x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 57 - CUTARWA

  • 168001 words
  • 171000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 512

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ga yadda ki ke yi mini kyau ba Salma, komai naki son shi nake, wallahi duk macen da na gani, sai in ga ba ta kai ki ba. Ina kaucewa auren Safiyya ne saboda a yanzu dai na ƙara aure ba zan iya adalci ba son da nake yi miki daban ne, a ƙasan zuciyata nake jin ki, bana son wani abu na rashin daɗi ya raɓe ki, ban san ya zan misalta miki ba ki gane ummi, kawai ni dai ki yadd ki saka a zuciyarki ina sonki, kuma wallahi ban taɓa ganin muninki ba ko sau ɗaya. Kawai ji nake duk matar da zan aura ba zan samu biyayya da kulawar da nake samu a wurinki ba, mutane kawai suna ganinmu ne, amma ba za su gane tarin baiwa da Allah ya yi miki kala-kala ba, su muninki suke gani, ni kuma abubuwan da nake gani game da ke ba zasu lissafu ba. Ina sonki kariun nisa'i"

Sanyin iskar wurin, da daɗin kalaman raihan, ya sanya wani irin shauƙi ya kama ummi, tare da jin ta a sama, kalaman na raihan suka sanya ta ji kamar a duniya babu wadda ta fita sa'ar miji. Abu kamar a mafarki ita da ake cewa ba zata auru ba, sai dai a taimaka a aureta saboda muninta, amma yau gashi Allah ya gwangwaje ta da miji na kere wa sa'a, kalaman na raihan ko ƙarya yake yi mata sun yi mata daɗi.

Ta rungume shi sosai ta ce "Allah ya barmu tare har aljanna Zaujul janna, kana cikin mutane masu muhimmancin da suka haska fitila a rayuwata mai cike da ƙalubale kala-kala, dan Allah kar ka daina sona, ko zaka yi aure a gaba ko ka so wata, dan Allah kar ka daina so na, ko da ka daina sona ka ɓoye mini dan Allah, kulawarka tayi tasiri a rayuwata idan na rasa soyayyarka da kulawarka komai nawa zai koma farko, kai kaɗai ne hope ɗina yanzu, an ce wataran ana gajiya da juna dan Allah kar ka gaji da ni" ta ƙarasa maganar kamar mai magiya.

Ya saka hannayensa biyu yana shafa bayanta, yana jin yadda take kuka.

"Soyayyar da aka gina da tubalin toka ita ke gushewa, tamu kuma da tubalin dutse muka gina ta, ni da ke har aljanna babyna" ya ƙarasa maganar yana ɗago fuskarta yana share mata hawaye.

Tausayin ummi ya cigaba da mamaye masa zuciya, tare da jin zai jure kowane ƙalubale ummi ta samu farinciki.

Kwanakin su ummi takwas a ƙasar, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci abinci tare da su ummi, ta nemi iznin ummi a kan tana son ɗora videonsu da suka yi ita da ummi, a YouTube, babu tunanin komai ummi ta ce mata to, saboda yadda ta san da shigarta ta mutunci a jikinta a ka yi videon.

Sai dai kwana ɗaya take nunawa ummi adadin views ɗin da videon ya samu, ya tafi viral da yadda mutanen ƙasar har ma da wasu suke sharhi a kan ummi.

Communication da mutanen yana bawa ummi wahala, dan su ba su iya turanci ba, ita kuma ba ta jin yarensu.

Amma duk da haka mutane ne masu tambaya, wasu lokutan har live videos suke yi da ummi, suna yi mata tambayoyi a kan mutanen Afrika, a gaya mata tambayar da turanci, ta basu amsa da turanci a fassara musu.

Raihan sai dai ya kalle su yayi dariya, ya san suna takura ummi, dan ba son mutane take yi ba, gashi kuma kamar tsoronsu ma take ji.

Sai dai ya ƙyalesu ne, saboda wataƙila a dalilin haka ummi ta samu wani cigaba a rayuwarta, da zai tabattarwa da duniya musamman masu nuna cewa ita mummuna ce, ba za ta yi acheiving wasu abubuwa a rayuwa ba saboda kalarta.

