Tausasan kalamanta sai suka sanya tausayinta ƙara shigarsa.
"Na san babu sauƙi, amma ki jure dan Allah na samu na yi wa mami biyayya ko na gama da duniya lafiya, idan ina ganinki a haka zan iya bujirewa, ki daure Salmana ki yi haƙuri na san da ciwo" ya din ga rarrashinta tana wata irin ajiyar zuciya, da sai da ta din ga bashi tsoro kar wani abu ya sameta.
Cikin dare jikinta yaƙi daɗi, dama tana zazzaɓinta a tsatstsaye, idan ta ci abinci tayi ta amai, ba abun da yake zama a cikin ta, sai dai na yau ya tsananta, da har sai da raihan ya gane, tun tana iya zuwa banɗaki yin aman har ta kasa.
Ranga-ranga ya tafi da ita asibiti, a karon farko gwaje-gwaje suka tabattar da ciki ne da ita. Raihan kamar yayi tsalle dan murna. Tun da tayi ɓarin nan ba ta ƙara yin period ba.
Aka din ga saka mata ruwa, sai dai zazzaɓi ba ya sauka, kuma ko ta ci abinci ko ba ta ci ba sai tayi amai.
Tausayinta ya cika raihan, ga zafin laulayi ga kishi, sai da likita ya zo dubata ne ma take gaya masa ta fi wata tana zazzaɓi a kaɗan-kaɗan.
Raihan yana saka ran a sallame su, amma likita ya ce sai sun riƙe ta, saboda low bp, ga jininta ma yayi ƙasa, sai an ba ta kulawa ta musamman.
Kwananta biyu a asibiti, da sassafe ya dafa tea zai kai mata, ya fito daga motar sa, sai ga kiran wayar Alhaji.
Ya ɗaga yana gaida Alhaji sai dai yanayin muryarsa ya tabattar masa ba lafiya ba.
"Kana ina?"
"Ina Abuja Alhaji lafiya?"
"Ban sani ba, ina ummi take?"
Gaban raihan ya faɗi ya ce "Tana gida?"
"Ni zaka yi wa ƙarya? Ashe baka da hankali ba ka da mutunci raihan? Jiya da daddare babanta ya kirani cikin damuwa ashe sakar masa ƴa ka yi, kuma an nemi in da take an rasa, ga wani case can a familynsu ma ana ta nemanta, ka gaya mini ka sakar masa ƴa? A baka yarinya cikin girma da mutunci amma ka wulaƙanta ta, yarinya mai tarbiyya da nutsuwa, bilki ce ta saka ka saketa ko?"
Raihan ya girgiza kai ya ce "A'a ba ita ba ce ba".
"Koma waye ya saka ka, ka cuci kanka, kana ina? Kuma ina ƴar mutane"
Raihan ya ce "Muna tare a nan Abuja"
"Uban me ka ɗauketa ka yi mata a abujan bayan ka saketa?"
"Alhaji ba sakinta na yi ba, rashin fahimta ne"
A fusace ya ce "Kai ka sani, baka ma da kunya, in anjima zan shigo garin Abujan, ka bani ƴar mutane da takardarta na danƙawa mahaifinta ita, kai kuma tun da mutumin banza ne ka je ka ƙarata, am so disappointed on you!.
08081012143
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
45
Raihan ya rasa ta ina zai fara kare kansa ma, haka yayi shiru Alhaji ya gama faɗan ya kashe wayarsa.
Kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa, haka ya ƙarasa cikin asibitin, ya taimakawa ummi ta wanke baki, ya haɗa mata tea da dankali yana bata. Cikin ɗari-ɗari take ci, dan ta san ƙarshen abun ta amayar da abun da ta ci, ga yunwa tana ji sosai.
"MD ka ga wancan cikin ban san ma da shi ba, ban yi laulayi ba wannan kuwa sai wahala nake sha"
Yayi murmushi da ƙyar ya ce "Wancan kin ci bonus"
"Wai ya na ganka duk wani iri ne? Na san zaman asibiti da gajiya, ba daɗi shiyasa gara ka mayar da ni maiduguri"
Raihan ya ce "No, ba gajiya na yi ba, da ke da babyna kuna buƙatar kulawata. Ai gazawa ce in ce ki koma gida dan baki da lafiya, ni zan yi abun da ya dace na kula da ku"
Tayi murmushi ta ce "To aikin fa?"
"Shima duk zan iya"
"Ɗan Aljannana, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ya barmu tare har aljanna"
Ya amsa mata da Amin, ƙasan zuciyarsa yana fargabar hukuncin Alhaji, dan daga ji ya ɗau zafi sosai.
