nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni".
Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo.
Ta tarar da noor a ɗakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiɗa.
"Mama" ta kirata kamar yadda take kiranta.
Noor ta ɗago ta kalleta.
"Meyasa ba kya jin magana ne?"
"Me nayi?" Tayi maganar cikin tura baki.
"Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?"
Noor ta ce "Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina".
Ummi ta ce "To ai ke ɗin ce ba kya ji mama"
"Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya"
"Au ba ki ji faɗan da nayi miki ba ko? Zaki ga a auro muku kishiya, idan aka auro wadda zata din ga hanaki abinci, tashi ki bar mini ɗaki tunda ba kya ji"
Noor ta ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na daina"
Can falo kuwa, ganin farida ta haƙiƙance tana ta bala'i, ya sanya dr. Bar mata falon shi ma.
Ya rufe ƙofar ɗakinsa, ya zauna ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya kara a kunnensa.
Amsa sallamar ya yi, sannan ya ce "Barka da yamma, kuna lafiya?".
Yaya maryam ta ce "Lafiya ƙalau ya iyali?"
Ya amsa da "Lafiya lau Alhamdilillah, ya mai jikin kuma?"
"Jikinta da sauƙi Alhamdilillah, zasu sallame mu ma yau, ta warware zazzaɓin ma babu"
Ya amsa da masha Allah "Ranar monday ne appointment ɗin ta na ganin psychiatric doctor ɗin nan ko?"
"Eh in sha Allah"
"To, ko zaku bari ta ƙara warwarewa daga zazzaɓin, kafin ku je ganin likitan"
"To shikenan, ana samun cigaba sosai da sosai, domin kuwa shekranjiya take cewa ita fa kamar ka zo, kamar ta ganka ko mafarki take yi".
Dr. Yayi murmushi ya ce "Masha Allah, da haka da haka, in sha Allah zata warware gaba ɗaya, a cikin watan nan zan shigo in ga jikin nata in Allah ya yarda".
Yaya maryam ta ce "Ubangiji Allah ya kawo ka lafiya, muna ta godiya Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya jiƙan magabata".
Ya amsa da Amin.
Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala'in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake ciki, dan taga kamar ya ɗau maganar noor serious.
Gaba ɗaya ma dariya ta bashi, dan haka ya shareta ta cigaba da banbaminta
***
Haka nan ummi ta ɗan damu, kwana biyu shiru ba Raihan babu labarin sa, ya daina nemanta a wayar ma, kamar za ta damu, kuma ta basar ta manta, ta cigaba da sabgoginta.
"Hi dear" taga message ta what's app ɗin ta, what's app ɗin da ta fi ƙarfin sati uku ba ta buɗe shi ba saboda rashin data, sai yau da ta samu ta saka ɗari biyu.
Baƙuwar lamba ce, ba ta san waye ba, dan haka tayi replying da Assalamu alaikum.
Ta tsaya ta ƙurawa message ɗin ido, hi dear, dear kalma ce da ake iya gaya wa kowa, amma mussman wanda yake da muhimmanci.
To ita akwai wani wanda take da muhimmanci a gare shi, da har zai ce dear.
Tayi guntun tsaki da ta tuna, akwai mutanen banza a what's app, wanda ba su sanka ba, amma su yi maka maganar banza.
Ta cigaba da shirinta na tafiya wurin aiki, ba ta taso ba sai ƙarfe huɗu da rabi, a hankali take tafiya, sai dai wata mota ta cika mata kunne da horn. Ta matsa gefe amma ya cigaba da yi mata horn.
Gefe ta koma ta bar wa motar hanyar, ta cigaba da tafiyarta.
"A wannan yangar da iyayin naki, sai kin fusata mutum ya ture ki" cak ta tsaya, ta waiwayo da mamaki ta ce "Laa raihan, yi haƙuri ban san kai ne ba".
"Eh shi ne ki ka bar mini hanyar, wato na ci kaina, ban isheki kallo ba"
Ummi ta ce "Eyya ba haka bane ba, ban san kai bane" tayi maganar tana kallon sa, idonsa yayi ja, kamar daga wani wurin yake.
"Wucewa na zo yi, na san sai yamma ki ke tashi, na tsaya ki fito mu tafi".
Ɗan shiru ta yi tana kallon sa, ba ta son shiga motar nan tasa, kar a fara zargin wani abu.
Ya ɗan marairaice ya ce "Nayi awa a wurin nan ina jiranki, dan Allah kar ki ce a'a".
Ta ce "To" tabi bayansa, suka nufi motarsa.
Suna tafe a hanya, har lumshe ido take yi, saboda gajiya.
"Yaya ummi kwana biyu ko ki neme ni, anya za ayi zumuncin nan da ni kuwa? Na yi busy sosai kwana biyun nan, ko waya bamu yi ba, kuma baki nemi in da ƙanin naki yake ba".
"Yi haƙuri ba haka bane ba, zan din ga kiranka in sha Allah".
"Allah ya sa, ya karatu ya ɗalibai?"
Ta amsa da"lafiya ƙalau Alhamdilillah"
"Masha Allah, nima kwana biyu Alhaji ne ya sakani aiki, ya ga ina sararawa bana aikin komai, ina ga gani yayi sharholiya ta yi mini yawa, ya sani aiki ko cikakken lokaci bani da shi, duk na rame na zama baƙi"
Ummi ta ɗan yi murmushin yaƙe, cikin fargabar abun da ka iya biyo bayan maganar sa, wataƙila cin zarafin kalar fatarta.
Bai damu ba ya cigaba da maganar sa, "Ni fa yunwa ma nake ji, ko mu tsaya mu ci abinci?"
Tayi farat ta ce "A'a, na ƙoshi ma ai, a ƙoshe nake ai"
"Yaya ummi kenan, da abinci ki ke zuwa kenan? Tun safe fa kina wurin nan, to idan kin zo da abincin ki din ga ci kina rage mini, dan ni yau tun da aka kirsheni a wuri ɗaya tun ina ganewa har na daina, bari na yo takeaway a wannan wurin abincin". Ta ce "To".
Ta kai mintuna sha biyar a motar, sannan ya dawo da manyan ledoji, ya tarar ta sauke facemask ɗin ta.
"Sannu na bar ki kina jira ko? Tuwo na so in samu, babu sai shinkafa ni kuma damuna take yi"
Tayi murmushi ta ce "Kana cin tuwo kenan? Abdul ɗin gidanmu baya son tuwo"
"Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata"
Tayi dariya ta ce "Ka fi son dai a din ga ccacanzawa"
"Yauwwa, ba kullum abu ɗaya ba"
Yau dai yayi sa'a, ta ɗan saki jiki kaɗan, dan yau har da dariya.
Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa.
"Ummi"
Ta ce "Na'am"
"Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daɗi, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?"
Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi.
"Babu"
"Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?"
Ta sunkuyar da kai ta yi shiru.
"No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini"
"Babu" ta sake bashi amsa.
Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta.
Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce "A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?" Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba.
"Bayan ƴan uwa let's be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama ƴan uwa kuma abokai saboda Allah"
"To in sha Allah"
Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce "Ungo naki" ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhh".
"Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare" ta jinjina kai, ta fice daga motar.
Addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banɗaki, ta wuce ta shiga har ɗakinta ba ta haɗu da kowa ba.
Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma ɗakin ta duba ledar da Raihan ya bata.
Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad.
Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaɗai?.
Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida.
Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita.
Ummi ta ce "Yaya Abdul kana nan dama?"
"A'a yanzu na shigo, wani ɗan rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buɗe shago a tal'udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba".
Ummi ta ce "Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so"
Ya kalleta ya ce "Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen"
"Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi"
Abdul ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan".
"Yauwwa zai yadda ma in sha Allah" tayi maganar tana addu'ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata.
Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya.
Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa'arta.
Noor ta din ga murna ta ce "Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu".
Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba.
Masu nema daga farko dan Allah ku duba a watpad
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA!*
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
24
Ummi ta kalli noor ta ce "Dan Allah noor kar ki gayawa kowa kin ji"
Noor ta ce "Yaya ummi ina da wayona fa, ba wanda zan gayawa wallahi, kazar nan tayi daɗi sosai"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa maman".
Raihan kuwa tun da yaje gida, ɗakinsa ya wuce ya samu ya kwanta ya huta, ana kiran magariba ya fice, da aka idar da sallar isha'i, ya tafi gym domin motsa jikinsa.
Bai sake komawa gida ba sai wajen ƙarfe goma, ya shiga sashin mami.
"Wai yau ina ka shiga ne, tun safe ban sake saka ka a idona ba?"
"Kasuwa na je" ya bata amsa tare da ɓoye mata aikin da Alhajinsu ya sanya shi.
"Aikuwa ka kyautawa kanka, Allah ya taimaka" ya amsa mata da "Amin"
Washegari da sassafe, raihan ko karyawa bai yi ba, ya ɗauki mota ya fita, dan yaje ya ɗauki ummi kar ta makara, dama yau zai zauna da cheif accountant na mahaifinsu su cigaba da aikin da ya saka shi.
Ƙarfe bakwai da rabi, ummi ta ga kiran raihan.
Ta ɗaga wayar tare da yin sallama.
Ya amsa mata ya ce "Ina waje, idan kin shirya ki fito mu tafi"
Ummi ta ce "Eyya, sai takwas da rabi nake fita ai, kayi tafiyarka wallahi bakomai, na gode sosai "
Raihan ya ce "No, ina jiranki, idan kin kammala sai mu tafi, na zaci da wuri ki ke fita sosai, shiyasa ko karyawa ban yi ba na fito".
"Amma ai zaka gaji".
"Bakomai take your time"
A gurguje ummi ta kammala duk abun da zata yi, saboda kar ta bar shi yana jira, ta juyo abincin breakfast ɗin ta, a flask, lokacin farida ko tashi ba ta yi ba, ta riƙo niƙab ɗin ta a hannu ta fice.
Yana zaune a cikin mota, ya kashingiɗa yana danna wayarsa, ta buɗe ta shiga ta zauna.
"Raihan, ka yi haƙuri dan Allah, na barka kana jira, na ce ka yi tafiyarka ka ƙi".
Ya gyara zamansa ya ce "Ai na ce ki yi a hankali ki shirya a tsanake, shi ne ki ka fito a haka kamar an koro ki?"
"Ai bana son in barka kana jira ne, jira babu daɗi, ina kwana ya su mami?".
"Lafiya ƙalau, duk suna lafiya, ya gida?".
"Alhamdilillah" tayi maganar tana ƙara kintsawa, ya kalli jakarta data buɗe, kamar jakar wanzamai, duk ta tsufa, daga ƴar ƙaramar robar Vaseline sai turare ɗan ɗuri, da tarkacen kuɗin da idan ka tattare su ba su fi naira ɗari da hamsin ba.
"Me ma ki ka ce sunana?"
Ta ce "Raihan"
"Ba rayyan sunana ba fa, raihan"
A ɗan marairaice ta ce "Ai haka na ce"
Ya ce "Sake faɗa to"
Ta ce "Raihan"
"Idan na ce iyayi yayi miki yawa ki ce ba haka ba, Kamar rain kamar rayyan ki ke cewa fa"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Ni dai bana wani iyayi".
"To sake cewa raihan in ji"
"Ba zan faɗa ba" tayi maganar tana dariya, har dimples ɗin ta suka lotsa.
Ya sanya seat belt yana murmushi, ya ce "Meye a cikin flask ɗin nan ne, ƙamshinsa ya cika mini hanci?"
Ta ɗago idonta ta ce "Kai na zubowa abinci ka ce baka karya ba, kunun alkama ne da ƙosai, ban sani ba ko zaka iya ci?"
"Saboda me ba zan iya ci ba?"
"Abincin gargajiya ne, na ƴan ƙauye zaka iya ci?"
Juyowa yayi yana kallon idonta, "Ke ƴar ƙauyen ce da ki ke iya ci?".
"Eh mana, ni ƴar ƙauyen gagarawa ce jihar jigawa".
"Ban ga alama ba, na gode sosai, dan aikin nan ko cikakken abinci bana iya ci, na kasa nutsuwa sai mun kammala, Alhaji ya ga sharholiya tayi mini yawa ya haɗani da aiki, ashe aikin ja ne ba ƙarami ba".
"Allah sarki, Allah ya baka ikon yi, ni ko a mintuna goma da zan sake ganinsa ya sakani aikin da na so, sai dai ba zan sake ganin baba ba, Allah yayi masa rahama"
Cikin kulawa raihan ya ce "Eyya, Amin ya Allah, Allah ya jiƙansa"
Ta amsa da amin na gode.
"To mama fa, tana raye?" Ta ce "Ina ga tana raye"
"Kamar yaya kina ga? Tana ina ita?".
"Rabona da ita tun ina shekara bakwai da baba ya rasu, ban ƙara ganinta ba".
"Amma meyasa?".
"Bakomai" ta faɗa tare da ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗaci a ƙirjinta.
Ta ɗaga hannunta tana ƙoƙarin sanya niƙab ɗin ta.
"Wai shi wannan niƙab ɗin meye amfanin saka shi, kullum ke ko gajiya ba kya yi ne?"
Ummi ta ce "Ai saboda idona".
"Meye da idon naki?".
"Bana son mutane su din ga tanka mini ido, ko fatata, shiyasa idan na saka shikenan ba wanda ya gani, ana cewa idona irin na akuya, ko na mage, duk bana so shiyasa bana son a din ga gani" tayi maganar a ɗan shagwaɓe da take ɗabi'arta, wanda ita a zahiri cikin damuwa ta yi maganar.
"Ummi"
"Na'am"
"Meyasa zaki bari surutun mutane ya yi tasiri a zuciyarki? Ke ki ka yi kanki, duk wanda ya tanka ki, kice masa tubarkallah idan yana da dama ya sauya abun da Allah ya yi miki. Idanunki me kyau ne masha Allah, meye da kalar fatar ta ki, dan Allah idan dan haka ki ke saka niƙab ɗin nan ki daina".
Murmushi kawai ta yi, irin ba zaka gane ɗin nan ba, hakan yayi dai-dai da ƙarasowarsu ƙofar gate ɗin wurin aikin su ummi.
Ummi ta ajiye masa kayan abincin, ta ce "Na gode sosai, sai anjima"
"Idan an tashi ki jirani, saura ki tafi" ba ta ce komai ba, ta buɗe ta fita.
Ya daɗe yana nazarin, ta ina zai taimakawa ummi, babanta ya rasu, ba ta san in da mamanta take ba how? Kuma yau ta ɗan sake da shi fiye da da, lallai idan ya cigaba da lallaɓata har ya ƙara saninta sosai da sosai, dan ya fuskanci akwai abubuwa na damuwa sosai da sosai a cikin rayuwarta.
Kiran wayar accountant ne ya dawo da shi hayacinsa, ya ja motarsa ya tafi.
A motar ya gama karyawa, sannan ya tafi babban office ɗin su, in da suke aikin lissafin.
Aiki raihan suke yi, suna ta aikin lissafi, amma rabin hanakalin raihan yana kan ummi.
Da suka tashi ma daga aikin, a waje ta tarar da shi, ya zo yana jiranta ya ɗauke ta ya mayar da ita gida.
Washegari da safe ummi na ta ɗawainiyar sallamar kowa, masu tafiya makaranta su tafi, ta gama abun da take yi, ita ma ta fara nata shirin, Abdul ya sameta a kitchen hannunsa riƙe da waya.
Ya ƙarasa ya miƙa mata wayar, ta karɓa ta kara a kunnenta.