da ma ke ce? Kina nan dama" ya fara maganar cikin kame-kame.
"A ina ki ka san shi?"
Ummi ta ce "Ɗan ajinmu ne a University"
Raihan ya ce "Ɗan ajinku? Amma yake neman shara?"
"Wallahi yallaɓai korata aka yi daga makaranta, dan Allah ka taimaka mini"
Raihan ya ƙare masa kallo ya ce "Kana cikin wanda ku ka din ga muzanta mini mata kuna makaranta ko?"
"Dan Allah ka yi mini rai yallaɓai, lamarin Allah kenan, gashi yau ina neman alfarma a wurinta, na yi nadama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini"
Gwiwoyi a ƙasa yake yi musu magiya, ummi ta ce "Kar ka damu, ba ni nake ɗaukar aiki ba, ni abun da ya faru ya wuce a wurina, wannan wurin kuma ba ni da hurumin ɗaukar ka aiki, idan ya baka haka nake fata, idan bai ba ka ba ka yi masa uzuri wataƙila babu vacancy ne" daga haka ta ja jikinta ta yi gaba zuwa office ɗin raihan.
Ba ta san yadda suka ƙare ba, shima da ya zo office ɗin bai gaya mata yadda suka yi ba, noor ta ce "MD a ina yaya Abdul yake?"
Raihan ya ce "Ai ba a nan branch ɗin yake ba, yana sharaɗa shi".
"To ina first born?"
Ya kalleta ya ce "Wa kenan?"
"Yaya Salim mana, ba ka san last born yake ce mini ba, shi kuma first born?"
Raihan ya yi dariya ya ce "Ni ina zan sani, baya nan"
Noor ta ce "Na ga motarsa fa"
Ummi ta ce "Kai noor, me zaki yi masa an ce miki baya nan"
Raihan ya ce "Da gaske kin ga motarsa?"
"Wallahi na ganta"
Raihan yayi murmushi ya ce "Yaya hukuma sai da rarrashi, office fa na bashi, nake ta bin sa ina yi masa magiya, ofishin kula da ma'aikata da ladabtar da au na bashi, ya ce ba ya so ba zai yi ba wai wata sana'ar zai yi. Na ce Alhaji ya saka baki, amma ya ƙi shi ne yau ya zo ban sani ba, ko ma ya neme ni, bari na je office ɗin nasa na duba"
Noor ta bi raihan har office ɗin da Salim yake, sai haɗe rai yake yi.
Ya kalli raihan zai yi mita, sai ya ga noor a bayansa, sai kuma ya saki fuska.
Raihan ya ce "Yaya ashe ka zo ɗin ban sani ba".
"Eh da ka je ka haɗa ni da hajiyan Bauchi ko?"
Raihan ya sosa kai ya ce "Tuba nake babban yaya, with due respect kuma kai ne mataimaki na zan ɗebo sauran ayyukan da nake gabatarwa, na kawo maka zuwa next few months kuma, i will step down ka yi taking over"
Salim ya yi masa wani mugun kallo ya ce "Raihan ba ka da hankali ko? Tayaya makakke zai jagoranci wannan abun, kai da ka ke a nutse ma kana fama"
Noor ta ce "Ahh ba ka daina ba? Ka ce mini ka rage sosai ai" Raihan yana ja da baya yana dariya ya ce "Yauwwa noor gaya masa dai"
Kwanaki suka cigaba da tafiya, wasu rayuwarsu na daidaituwa, wasu kuma suna girbar abun da suka shuka.
Ummi ta shiga watan haihuwa, dr. Suka dawo ya kammala karatun da zai ba shi damar zama professor.
Duk wanda ya kalli mariya ya san ta samu kwanciyar hankali, shi kamaa dr. Ya canza.
Bai sauka a ko ina ba sai tsohon gidansa, in da za su zauna da mariya, gida yayi kyau ummi ta gyara komai.
Abdul ne ya ɗaukko su daga airport ma, farida sam ba ta san ma sun dawo ba.
Ummi ta yi wa Allah godiya, ganin mama cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.
Dr. Ya ce noor ta kwana tare da mariya, duk da jikinta yayi sauƙi sosai da sosai, shi kuma ya tafi can gidansa, sai dai ko kallon kirki bai samu daga farida ba, balle karɓa mai kyau.
Tana saka ran asirin da ta yi ya ci shi, ya biyo ta yana lallaɓata, amma ta ga ko ta kanta bai bi ba shi ma, yayi wanka ya shiga ɗakinsa ya hau bacci.
Tsananin takaici da baƙin ciki ya sanya ta je ta tashe shi da masifa, har da iƙirarin sai ta kashe mariya, bayan ta gama ci mata mutunci da kiranta mahaukaciya.
"Wallahi farida ban taɓa gaya miki ba, amma yau zan faɗa na yi dana sanin aurenki farida, baki da tarbiyya ko kaɗan. Suffar da ki ka mu'amalance ni daban kan na aureki, wadda ki ka nuna mini bayan auren daban. Wallahi na yi dana sanin rashin auren mahaukaciyar da ki ke faɗa tuntuni ta fiki sanin darajata.
Wallahi ki ka kuskura ki ka yi mata wani abu, a shirye nake da kowa ya kama gabansa da ni da ke, ba zaki kashe ni ba wallahi" ta dafe ƙirji tana zazzaro ido "Da can ba ka san bani da tarbiyya ba sai da ka auri mahaukaciya?"
"Na sani mana, kara nake yi miki ina yi miki kawaici, ke kuma ba kya gani, gara na fito miki a mutum, ina kuma jaddada miki, idan ki ka kuskura ki ka taɓa mariya kin taɓa igiyar aurenki, dan ba zaki cutar da abun da nake samun farinciki daga gare shi ba".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku wallahi yahaya kai butulu ne, azzalumi ni ka ke gaya wa haka?"
Dr. Ya ce "Ke ki ka so, ai ni ban san tuntuni kamar a kurku nake ba, sai yanzu na yi ƴanci ai. Ke ki ka janyo duk abun da na yi miki, ke ma kin san na yi haƙuri da ke, kuma bani da niyyar cutar da ke, amma halinki ya fara kaini bango"
Gaba ɗaya farida ta ji duniyar tayi mata zafi, komai ne naman ƙwace mata.
Washegari dr. Ya shirya ya tafi gagarawa duba iya, babu yadda bai yi da mariya ba, ta ce masa ita fa ko rasuwa iya ta yi ba za ta je ba. Sam mariya ba ta da zafi, amma tun da ta faɗi haka ya san abubuwan da iya tayi mata suna cigaba da ƙona mata zuciya ne, dan haka ya ƙyaleta.
Ya je ya tarar an mayar da iya asibiti, babu wata kulawar kirki, babu jinya mai kyau tana iya magana amma ba sosai ba, sai ta yi zawo har ya fara bushewa a jikinta ba a ɗagata an gyara ta ba.
A wannan karon mariya ta matsa sosai a kan lallai sai ta je sun gaisa da maman raihan.
Raihan ya sanar da Alhaji, Alhaji ya ja wa mami kunne sosai a kan kar ta kuskura ta wulaƙantawa ummi uwa.
Mai hali baya fasa halinsa, dan sai da tayi abun da mariya ta fuskanci akwai wani abu a ƙasa, Hajiya kuwa ta karramata sosai da sosai.
Sai dai mami ta yi mamakin ganin maman ummi, sam ba baƙa ba ce ba ga dogon hanci har baka.
Sati biyu da dawowar su dr., Ƴan maiduguri suka zo ganin gidan mariya, suka din ga murna ganin yadda ta yi ƙalau da ita.
Bayan ummi ta koma gida daga gidan mariya, cikin dare naƙuda ta tayar mata.
A cikin daren ita da raihan suka tafi asibiti, dan noor ta gudu wurin mariya, wia sai ummi ta haihu za ta dawo, yanzu ta zama masifaffiya.
Da safe raihan ya kira waya ya sanar suna asibiti, sai dai haihuwa ta gagari ummi, ga ciwo amma labor baya gaba, duk ta galabaita, likita ya ce sai dai ayi mata aiki.
Alhaji ya ce lallai sai mami ta je asibiti ita ma, ayi komai da ita ai matar ɗanta ce.
Ummi ta tayat da hankalinta, ta din ga kuka tana cewa tsoro take ji, duk aka kewayeta ana rarrashinta.
Noor kuma tana gefen ta tana tayata kukan.
Ummi ta kalli mariya, ga mama matar kakanta, ga Anty maryam, ga hajiyar su raihan, ga Abdul ga raihan kansa har da Salim, ga Nihal ƙanwar raihan, ana rarrashinta. Duk da mami ita sai yatsuna fuska take yi.
A ranta ta ce "Allah sarki, haka family suke dama? Kowa ya damu da kai" wani irin farinciki ya cika mata zuciya.
Ta ce sai dai a shiga aikin har da raihan, idan mutuwa za ta yi ya riƙe hannunta.
Mami ta ja wani uban tsaki, raihan kuwa ya riƙe hannunta yana ta kwantar mata da hankali.
Raihan ya kasa zaune ya kasa tsaye, aka shiga da ummi, awa guda da wani abu, aka fara fito da jarirai, mace da namiji.
Sai dai hankalinsa ba a kansu yake ba, Ummi yake jira a fito da ita.
Yana nan tsaye aka turo ta a kan gado idonta a rufe, an rufeta da green ɗin yadi.
"Salma" ya kira sunanta da ɗan ƙarfi.
Ta buɗe ido tare da riƙe hannunsa ta ce "Ka yi magana a hankali mana, ban mutu ba" yayi dariya ya durƙusa ya sumbaci goshinta ya ce "Thank you very much sweetheart, Allah ya baki lafiya"
Can waje kuwa ana ta murna an fito da jarirai, mami ta kallesu ta ce "Taɓ, wannan wane irin yara ne, mu kaf danginmu babu wannan kalar, meye wannan?"
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
49
Tsit kowa ya yi ya zuba wa mami ido, tana wani yatsune fuska.
Hajiya ta ce "Amma meyasa zaki ce haka? Wannan ai ba magana ba ce ba"
"Eh na faɗa, ko a dangina kin taɓa ganin irin wannan?, kalli kalar uwarsu ki kalli raihan ki kalli yaran".
Jajawur yaran, haskensu ya wuce ace hasken raihan kawai suka ɗaukko, gasu manya sosai, kuma kansu ƙwal babu gashi, kuma ba su da gashin gira ko kaɗan sai alamarta.
Mariya cikin jin kunya ta ce wa Hajiya "Bari na gansu"
Aka miƙa mata yaran, ta zuba musu ido tana murmushi sannan ta kalli mami ta ce "Hajiya, ai yaran nan da babansu su ke kama, haka na haifi ummi, Iya ta din ga ce mata aljana, sai dai kwana biyu kanta ya cika da gashi ko anty maryam, sai dai ummi tun tana jaririya baƙa ce".
Wani mugun kallo ta yi wa mariya ta ce "To ni danginmu babu irin wannan abubuwan, ni ban taɓa ganin jarirai a haka ba, danginmu dai kaf babu mai wannan farin"
Nan da nan Maryam ta harzuƙa ta ce "To mu namu akwai, duk tsiya dai ai na ɗanki ne ba wani ba"
"Ba ni da tabbas, ni ɗa na ma ba shi da cikakkiyar lafiya"
Hajiya da ta fara fusata ta ce "Ke dai ya rainawa hankali, dan ya tsallake son zuciyarki"
Mariya ce ta din ga basu haƙuri.
Raihan kuwa yana can ɗakin da aka kai ummi, sai zuba yake yi yana yi mata kalamai masu kwantar da hankali da ƙwarin gwiwa.
Likitan da yake yi mata allura ya ce "Maman twins ai ba Kya buƙatar maganinmu, wannan kalaman sun ishe ki warkewa" suka din ga dariya, sai da bacci ya ɗauke ta sannan ya tafi ɗakin da su Hajiya suke.
Noor ji take kamar ta kwaɗawa mamin raihan mari, ko karar ganin idon mariya bai saka ta yi alkunya ba.
Abdul da yake ɗakin ya tashi ya fita, Salim ma surutun ya ishe shi, ransa ya fara ɓaci.
Mariya ta kalli Salim ta ce "Salim, dan Allah jariran nan ba da babansu suke kama ba, dan Allah kar ki saka zargi a kansu tun suna jarirai, su sha wahala kamar ummi, idan ta tashi ta ji, ba za ta ji daɗi ba".
Salim ya ce "Mama, muna murna muna fatan Allah ya bawa ummi lafiya, mun gode wa Allah kyautar da ya bamu" ya ƙarasa maganar yana yi wa mami mugun kallo.
Kamar daga sama raihan ya shigo ya ce "Hajiya ba ni su na gansu"
Hajiya ta maze kamar babu abun da yake faruwa ta ce "Tun yanzu ka fara nuna wariya, ka tafi wurin matarka ko ɗaukar su ba ka yi ba" cikin washe baki ya ce "Tuba nake, dole in fara zuwa kanta, saboda su an yanka mini mata" yayi maganar ko a jikinsa yana ɗaukar su, wanda hakan ya sake ƙular da mami.
Ya ce "Tubarkallah, Hajiya irin idon ummi ne da su, brown masu kyau masha Allah, yaya ka ga namijin kallesu duk farare. Alhamdilillah" yayi maganar yana kallon Salim.
Farincikin da mariya ta gani a fuskar raihan, sai ya mantar da ita takaicin abun da mami ta yi musu.
Sauran mutanen maiduguri da suka zo ganin gidan mariya, suka cika asibitin. Ana jimawa ma sai ga dr. Ga Alhaji.
Raihan ya din ga sanar da ƴan uwa batun haihuwar.
Tsabar takaicin yadda raihan yake rawar ƙafa, ya sanya ta tashi ta bar asibitin.
Sai da ummi ta yi awa shida tana bacci, sannan nurses suka tasheta, suka ɗagata aka wanke ta, sannan aka bata abinci.
Ta saka kaya tayi kyau, kamar ba ita ba, sannan aka turo ta a kan gado aka mayar da ita main ɗakin da take.
Suka din ga murna ganin an fito da ummi ras da ita.
Sai jerawa ummi sannu ake yi, aka miƙo mata yaran dan ta shayar da su, amma ta kasa saboda yadda ido ya yi yawa.
Hajiya tare da Salim suka koma gida, ta yi wanka ta yo girki, suka dawo da Alhaji.
Shi ma Alhaji baki buɗe yake ta murna, yana yi wa jariran addu'a, duk da babu wanda ya gaya masa abun da matarsa ta yi.
Sai dai noor ta gaya wa ummi, abun da mamin ta ce, wanda ba ƙaramin ciwo yayi mata ba, sai dai ta basar saboda tana cikin murnar kyautar da Allah ya bata.
Ummi ta ce "Mama, jikin yaran nan kamar jariran mage, basu da gashi kwata-kwata".
"Me ki ke ci na baka na zuba? Zai fito in sha Allah"
Dr. Ma da daddare ya zo ganin jariran, tare da yi mata sannu.
Kusan kwanaki uku, ana ta shigowa ana fita duba ummi, a kwanaki ukun nan gashi ya cika kan yaran nan fal.
Kwanan ummi biyar, aka sallame su daga asibiti, raihan ya ce bai yadda a ɗauki hoton yaransa ba a saka a waya. Saboda masha Allah kai ba zaka ce ummi ce ta haife su ba, dan sun fi kama da larabawa sosai.
Su Hajiya Aishan bauchi, da sauran jama'arta, duk suna kano, sai da ummi ta yi kwana goma da haihuwa, sannan aka shirya gagarumin taron suna a wani katafaren event center.
Sai ranar suna ƴan gagarawa suka zo, aka ci aka sha, ummi sun samu kyaututtuka sosai da sosai ita da yaran, manyan mutane abokan hulɗar Alhaji Tahir, da abokan aikin Raihan, ban da ƴan uwa da abokan arziki.
Sai dai kan ranar sunan nan, yaran nan sun juye kalar larabawa sosai da sosai, gashi ya cika kansu da girarsu, kuma dukkansu brown eyes ne da su, namijin mai baƙin gashi, macen kuma irin na ummi.
Sai dai sunan da aka sakawa yaran ya yamutsa hazo, dan kuwa raihan sunan ummi ya saka wa macen Salma, namijin ya saka masa Muhammad, wai ya yi wa kansa takwara, ya yi wa Alhajin su, kuma ya yi wa mahaifin Ummi, tun da duk sunansu Muhammad laƙanin ne daban-daban, aka yi musu laƙani da Iman da kuma Ayman.
Ba yadda ummi ba ta yi da raihan ba, a kan ya canzawa macen suna, kar ya janyo mata magana a cikin dangi.
Amma ya ce "Kome mutum zai ce ya ce, son da nake yi miki, dole na yi miki takwara dole duniya ta shaida ina son matata".
Noor ta sha kwalliya, kamar amarya.
Ta je ta saka salim a gaba, sai ya yi mata hotuna da iphone ɗin sa.
Ya gama yi mata hotunan yana nuna mata, sai murmushi take yi, ya kalleta ya ce "Kin yi kyau kamar ranar bikinmu" a razane ta kalleshi ta ce "Bikinmu kuma?"
"Eh mana, ko ba kya so na?"
Ta ɗan sosa kai ta ce "Yarinya ce fa ni"
"Ba kya son tsoho ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a kai ba tsoho ba ne"
Ya ce "Tsoho ne mana a kan ki, am 37 you are just 15, dama so nake bayan suna in yi wa Alhajinmu magana, amma tun da kin ce haka shikenan, idan kin gama hotunan ki kawo mini wayar"sai kuma ta ji babu daɗi.
Mami kuwa a ranar sunan sai da ta kira raihan, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, wai ya ƙare a gidin mace, saboda asara har da saka wa ƴar sa sunanta, bayan uban kuɗin da ya kashe mata ita da yaranta.
Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, dan ya san duk abun da ya yi wa ummi bai faɗi ba, kuma ba zai yi hidimar da Alhajinsu yake yi wa iyalinsa ba.
Da daddare ummi ta yi wanka ta saka kaya, Anty maryam ma ta wanke jariran, an samu sun yi bacci saboda sun gaji, sun sha kuka da jagwalgwalon ƴan suna.
Raihan ya shigo yana yi wa ummi murmushi.
"My MD, murmushin me ka ke yi ne?"
"Kallonki kawai yana sani murmushi, amma murmushin na yau na musamman ne, guess what?"
Ta girgiza masa kai ta ce "I have no idea"
Ya kamo hannunta ya danƙa mata mukullin mota ya ce "Gashi in ji Alhaji, ya ce a baki ya riga ni"
Ummi ta waro ido ta ce "MD mota Alhaji ya bani" ta rungume raihan tana murna, ta din ga zuba masa addu'a da shi da Alhaji.
Da gudu ta fita falo, tana nuna wa su mama da ba su riga sun bar gidan ba, aka din ga yi mata murna.
Noor ta ce "Yaya ummi baki ji zuciyata ba, na taya ki murna, amma ina son mu yi magana"
Suka keɓe da noor, ta gaya wa ummi abun da ya faru tsakaninta da Salim.
"Noor meyasa baki da wayo ne? To meye aibun yayan?"
Noor ta ce "To ai ni yarinya ce, kuma ni bana son ayi ta yi mini surutu kamar yadda aka yi miki"
"To sai me? Wataƙila da ina nan a gida ban yi auren ba, ai yanzu ki samu mai sonki tsakani da Allah shi ne. Shi da ake son ya yi auren ma, kin san da