"A'a yaya, akwai matsala ne, ina so ka taimaka mini ina gagarawa yanzu haka"
"Subhanallah, matsalar me kuma?"
Ummi ta ce "Aurena ne ya samu matsala, can gidanmu anty farida ta ce ba zan zauna ba, nan ma Iya ta ce sai na tafi"
Hashim ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutuwa auren yayi?"
"Eh, mamansa ce ta saka ya sake ni, ba na son zuwa maiduguri in ɗora musu nauyi daga yin aurena, ga dr. Ba ya gari"
"Kin san menene, ni yanzu ina dutse ni da matata, ki saurara da kyau, zan yi miki kwatancen gidana, akwai mukulli a maƙwabta, zan kira su su baki, ki buɗe ki shiga ki zauna, ki bani account number ki in turo miki kuɗi, ko zaki buƙaci wani abun, amma Abdul ya kirani ana nemanki, basu san in da ki ke ba, ai ban san kina gagarawa ba".
Ummi ta ce "Dan girman Allah ko ya sake kiranka kar ka gaya wa kowa ina gagarawa, kuma ba wanda zan gayawa ina gidanka, dan Allah kar ka gayawa kowa idan ku ka dawo zan yi maka bayanin komai"
Ya ce "To shikenan, ki turo mini account number"
"Kar ka damu, akwai isashshen kuɗi a hannuna".
Ana idar da sallar asuba, Ummi ta ɗebi kayanta ta bar gidan iya, sai dai ba ta bar gagarawa ba sai da ta je ta shigar da ƙara a kotu, sannan ta tafi gidan magaji da ba a cikin gagarawa yake ba.
Ko da magaji ya dawo ummi ta kwashe komai ta gaya masa, sai dai ya ji zafin kora da wulaƙanci da Iya ta yi mata, sai dai ba ta gaya masa batun kai ƙara kotu ba, dan haka da ya je gagarawa bai nuna musu ya san meyafaru ba.
Sai dai tun da ya ji ta'asar da Iya ta aikata, ya kasa komawa gidansa, saboda damuwa da fargaba, ya kasa komawa gidansa ya kalli ummi, ashe duk tsawon lokacin nan kallon da take yi masa kenan?.
Ganin ba shi da wani zaɓi, ya sanya ya koma gidan, ya tarar da ummi da matarsa suna hira.
Ummi ta ce "Eh, dama ina son zan yi maka bayani, na san zaka fuskance ni"
Ya ƙarasa gaban ummi ya zube a kan gwiwoyinsa, sai ga hawaye ya ce "Wallahi! wallahi! wallahi ummi ban aikata abun da Iya ta gaya miki ba, bani bane ba ummi, ban taɓa sanin abun da ta gaya miki ba kenan, dama da abun ki ke kallona? Wallahi ummi Idris ne, nima ban san an yi ba sai lokacin da za ta yi miki auren huce takaici da shi, na nuna mata illar yin hakan, saboda kina da ƙananan shekaru kuma ba ya ƙaunar ki, amma ta gaya mini ga abun da ya faru shekarun baya, aurensa shi ne rufin asirin ki, wanda a kan haka sai da ta haɗa ni da babanmu kamar zai tsine mini, kuma still bayan auren da ya zo yana faɗar maganganu a kan an bashi ragowa na tuna masa koma menene shi ya fara, ya je ya gaya wa Iya ta sake ci mini mutunci da barazanar na sake ɗaga maganar sai ta tsine mini, ina ji ina gani yayi ta yamaɗiɗin ragowa aka bashi ke, ga kuma larura kina da ita, ba yadda na iya, amma ko Alqur'ani aka bani zan rantse wallahi ummi bani bane ba"
Ummi cikin sheshsheƙa ta ce "Ka yi haƙuri yaya magaji, nima zuciyata ta daɗe tana yi mini wasi-wasi a kan hakan, amma ba yadda na iya tura ta kai bango, na gaji da abun da Iya take yi wa rayuwata, shiyasa na zaɓi fesar da abun da yake zuciyata ko da kuwa zumuncin zai tarwatse. An cutar da ni da yawa me nayi da na cancanci haka yaya magaji?"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ummi ba zan hana ki ba, ba zan dakatar da ke ba, Iya ita ta rusa duk wani tubalin soyayya da ƙauna da tarwatsa kan iyalanta, ta hanyar fifita wasu a kan wasu saboda zunzurutun tsagwaron son zuciya da abun duniya, ta yi miki CUTARWA ma fi muni wallahi kowane mataki zaki ɗauka ba ruwana, ni dai ki yafe mini wallahi bani bane ba"
Ummi ta share hawaye ta ce "Ni yakamata na nemi yafiyarka yaya, amma ba zan ɓoye maka ba har iyayenmu dr. Kawai na cire amma suna kallon yadda rayuwata ta wulaƙanta cikinsu ɗaya da mahaifina saboda bai mutu ya bar mini komai ba, aka rasa wanda zai kula da rayuwata, aishikenan"
Cikin sanyin jiki matar magaji ta ce "Ummi abun da haƙuri bai bayar ba, akasin ba zai bayar ba ki yi haƙuri ki yafe musu mana"
Ummi ta ce "Ai da fari na yafe musun, sai na ga idan ba rayuwata ce ta ƙare ba, ba za a daina cutar da ni ba. Mijina yana yawan gaya mini in tsaya da ƙafata a rayuwa in fuskanci kowane irin ƙalubale".
Yayi nisa a zurfin tunani, ya ji ana bugun ƙofar falo kamar za a karyata, babu shiri ya tashi ya je ya buɗe a fusace, sai dai ganin Mami a tsaye ya sanya shi haɗiye masifar da ya ƙunso ya saukewa mai bugawar.
"Raihan, meye haka? Amai da gudawa ka yi ne kayi wannan mummunar ramar?" Ya girgiza mata kai tare da shigewa falon.
Ta bi bayansa, tana ƙare masa kallo.
"Ya aka yi na je office ba ka je ba? Me ka ke yi a gida?".
"Mami ba a san fa in da Ummi take ba"
"Shi ne me? Ƙaramar yarinya ce ita? Saboda haka ne nake ta kiranka a waya kashe wayoyinka?"
Yayi shiru bai ce komai ba.
"Alhaji yana nemanka, za ku yi magana a kan kai kuɗin Safiyya, kuma a yau ba sai gobe ba, ka je ka ji me take buƙata na shirin biki, kuma idan ka kuskura ya san na saka ka saketa sai na yi mummunan ɓata maka rai" bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka mata, tayi ta gama ta tafi.
Me zai yi da wata safiyya? Ya tuna yadda take yawo da wani ɗagaggen mayafi tana gantsare-gantsare kamar an banƙare kaza, gaba ɗaya baya ganin kyan kowa idan ba Salmansa ba.
Bai san lokacin da ya ja wani guntun tsaki ba.
Gaba ɗaya gidan yayi ƙura saboda ba ummi, ya tara wanke-wanke a kitchen, da ƙyar yake iya yi. Daga baya ma sai dai ya sayo fruita ya ci duk ya zubar a wurin.
Yayi wanka ya shirya ya je gida ya samu Alhaji.
Shi kansa sai da ya tambayi raihan ko ba shi da lafiya ne? Ya ce masa lafiyarsa ƙalau.
"To kai babarka ta ce wannan juma'ar kai kuɗin aure, ni ban ganka ba. Ka zo ka kawo mini kuɗin, da sauran shirye-shirye amma ba ka ce komai ba, na san ba so ka ke yi ba amma ka daure ka yi mata biyayya".
Raihan kamar zai yi kuka ya ce "Ni fa bani da kuɗi"
Alhaji ya ce "Kai babban mutum, ba ka da kuɗi kuma? A auren Salma ne ka ke da kuɗi kenan?" Yayi shiru.
Alhaji ya kira mami a waya, ta zo ta same su, ya sanar mata raihan ya ce ba shi da kuɗin ƙara aure a yanzu.
Mami ta ce "Duk dan ya kaucewa umarnina ne, ni ina da kuɗin zan bashi"
Alhaji ya ce "Dakata tukuna, me za a yi wa ƴa ta wanda zai kwantar mata da hankali? Ba zai yiwu watanni takwas da yin aure, ba dan ta gaza ta ko ina ba ace za a ƙara mata kishiya ba tare da yi mata wani abu da zai kwantar mata da hankali ba".
"Alhaji me kuma za ayi mata? Ta ci nata rabon ai"
Alhaji ya katse ta da cewa "Da ki ka hana ayi mata lefen sai ta ɓarauniyar hanya ya yi mata? Ke ma da ban bayar da kayan faɗar kishiya ba, duk da Hajiya na da haƙuri, da ba ki shigo ta daɗin rai ba, gara ita ta daɗe na aure ki? Wannan fa?. Na gargaɗe ki kar ki yi abun da zaki zo ki na dana sani, amma kin ƙi. Kar ku jefa yarinya a halaka ƙiyayyar ɗa namiji masifa ce, kin ƙi ai shikenan"
Ta ɓata fuska ta ce "Ba wata ƙiyayya, iskanci ne kawai da kuma asiri da yake ɗawainiya da shi"
Alhaji ya kalli raihan ya yi murmushi ya ce "Ba wani asiri, ta iya kiwo ne kawai, ke ba abun alfaharinki bane a. Mallake ɗanki ana kula da shi, nan ya zo ana bani labarin hannunta akwai maggi, ta iya girki, nima shaida ne ta iya girki. Dan haka ko dai a samu wadda ta fita ko kai ɗaya da ita idan ana son zaman lafiya, amma shawara ce na bayar. Babban mutum, me zaka bawa ummi da zaka kwantar mata da hankali?" Raihan ya ji kamar Alhaji yana shiga zuciyarsa yana karanto damuwarsa ne.
"Alhaji ban san kan abun ba, ban san me ake bayarwa ba".
"Eh to, ka ga recently kun fita waje, amma wannan cikin honeymoon ɗinku ne, kyauta zaka yi mata ta bajinta, ka gane me nake nufi ai kyauta mai sunan kyauta.
A samu danƙareriyar mota a bata, idan da hali gidan da ke ciki a bata takardunsa, ita amaryar sai a nema mata haya a wani wurin, gidan ya zamana nata ne"
Cikin tashin hankali mami ta zabura ta ce "Alhaji wannan kyautar ai sai kai? Idan ya bata gidansa shi shikenan ko oho? Wai meyasa kamar goya masa baya ka ke yi ya bujire mini ne?"
"Yanzu ya ce ba shi da kuɗin aure kin ce zaki bashi, ita wannan saboda ba ƴar ki ba ce ba, kin hana a bata kyauta, ta samu kwanciyar hankali, ba zan so raihan ya rabu da gidansa ba, amma muddin kina so na tsaya yadda yakamata ya ƙara aure, sai an yi balancing, tun da ba shi da kuɗi, ke ki biya masa kuɗi yayi aure, ni kuma zan yi mata kyautar da zata sanya hankalinta ya ɗan kwanta ya rage mata zafin kishi". Raihan yayi murmushi ya ce "Alhaji na gode sosai da sosai"
"Wallahi ba zai yiwu ba, ƙarya yake yi yana da kuɗi, kuma sai ka fito da su"
"To ya rage naku dai, ni dai idan aka yi wa Ummi kishiya, in sha Allah zan yi mata kyautar ban mamaki, sirikata ba ta yi laifin komai ba, marainiyar Allah ba zan bari a cutar da ita ba"
Duk maganar da yake yi, yana observing ɗin raihan da ita kanta mamin, dan yana sane yake faɗar wasu abubuwan.
Ya sake nisawa ya ce "To duk kun yi shiru, kai babban mutum ka fito da kuɗi mana, kuɗi fa akwai su"
Raihan ya karkace kai ya ce "Dan Allah Alhaji a bar maganar auren nan yanzu, nifa ba ni da lafiya ma"
Gaba ɗaya suka kalle shi.
Mami ta ce "Kamar yaya ba ka da lafiya?".
Ya ce "Ba zan iya ƙara aure ba, a bari na nemi magani" ya bata amsa kansa tsaye.
Alhaji ya sunkuyar da kai kamar ya kece da dariya, raihan ba saiti wasu lokutan.
Ya maze ya ce "me yake damunka?"
Ya sosa kai ya ce "Ai kawai muna zaune ne da salman, magani nake nema"
"Amma ba dawowarku aka ce tayi ɓari ba?" Tayi maganar a hasale.
Ya ce "Eh, amma bani da lafiya, dan Allah idan ba asirina ki ke son ya tonu ba, dan Allah mami ki bar maganar auren nan na samu magani"
Yadda raihan ke tsara maganar kawai Alhaji ya san ƙarya yake yi, yayi wani irin ƙasaitaccen murmushi na manya ya ce "This is serious, dole a jinkirta maganar nan, dan wannan ba issue ne ƙarami ba"
Ba tare da mami ta ce komai ba, ta hau zancen zuci, da ƙoƙarin gane ƙarya raihan yake yi, ko kuma da gaske? To me za ta cewa su Safiyya? Amma ba shi da lafiya ummi ta yi ɓari".
"Kin ga bilki, ki tashi ki je zamu yi magana da shi" Ummi ta yi wa raihan wani mugun kallo, amma yaƙi kallonta.
Bayan ta fita Alhaji ya yi ƴar dariya ya girgiza kai ya ce "Ɗan zamani da uwar zamani, tashi ka je Allah ya shiryeka babban mutum" ko a jikinsa ya tashi ya bar falon, dan dama haka yake so, kuma ya ƙudirce idan mami ta cigaba da uzzura masa sai ya gaya wa safiyya da Yaya rakiya ba shi da lafiyar da zai auri safiyya ummi ma rufa masa asiri take yi.
Ganin ya kwantar da tarzomar wannan maganar, ya sanya ya sake tatara hankalinsa a kan neman ummi.
Ya ɗauki wayarta yana duddubawa, ya tarar da gmail a wayarta, wani babban gidan talabijin na jamus, suna son bawa ummi aiki. Idan tana da buƙata ta tura takardunta ayi interview da ita. Tsaki yayi ya ajiye wayar ya dafe kansa yana tunani, ko a gidan ubanwa ma suka san ummi oho.
Managern su ne ya faɗo masa, dan ya gaya masa yadda ummi ta ɗauki hankalin mutane.
Ranar da aka fara shari'ar su ummi, ba ta je kotu ba sai lawyernta, kasancewar ATM ɗin ta na hannunta, kuma raihan yana saka kuɗi a cikin account ɗin ta, ya sanya ta saki kuɗi.
Alƙali ya bi komai tiryan-tiryan, tare da neman a kawo duk wani abu da aininhin kakan su ummi ya mallaka, da yayyensa suka hau suka turmushe, a zama na gaba.
Su kawu Ilyasu suka cigaba da kururwar neman agaji, suna kiran Abdul a waya, ya ce shi ba abun da zai iya yi, tun da ba a san in da take ba.
Sati ɗaya aka koma kotu, Aka je da komai na kakansu ummi. Gidan da suke ciki, aka ce ba zai rabu ba, saboda wasu sun rasu sai ƴaƴansu, wasu duk sun ja wuri sun yi gini a ciki, sai dai a yi wa gida kuɗi, a raba a fitar da gadon ummi, da tumunin mahaifiyarta, sai su biya su.
