar, gashinta har goshi, jawur da ita.
Ya kalli ummi ya ce "Na ga ƙunarki da sauƙi, in sha Allah ranar monday zaki koma school gaba ɗaya"
Ta ce "To Allah ya kaimu"
"Amin, ki je ki kwanta sai da safe" ta juya ta nufi hanyar ɗakinta, kamar ta ce ya bata ƴar su kwana tare.
Ranar Litinin ta koma ta cigaba da zuwa makaranta, ranar da ta je islamiyya, Maryam ce ta fara ganinta, da sauri ta tashi ta nufi ummi ta ce
"ya jiki?".
Ummi ta ce "Na ji sauƙi"
"Kin warke duka ƙonuwar ta warke?"
Ummi ta jinjina mata kai alamar eh.
Ta ce "Alhamdilillah, dan Allah ki yi haƙuri, tun ranar da abun ya faru na kasa mantawa, kuma ban san gidanku ba, na gaya wa mamanmu ta din ga yi mini faɗa, ba ina sane na tureki ba ta ce in nemi yafiyarki".
Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai bakomai, na samu sauƙi".
"Amma ya aka yi ki ka ƙone a ciki da ruwan zafi?".
Ummi ta ce "Zubo mini yayi".
"To Allah ya ƙara afuwa"
Ummi ta amsa da "Amin".
Maryam ta liƙewa ummi, sai dai ummi sai ɗari-ɗari take yi da ita, saboda ba ta son wani abu ya haɗa su tayi mata tijara da tashin hankali, saboda ita bata iya faɗa ba, maryam kuwa dage ce, akwai masifa.
Ga maryam da azabar kashe-kashen kuɗi, banda kayan ciye-ciye da take zuwa da su.
Komai za ta ci sai ta bawa ummi, ummi kuma ta ce ba zata ci ba.
Tun tana ɗan ɗari-ɗari da ita, har ta ɗan fara sabawa da ita kaɗan.
Can gida kuwa kawu yahaya ya sanar musu matarsa an yi mata aiki, an ciro ƴa mace, sai dai likitoci sun ce sai matar ta huta sosai za azo dubiya. Saboda yana gudun su zo barka, Iya ta faɗi wani abun, da zai yi wa ummi mummunan tabo a nan. Dama kuma gashi ba shiri suke yi da farida ba, dan ita da Iya kar ta san kar ne, iyan za ta iya zuwa ta bar ta a falo ta cigaba da sabgoginta ba tare da ta bata ko ruwa ba.
Ummi ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa jaririya noor, idan uwar ta yasar da ita, sai ta ɗauke ta ta goyata, tayi ta jijjigata tana aikin gidan da ita a bayanta, dan ko da yarinyar ta fara dariya ummi ta fara yi wa.
Duk wannan soyayyar da ummi ke nunawa ƴar farida, bai sanya ta sassauta mata daga baƙar azaba da mugunta ba, da ita da ƴaƴanta da ƙanwarta, dan ummi ba sabon abu bane a wurinta, kaiwa ƙarfe ɗaya na dare ba ta kwanta ba, saboda azabar aiki.
Ga wani sabon salon zalunci, har maƙwabta sai su aiko ummi ta je, a sakata aiki, har wankin labulaye da carfet, sai a sakata, gyaran kaji da fige su, sai a saka ummi.
Makaranta kuma maryam na ta sake shishshigewa ummi, sai dai ummi ta fuskanci maryam ɗin na ƙoƙarin mayar da ita ƙarƙashin ta ta din ga mulkata ta zama kamar ƴar korenta, ummi ta cigaba da janye jikinta, maryam ta kasa samun damar hakan, saboda ummin na da mugun gudun abun hannunta.
Wasu lokutan haka ummi za ta zo ba ta ci abinci ba, maryam ta zo da abinci na alfarma amma fafur taƙi ci.
Kusan wata uku da haihuwar noor, kawu yahaya ya ce idan suka tashi suka koma sabon gida, sai su iya su zo, su ga noor, kuma su ga sabon gida.
Dan yana tsoron Iya ta zo ta saki baki ta faɗi wani abu da zata ɓata ummi, dan ya ƙudurce a ransa sai ya je yayi mata kashedi a kan ummi kan su zo, kuma gashi ba jituwa suke yi da iyalinsa ba, duk zuwa sai Iya ta ce an yi mata laifi, duk zalamar iya da son abun duniyarta ba ta ƙaunar zuwa gidan yahaya, wannan karon ma shi kawun ne ya takura su zo, kar abun ya zama surutu, an yi mata aiki ba su zo ba, ga kuma tariya a sabon gida.
Ɓangaren ummi kuwa sumul ta samu lafiya, kamar ba ta taɓa yin larurar sanyi ba, kuma lokaci zuwa lokaci, kawu yahaya ko bai sayi abu ya bata ba saboda matarsa, ya kan ɗan bata kuɗi ta sai abun da take buƙata.
Suka fara shirin tashi daga gidan, dama ƴan kayan ummi ba su da yawa tuni ta tattare su ta ƙulle.
Hatta su intee ummi ce ta haɗa musu kayansu, sannan ta koma ta haɗa na rahama, ga yau noor sai koke-koke take yi zazzaɓi na damunta, kai ka ce ummi ce ta haifeta, ta bata magani ta haɗa madara ta bata, sannan ta cigaba da aikin da ita a bayanta.
Suka gama haɗa kaya cif, washegari tun safe mota ta zo ta kwashi kayan su, zuwa sabon gida.
Gidan da suka koma, ƙato ne yafi wancan girma da kyau, a ɗan gaban unguwar da suke da yake, ƴan uwan su farida suka cika gidan, ummi na ganinsu suna ta binne-binne.
An canza furnitures, duk ta rabawa ƴan uwanta tsofaffin, ummi kuwa da tsohuwar katifarta ta dawo gidan, sai dai hakan ko a jikinta, ɗakinta shi ne na farko, baya cikin ainihin falon da zai sadaka da sashen kowa, Abdul sashinsa daban ba a cikin falon ba, da kitchen ɗin sa da banɗaki, a can gefe ɗaya.
Gidan ya ƙawatu yayi kyau matuƙa, ko ina ya sha flowers, sai ƙamshin sabunta yake yi.
Hatta ɗakin su intee kamar ɗakin wata amaryar, dr. Yayi ƙoƙari sosai da sosai, dama mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai da sosai.
Bayan magariba ummi ta gaji matuƙa, har wani jiri take ji, ga ciwo da mararta take yi, wanda tun da take bata taɓa jin irin ciwon ba.
Tana ta ƙoƙarin gyara nata ɗakin, dan kuwa ba ta gyara komai ba, tana ta fama da aiki, da rigimar noor.
Ƴan uwan farida suna ta cewa ta karɓe ƴar ta daga hannun ummi, kar ta shafa mata baƙi da muni.
"Ke!"
Ummi ta waiwayo ta kalli rahama da ke tsaye.
Ta ce "Bani kuɗin nan da zobena"
Ummi tayi saroro ta ce "Wane kuɗin?"
"Ba ke kika haɗa mini kayana ba?"
"Eh nice" ummi ta amsa.
"Kuɗin da suke cikin wardrobe ɗina, kuɗin anty farida ne"
Ummi cikin faɗuwar gaba ta ce "A'a anty rahama, ban ga kuɗi ba wallahi, kayanki kawai na haɗa miki a cikin akwatin da sauran kayanki a cikin jakunkunan da ki ka bani, dubu biyun nan ce kawai kuma kin ɗauketa, amma ban ga kuɗinki ba".
"Ke rufe mini baki ko na dalla miki mari, kuɗin anty farida ne dubu hamsin"
"Wallahi wallahi anty rahama ban gani ba, ki cajeni ki caje kayana, wallahi ban ɗauka ba" ummi tayi maganar jikinta yana rawa tana tuna irin tozarcin da aka yi mata lokacin da iya ta ce ta yi mata sata.
"Rahama ina kuɗin ne? Ta baki?"
"A'a fa sai kin zo da kanki, ta ce ita ba ta ɗauka ba".