Yadda ta gama cin dankalin nan, sai da ta amayar da shi gaba ɗaya, abun har tsoro yake bawa raihan, duk ta rame saboda laulayi.
Yana nan zaune tare da ita, har ta samu bacci, bayan wasu awanni ta din ga jin hayaniya kamar a mafarki. Ta buɗe idonta, ta ga Alhaji a ɗakin tare da Salim, ga raihan a gefe ransa a haɗe sai kuma likita a tsaye da file.
A hankali ta tashi zaune, tana mamakin zuwansu ta ce "Alhaji sannu da zuwa"
Ya dubi Ummi ya ce "Sannu ya jikin? Dan Allah kalli yadda duk ta bi ta ƙare ta rame, meke damunta ne? Ko kuma duk tsiyataku da rashin mutuncinka ne ya sanya ta rame" Yayi maganar yana kallon raihan.
Likita ya ce "Ahh ba wani abun damuwa bane, laulayi ne na mata, ba ta iya cin komai shiyasa muka ajiyeta mu ke ta saka mata ruwa"
Alhaji ya ce "Ka rubuta mata sallama, gida kano zamu tafi, za a cigaba da kula da ita a can"
Ya mayar da idonsa kan ummi ya ce "Banda abunki ummi, gani menene amfanina? Ko dr. Ba ya nan wani abu ya haɗaku sai ki zo ki gaya mini, ni ƴa ta ce ke ba sirika ba, kawai sai ki biye masa ki tafi wani wurin ace ba a san ma in da ki ke ba? Kuma dan baka da kunya ka lallaɓa ka mayar da ita ka taho da ita nan ba wanda ya sani, hankalin mahaifinta na can a tashe bai san ina take ba, ka bani kunya" daga ummi har raihan aka rasa mai magana, ummi ba ta taɓa zaton Alhaji ya iya faɗa haka ba, saboda kullum fuskarsa cikin murmushi yake.
Haka aka sallami ummi, suka nufo kano, raihan ya sha faɗa a wurin Alhaji,kuma yayi shiru bai ce komai ba ummi gaba ɗaya ta ji babu daɗi.
Asibiti suka zarce da ummi, aka cigaba da ba ta kulawa ta musamman, saboda suna tafe a hanya ma tana amai.
Alhaji ya kira dr. A waya ya sanar masa ya gano ummi, tana tare da raihan a maiduguri.
Dr. Ya ce ya haɗa shi da ummin a waya, Alhaji ya ce masa ba ta da lafiya, ba za ta iya amsa waya ba.
Dr. Ya ce a cikin satin zai shigo Nigeria, dan hakan yayi dai-dai da lokacin zuwansa hutu. Ya karɓi kwatancen asibitin, ya kira Abdul a waya, ya ce su je asibiti da shi da noor, su duba masa jikin ummi.
Ko da suka je, sai da Abdul ya yi wa raihan ƙorafin, meyasa bai gaya masa ba ya ga ummi.
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda Salim da noor suke yi wa juna murmushi ba, kamar sun saba. Kuma a iya sanin ummi ba shi da fara'a ko kaɗan.
Noor ta ƙarasa gaban gadon ummi ta na yi mata sannu.
"Yaya ummi shi ne ki ka tafi aka neme ki aka rasa ko? To ƴan gagarawa ne suka samo wani abokin Abba, suka saka ya kira musu shi, aka gaya masa abun da ki ka yi, ya bi ba'asi ban san dai me suka ce masa ba, ya kira waya yana faɗa ya cewa yaya Abdul ya je gidanki ya duba masa ke dama ba ya samunki a waya, aikuwa dai ya gaya masa gaskiya, amma fa mun sha faɗa saura ke idan ya dawo dan ransa ya ɓaci"
Salim ya ce "Ba ki ga bata da lafiya bane?"
Ta ce "Au, haka ne fa, zumuɗi nake na ganta, ba ka san yadda na shiga tashin hankali ba da aka ce ta ɓata".
Yayi murmushi ya ce "I see"
Alhaji ya ce "Ai daga ita har shi, sun yi laifi, kuma ba zan matsa da bincike ba, sai dr. Ya dawo, amma fushi dole ayi fushi da su"
shi dai raihan ya rasa menene yake yi masa daɗi, ga rashin lafiyar ummi, ga faɗan Alhaji da yaƙi saurarensa.
Salim ya ɗauki Alhaji suka tafi gida, tun da yaje gida yake cigaba da faɗa a kan abun da ya faru, hankalin mami yayi mugun tashi, dan yadda ransa ya yi mummunan ɓacin nan, zai iya aikata komai dan kamar ƴar cikinsa aka yi wa haka ɗauki lamarin da zafin gaske.
Ta din ga kiran raihan tana jaddada masa, kar ya kuskura ya gaya wa Alhaji ita ce ta saka ya saki ummi.
"Mami na ji, ni ba zan faɗa ba, amma ummi fa?"
"Au kai sai ka bari ta faɗa ɗin?"
"Mami ya zan yi, tayaya? Zan yi mata dole ne, tana kwance muna fama ba ta da lafiya, ba zama ta fahimci me nake nufi ba" mursisi raihan ya nuna wa mami ba zai tursasa ummi ba. Bayan ya kashe wayar ya kalli wayar ya ce "Mami ina fatan zaki fahimci cewa, ɗan adam duk ƙin da ki ke yi masa wataran zai iya yi miki rana, ko ki nemi alfarma a wurinsa.
Kwana biyu ummi ta ɗan warware, ranar dr. Ya dawo, Alhaji dai tare da Salim suke zuwa asibiti, haka Hajiya ma take sintiri.
Tun da raihan yayi aure, Alhaji da Salim suke ɗasawa saboda Alhaji ya jinjinawa Salim yadda yayi playing role ɗin sa na babban yaya ga raihan ba tare da wata adawa ba. Kuma a hankali ya lura da ya rage fitina sosai da sosai, dan ko fita baya son yi suna tare da Alhaji.
Alhaji ya kasa shiru, sai da ya tambaye shi, dalilin canzawarsa lokaci ɗaya yayi murmushi ya ce "Alhaji kenan, ai ko dabba idan kana mutunta uwata zata so ka, balle ɗan Adam ni dama wasu lokutan babarsa ke sanyawa nake ja baya da shi, duk abun da yake faruwa ina sane da yadda mutunta da girmama mahaifiyarmu. Da na raka shi maiduguri ma, yadda dangin matarsa suka din ga yaba kamalarmu na ji daɗin hakan sosai, na ƙara yadda da zama mutumin banza ba shi da wata fa'ida. kuma ƙanina zai yi aure very soon zai fara tara zuriya, kuma yaransa namu ne, abun kunya ne a garemu yaranmu su taso su ganmu a irin wannan yanayin. Ina ta addu'a kuma ina jan hankalin Sagir ma. Abu na gaba rayuwar raihan da matarsa ta burgeni, da har na ji nima ina son yin aure, amma na san za a iya hanani aure saboda halina, duk ruɗin abokai ne dama, amma yanzu Alhamdilillah ina ta ƙoƙarin gyara kuskure na na baya, a cigaba da yi mana addu'a".
Alhaji ya ji daɗin kalaman Salim ya din ga saka masa albarka, tare da alwashin duk yarinyar da yake so ya sanar masa, zai nema masa aurenta, tun da matar na tuba ba ta rasa miji.
Daga haka ya ƙara janyo shi a jikinsa, da cigaba da rarrashin sa da yi masa nasiha.
Murna ta saka sai da ya bawa Hajiya labari, Hajiya ta din ga murna ta ce "Aini auro ummi cikin familyn nan ya zame mini alkhairi mai tarin yawa, ba abun da zan cewa Allah sai godiya, Allah ya ƙara musu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya ƙara haɗa kan zuriyarmu".
Yadda ummi ke ƙara girmama shi, yaya sama yaya ƙasa, mutuntawa ta kowane fanni, ga yadda ita ma ta ɗora da kyautatwa mahaifiyarsu, dama can kuma kan a aurota, ya san yadda take mutunta kowa a gidan, hakan ya sanya shi ma yake girmamata da jin nauyinta.
Dan wasu lokutan ta kan tsokane shi, da shi ne ɗan uwanta da mama ta faɗa, lokacin da suka je maiduguri, babu wasan ƙanin miji tsakaninsu sai girmamawa da mutunta juna.
A falon gidan dr. Kuwa, ga raihan, ga ummi, ga dr. Da Alhaji, sai Abdul da Salim.
Alhaji ya kalli raihan ya ce "To ayi ta ƙeƙe da ƙeƙe a gaban mahaifinta ka faɗi saki nawa ka yi mata? Tun da dama abu kan ya faru ake magance shi, da ka sanar akwai matsala ne sai a sasanta ku, kan a kawo nan amma tun da aka zo nan, sai ayi ta ta ƙare.
Raihan ya yi shiru bai ce komai ba.
"Ba magana nake yi maka ba?"
Kamar zai yi kuka ya ce "Alhaji wallahi ban saki matata ba, idan ma na saketa a na mayar da ita"
"Rufe mini baki, abun da na ce shi zaka yi tun da har ka yi ƙwarin sakin mace, tun da ka ke ko tafi gidanku ka ga na taɓa cewa wata a matana?"
Ganin Alhaji zai sake rufe raihan da faɗa ya sanya ta ce "Alhaji ka yi haƙuri, ba laifinsa bane ba laifina ne, rashin fahimta ne na zata sakina zai yi shi ne na tafi"
"A'a ban yadda ba, ƙoƙarin kare shi ki ke yi, babu yadda za ayi ki tafi ba tare da izininsa ba"
Dr. Ya ce "Ni bama haka ba, banda abunki ummi, da lamarin ya faru maimakon ki taho gida, sai ki yi wani wurin, ayi ta nemanki ba a san in da ki ke ba, haka ake yi? Ba ki taɓa ɓata mini rai kamar a wannan karon ba, ummi kuma saboda rashin neman albarka gidanmu na gado na iyaye da kakanni, ki ka sayar da shi haryanzu ina tantama idan ke ki ka aikata haka, kin bani kunya kuma fushi nake yi da ke"
Alhaji ya ce "A'a dr. Ban tari numfashinka ba, a fara jin ta bakinta"
"Haba Alhaji Tahir, ai komenene hanzarinta abun da ta aikata yayi muni, iyayenta ne fa a ciki har da babarmu, wane irin abu ne wannan? An ce mini ma ke ki ka yi sayi gidan, a ina ki ka samo kuɗin sayen gidan?"
Ummi ta fashe da kuka, sai kuma nadamar abun da ta yi ya ziyarci zuciyarta, ta ga lallai ta yanke mummunan hukunci cikin fushi.
Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, ka yi mana afuwa mun yi kuskure, ba laifin ummi bane ba, ni ne na sayi gidan, saboda ta dawo, dan Allah ku yi haƙuri ku yafe mana mu koma gida ba ta da lafiya"
Salim ya girgiza kai, ana ƙoƙarin gyara abu, shi ta a koma gida yake yi, kuma sai ƙumbiya-ƙumbiya suke yi, sun ƙi magana sai kare juna.
Ummi ta ƙarasa gaban dr., Tana kuka ta riƙe ƙafarsa ta ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, fushinka a gareni fitina ne, na yi laifi na yanke hukunci cikin fushi, na yi haka ne dan rage raɗaɗin da yake zuciyata, wallahi dr. Wanda ku ke so na a duniyar nan ba afi a ƙirga ku ba, shikenan ranar da babu ku haka zan tagayyara?.
Na zo gidan nan, Anty ta ce ba zan zauna ba, ba zan sake zaunar mata a gida ba, na je gagarawa iya ta kore ni, wai bani da mutunci babu gadon ubana a gidan, tayaya zan koma maiduguri daga yin aurena ace ya mutu, ai sai su tsane ni, na rasa yadda zan yi na kasa tunanin komai, zuciya ta ɗebe ni na yi abun da na aikata dan Allah ka yi haƙuri kawu"
Cikin takaici ya ce "Faridan ce ta kore ki daga gidan nan?x ummi ta jinjina kai alamar eh.
Raihan ya ce "Dan Allah kawu ka yi haƙuri, mun yi laifi ".
"Rufewa mutane baki, duk da baka saketa ba ya za ayi haka ta faru, kuma kema ummi waye ya gaya miki dr. ne kawai babanki, ni meyasa baki zo wurina ba? Ina da masaukin da zan ajiyeki ko da ba kwa tare da raihan, tun da ba shi da kirki bai san halacci ba".
Salim ya yi gyaran murya ya ce "Raihan ka yi haƙuri da abun da zan faɗa, Alhaji da raihan da ummi, duk ƙannena ne, kuma stll ina da ƴan uwa mata, da ba zan so su tozarta a gidan aure ba. Ummi da raihan suna zaune lafiya da junansu, mami ce ta saka ya saki ummi" gaba ɗaya suka kalli Salim. Bai damu ba ya cigaba da cewa "Na je gidan Raihan maigafi ya ce mini kwananta biyu ba ta gidan, kawai na ji jikina bai bani ba, mussaman tun da na ga maryam ta zo gida, da kuma saɓanin da suka samu.
Na zo nan gidan, na yi sa'a na haɗu da noor, ita ta gaya mini raihan ya saki ummi, kuma mami ce ta saka shi, nan gidan kuma matar gidan ta ce ba zata zauna ba.
Na koma gida na ritsa Nihal ta sake tabattar mini da hakan. Na je garinsu can gagarawa, na haɗu da ummi kan ta bar gidan, ta gaya