Duk wannan abun, ƙarƙashin jagorancin lawyern ummi ake yin sa, dan ko sau ɗaya ba ta je kotun ba.
Aka shafe wata guda da sati biyu, ba ummi babu labarinta, har Abdul sai da hankalinsa ya tashi, wurin neman ina ummi take?.
Mami ta ce zata saka raihan a gaba ta nema masa magani, ya ce mata shi yana zuwa wurin likita ana duba shi, dan ta san komai za ta yi ba zai sha maganin hausa ba.
Amma duk da haka ba ta haƙura ba, ta cigaba da saka pressure sai da aka kai kuɗin nan!
Raihan duk yayi baƙi ya lalace, gashi kwatsam! Dr. Yayi masa magana a what's app cewar ba ya samun ummi a waya, shi ma tasa wayar ce ta lalace amma kwana biyu ba ta gaishe shi ba.
Raihan ya yi masa ƙaryar ita ma ta ta wayar ta lalace amma zai haɗa su.
Duk wannan abun, Salim bai kuma tsoma baki a kan lamarin raihan da ummi ba, gashi bin ƙwƙƙwafin da Alhaji yake yi, yana daf da gano ummi ba ta nan, dan kuwa yana ta cewa raihan kwana biyu fa bai kawo sirikarsa sun gaisa ba
Gagarawa kuwa, da ummi da mariya aka yi ƙiyasin suna da naira miliyan uku da rabi a gidan, dan haka Alƙali ya ce ko su kawo wannan kuɗin su fitar da ummi da mahaifiyar ta, ko Alƙali ya saka gida a kasuwa a sayar, a sallame su, kuma aka basu wa'adin sati biyu.
Sun san ko giyar wake suka sha, ba su da wannan kuɗin, ga kotu ta saka an yi wa sauran gonakin su kuɗi, za a cire gadon bashir, sannan a cire na ummi da mariya. Alƙali ya ce su haɗa su biya su ummi, sai su riƙe gida da gonaki.
Raihan yana office baya gane komai, wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga a hankali ya kara a kunnensa.
"Barka da rana" tayi maganar cikin sassanyar muryarta. A zabure ya tashi tsaye yana faɗin "Ummi, kina ina? Ina ki ka shiga haka?"
"Ina nan cikin ƙoshin lafiya" ta bashi amsa.
"Haba Salma, kin san yadda ki ka tayar mini da hankali kuwa? Kina ina ki tsaya na zo na ɗauke ki".
Ummi ta ce "Ka zo ka kawo mini takarda ta dai. Dan Allah wani abu nake son ka yi mini, family house ɗinmu na gagarawa kotu za ta saka a kasuwa nan da sati biyu, dan Allah da an saka a kasuwa idan kana da hali, ka sai gidan ka basu short notice su tashi, da k yi haka zan gaya maka in da nake a Maiduguri ka zo ka kawo mini takardata, kar kuma kayi tracking ɗina, sannan bana gidan mama, naira miliyan goma sha huɗu aka yi masa kuɗi burina kawai ka sayi gidan ka tashe su!"
Turus raihan ya yi yana kallon wayar, me zai saka ummi ta yi haka? Lallai akwai wani abu a ɓoye, amma idan har zai ganta kuɗi ko na Alhaji ne zai ɗiba ya sai gidan kamar yadda ta buƙata, duk da bai san dalilinta na yin hakan ba!
Ayshercool
08081012143.
I hit the jackpot with PalmPay! Join PalmPay with my link or my code 'XWPK6722' within 72 hours to help me get my gift! >>https://link.palmpay.com/uwyy6
Team Ummi wanda ba su taɓa cike palmpay ba, dan Allah ga refaral ɗina a bi link a cike mini.
Ayshercool.
08081012143
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN