Raihan ya taimaketa da ya ɗaukkota, ba dan haka ba, sai ta ci uwa tafiya, kafin ta hau mota, dan kuɗin motarta ba yawa a jakar.
Har ta shiga gida, jikinta ƙamshin turaren raihan yake yi, kasancewar gaba ɗaya motar ma ƙamshin turaren take yi.
Yana zaune a motar ya kira lambar ummi, tana sauri zata shiga gida, wayarta ta fara ringing, ta ciro wayar ta ɗaga tana hello.
Kashewa yayi jin muryarta ce, yayi saving number da brown eyes.
Ummi ta shiga gida tana fatan Allah ya sa ba wanda ya ganta ta sauka daga motar raihan.
Bayan sallar isha'i maryam ta kira ummi a waya, tare da yi mata ciwon bakin bata nemanta.
Sosai suka fara hira da ummi, sai dai hirar ta daina yi wa ummi daɗi, lokacin da maryam ta fara yi mata zancen ita yaushe za ta yi aure? Ummi ta ƙarƙare hirar suka yi sallama.
***
GAGARAWA
Masifa da bala'i a gidan idris, kamar karnuka tun maƙwabta na shiga cikin lamarin, ana ƙoƙarin sasant al'amura, abu ya gagar a gaban yaran suke faɗa, suyi ta zage-zage da ashar kamar maguzawa.
Yarinyar sa ga fari kuwa, tun da aka je da ita family house, aka yi mata gori, Hindu ta wanke ƙafa taje har gidan tayi musu tijara da rashin mutunci.
Babu wanda hindu take saurarawa a dangin Idris, tun daga kan Iya har sauran mutanen gidan.
Dan haka Idris ya fara tunanin ƙara wani auren, ko ya samu sassaka daga masifa da bala'in hindu, gashi kamar tayi masa asiri, duk tijara da bala'in da zata yi masa ba zai iya sakinta ba.
Hashim kuwa ya kasa samun nutsuwar samun matar aure, saboda gaba ɗaya hankalinsa a kan ummi yake, sai dai iya tayi masa kandagarki, dan ta riga ta ce ba ta lamunce ba, dan haka ya san ko giyar wake ya sha, tun da iya ta furta ba ta so, babu mai goya masa baya.
***
Ƙarfe kusan goma na dare, Ummi ta yi wanka tana shirin kwanciya bacci, dan washegari asabar ce, za ta je islamiyya da safe ta koyar da yara, dan haka da wuri take son kwanciya dan ta kammala aikinta da wuri ta tafi da safe.
Kallon baƙuwar lambar take yi, sannan ta ɗaga tayi sallama.
Ba ta ɗau muryarsa ba da farko, dan haka gabanta ya faɗi, ko bisa tsautsayin wrong number, wani namiji bai taɓa kiranta ba.
Sai da ya ce "Yaya ummi" sannan ta ɗau muryar.
Ta ce "Au babban mutum, yanzu na ɗau muryarka ai".
"Ke, Alhajinmu ne fa kawai yake faɗar sunan da ki ka faɗa, sai Hajiya, waye ya gaya miki wannan sunan?".
Ummi ta yi murmushi ta ce "A bakin maryam na ji, kuma ai sunanka babbane, ba a faɗarsa anyhow"
"To sai ki ce Raihan ai"
"To shikenan, ya mami da su Hajiya?".
"Suna lafiya, ta kira ki kuwa?"
"Eh mun yi waya da ita, ka kyauta ai".
Ya ce "To Allah ya haɗamu a ladan baki ɗaya"
Ta amsa da "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum"
"Ya aikin?"
"Aiki Alhamdilillah"
Ya ce "Masha Allah, kiranki nayi na kwashi gaisuwa kawai, tun da mun yarda mu yi zumunci, tun da maryam ba ta nan, sai mu mu din ga yin zumuncin. Dama bani da abokai na yi ƙawa, ƙawar yayata ta zama ƙawata".
Ummi ta girgiza kai ta ce "Mace da namiji ba sa ƙawance ai, ƙanina ne kai".
Yana daga kwance ya tashi zaune ya ce "To shikenan, muje a haka yaya ummi"
Tayi murmushi ta ce "Sai da safe".
Ya ce "Allah ya tashemu lafiya yaya, sweet dreams".
Ummi ta ajiye wayar tana cigaba da murmushi. Ta bi wayar da kallo, ƙanne suna da daɗi, ta so ta rungumi su intee kamar ƙanneta, amma suka nuna mata ba haka ba, shima Abdul alaƙarsu farida ta saka musu ido, da ta gansu tare sai zagi da cin mutunci.
Ɓangaren Raihan ma, wayarsa ya bi da kallo, yana kallon lambar ummi da ya sakawa brown eyes, sanyin halinta ya burgeshi, abun da mami ta gaya masa game da ita, ya sanya masa tausayinta, dan haka yake jin ko na ƙanƙanin lokaci ne, zai shiga rayuwarta ya fahimci ta ina zai taimaketa, kuma zai yi mata addu'ar samun miji nagari mai ƙaunarta.
A rayuwarsa ummi ce mace ta farko da ya ji yana son shiga rayuwarta, idan ba iyayensa ba sai ƴan uwansa mata, ba ruwansa da shiga harkar kowacce yarinya, duk da suna yi masa shishshigi, saboda Raihan kyakykyawa ne kamar maryam, kamar sa ɗaya da mahaifinsu.
Washegari tana makarantar islamiyya, tana fama da ɗalibai, kusan ƙarfe goma da rabi, ta sake ganin kiran Raihan.
"Ina kwana yaya"
"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau, ya nake jin hayaniya kina ina ne?".
"Na je islamiyya, ne ina tare da ɗalibai" .
Ya ce "Ok, ashe sayyada ce, mu yi waya idan kun tashi, dama kira na yi idan kina lafiya"
Ta ce "To godiya nake, Allah yayi albarka"
Yayi murmushi ya ce "Dan Allah ki saki muryarki ki daina iyayi"
Dariya ce ta kamata, ta ce "Ka cuci iyayi kuwa"
"Am serious, na yi recording wayar nan, zan tura miki ta what's app ki ji yadda ki ke magana, sai anjima take care" yayi maganar a hankali.
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
23
Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faɗar Raihan rigiamamme ne.
A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi.
Ya sauka daga kan gadon sa, ya shiga banɗaki ya yi wanka yayi brush, ya sanya kayansa ya fita.
Sashin mami ya nufa, duk ba su tashi ba, ya duba kan dining an ajiye masa kayan breakfast da masu aiki suka girka.
Ya buɗe foodflask, ya tarar da doya ce da ƙwai, sai kayan tea, doyar ta ja mai sosai da sosai.
Yayi guntun tsaki, ya fice ya nufi sashin Hajiya, sai dai kai tsaye ɓangaren mahaifinsu ya wuce.
Yana zaune yana shan tea, gefen sa ƙaton tray ne, ɗauke da kayan marmari yana kallon labarai.
Ya ɗaga kai ya kalli raihan ya ce "Dama kana gidan nan?"
Raihan ya ƙarasa kusa da shi ya risuna ya ce "Barka da safiya"
"Yauuwa barka babban mutum, ka tashi lafiya?"
Alhamdilillah, ya amsa yana zama a kusa da Alhajin.
Ya ce "Alhajin Allah kana sararawa, ka bar mu a nan ka je ka huta ka dawo, ka ƙara fresh sosai"
Sanin halin raihan, na zolaya ya sanya shi yin murmushi ya ce "Ina wani hutu Raihan? Ina can ma aiki nake yi, haryanzu ban huta ba, zuwa yanzu yakamata ace ku kuke kula da komai, amma sai dai nayi da kaina, yayyenka sun fi mayar da hankali a kan shashashanci".
Cikin kulawa raihan ya ce "Ka yi haƙuri, ka daina damun kanka, kai ka ce ƙuruciya ce take damunsu, za su daina".
"Zuwa yaushe kenan? Idan ƙuruciya ce kai meyasa ba ka yi?"
Raihan ya ce "Haka ne, amma dai kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, abun da su Yaya Salim suke yi, ka ɗauka jarabta ce daga Allah.
Kalli shekarunka sun ja, ba hawan jini, ba ciwon suga, ga mu Allah ya baka, ga tarin dukiya da al'umma suke amfana ga Hajiya ga mami dukkan mu naka ne, idan ka duba wannan ni'imomin sai ka ga abun da suke yi bakomai bane ba, dan Allah kar ka saka damuwa a ranka wani ciwon ya kama mana kai".
Kallon Raihan yake yi, cikin tsananin soyayya da kulawa, ya tsiyayo tea cup, ya bawa raihan sannan ya ce "Madalla da yaron kirki, nasiharka na ratsa mini zuciya, in sha Allah zan cigaba da yi musu Addu'a"
Raihan ya ce "Yauwwa father like no other, we are proud of you, ka cigaba da yi musu addu'a in sha Allah zai zama labari"
Alhaji Tahir ya ce "Mahaifiyarka na ganin kamar laifin Hajiya ne ya sanya su lalacewa, amma kamar hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyya".
"Haba Alhaji, kar ka ɗorawa kowa laifi, Hajiya ba ta da sakaci ko kaɗan".
"Haka ne, ina son na roƙeka wata alfarma ne".
Raihan ya gyara zamansa ya ce "To Alhaji, Allah ya bani ikon yi".
Ya ce "Yauwwa, lissafin da muke yi na shekara shekara da manager, da kai nake so ku yi, a fitar da zakka, a fitar da wanda za a biyawa umara, harajinmu na nan gida da sauran ƙasashe, da duk wasu gyare-gyare da zamu yi, idan ku ka gama sai ka kawo mini na duba"
Raihan ya ɗan yi shiru yana nazari, "Ya dai na ji ka yi shiru?"
Raihan ya ɗago ya ce "Babu damuwa in sha Allah za ayi, zan je na same shi".
Alhaji Tahir yayi murmushi ya ce Yauwwa "Babban mutum, ka ga atleast na sake na huta sosai da sosai"
Raihan yayi murmushi yana cigaba da zuƙar shayi, nauyi ne mai girman gaske Alhajin ya haɗa shi da shi, dan aiki ne ba ƙarami ba.
Ya shanye shayin, ya miƙe tsaye ya ce "Bari na ƙarasa wurin Hajiya mu gaisa"
"To shikenan babu laifi"
A sanyaye Raihan ya tashi ya nufi sashin hajiya, ba zai iya cewa mahaifinsu a'a ba ne ba, amma wannan aikin kamar yayi masa yawa, ba zai iya jajircewa ya yi shi, kamar yadda shi Alhajin zai yi ba.
"Babban mutum ya dai, na ga kana tafiya a hankali, ko yunwa ka ke ji ne?"
Ya zauna yana faɗin "Eh, ina ɗan jin yunwa ma, me ku ka yi?".
"Ka san halinsu, kowa dafe-dafensa yayi, ni kuma tuwo na saka a ɗumama mini na sha da tea"
"To ni ma zan ci tuwon"
Ta ce "To bari a kawo, har da man shanu kuwa da yajin daddawa, mai ɗan karen daɗi"
Yayi murmushi ya ce "Hajiya kenan, ina su Yaya Sagir?"
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Ba su tashi ba".
Ya jinjina kai sannan ya ce "Yauwwa Hajiya, kin tuna yarinyar nan ummi? Ƙawar maryam?"
Ta ce "Eh, ya aka yi?".
"Yauwwa Alhamdilillah, dan Allah me ki ka sani a kanta?"
Hajiya ta ɗan yi shiru tana nazarin sa, sannan ta ce "Meyafaru da ita? Me ka ke son sani a kanta?".
"Ba wani abu bane ba, mami ta fara faɗa mini abubuwa a kan ta, so ina son sanin if their is way, we can help her, like she's not socially ok"
"To ai kaga ƙawar maryam ce, ni kuma ba wani son shiga harkata suke yi ba, amma dai ina ganinsu tare da maryam, yarinya ce mai matuƙar haƙuri da biyayya, kamar babanta ne ko babarta ce ɗaya daga ciki ya rasu, yayan babanta yake riƙonta, matarsa take maltreating ɗin ta, gaskiya i don't know much about her. Na so ace a cikin yaran nan akwai nutsatstse, ai da na haɗa su aure, tarbiyyar ta na burge ni sosai da sosai"
"Kin san meya ja hankalina, har na tambayeki?"
"A'a sai ka faɗa".
"Yadda maryam take yawan bani labarinta, da irin abubuwan da suka din ga yi mata na wulaƙanci suna makaranta, gidansu an yi maltreating ɗin ta, makaranta yara sun yi maltreating ɗin ta, wai wasu lokutan har da malamai, abun bai yi mini daɗi ba wallahi Hajiya"
Hajiya ta ce "Shiyasa nake yinka babban mutum, akwai hangen nesa da zurfafa tunani".
Cikin damuwa ya ce "Hajiya, kowace halitta da Allah yayi, tana da muhimmanci da kuma amfani, sosai nake jin zafi idan na tuna abun da maryam ke faɗa a kan ta, gaba ɗaya yanayin ta kamar a tsorace take da mutane ma, kuma ni banga muninta ba, baƙa ce kawai, meye abun aibata mutum a kan abun da baka da ikon yin sa?"
"Babu kam"
"Amma Hajiya kina ganin zan iya taimaka mata?"
"Me zai hana? Idan har da ɓangaren da zaka iya supporting ɗin ta, go ahead nima zan yi farinciki da hakan"
Raihan ya sake gyara zaman sa ya ce "Wallahi na so maganarki ta farko ta tabbata, ina ma akwai nutsatstse a cikin su yaya salim, da ɗaya daga cikin su, ko shi ko yaya sagir da wani ya aureta"
Cikin damuwa ta ce "To ya zan yi, sun ƙi karatu, sun ƙi kasuwa sai shirme, sai addu'a kawai"
"Kar ki damu Hajiyarmu, lokaci ne, zasu daina ne in sha Allah, ayi tayi mana Addu'a"
Hajiya ta ɗora hannunta kan na Raihan ta ce "Addu'a kullum cikin yi muku ita ake ai, ubangiji Allah ya tsare mana ku"
Ya amsa da Amin.
Sai da ya ci ya cika cikinsa, sannan ya tashi ya fita.
Har ummi ta koma gida, Raihan bai sake nemanta ba, tayi ta duba wayar amma bai kira ba.
Dr. Yan gari, yana ta ƙoƙari a kan kausar ta samu admission ita ma, domin kuwa a wannan karon, Farida ta ce ba zata sake aurar da ƴa ba, sai ta fara makaranta, saboda kar a sake kwata irin yadda aka yi a kan inteesar.
Suna falo suna kallo, dr. Ya ce lallai ummi ta fito falon ita ma, dan baya son duk suna tare a falo, amma ta din ga ware kanta ita kaɗai a ɗaki.
Ummi dai ta zo gefen kujeru ta zauna a ƙasa, tana kallon, wanda a son ranta tafi son zaman kaɗaicin a ɗakinta.
Noor ta hana su yin kallon, sai tsalle take a tsakar falon, tana karanta ayar Allahu nooro samawati wal ardi.
Abdul ya ce "Noor, dan girman Allah ki zauna wuri ɗaya ki yi karatun nan a nutse".
Sai ta koma hawa kan kujera tana dirowa.
"Ke dan ubanki ki nutsu" Kausar tayi mata tsawa.
Noor ta ce "Babanmu ɗaya"
Dr. Ya ce "Lafiya ce wannan tsalle-tsallen da take yi.
Farida ta ce "Duk ta bi ta ishi mutane da karaɗin tsiya".
Noor ta koma kusa da dr. Ta zauna ta ce "Dr."
Ya ce "Na'am shalelena, yau kuma a dr. Na nake"
"Ka san me? Wata a ajinmu, babansu ya auro kishiya, yanzu mamanta biyu kenan".
Yayi dariya ya ce "Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya".
Ta gyara zama ta ce "To Abba ni bani da wata maman sai maama, ita kuma ba ta so na"
"Tana sonki mana".
"Abba dan Allah muma ka auro mana kishiya, nima mamana ta zama guda biyu"
Ashar ɗin da farida ta yi mata sai da duk suka razana, ta zaburo zata make noor, amma noor ta tashi da gudu, tana murguɗa kwankwasonta tana dariya, ta tsaya daga can ƙarshen falon ta ce "Wallahi Maama idan ki ka kuma dukana, sai na ce Allah ya sa Abba ya auro kishiya"
Farida ta dafe kai ta ce "Na shiga uku da wannan yarinyar, anya nikaɗai aka yi wa tiyata a ɗakin nan ba ayi mini musanye ba, anya yarinyar nan tawa ce? Gaba ɗaya ƴa ba ta da mutunci sai iskanci da rashin mutunci. Kodayake ba laifinta bane ba, tun da aka saka mata sunan bare da babu dangin iya babu na baba, kuma ana koya mata yadda zata wulaƙanta ni".
Tsam ummi ta miƙe, dan ta san ƙarshe faɗan kanta zai dawo.
Ta tarar da noor a ɗakinta, ta haye wa ummi kan katifa, ta yaye mata zanin da ta shimfiɗa.
"Mama" ta kirata kamar yadda take kiranta.
Noor ta ɗago ta kalleta.
"Meyasa ba kya jin magana ne?"
"Me nayi?" Tayi maganar cikin tura baki.
"Ban hanaki yi wa maama rashin kunya ba?"
Noor ta ce "Ba kya nan jiya ta dakeni, tayi ta zagina".
Ummi ta ce "To ai ke ɗin ce ba kya ji mama"
"Ina ji mana, ai in dai ta dake ni, cewa zan din ga yi Allah ya sa Abba ya auro kishiya"
"Au ba ki ji faɗan da nayi miki ba ko? Zaki ga a auro muku kishiya, idan aka auro wadda zata din ga hanaki abinci, tashi ki bar mini ɗaki tunda ba kya ji"
Noor ta ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, na daina"
Can falo kuwa, ganin farida ta haƙiƙance tana ta bala'i, ya sanya dr. Bar mata falon shi ma.
Ya rufe ƙofar ɗakinsa, ya zauna ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya kara a kunnensa.
Amsa sallamar ya yi, sannan ya ce "Barka da yamma, kuna lafiya?".
Yaya maryam ta ce "Lafiya ƙalau ya iyali?"
Ya amsa da "Lafiya lau Alhamdilillah, ya mai jikin kuma?"
"Jikinta da sauƙi Alhamdilillah, zasu sallame mu ma yau, ta warware zazzaɓin ma babu"
Ya amsa da masha Allah "Ranar monday ne appointment ɗin ta na ganin psychiatric doctor ɗin nan ko?"
"Eh in sha Allah"
"To, ko zaku bari ta ƙara warwarewa daga zazzaɓin, kafin ku je ganin likitan"
"To shikenan, ana samun cigaba sosai da sosai, domin kuwa shekranjiya take cewa ita fa kamar ka zo, kamar ta ganka ko mafarki take yi".
Dr. Yayi murmushi ya ce "Masha Allah, da haka da haka, in sha Allah zata warware gaba ɗaya, a cikin watan nan zan shigo in ga jikin nata in Allah ya yarda".
Yaya maryam ta ce "Ubangiji Allah ya kawo ka lafiya, muna ta godiya Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya jiƙan magabata".
Ya amsa da Amin.
Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala'in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake