tana zancen zuci, ita dai tun da Allah ya sa kawu yahaya ɗaukkota, yayi ta ƙoƙarin saya mata magunguna, cikin ikon Allah ba ta sake jin wannan matsalar ba, ko maƙiyinta ba ta fatan Allah ya haɗa shi da bala'in da yake cikin larurar sanyi.
Tun da farida ta dawo daga gidan inteesar, tamkar ita za ayi wa kishiya, kamar za ta yi hauka, domin kuwa da ita da wasu daga ƙannenta suka dawo gidan, suna ta bata haƙuri, a kan sai ta daure ita ma, idan ba haka ba inteesar ba zata kwantar hankalinta ba.
Sun cika falo suna mayar da yadda aka yi, noor kuma na ta kokowa da remote tana ƙara volume ɗin tv.
"Wai ke noor baki da hankali ne? Ba ni san meya samu yayarki Inteesar ba ne?"
Noor ta juyo ta kalli mai maganar ta ce "Mutuwa ta yi ne?"
"Wane irin mutuwa, ke ko gidan nata ma baki je ba, balle a haɗu a rarrasheta da ke, kina kallon mahaifiyarku hankalinta a tashe, ita ma can muka baro ta tana kuka, amma ke kina nan kina ƙure wa mutane kunne da ƙarar tv"
Noor ta taɓe baki ta ce "To tun da dai ba mutuwa tayi ba ai barkanta, wanda ba shi da kunya ai dole ayi masa kishiya, haka wata malama ta ce rannan a tv, na ce ashe saura maama"
"Ke uwar taki ki ke cewa ayi wa kishiya?"
Kausar ta ce "Mama hadiza, ki ƙyale yarinyar nan kar ta saka hawan jininki ya tashi, ba isasshen kai ne da ita ba, yanzu sai ta yi miki rashin kunya, kuma ba kowa ne ke zigata yana koya mata wannan iskancin ba, ban da ummi, idan ba haka ba ta yaya ɗa zai yi fatan a yi wa uwarsa kishiya, banda shashasha mara hankali"
"Ni dai ban saka da daƙiƙi a maganata ba, mutum ya bari ya fara gane karatu" kausar ta ja bakinta tayi shiru, idan ta cigaba da tankawa noor, sai noor ta kunyata ta a gaban mutane.
Nan kuma akalar hirar ta koma kan ci wa ummi mutunci, da ziga farida a kan lallai yakamata ummi ta bar mata gida, tun da ta tsofe a gidan babu aure.
Suka gama soko burutsunsu, suka bar gidan.
Ummi kusan kwanan zaune tayi, tayi ta salloli tana kaiwa Allah kukanta, wayarta kuwa ta dubata babu adadi, amma babu saƙon raihan ɗaya da ya sake shigowa cikin wayarta.
Ƙasan zuciyarta ya shiga tabattar mata da sun rabu da raihan kenan.
Bayan ta idar da sallar asuba, message ya shigo wayarta, wani website da raihan ya saka ta shiga, ta yi submitting cv ɗin ta, an kira su screening ciki har da ita, wani sabon gidan talabijin da ba a daɗe da fara shirye-shirye a cikin sa ba.
Yau da safe aka ce su je wurin, ba ta ga saƙon ba sai yanzu, cikin sauri ta tashi ta haɗa credentials ɗin ta, agogo ta kalla, muddin ta ce za ta jira ta yi musu girki, to fa zata makara, dan haka ta dudduba jakunkunanta, ta samu kuɗi ta fito, ta turawa Abdul message na in da ta tafi.
Ko da ta je wurin ta tarar da mutane da yawa, haka nan ta fara bin layi ita ma, ta din ga duba wayarta tana tunanin raihan, shi ne mutum na farko da yakamata ta kira, ta sanar masa da an kirata screening, sai dai ba ta da wannan damar a yanzu.
"Dama na sani, babu lallai ka dawo gareni raihan, amma duk da haka ba zan ga laifinka ba, ina yi maka fatan alkhairi a duk in da ka ke".
Farida tamkar ita aka yi wa kishiyar, ko bacci gagararta yayi, ta taso da nufin ta tarar da abincin safe, Abdul ya shigo ya sanar da ita saƙon ummi, tana fara zage-zagenta, ya fice ya bar mata falon.
Raihan yana zaune yana ta juyi a kan kujera a office ɗin sa, ya kasa taɓuka komai, ya juya kai nan ya juya kai can, in aka jima sai ya ciro wayarsa ya duba ya mayar ya ajiye.
Ya kifa kansa a kan teburin gabansa, yana jin yadda kansa yake masa wani irin zafi.
Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa.
"Yaya raihan, barka da rana?"
"Yauwwa sannu"
Ta nemi wuri ta zauna ta ce "Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa"
Yayi shiru bai ce mata komai ba.
"Are you ok?" Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office ɗin.
Rau ta ji goshin nasa ya ɗau zafi, ta ce "Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi"
Ya ɗago a hankali ya ce "Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni"
"Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?"
Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu.
"Ki tafi na ce" yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai.
Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar ƴar tsana.
Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce "Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba" tayi sauri ta fice tana waiwayensa.
Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waɗanda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview.
Kuɗin hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira.
Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a ɗan tsorace take, ga yunwa tana ji, ɗaya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daɗi.
Ɗayan ya ce "Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke ɗokin gani"
Shugaban wurin ne ya shigo, ma'aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce "Wannan fa?"
"Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!"
Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa.
Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin.
"Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi"
Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru.
Ta wuni da yunwa, haka ta kwana da wata.
Kwanaki huɗu rabon raihan da ummi, yayi ƙoƙarin sanya abun da ta gaya masa a matsayin hujjar da za ta rabu da shi, amma shi sam bai ji hakan a matsayin hujja ba, dan damuwa yake ƙara shiga na rashin ta, ya zuba mata ido ya ga iya gudun ruwan ta, ko za ta neme shi, amma ya ji shiru.
Hakan ya sanya ya fara zargin anya ba da gaske take ba ta son sa ba, tun da ta iya gaya masa cewar su rabu, kwanaki huɗu amma ba ta sake nemansa ba, dan haka tsoro ya sake shiga zuciyar sa, ummi ba ta son sa.
Ƙasan zuciyarsa yana mamakin yadda ta ce masa ta taɓa aure, shi ba auren ta ne ya dame shi ba, meya kashe auren? A yadda ummi take har ace namiji ya sake ta?.
Daurewa yayi, ya sake bawa ummi kwana ɗaya, ya zamana kwanaki biyar, amma shiru ba ta neme shi ba.
Kwana na biyar, da yamma ya koma gidansu ummi, sai dai ya kira wayarta amma ba ta shiga.
Yana tsaye sai ga motar dr. Raihan ya risuna ya gaishe shi, dr. Ya amsa masa, yayi parking a waje, ya shiga cikin gida.
Raihan ya dudduba, mai gadin gidan ma baya nan, yayi ta kiran lambarta amma shiru ba ta shiga.
Ya samu wuri ya zauna a ƙofar gidan, yana cigaba da dannan wayarsa.
Dr. Ya sake fitowa, ya ga raihan, ya kalli raihan ya ce "Yarona wa ka ke nema ne? Ko wurin Abdul ka zo?"
Raihan ya ce "A'a Abba, wurin Ummi na zo"
Dr. Ya ce "Too, ummi kuma lafiya dai ko?"
"Eh lafiya ƙalau, wurinta dai na zo, na kira wayarta ba ta shiga ne"
"Amma wani abun tayi maka ne?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a, ba ta yi mini komai ba"
Dr. Ya jinjina kai ya ce "Yaron kirki, ai babu lallai ummi ta tsaya ta saurareka, a yanzu mijin aure ne ya dace ya zo wurinta, ba wanda za a yi soyayya ba kawai, wannan idan ba ku yi sa'anni ba, ba zaka girmeta da yawa ba.
Ka yi haƙuri ka ji ɗana.
Cikin girmamawa raihan ya ce "Abba ummi ta sanni, akwai alaƙa tsakani na da ita, wallahi abba ba ɓata mata lokaci zan yi ba, aurenta zai yi, ina son ta wallahi".
Dr. Yayi shiru yana kallonsa, sannan ya yi murmushi ya ce "Meye matakin karatunka?"
"Na yi degree a ɓangaren Business administration, a ATBU"
"Idan da gaske ka ke zaka aureta, ranar lahadi ka turo mini mahaifinka mu yi magana da shi"
Raihan ya washe baki ya ce "To Abba, in sha Allah zan gaya masa, na gode sosai da sosai"
Dr. Yayi murmushi yayi gaba, a tunaninsa yayi maganin raihan, dan ya zata irin yaran nan ne marasa ji, amma duk da haka nutsuwa da kamalar raihan ɗin.
Raihan tafiya yayi yana murmushi, yana ganin abun kamar a mafarki, yau ya tsinci dami a kala, abun kamar a shirin film, wai ya tura Alhajinsa a nema masa aure? Kai tsaye gida ya tafi.
Sai dai ƙasan zuciyarsa yana tunanin, ummi za ta amince ko kuwa za ta cigaba da gardama ne? Dan ya ga kamar ta raina shi ne a matsayin mijin aure, yayi mata ƙanƙanta.
Yana zuwa ya tafi sashin Alhaji, dan kwanakin nan kusan kullum Alhajin yana gida, ya daki sa'a shikaɗai ya tarar a sashin nasa.
Alhaji Tahir ya gyara zaman tabaran sa, ya ce "Ya aka yi ne? Yanayin farinciki haɗe da damuwa a fuskar babban mutum"
Raihan ya je ya zauna a kusa da shi, ya ce "Kowanne akwai Alhaji"
"Bani labari"
Ya ciro wayarsa, ya nemo hoton ummi da yayi mata, lokacin da suka sayo dogwayen riguna, ya ce "Alhaji ka ga wannan"
Alhaji ya karɓi wayar, ya ƙare wa hoton kallo ya ce "Na gani, meyafaru?"
"Alhaji tana da kyau?"
Ya ce "Masha Allah, very beautiful kuwa, da gani kuma tana da kunya"
"Ita nake son aura Alhaji, zaka nema mini aurenta?"
Alhaji Tahir ya kalli raihan yayi murmushi ya ce "Babban mutum wannan ai matar manyan ce, anya ba ka yi tsaurin ido ba kuwa?"
"A'a Alhaji, ai nima babban mutum ne, dan Allah tayi? Wallahi mutuniyar kirki ce"
Alhaji ya yi shiru ya ce "Ai ni kallon sani nake yi mata ma"
Raihan ya ce "Eh, ƙawar maryam ce, amma ita ba ta girme ni ba, shekrunmu ɗaya da ita, kuma mutuniyar kirki ce ka tambayi Hajiya ma ka ji"
Alhaji Tahir ya dafa kafaɗar raihan ya ce "Easy my dear, in dai kana son ta tayi mini, za a nemi aurenta in dai za a bamu"
Raihan ya washe baki ya ce "Babanta ya ce ranar Sunday wai ka je ku yi magana, gani yake yi kamar ba aurenta zan yi ba, Alhaji tana bani shawarari masu kyau, tana da kirki sosai"
"Allah ya kaimu lahadin, zan je in sha Allah, ko a lokacin suka ce sai a ɗaura, Ubangiji Allah ya sa abokiyar zama ta gari ce"
Raihan ya sosa kai ya ce "Alhaji saura abu ɗaya"
"Ok to ina jinka"
Raihan ya ce "Dan Allah kar ka gaya wa mami sai maganar ta faɗa, ban san yadda za ta karɓi maganar ba.
I really have to marry her, Alhaji rayuwar ummi akwai ƙalubale da ban tausayi, dan Allah ka tsaya mini"
Alhaji Tahir ya jinjina kai ya ce "In dai ni ne ka san baka da matsala da ni, ko tsohuwa ka ce kana so, zan wuce maka gaba in dai tana da tarbiyya, kuma ko a hoto, ni yarinyar ban ga aibunta ba, ko ta girmeka in dai kana son ta shikenan, ai soyayya ba ƙarya ba ce raihan, mune muke barin al'ada na rage mana jin daɗin abun da addini ya halatta mana. Allah ya sanya alkhairi ango"
Raihan ya sunkuyar da kai yana murmushi, wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa.
Dr. Ya manta da batun haɗuwarsa da raihan, dan ko ummi ma bai nema da maganar ba, sai dai ya rage ganin gilmawarta ko a gidan, ya bar hakan a wataƙila takurar farida ce ta saka ta ƙara takura kanta.
Washegari raihan ya tafi wurin aikin Ummi, amma manager ya ce "Ai ummi yau kusan kwana uku ba ta zo ba, ni ban sani ba, ba ta da lafiya ne ko ya aka yi ban sani ba, kawai ta ce mini za ta je screening, tun ranar ba ta sake zuwa ba, na zata ma ko ba ta gama ba ne ba".
Raihan ya yi shiru ya ce "kira ta a waya ka ce ko ta dawo aiki, ko zaka koreta".
Manager ya zare ido ya ce "Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake yabawa ƙoƙarin ta, da yabawa amanarta"
Raihan ya ce "Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo aiki.
"Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba"
Raihan ya sassauta murya ya ce "Haba manager, dan Allah ka taimaka Please"
"Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi ƙoƙarin ta dawo ɗin"
Raihan yayi dariya ya ce "Allah ya bar mini manager"
Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi.
Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo ɗaya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta.
Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo.
Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi.
Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaɗan da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya.
Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass ɗin motar suka haɗa ido, sai da ta ɗan razana, ya buɗe mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba.
Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taɓa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta ɗosana ta shiga motar.
"Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr."
A razane ta kalleshi, tana ƙifta ido.
"Eh, mun haɗu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin ƙi ɗaga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana"
"Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataƙila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na riƙe ki da kulawa da girmamawa".
"Raihan zaka aureni ina bazawara"
"Kar ki sake kawo mini maganar kin taɓa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taɓa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa"
Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta.
"Meya rabaku da tsohon mijinki?"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kakarmu ce ta haɗa auren, ba ya so na, an kai kuɗin aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni"
Ya ce "Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu'a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka na ji kin ce a matse ki ke ko?"
"Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba"
Ya ce "Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa" ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan yake ba.
"Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?"
Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba"
"Kamar yaya kenan?"
"Haka mai wurin ya ce"
Kawai ta ga yayi parking ɗin motar, ya kalli ummi ya ce "Ke kuma ki ka ce masa me?"
Tayi shiru tana kallon sa.
"Magana nake yi miki?"
"Ni ban ce komai ba"
Raihan ya ce "Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka"
Ta ce "A'a ai ban yi kukan ba"
Ya danƙo kunnenta ya ce "Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki ɗau wani mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun