juyi a tsakiyar ɗakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu tsada, ta kalli takalmin ƙafarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a ɗakin.
"Allah ya ƙaro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira" hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ƴar gayu.
***
Gaba ɗaya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ƙara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce.
Da ya ce kan ya ƙara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuɗin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sauƙi.
Gefe ga kausar dr. Ya ƙara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji.
Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ƙauye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ƴar ta ita kaɗai ba.
Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaɗan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tanƙwarata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ƙanan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu'a, tare da yi mata fatan shiriya.
Gashi farida ta ɗora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa ƴar ta kunne.
Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk abun da za ayi sai dai tayi shiru.
Babban abun da ya ɗaga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba.
Ta amsa masa da to, amma ƙasan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ƙara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma ƙara tabattar mata da barin gidan.
Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karɓo masa ba zai ci na gida ba.
Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya ɗauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya danƙawa raiha, a matsayinsa na ƙaramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra'ayi ba.
Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaɓa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce ba ruwansa da zaɓa wa raihan ɗin matar aure, balle auren yaƙi daɗi ace laifinsa ne.
Shima Alhajin yayi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu matsayi.
Raihan ya ce "Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka ɗora mini?"
Alhaji ya ce "Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai".
Raihan ya ce "To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya"
Alhaji ya ce "Ba maminka ba?".
"A'a Hajiya"
"Ɗan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum".
Gidansu ummi kuwa yau gaba ɗaya jikinta babu daɗi, ta gaji sosai da sosai, dan farida baƙi tayi, kan ummi sai ciwo yake yi, kamar za ta yi zazzaɓi da ƙyar ta lallaɓa ta yi aikace-aikace.
Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu zazzaɓi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki.
Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti.
Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what's app, dan kuwa baya ƙasar gaba ɗaya, dan haka bai san halin da take ciki ba.
Tun ƙarfe shida ummi ta ga farida sun ɗauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki yaƙi samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna ɗanta ya fi ƙarfin wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi.
Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a ɗakin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai.
Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ƙyar ta ɗaga ta yi sallama.
"Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in ganki".
Cikin ƙarfin hali ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, bana jin daɗi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira ka".
Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce "Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?".
"A'a ina gida ne, zan warware in sha Allah" tayi maganar da ƙyar kanta na sarawa.
"Bani 20minutes gani nan" kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri.
Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ƙofar ɗakinta.
A hankali ta ce "Waye?".
"Mai gadi ne, kin yi baƙo ne, yana sallama"
Ummi ta ce "To" maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ƙalla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya fitowa.
Hankalin raihan ba ƙaramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje.
Tana ƙarasawa ta nemi wuri zata zauna a ƙasa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar.
Tun da ya ja motar yake faɗa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaɓi.
Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba.
Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ƙyar take iya amsawa saboda ciwo, kuma hankalinta yayi gida.
Ya ce "Akwai ciki ne?" Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana.
Raihan ya ce "Babu".
"Ka tabattar? When last ta yi period?"
Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce "Yana tambayar ki".
Likitan ya ce "Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki"
Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce "Ai da yake bana gari, shiyasa ban riƙe ba, ummi ki gaya masa" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, kamar ta buɗe ido ta ga ta ɓace, raihan ya gama da ita gaba ɗaya.
Raihan ya ce "She can't recall, but she's not pregnant"
Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu.
Likita ya ce a bari ta kwana ɗaya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faɗa a wurin raihan kan rashin kula da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman.
Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, taƙi yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi mata, gara aikin gidan.
Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la'asar zata dawo.
Haka ta lallaɓa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa hankalinsa ya ƙi kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a ɗaukko a bata.
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba, har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuɗin makaranta take biya, wurin ɗaukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta.
Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi.
Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaɓa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san da alaƙarsu, alaƙar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba.
Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani.
Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a riƙeta a can.
Raihan ya ce "Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ƙoƙarinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ƙoƙarin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka riƙe ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki"
Ɗan buɗe baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar.
"Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?"
"Yaya zamu yi dai? A ƴan uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure"
Ummi tayi dariya ta ce "Daɗina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta"
Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin tayani da addu'a, akwai ƙalubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faɗa, akwai buƙatar yadda ki ka gaya mini, ina buƙatar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taɓa budurwa ba, kuma bana son auren haɗi, ni ba zan auri matar da bana so ba"
Ummi ta yi dariya ta ce "Za a sha ƙiriniya, amaryar ka za ta sha fama da ƙuruciya"
Kallonta yayi ya ce "Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki ke cewa za a sha ƙuruciya"
Ummi ta waro masa idanunta ta ce "24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?"
Ya ce "Wallahi na cika 24yrs"
Da suka yi lissafi, watanni goma sha huɗu ummi ta bashi.
Ya ce "Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa'ata ce na ma fa fiki girma ummi, daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini"
Ummi ta ce "To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna, ni yayarka ce"
Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu.
"Me ka ke kallo ne?"
"Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki"
Ummi ta rausayar da kai ta ce "Idan ka faɗi haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na akuya ne da mage? Sai ya ce A'a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina"
Raihan ya ce "Allah sarki, Allah ya jiƙan baba da rahama"
"Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai"
Yayi murmushi ya ce "Han sai ka ce sunan ƴan china, amma duk yadda ki ka faɗa zan amsa, ki kula da kanki sosai a garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo"
Ummi ta ce "To, in sha Allah"
Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da tambayar bai taɓa ganin ta saka kayan da ya bata ba.
Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta.
Ranar tafiyarsu gagarawa na ƙaratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ƙaruwa, sai dai ta na ta addu'a a kan Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ƙi.
Ta ɗauki ɗaya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haɗa kayan da zata yi tafiyar da su.
Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daɗi.
Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ƙaruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haɗu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa.
Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da yawansu bayan ta baro garin aka haife su.
Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta.
Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo.
A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan.
Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta ɗaga kai ta kalli ɗakinsu, ɗakin mai ɗauke da ɗumbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a ɗakin, amma ba ta san suwaye a ɗakin ba.
Ɗakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar ɗakin ta, tana ta bayar da umarni.
Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ƙarfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya.
"Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?" Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai.
Noor dai ta kame tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.
Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa ɗakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko taƙi amincewa da rufin asirin aure, ya goya mata baya, haka zata riƙe a gida ba aure.
Aikuwa kawu yahaya ya haɗe rai ya ce "Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?".
Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin.
Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daɗe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaɓewa a cikin dangin nasu.
Abubuwan duk babu daɗin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ƙalubalen da take fuskanta ya sanya ta fara fanɗarewa ita ma.
Al'amarin bai yi wa ummi daɗi ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan.
Washegari ɗaurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na'ima, amma ta tarar maman na'ima ta rasu, ƙannenta duk sun yi aure.
Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta.
Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ƴar wurin bashir, da Idiris ya aura taƙi zama, ta bi kawu yahaya gashi haryanzu ta gama balagewa ta riƙa ba aure shi yanzu yana da yara biyar.
Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ƙalubale a in da take ba.
Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi.
Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama ɗan shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana'ar kirki ya zama criminal.
Alhassan ma babu sana'ar kirki, sai kamasho da ƴan buge-buge.
Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ƙalau.
Ana dawowa daga ɗaurin aure, kawu yahaya ya ce zasu koma gida, sai dai ummi ta sha surutun mutanen gidan na rashin aure.
Suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha, a kan ta kwantar da hankalinta a kan rashin aure, saboda lokaci ne, shi aure ba gaggawa ba samun nagartaccen miji da gidan aure mai cike da farinciki shi ne abun fata.
Ita dai ummi ganin sun taho daga gagarawa ya fi komai faranta mata rai.
Tashin hankali ba a saka masa rana, bayan su ummi sun sauka a kano gida, ummi ta tarar da ɗakinta a garƙame an saka masa mukulli.