kashe mini ɗa suna bibiyata saboda ƴar su na hannuna, ba dole mariya ta haukace ba, ai kaɗan ta gani, hauka bata ma fara shi ba, tun shekarun baya da na karɓi ƴar ba ta yi haukan ba sai yanzu, Allah ya ƙara tuburata, yadda ta rabani da ɗa na babu ita babu sukunin duniya!!".
Bright pens fans group, da sauran masoya ummin Iya, ina ganin sharhinku, ina godiya sosai da sosai 🙏🙏🙏
Ayshercool
08081012143
*CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
P9
Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba.
Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa "Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala'i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna".
Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan.
Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi.
Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka.
Ummi ba ta samu fitowa daga ɗakin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita.
Ta yo alwala ta dawo ɗakin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi.
Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince.
Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya ɗan sirka, kuma su kumbura.
Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta.
Ba tsammani ta ga magaji a kanta.
"Ummi" ya kira sunanta a hankali.
Ta ɗaga kai tana kallonsa. "Kukan me ki ke yi?"
"Yaya magaji"
"Na'am ummi".
"Wai mamana ta haukace?" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta.
"Subhanallah waye ya gaya miki haka?"
"Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuɗin"
Hashim ya ce "Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce"
"Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa"
"Ba haka bane ba"
"To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?".
"Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya"
"Dan Allah yaya magaji ka kai ni wurinta, ina son in ganta dan Allah" tayi maganar tana haɗe hannayenta alamar magiya, tana kuka.
Cikin matsanancin tausayinta ya ce "Ummi Maiduguri ba nan ba ce akwai nisa, kuma ban san a ina mahaifiyarki take a Maiduguri ba, lokacin da aka aureta muna yara, kuma kin ga ba taɓa zuwa muka yi ba. Amma ki yi haƙuri ki daina kuka, zan bincika miki in sha Allah"
"Gidan uwarka zaka bincika mata, munafukin Allah ta'ala, to kar ka fasa, wallahi magaji idan ba ka kiyaye ni ba, sai na hau kujerar tsiya na ci ubanka la'ada waje a kanta, kar ka fasa kai ta inda uwarta take, zaka ga cin mutuncin da zan yi maka, dai-dai nake da kai.
Kema tsohuwar munafuka, halin uwarki haka halinki yake, duk wannan ƙoƙarin da nake yi a kanki ba kya gani, da ki ke hannunmu mutuwa ki ka yi? Kowa yazo sai ki ɓare baki, ke a kai ki wurinta, tun da namanki nake gutsura in ci, to ki cigaba kar ki fasa, amma ki sani nayi alwashin yadda mariya ta rabani da ɗa na, ke da ita har abada, sai ta ɗanɗani abun da ta ƙunsa mini, wannan kuɗin na meye?" Tayi maganar tana nuna kuɗin da ummi ta watsar a wurin.
Hashim ya ce "Yayan babarta ne ya bata"
"Tattaro mini su ki miƙo mini" ummi ta tarkata kuɗin ta miƙa mata.
Ta karɓe ta kalli Hashim ta ce "Zaka tashi ka fita ko sai na ɓata maka rai, kuma daga yau na yi maka tsakani da ita, tun da kai ne ka ke zigata, shashashai kawai"
Hashim ya tashi zuciyarsa na yi masa zafi, muddin ya buɗe bakinsa, zai iya ɗurawa Iya ashar, dan haka yayi shiru ya bar ɗakin.
"Tashi ki fice ki auni dawa ki surfa mini, tun da baki je makarantar allon ba"
Haka Ummi ta ja jiki ta fito, ta fara ƙoƙarin aikin da Iya ta saka ta, ƙasan zuciyarta tana fatan, ina ma Maiduguri babu nisa da guduwa za ta yi, ta tafi wurin mamanta.
Kayan da yaya ɗanlami ya kawowa Ummi kuwa, Iya ta tsince wanda zata tsince ta ce a fita da sauran, ba ta ƙaunar duk wani abu da ya shafi Mariya.
Duk salla sai ummi ta yi addu'ar Allah ya jiƙan babanta, ya bawa mamanta lafiya, ya sa ta dawo ta ɗauke ta.
Tun wannan tafiya da yaya ɗanlami yayi, wani daga danginsu, bai sake waiwayo in da Ummi take ba, suka mayar da hankalinsu a kan lafiyar ƴar uwar su. Dan abun na mariya gaba ya din ga yi, babu sauƙi ko sassauci, yanzu tana zaune lafiya idan aka jima, sai ta hau kuka tana burgima tare da surutai, irin na masu taɓin hankali.
Ummi kuma ta cigaba da karɓar gashi a gidansu, tsangwama da kyara a cikin yara a makaranta ko kuma a gida.