Har tambayarta suke yi a kan ƙabilar hausawa, da Nigeria baki ɗaya, duk da akwai masu tambaya cike da izgili ga ƙasar sai dai cikin hikima da dabara ta aiki ummi take basu amsa.

Sai da ummi ta fara damuwa da yadda adadin masu zuwa ganinta da hotuna da ita ke ƙara yawa kamar wata halitta ta daban, ga kuma kyaututtuka da ake ba ta.

A daddafe suka yi wata ɗaya, fatarta ta ƙara kyau, duk da daga ita har raihan abinci ba kowane iri suke iya sakin jiki su ci ba.

Ummi ta tara kyaututtuka sosai, ranar da zasu tafi ƙawarta da suke video ta ba ta kyaututtuka, ɗan zaman da suka yi sun saba da ita, suka yi ta tambayarsu yaushe za su dawo, raihan ya ce musu sai wani lokacin.

A jirgi ya din ga yi wa ummi mitar daga zuwa ƙasar mutane ta zama cele, shi fa haushi yake ji yadda ake sakata a social media.

Cikin damuwa ta ce "Meyasa baka gaya mini ba ka so ba? Ka bari muke yi, ni bana son su ga kamar na yi musu wulaƙanci ne"

Yayi murmushi ya ce "Sweetheart, komai yana da sila, tsakani da Allah zuciyata kamar ta fashe, ana talla da matata, amma sai na tuna ke ƴar jarida ce tun ainihinki ma, kuma ban san alkhairin da zaki iya samu a sanadin hakan ba, ina fatan ko iya haka a ranki zaki ji cewa ke ta mussman ce, kalli dubban mutanen da ke bibiyar live ɗin da ku ke yi, ba kuma wai dan kina wani abu na musamman ba, kalarki da irin halittarki da mutanenmu suke kushewa, su ita ta ja hankalinsu"

Tayi shiru ba ta ce komai ba, ta cigaba da wasa da yatsun raihan da ke hannunta.

Ko da suka dawo ya hanata gaya wa kowa sun dawo, ya ce sai sun gama hutawa. Ita kuwa ba ta zauna hutun ba, saboda ganin yadda gidan yayi mata ƙura da yawa.

"Dan Allah ki zauna ki huta, aikin nan yayi miki yawa, ki yi da kaɗan-kaɗan, an ce a samo miki ƴar aiki kin ce ba kya so".

Ta ce "Bana son in ga wurin da datti ne, dan Allah ka yi haƙuri" haka ya ƙyaleta ta yi ta share-sharenta.

Sai da suka kwana biyu da dawowa, ya je gida, ya gaida su mami. Alhaji ya din ga mitar meyasa bai zo da ummi ba.

Raihan ya ce "Ta gaji ne sosai, ba ta saba doguwar tafiya ba, kamar ma dai ba ta jin daɗi shiyasa na baro ta a gida".

"Allah sarki, with time za ta saba ne in sha Allah" ya samu kyakkyawar karɓa daga Hajiya da Alhaji banda mami, da ke masa abu kamar agola ba ɗanta ba.

Ganin shirun yayi yawa ya sanya ya miƙe zai tafi, da mamaki mami take kallonsa kamar yanayin ko in kular da take yi masa baya damunsa balle ya saduda.

"Ya maganar mu?"

Ya ɗan yi turus ya ce "Wace maganar?"

Ta ce "Tambayata ma ka ke yi?"

"Mami ki dubi girman Allah ki yi haƙuri, wallahi ni bana son yarinyar nan, ummi ba ta yi mini laifin komai ba, watanmu shida fa da aure har kuma sai na ƙara aure, da ƙanan shekaruna in tara mata"

"Raihan ni ka ke gayawa ba ka son safiyya? Kuma da ka ji maganata tun farko ai da haka ba ta faru ba, kuma wallahi ka cigaba da bujire mini sai na kashe auren nan a kwanakin nan dan bana ƙaunar yarinyar nan".

"Mami, dan Allah ki taimaki rayuwata, ki ka rabani da ummi, ba zaki iya sama mini matar da zata maye mini gurbinta ba!.

Ayshercool
08081012143

                      *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

40

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

41

Galala mami ta buɗe baki tana kallon raihan, ba ta taɓa zaton wannan kalaman daga bakinsa ba ko a mafarki, ta rasa wace amsar ma yakamata ta bashi, ganin ba ta da abun cewa ya sanya jiki a sanyaye ya fice, zuciyarsa na wani irin zafi.

Har ya nufi motarsa ya ji an riƙe hannunsa, ya waiwaya ya ga Salim.

Ya gyara nutsuwarsa cikin girmamawa ya ce "Yaya ina wuni?"

"Meyafaru ne?"

Raihan ya kalleshi ya ce "A ina?"

"Dambe ka yi ne? Ba ka ga yadda ka ke gumi ba, idonka ma yayi ja?"

Ya girgiza kai ya ce "Bakomai, dama mun dawo ne na zo gida mu gaisa ban zaci ma kana nan ba"

Salim ya kama hannun raihan ya wuce da shi ɗakinsa, Sagir na kwance a falo yana kallon tv suka shigo, sallamar su kawai ya amsa ya cigaba da abun da yake yi.

Ya zaunar da raihan a kan kujera, shima ya mayar da hankali a kan kallon ba tare da ya cewa raihan ɗin komai ba.

Sun shafe a ƙalla mintuna talatin a haka, sannan Salim ya numfasa ya kalli raihan ya ce "Are you ok now?"

Ya jinjina masa kai ya ce "Yes, na gode sosai"

Salim ya sake tattara nutsuwar sa a kan raihan ya ce "Me yake faruwa? Kar ka ɓoye mini" raihan ya yi shiru yana yi wa Salim kallon mamaki, dan sam ba mai shiga abun da bai shafe shi ba ne ba.

Kamar ya san me raihan yake tunani a kai ya ce "Na san zaka yi mamakin tambayarka da nake yi, na samu labarin matsin lambar da ake yi maka a kan ƙara aure a wurin Hajiya, kuma daga dawowarka ba zai yiwu ace har  wani abun ɓacin rai ya faru da za ka shiga cikin tashin hankali ba, in dai ba a kan maganar ba ne ba.
Ka san meyasa na titsuyeka nake tambayar ka?"

Raihan ya girgiza masa kai alamar a'a.

"Alƙawarin da muka ɗaukko wa mahaifiyarta da ni da kai, Allah ya sani ina tausayin baiwar Allah nan sosai, kuma kai ka bani labarin irin wahalar da take sha a rayuwa, idan har ka rabu da ita, ka yi wa mahaifiyarka biyayya haka ake son ɗa na gari amma ka sa a ranka ko da ranka ko bayan ranka sai wani ya auri ƴar ka ya saketa!.
Haka zalika idan ka auri wannan yarinyar ka zalunci ummi, ko ita wadda zaka aura ɗin, shi ma ka shirya kare kanka a gaban Allah"

Gaba ɗaya raihan ya sake rikicewa ya ce "Wallahi yaya na rasa yadda zan yi, ina son ummi muna zaune lafiya tana kyautata mini, me zai saka na saketa ko ace sai na yi wani auren? Ni ba na son safiyya a matsayin matar aure, kuma bana son saɓa wa mami"

Salim ya kaɗa ƙafa ya ce "Am sorry to say, iyayenmu mata wasu lokutan na da gajeren tunani, iyayenmu da suke aure fa, ba daga sama suka faɗo ba, su ma ƴaƴan wasu ne. Anyway Allah ya kyauta, na kira ka ne dama dan na yi maka tuni a kan amanar da ka ɗaukko, kayi ƙoƙarin gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka, ba tare da wani ya cutu ba".

Raihan ya jinjina kai ya ce "Na gode sosai yaya da tunatarwa, zan yi iya ƙoƙarina in sha Allah" yayi musu sallama ya fice.

Sagir ya bi bayansa da kallo, yana wani tunani a ransa na kowa da irin jarrabawar sa, shi da yake mai biyayya babarsa ta saka shi a gaba, su da suke sai a hankali su suka saka tasu uwar a gaba, kuma ya san su ta su uwar ba za ta taɓa yi musu haka ba, amma tabbas da shi ne a matsayin raihan, ba wanda ya isa ya tursasa shi yin abun da ba ya so.

Mami kuwa hankalinta ya gama tashi, tare da tabattar wa da kanta, ummi da danginta sun haɗu sun mallake mata ɗa, dama ance irin su ba sa zaman aure haka sai sun yi asiri.

Cikin rashin dabara, ta kira yayarta da ke yi mata baƙi jagoranci, ta zayyane mata komai, aikuwa ta ƙara zigata a kan ko dai ta raba raihan da ummi, ko kuma maganar Hajiya ta zama gaskiya, ɗan so ya auri matar so!.

Raihan ya koma gida, yana ta saƙe-saƙe, amma tunda ya ci ya ƙoshi, suka shiga soyayyarsu da ummi sai ya manta, ta hau bashi labarin aikin da ta sha na gyara gidan jikinta sai ciwo yake.

Ya yamutsa fuska ya ce "Ki daina gaya mini kin wahalar mini da kanki, tun da dai ba kya jin magana".

Tayi murmushi ta ce "Zaujul janna, wata alfarma nake nema dan Allah"

Ya ce "Yau Allah ya yi kenan, tun kan mu tafi nake ganin alamar akwai magana a bakinki, kin ƙi faɗa ne kawai. Ina jinki"

Ta ɗan yi jimm tana jujjuya maganar sannan ta ce "Dan Allah idan ban takura maka ba, dan Allah so nake idan da ɗan space a taimaka a ɗauki yaya Abdul aiki dan Allah, amma idan babu shikenan bakomai"

Kawai ya zuba mata ido, dama wannan maganar take ta yi wa kwana-kwana.

Ya maze ya ce "Ki rubuta a rubuce ki kai mini office" hararsa tayi ta ce "zaka sake kenan ko?"

Yayi dariya ya ce "Ashe baki manta ba?"

"Ya za ayi na manta, waccan ranar sai da na yi kuka"

"Koma me na yi miki ai ke ki ka janyo, handsome guy kamar ni, a wanke hannu a taɓa ɗan kyakykyawa da ni, wai ki ka rufe ido ba zaki aureni ba, wai ni yaro ne ko?" Ta tura baki tana kawar da kanta gefe.

"Kuma yanzu ko kunya ba kya ji, kin kwanta a jikin yaro kina shagwaɓa, ko kuma yanzu na girma ne?"

"Wai kai abu ba ya wucewa?"

Yayi dariya ya ce "Ina zai wuce, memory ne mai girman gaske da ba zai shafe ba" yayi maganar yana kai bakinsa na ta, ta lumshe idonta ya ce "To buɗe idonki na fasa, ai ni yaro ne, ba ma a yaye ni ba, ki ke wani lumshe ido"

Ta buɗe idonta tana kallon sa, ba ta ce masa komai ba, tayi murmushi, dan ta fuskanci tsokana yake ji, ta shammace shi ta yi kissing ɗin sa.

"Eh lallai kin waye baby, ke da ko kallon mutane ba kya iya yi"

"Ba zan kula ka yanzu ba, zan rama ne" ya rungume ta ya ce "Ai ba zaki iya hukunta ni ba, duk laifin da zan yi, ki tura mini CV Abdul ta email ɗina, i will find a position that will suit him, ko akwai wani position da ki ke so a bashi ne?"

"A'a kowanne ka bashi yayi, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

"Never mind sweetheart, ko wa ki ka kawo ki ka ce na yi masa abu zan yi masa, wannan dolena ne kar ki ji komai, gobe in Allah ya kaimu zan cigaba da koya miki driving, na ga kina da saurin gane abu, motarki ta kusa zuwa in sha Allah, da ke da mami da yaya Salim"

Ummi ta ce "A'a ni a naka ka bani ɗaya, sai ka canza wata kar mami tayi maka faɗa" kamar bai ji ba, ya bar maganar suka shiga wata.

Bayan sallar asuba cikin bacci ya ji ummi na ƙwala masa kira a banɗaki, yana zuwa ya tarar da ita a tsaye jini yana bin ƙafafuwan ta.

A kiɗime ya ce "Lafiya kuwa?"

Cikin kuka ta ce "Kawai marata na ji tana ciwo, sai kuma jini yake ta zuba da yawa, ba haka na saba yin period ba"

Ya girgiza kai ya ce "Wannan ai ya fi ƙarfin period, asibiti zamu tafi"

Nan da nan ya taimaka mata ta kintsa jikinta suka tafi asibiti. Aka yi wa ummi gwaje-gwaje aka tabattar musu da cewa ɓari ne, kuma sai an yi mata wankin ciki dan da saura bai faɗi duka ba.

Hankalin raihan ya tashi sosai, dan daga shi har ita babu wanda ya san da cikin, sai kuma ya ji matsanancin ƙaunar cikin, ya aka yi be san da cikin ba?.

Yana nan tsaye yana jira aka fito da ummi daga wurin wankin cikin, fuskarta kawai ya kalla ya san abun babu sauƙi.

Aka kaita ɗakin da za ta huta, aka ɗebi jininta dan yin gwaje-gwaje aka saka mata ruwa.

Ya zauna a gaban gadon ya riƙe hannunta yana yi mata sannu. Can ya numfasa ya ce "Salma ya aka yi ba ki gaya mini ki na da ciki ba?"

Ta ɗaga ta kalleshi ta ce "Nima ban san da shi ba"

"Abu a jikinki ki ce ba ki san da shi ba? Ke fa ki na da zurfin ciki, abu har wata uku baki sani ba? Ba ki ga kin daina period ba?"

Ummi ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wasu lokutan ina yin irregular periods, kuma ni ban yi rashin lafiya ba, ban san da shi ba"

Raihan yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, Allah ya mayar mana da alkhairi. Wataƙila ma wannan aikin da ki ka din ga yi ne ya zube, kin ƙi yarda a samo mai tayaki aiki, gashi kin yi mana asarar baby" shiru ta yi masa taƙi kula shi.

"Ina magana ki ka yi mini banza?"

Kamar za ta fashe da kuka ta ce "To me zan ce maka? Kana kallon na sha wahala kuma kana yi mini faɗa, ka ga ƙarafunan da aka saka a jikina kan ayi wankin cikin? Gashi wai wataƙila a ƙara mini jini, amma kana yi mini faɗa" tayi maganar har da hawaye.

Ya zuba mata ido yana kallon fuskarta, sarai ya gano ta fake da haka ne dan tayi kukan zubewar cikin.

Yayi ƙasa da murya ya ce "Is ok na yi laifi ba zan sake ba, na daina yi miki faɗan, have some rest" yayi maganar yana shafa gashin kanta.

Raihan ne kawai a wurinta, ya din ga kaiwa yana komowa duk abun da aka buƙata shi yake kawowa, sai wurin la'asar ummi ta ɗan warware, dan jiri ta din ga yi da farko saboda jininta da ya yi ƙasa.

Yana cikin ba ta abinci Alhaji ya kira shi a waya, yana son ganinsa, ba ɓoye-ɓoye ya gaya wa Alhajin suna asibiti ummi tayi ɓari.

Cikin kulawa da tausayawa Alhaji ya jajanta wa raihan, tare da nanata masa ya rarrashi ummi, sannan su yi fatan Allah ya basu mai amfani, zai gaya wa mutanen gidan azo a duba ummi.

Ummi ta dafe kai tayi shiru cikin matsananciyar kunya, sai da ya gama wayar ya kalleta ya ce "Ya dai?"

"MD dan Allah kai ba ka jin kunya, ka cewa Alhaji ɓari na yi"

Cikin ko in kula ya ce "To
End Ads