ƙuda" ko jiran amsar farida ba ta jira ba, ta bar falon ta bi wata hanyar, ta tafi can bedroom ɗin da noor take, wadda ba ta san ma farida ta zo ba.
Ƙarfe huɗun yamma, dr. Ya sauka, basu tsaya ko ina ba sai gidan raihan, ta rungume ummi suka din ga murna, kamar sun shekara ba su ga juna ba.
Sam farida ba ta san ranar ma maiduguri ya je ba, yana komawa gida, ta dira masa bala'i tana gaya masa abun da ummi ta yi mata.
Kai tsaye ya ce ƙarya take yi wa ummi, sharrinta ne kawai ummi ba zata aikata haka ba, tsabar kishi ne kawai, idam ma hakan ne meyasa da ba ta je gidan ummi ba sai yanzu da wannan lamarin ya zo.
Abun duniya duk ya ishi farida, asirin tayi har ta gaji, ya shammaceta, da kan ayi ne da ta yi yaƙinin asirin zai kama shi, maganar ta rushe.
Raihan ma ba ƙaramin daɗin zuwan mariya ya ji ba, tayi ƙalau da ita.
Noor kuwa tun bikin ummi da suka je maiduguri, suka saba da mama, tun da dr. Ya gaya mata takwararta ce.
Kuma aka yi sa'a ba ta manta ta ba, a ranar da daddare, sai ga Salim ya zo har da Sagir.
Mariya ta din ga murna, duk idan tana magana wasu lokutan ta kan haɗa da shirme, amma a hakan take yi musu nasiha, tare da ƙara musu haske a kan rayuwa.
Sagir ya din ga mamaki da aka ce ita ce maman ummi, ita da haskenta ma, ummi ce dai baƙa, sai dai idan tayi wani abun kamar ummin.
Ta tsiro da batun cewa lallai, a kai ta su gaisa da babar raihan, da babansa sun gaisa da Alhaji, babar raihan ce ba su taɓa haɗuwa ba.
Gaban raihan ya faɗi, amma ya basar ya ce zai kaita su gaisa.
Su Salim sun daɗe sosai, duk da a zahiri bayan mama, noor ce ta riƙe shi, dan chatting suke a wayar ummi ba ta sani ba, idan suka gama sai ta goge.
Ummi ta yi iya ƙoƙarinta, ta mantar da mariya, batun haɗuwa da babar raihan.
Allah ya taimaki Iya, ba ta samu mumunan rauni ba, sai dai ta fasa kai, fuskarta duk ta ƙuje, sannan ta targaɗe ƙashin ƙafarta, da hannunta, gashi kuma kanta sai da aka yi mata ɗinki, kan ayi ɗinkin nan kuwa sai da aka sauke gashin kan gaba ɗaya, ga bakinta ya kumbura saboda wahala.
Da ƙyar suka yi karo-karon haɗa kuɗin magani, likita ya rubuta hoton ƙwaƙwalwa, saboda kai da take ta kuka da shi, amma babu kuɗin yi, maganin ma ba duka suka saya ba.
Suna tsaka da wannan gaganiyar, ana ƙoƙarin kiran dr. Suka samu labarin yayi aure, ya auri mariya.
Gaba ɗaya sai suka manta da halin da iya take ciki, suka shiga salallami.
Iya na daga kwance ta tuna yadda tun bayan ya gano in da mariya take, ya ce zai aureta, amma ta ce ba ta lamunta ba, tun da ya riƙe ummi shikenan, ba zai sake kwasota ya kawo musu dangi ba, saboda a cewarta mariya annoba ce, mugun abun ta ne ya sanya ta haukace.
Su ummi suna airport, tare da dr., Ta wani ɓangaren ransa a ɓace, saboda tijarar da ya sha a wurin farida daren jiya, da ya ce yau zai koma uganda, tare da babar ummi.
Har da zaginsa ta ƙare masa cin mutunci, abubuwa da dama yana duba yaransu ne ya sanya yake ɗaga mata ƙafa, kuma tun ainihi, shi mutum ne mai sanyi ba shi da hayaniya, shiyasa take yi masa duk abun da ta ga dama.
Suna airport sun rako su dr. Mariya sai kalle-kalle take yi, da alama a tsorace take.
Sai ga wayar kawu Sagir, dr. Ya ɗaga tare da amsa masa sallamar.
"Yanzu yahaya tsakaninmu da kai abun har ya kai haka? Muna ƴan uwanka amma sai dai mu ji a gari ka yi aure? Abokanka sun fi mu kenan?"
Dr. Ya ce "Ba abun ɗaga hankali bane ba, abun ne ya zo ba shiri, na ga akwai buƙatar tun ina raye ya zamana ummi tana da madogara ko bayan raina, dan yadda ba a kula da ita bayan ran mahaifinta ba, bayan raina ma ba za ta sauya zani ba, dan na san kun san wadda na aura, kuma da na neme ku, ba zaku bari ba, da kaina zan zo har gida na yi muku bayanu"
"Aishikenan, ni ba ma wannan ba, ka ganmu fa a asibiti da iya"
"Subhanallah me ya same ta?"
"Wallahi dai tsautsayi ne, Auwwalu ne ya sha ta gaya masa ƙarya, ta yi masa faɗan rashin sana'a sai bacci, ya din ga tamaula da ita, saura ƙiris ya jefa ta a rijiya. Yanzu dai gamu a asibiti, magunguna an sayi wasu, wasu kuma ba a saya ba, ga hoton kai an rubuta shi ma ba kuɗin"
Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga illar rashin mayar da hankali a kan tarbiyyar yara da iliminsu ko? Ina Auwwalun yake?"
"Ya gudu ba a san in da yake ba".
"To ka ga ni yanzu ina filin jirgin sama, zan koma makaranta, zan turawa Abdul kuɗi ya zo ya dubata ya baku, Ubangiji Allah ya sauwwaƙe"
"Amin, amma dan Allah yayi sauri ana buƙatar kuɗin"
Dr. Ya ce "Sai ya tura muku, idan ya so daga baya sai ya zo ya dubata"
Kawu Sagir ya ce "To hakan ma yayi, bari na ga Idris yana da lambar banki, sai a turo ya saka kuɗin, an gode" bayan dr. Ya gama wayar suka din ga jajantawa, mariya kuwa ko Allah ya kyauta ba ta ce ba.
Ummi har da hawayen murna, ganin mama tare da dr. Za su keta hazo tare, ko ba komai tana sanyawa mama ran samun kulawa daga dr. Kasancewarsa jajirtaccen mutum.
A ranta ta ce "So so ne, amma son kai ya fi, in sha Allah a kujerun hajji da umaran da Alhaji yake rabawa sai kun samu, ko ban je ba ku je a tare hakan nan, ku yi mini Addu'a.
Bayan jirginsu ya ɗaga, suka koma gida.
A cikin jirgin ƙanƙame dr. Ta yi, saboda gani take kamar za su faɗo daga cikin jirgin.
Dariya ya din ga yi mata, ganin yadda take a rikice gaba ɗaya, hakan ya bashi damar rungumeta a jikinsa, sai wani irin daddaɗan ƙamshi take yi.
A hankali take tambayar sa "Baban ummi ba zamu faɗo ba kuwa? Tsoro nake ji sosai"
"In sha Allah ba zamu faɗo ba, lafiya zamu sauka".
Dr. Dubu hamsin ya turawa Abdul, ya ce masa ya tura wa su iya idan sun turo account number, shima ya ƙara dubu talatin ya tura musu dubu tamanin.
Ummi bayan sun koma gida, raihan ne ya sakata a gaba, yana mammatsa mata jikinta a hankali cikin tsantsar soyayya da kulawa yake ce mata "Am sorry sweetheart, kwanan nan am very busy, kamar bana kula da ke sosai, kuma na san kina buƙatata"
Tayi murmushi ta ce "Saboda jin daɗi yayi mini yawa ko? A cikin mata hamsin nawa ne suke samun kulawar da nake samu, idan suna da juna biyu, kana iya yinka aiki ne yayi maka yawa".
Ya numfasa ya ce "Duk da haka dai, wallahi ummi wasu lokutan kaina kamar ya fashe, ina jinjinawa Alhaji yayi ƙoƙari, kin ga yakamata ace Yaya salim yana cikin system ɗin nan, tun da bamu muka tara dukiyar ba, mu kula mu tattalata ta haɓaka, ga branch ɗin mu na Abuja, ina ga a watan da zaki haihu za a buɗe shi, ban san ma ya zan yi ba, wa za a mayar can Abujan, atleast yakamata ace da wani daga cikin mu"
Ummi ta ce "Mhmm ka lura zuwan yaya Salim gidan nan ya ƙaru sosai?"
Ya jinjina kai ya ce "Magana ce kawai ban yi ba"
"Anya nan gaba magana ba zata taso tsakanin sa da noor ba, shaƙuwarsu ta yi yawa"
Cikin murna raihan ya ce "Wallahi sam ban kula ba, tun da ya ce ke ƙanwarsa ce na zata saboda ke ne, yana cigaba da bibiyata ne kar na yi miki wani abu. Amma kina ganin dr. Zai bashi ita? Kamar yayi mata tsufa kuma ga yanayin sa"
Ummi ta ce 'Aikuwa yaya Salim ya shiryu, a kan lokacin da na san shi, ba abun da zai hana ya bashi ita, nima haka aka yi mini surtu da na aureka, in dai suna son juna ba shikenan ba"
Ya jinjina kai ya ce "To Allah ya tabattar mana da alkhairi, Kairun nisa'i, wannan cikin naki kamar ya fi ƙarfin watanninsa, kafin mu koma awo, sai mu je ayi miki scanic kawai mu tafi da shi"
Ummi ta shafa cikin ta ce "Nima na gani, kamar girman yayi yawa a wata biyar, amma sai a sake hoton"
Sun jima suna hirarsu cikin nishadi, har ta nemi izininsa a kan zuwa duba Iya, an kai ruwa rana kan ya amince, ta ce idan Abdul zai tafi sai ta bishi ita da noor.
Ummi tun bayan dawowarta, ta duƙufa Addu'a, da roƙon Allah ya sassauta mata mugun kishin da yake damunta.
Babu dare ba rana, ta miƙe da yawan tasbihi da bayar da sadaka, tare da tawasalli da ayyukan alkhairin ta, tana roƙon Allah idan auren Raihan da alkhairi Allah ya tabattar ya rage mata kishi, idan babu kuma, Allah ya rusa abun, ya musanya da mafi alkhairi, yayi mata maganin duk wani abu da zai tayar mata da hankali, ko kawo cikas ga rayuwar aurenta.
Sannan ta tsananta addu'a, a kan Allah ya ƙara qa raihan son ta, da ƙaunarta ita kuma Allah ya bata ikon yi masa biyayya.
A hankali ta ji zafin kishin yana raguwa, bayan auren mamanta da dr. Ta din ga istigfari a kan ɗagawa raihan hankali a kan maganar auren sa, wataƙila da ta cigaba da matsawa, da ba ayi na mamanta ba.
Lokaci ɗaya mami ta daina kira tana ɗagawa raihan hankali a kan auren nan a gabanta, kuma ta daina zuwa ci mata mutunci, dama tuni ta saka lambar maryam a blacklist.
Gidansu raihan kuwa, rana tsaka babu notice, Hajiya Aisha ta dira a gidan Alhaji Tahir.
Sai da yayi mamkin ganinta, ya ce "Ke hajjaju, zuwa ba sanarwa matan gidan babu wanda ya sanar mini zaki zo ai".
"Ina na ga ta tsayawa jiran notice, ashe raihan zai ƙara aure, kuma daga ɓangaren uwarsa, haba Tahir, kuma kana kallo, yaushe yayi auren farin zaku ɗora masa ɗawainiyar auren matan biyu?"
Alhaji ya ce "Ke daɗina da ke, ba kya ɗaukar abu da sauƙi a kan raihan, babarsa ce take son ya ƙara"
"A'a ban lamunta ba, yanzun ma ba dan Salim ya gaya mini ba, ba zan sani ba kenan? Kuma a rasa wa zai aura sai wannan dangin masifa da bala'in, ashe har ƙarya yayi muku bashi da lafiya dan ku ƙyale shi, amma abu kamar bala'i, kuma saboda tumasanci irin na bilki har da sakawa ya saki ƴar mutane, to mu ba haka muke ba, ko da muka yi bore da ka aure ta, ka juyawa ƴar mu baya, bamu ce ka saketa ba, dan haka da kaina na zo na yi wa tufkar hanci, ba zai auri ƴar rakiyar ba".
Alhaji ya ce "Ke ki daina yi mini faɗa kamar wani ɗanki mana, har kuɗi fa an kai".
"Amma ai ya ce ba ya so, dole na yi maka faɗa, ba fa kowane lokaci yakamata ka din ga biye wa matanka da yaranka suna abun da suke so ba. Wallahi muddin ta ce sai yayi auren nan, sai dai ta nema masa wata sana'ar ta kafa shi, ya bar shugabancin kasuwancin ka, dan na san da shi take taƙama, idan ba zaka iya cewa an fasa ba, zan je na yi wa ita rakiyar magana, dama ni da ita kar ta san kar ne ai.
Su riƙe kuɗin an bar musu, amma ƙara aure ba yanzu ba". Tana tsaka da masifar, Hajiya ta kawo mata abinci, ita ma ta rufeta da faɗa a kan, meyasa ba a gaya mata abun da yake faruwa ba, dan haka ta je ta kirawo mata bilki, kuma a kirawo mata Salim, dan ta tabattar mata shi ya gaya mata ba Raihan ba.
Aikuwa ranar mami ta ga ta kanta, dan cin mutuncin da hajiya Aisha ta yi mata sai da ta yi kuka, sannan ta ɗora da cewa "Ke ma ki ji idan da daɗi abun da ki ke yi wa taki sirikar, saura maryam dan ubanta, zan iya wanke ƙafa na je har fatakol ɗin, ba a barikin soja ba, idan a cikin bindiga take na je na ci ubanta a kan matar raihan. Raihan ɗin sai ka ce wani ɗan gwal da ake ta wannan tsiyar a kansa, ita ba uwa ce tayi naƙuda ta haifeta ba? Da ki ke mata iƙrarin munin ke halitta ki ke yi, da hancinki kamar pipe ɗin ruwa. Mu danginmu bamu sabawa yi wa sirikai rashin daraja ba, dan haka ba zaki fara ba. Tun wuri ki samu rakiyar ki yi mata bayani, idan kuma ki ka bari na yi mata abun ba zai yi muku daɗi ba".
Duk da haka sai da suka yi faɗa da Alhaji, yayi mata ƙorafin za ta mayar da su ƙanan mutane.
Bayan su hajiya sun tafi ta ce masa "Yarinyar nake yi wa gata, na lura matar raihan irin matan nan ne da ba kowace irin mace za ta iya gogayya da su ba a kishi, ai ko ba ƙarara ba yana faɗa, kai ka sani, idan aka yi masa auren dole matar wahala kawai za ta sha, shi wannan dai da ake yi wa kallon mummuna ita ce tayi masa, da azo ya auri ƴar mutane ta wahala a banza ai gara ba ayi ba".
Ya ce "Na nuna wa bilkin haka, amma taƙi ganewa, kuma uwar yarinyar ce take zigata, amma tun da ke tana tsoranki, ƙila ta ji.
***
Dr. Kuwa kwanansu uku a uganda, dama akwai abokinsa da yake zaune a can yake lecturing, kasancewar babban gida ne sosai da gwamnatin ƙasar ta bashi, a wani sashe na gidan dr. Yake zaune.
Kamar wanda ya auri yarinya ƙarama, haka yake jin kansa, ya tuna abun da farida ta ce na ba uwar da za ta tsinana masa, amma ya ga abun da bai yi tsammani ba.
Tun ranar da suka je, take mugun jin kunyarsa, ko kallonsa ba ta iya yi, da safe idan ta gaishe shi, komai zai ce mata sai dai ta bashi amsa da ka, amma ba zata yi magana ba, kamar ya auri budurwar ƙauye.
Shi gaba ɗaya ma dariya take bashi, jin sa yake hankalinsa a kwance ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saɓanin idan yana tare da farida, da wani lokacin rashin mutuncinta ba ya motsawa, sai yana buƙatar ta, sai ta tsiro da na ta buƙatun, sai ya yadda zai yi, koma ya yi mata sannan ta yadda da shi, kamar masu zaman dadiro ba aure ba.
Ya zuba mata ido, ta koma gefen kujera tana ta sinne kai, ya ɗaukko wayarsa ya duba ummi na online, ya kirata voice call.
Mariya na jin muryar ummi, ta tattara hankalinta a kansa.
Suka gaisa da dr., Yake tambayar ta ko sun je duba Iya, ta ce masa a'a sai cikin satin.
Mariya ta ƙura masa ido, ya ce "Ko in baki ku gaisa?" Ta jinjina masa kai da sauri.
Ta matsa kusa da shi ta karɓi wayar, ta saka a kunnenta ta ce "Ƴar baƙa kyakykyawa"
Ummi ta yi dariya ta ce "Mama Amarya"
Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Zan ci gidanku"
Ummi ta yi murmushi ta ce "To ya ugandan? Kin fara jin yaren su"
Ta ce "A'a ni ban taɓa fita ba ma, amma daga nan gidanki ba nisa ko? Ai zan iya zuwa"
Ummi ta ce "Haba mama, ba fa Nigeria ba ce ba, ba ki ga sai da ku ka hau jirgi ba"
Ta ce "Eh to haka ne, to ya cikin naki ashe kin kusa haihuwa"
Ummi ta yi sauri ta kashe wayar dan kunya, tun da mama tazo manyan riguna take sakawa da hijjabi, dan kar ta ga cikin, kuma har ta gama kwanakinta ba ta nuna mata ta ga cikin ba sai yanzu.
Ta kalli dr. Ta ce "Ka ga na daina jin ta, ɗan dubo mini ita"
Yayi dariya ya ce "Kunya ki ka bata ta kashe wayar, ina ruwanki da cikinta" yayi maganar yana matsawa daf da ita.
"Ni mamaki ma nake yi, har ummi ce da ciki, ohh kwanci tashi asarar mai rai. Aka yi ta cewa ba zata yi aure ba, gashi ma har za ta haihu"
Dr. Ya ce "Eh haka lamarin Allah yake, amma dai dan Allah ki daina guduna, ni ba dodo bane ba, yanzu saboda maganar ummi ce shi ne ki ka kula ni, bayan tun safe kin ƙi kulani"
Ta sunkuyar da kai kamar ta yi layar zana ta ɓace.
Ya ɗago haɓarta, amma ta ƙi kallonsa.
Yayi murmushi ya ce "Zo mu tattaka, mu je kasuwa ki ga garin" ya riƙe hannunta ta tashi tsaye, suka nufi bedroom.
Kusan kwana huɗu, da Abdul ya tura kuɗi, kawu Ilyasu ya kira Abdul yana tambayar sa, wai shiru fa ba su ga kuɗi ba, jikin Iya yana tsamari, za a sallame su ma saboda rashin kuɗin.
Abdul ya ce "Ai tun a ranar na tura dubu tamanin, dr. Bai hau jirgi ba sai da ya tura mini kuɗin, ni kuma na ƙara na tura".
"To ya haka? Idris ya ce ba su shigo ba".
Abdul ya ce "A'a dai, ya sake bincikawa, dan ta application na tura kuɗin"
Ya din ga mamaki, ya duba wayarsa har da receipt kuɗi sun fita.
Washegari tun da safe suka shirya, raihan ya je Abuja, noor da Abdul sai ummi suka tafi Jigawa duba Iya.
Sai dai da suka je asibitin, sai da ummu ta ɗan tsorata, Iyan duk ta zama abun tsoro, fatarta ta yamushe, gashi an aske gashi, duk an liƙe kan da bandeji, hannunta da ƙafrta ma haka, idonta yayi ja saboda azabar ciwon kai, ba ayi hoton ƙwaƙwalwa ba, balle a san menene yake faruwa.
Noor ta ce "Kai na ga iya ta koma kamar simigul"
Abdul ya galla mata harara, ummi ta ce "Sannu iya ya jiki?" Iya ba baki sai kallon ummi da take yi.
Ta kalli amaryar kawu Ilyasu ta ce "Ga abinci mun zo da shi a bata, amma kunu ai ba zai riƙe ta ba".
Suna nan zaune su kawu Sagir suka zo, aka gaggaisa,