Iya ta sanya ido sosai a kan magaji, ɗan taimakon da yake yi wa ummi, ta tasaya tsyin daka ta hana shi.
BAYAN SHEKARU BIYU!.
Sauri-sauri ta kammala tulin wanke-wanken da ke tsakar gidan, ta warewa kowane sashi kwanukansu ta kai musu.
Duk in da ta faki ido ta tsaya, sai ta yi soshe-soshe, dan itakaɗai ta san me take ji.
Guntun omon da ya ragu, da shi ta wanke kayan makarantar bokonta, duk hantsar wandon ta fatattake, sun koɗe sun jeme, ƙafar wandon duk ta ɗage ta tattare, gwiwar duk a farfashe.
Kasancewar lokacin rani ne, rijiyoyi duk sun ƙafe, ta ɗau bokiti ta samo ruwan wanka, ta ɗauki ledar omon da babu komai a ciki, ta faɗa banɗaki wanka, da sosonta na buhu.
Ta daɗe a tsaye tana fargabar ta ina zata fara? Tun safe a makarantar boko take jin fitsari, ta riƙe shi bata yi ba, saboda azabar da take sha.
A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaɗe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take ɗaure kan da shi, ta ɗaure yadda ba zai jiƙe ba.
Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-robar jiki ta zaro, har da in da aka yi ɗinkin zare da allura a jikin phant ɗin, haka ta rataye shi a jikin ƙofar banɗaki, sai tsami yake mara daɗi.
Ta koma gefe ɗaya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu.
Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raɗaɗi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har ƙafafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ƙulle kan fitsarin ya fita.
Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga.
A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ƙarni mai haɗe da wari ya daki hancinta, ta ɗebo ruwan nan da sanyinsa da komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ƙarni mara daɗi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ƙaiƙayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ƙurajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daɗin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ƙarfin ta, saboda azabar ƙaiƙayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini.
Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banɗakin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaɗai ce take fama da wannan masifar da bala'in, to idan ma haka ne wa zata tambaya?
Da ƙyar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ƙarshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta mayar shi jikinta a jiƙen, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana ɗan buɗe ƙafarta, saboda raɗaɗin da wurin yake yi mata.
Man kaɗanyarta da na'ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform ɗin ta, ƙungun wandon saboda rashin roba, da leda take kama wani sashin ta ɗaure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta ɗaure shi da shi, ta saka.
Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala'in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu.
Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi yaƙi karatun boko yaƙi na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaɗa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba.
Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris ɗin nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haɗu su yi masa aure.
Aka kama masa hayar wani gida mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, ginin ƙasa ne dai, amma an yi floor, da plastar ƙasa an shafa farar ƙasa.
Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren ƴar mai suna Hindu.
Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka.
Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara.
Ana ta shirye shiryen biki, gida ya ɗau harama, ƴan uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, ɗan wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, ɗan wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni.
Yau kusan tun bayan azahar, yanayi ya nuna akwai matsala, duba da yadda Iya ke ta shiga tana fita ita da mahaifin su magaji, kasancewar ba abun da ya shafi ummi bane, ya sanya ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta.
Shi kansa yanayin Idirs ya nuna hankalinsa a matuƙar tashe yake, alamu suka tabattar da akwai matsala.
Ba a tsaya da shirye-shiryen biki ba, dan magana ake ta bai fi saura kwana huɗu a shiga hidimar biki ba.
Da yamma hashim ya shigo, ya tarar ummi na cikin mutane ana ta aiki, yayi mata nuni da ta zo.
Ta wanke hannunta ta bi shi, ya kalleta ya ce "Ke ina naki shirin bukin, ki ke ta fama da aiki haka, ko gajiya ba kya yi?"
Murmushi ta yi masa, sai da fararen haƙoranta suka haska fuskarta, fiƙarta da ta karye tana nan a yadda take, sai ƴar siriryar wushiryarta ta ce "To yaya magaji wani shiri zan yi? Ina da atamfata sabuwa da takalmin da zan saka"
"Ke ba zaki yi ɗan lallen da ake yi na zamani ba?"
Ta kalli hannunta, ta ɗan rausayar da kai ta ce "Bana so, ba zai yi mini kyau ba"
Ya kamo hannunta ya ce "Jan nan da ake yi tafin hannunki fari ne masha Allah, ko kitson ma ba ayi miki ba, kin cukurkuɗe gashi kin ɗaure"
Yayi maganar yana kallon yadda ɗankwalin kanta yake cike fam, ko ba a gaya maka ba, ka san wannan uban gashin nata ta ɗaure.
"Ai ka san ni ba a iya yi mini kitso, duk sanda na cewa yayi mini kitso, sai ya ce wai bs zai iya ba kaina ba zai yi ba, lalle kuma ai sai an biya ɗari biyu huwaila take yi hannu da ƙafa" tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa da Iya take cewa sangarta.
Ya ce "To shikenan, da safe zan baki kuɗin lallen, kitson kuma sai na yi miki"
Tayi dariya ta ce "To mata ne kawai suke yi wa mata kitso ban da maza"
Ya ce "Shikenan, je ki sai goben in Allah ya kaimu"
Cikin murna ta tafi ta cigaba da aikin, tana matuƙar son lalle, amma rabon da ayi mata, tun kan na'ima tayi aure, da take yi musu, yanzu yaran na'ima biyu a gidan miji.
Da magariba Saminu baban su Idris ya shigo hankali a tashe ya ja hannun Iya suka fita, wata duhuwa ya ja ta ya ce "Iya muna cikin tashin hankali da masifa, Idris ya zubar mana da mutunci"
Cikin kaɗuwa ta ce "Menene? Meyafaru?"
"Ban da masifa da bala'i, saura ƴan kwanaki a ɗaura maka aure, a ganka kana watsewa da wata, saboda rashin mutunci"
Iya ta ce "To ba mun gama wannan maganar ba? Har wurin maude mai babban carbi na je, ya yi mini aiki ya ce maganar an bar ta har abada, ba zata fasu ba, ko ta fasun ne?"
"To yanzun nan ƙanin baban yarinyar da zai aura ɗin, ya dawo da kuɗin auren, sun ce aje a karɓi kayan auren gobe da safe, ba za su bawa mutumin banza ƴa ba" yayi maganar yana nuna mata kuɗin.
Iya ta dafe ƙirji ta ce "Mun shiga uku, amma mutanen nan basu da mutunci, basu san tsautsayi ba?"
"Koma menene ai shi ya janyo wa kansa, da bai yi ba wa zai ce yayi, ni wannan mutanen da muka tara ne, ban san ya zamu yi da su ba"
Iya ta ce "Ni kuma tashin hankalina, garin Allah ya waye a dawo da kayan nan, kowa ya ji abun da ya faru, da sassafe ka je da kanka ka karɓo kayan, ka kai mini gidan kuluwa".
"Ni kuma Iya? Ni zan je ɗaukko kayan?"
"To kar ka je tsaya asirinmu ya tonu, sai ka ji daɗi, santolo kawai".
"To Shikenan zan je in sha Allah "
"Kai ka ga idan da hali, ka tafi yanzu cikin daren nan, ka tafi da babur ba wanda ya ji balle ya gani"
"To bari sahu ya ƙara ɗaukewa, amma Iya yaya zamu yi da wannan mutanen, ta yaya zamu ce musu an fasa auren nan?"
Iya ta ce "Nima shi nake tunani, dama ga akuyarsa tayi kuka a dangi, dan ma ana tsoro na ne, ya sanya ba a magana, amma jeka na san abun yi "
"Meye abun yin to?"
"Ka tafi na ce, idan ka dawo sai ka ji" ya jinjina mata kai ya tafi.
Ɗakin samarin ta shiga, neman Idris, amma ba ta tarar da shi ba, dan haka ta juya ta tafi.
A daren saminu yayi yadda Iya ta ce, ya je ya karɓo kayan a daren.
Sosai Saminu, ya din ga yi wa idiris faɗa, a kan tashin hankalin da ya sanya su a ciki.
Washegari kamar yadda Hashim ya yi wa ummi alƙawari, ya bata kuɗi ta je aka yi mata lalle.
A ƙofar gida ta gan shi ya karɓo kayan guga, tun daga nesa take ɗaga masa hannu ta ce "Yaya ka ga lalle na?"
Yayi murmushi ya ce "Inyee an sha kyau, lalle yayi kyau, ki yi sauri ki shiga gida, Iya ta fara faɗa ana nemanki"
Cikin faɗuwar gaba ummi, ta ce "Bari na yi sauri" ta yi cikin gida da gudu.
Cikin damuwa Saminu ya kalli Iya ya ce "Iya kina ganin babu matsala, ba fa son yarinyar nan yake yi ba, kuma shekarar ta goma sha uku ne kawai"
"To yaya ka ke son mu yi? Asirinmu da nasa ya tonu, idan ba haka ba kawo wata mafitar"
Ya girgiza kai ya ce "Ba ni da wata mafitar".
"To na yanke hukunci, ya auri ummi dan mutuncinmu ba zai zube ba, a sakamu a bakin duniya da wannan iskancin da yayi ba kamar ɗan taure"
Ayshercool
08081012143.
*CUTARWA*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
*BRIGHT PENS (FREE BATCH)*
Mafaka gidan ƙamshi, na da kyakywan albishir ga amare uwar gida, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine