x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 55 - CUTARWA

  • 162001 words
  • 165000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 544

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tsallake bai aure su ba, ke ya auro ki ya kai ki gidansa, ko da ya kasance mai kule-kule ke ɗin dai ke ya zaɓa, dan me zai kai ki gidansa ki din ga yi masa gidadanci, ba ko yaushe kunya take da muhalli a aure ba" ummi ta shagala tana kallo, malamar har da demonstration na yadda za a yi wa miji kissa.

Ji ta yi ana danna bell ɗin ƙofar falon, ta ajiye wayar ta tashi ta buɗe.

Ta faɗaɗa murmushinta, ganin wata babbar mace da wata.

Tayi musu maraba zuwa cikin falon, tana ta jera musu sannu da zuwa.

Matar ta kalleta ta ce "Kin gane ni ne?"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Na gane ki, maman bauchi ce, ai ya nuna mini a hoto"

Hajiya Aisha tayi murmushi ta ce "Lallai kin yi kyan kai, ina can ya aike ni bana ƙasar, ban samu zuwa bikinku ba, na je umara daga nan na tafi aiken raihan"

Ummi ta yi murmushi ta kawo musu ruwa, da lemo.

Ta ce "Daga baucin ku ka taho?"

Hajiya Aisha ta ce "Daga can muke, tun safe muka taho ai"

Ummi ta ce "Be gaya mini ba, ai da na ɗora muku girki tun kan ku ƙaraso"

"Be san zamu zo ba shi ma, amma yana gida ai ko?"

Ummi ta ce "A'a ya fita tun ɗazu"

Ta kawo musu kayan tea, ta shiga kitchen ta ɗora tukunya.

Siyama ta kalli Hajiya Aisha ta ce "Mummy, ga fa kairun nisa'i in ji raihan, ki ga rashin mutuncin da yake yi mini a kan matar nan, wai duk matan ƙarshen zamani ita suka rako"

Hajiya Aisha ta yi dariya ta ce "Raihan ne fa, haka nima yake ce mini duk ranar da na zo gidansa na ci girkin ummi, wai sai na koma bauci ba yatsu saboda daɗi, hannunta akwai maggi"

Suka yi ta dariya, nan da nan ummi ta din ga yi musu hidima, ta kawo wannan ta kawo wancan.

Duk rashin son sakewa da mutane irin na ummi, ta ɗan sake da hajiya Aisha, suna ta hirar duniya.

Hajiya Aisha ta kira raihan a waya tana faɗan ina ya tafi weekends, ta zo baya nan.

Ya ce mata yana gida, ta ce ita ba zata kwana a kano ba, ya dawo za ta tafi.

Dama duk a takure yake, kiransa kawai ta yi ta zaunar da shi, Safiyya na ta kaiwa tana komowa tayi kwalliya, sai dai ko kallo ba ta ishe shi ba, hankalinsa yana kan wayarsa yana kallon hotunan ummi.

Idan ya kalli safiyya sai ya ganta wani iri, shi dai a wurinsa ya fi ganin kyan ummi nesa ba kusa ba, ita baƙinta ke hana a ga kyawunta, kuma yanzu ta washe ta ƙara kyau.

Duk da yana complain da kunyarta ta yi yawa, amma yana jin daɗin wuninsa a gida tare da ita, ya ci abinci da ita, ya shaƙi daddaɗan ƙamashin turarukan ta, uwa uba lallausar fatarta da ba ya gajiya da taɓawa, jikinta tamkar jikin tarwaɗa, ko kuma wata fulawa.
Shi komai na ta burgeshi yake yi.

Raihan ya kalli mami ya ce  "Maman bauci tazo tana gidanmu tana jirana"

"Saura ka je ka gaya mata wani abu, ta zo ta cika mini kunne da masifa".

Mintuna arba'in sai ga raihan ya dawo.

Aikuwa hajiya Aisha ta din ga masifar weekend ya zauna a gida da matarsa, amma ya fita yawo, idan ya je wurin mamin shayar da shi take ko kuwa?.

Shi dai bai ce komai ba ya ce "Ayi haƙuri na daina, amma kar a juya mini baya a koma wurin ummi"

Ta ce "A'a ni fa na yi ƴa, ga iya girki ga mutunci, kalli yadda ka yi ƙiba fa, ummi ta iya kiwo, ya ma sunan da ka ke gaya mata"

Ba kunya raihan ya ce "Khairun nisa'i"

Ummi kuwa kamar ta nutse, ta tashi ta tafi kitchen tana wanke kwanuka.

Ya sameta a kitchen ya ce "Madam sannu da ƙoƙari, Mummy na ta yaba miki, ina godiya sosai da sosai"

Hararsa tayi ta ce "Baƙina ne ai ba naka ba"

Ya ce "To ai shikenan, zo ku yi sallama"

Ummi ta ce "Har tafiya za su yi?"

"Wallahi kuwa, ta ce ko gidanmu ba zata ba bauchi zasu koma, gashi ba su taho da direba ba, kar su yi dare".

Ta ce "To yi gaba zan taho"

"Saboda me?"

"To kawai sai kuma a ga mun jero tare?"

Danƙo hannunta yayi suka yi waje, turus ummi ta yi ganin iyayen akwatuna a falo.

Hajiya Aisha ta ce "To ga kayanku nan, ku duba abun da bai yi miki ba, sai a canzo, ko kuma ma yi waya kawai, tafiya zamu yi"

Ummi ta ce "Mummy ki bari ki kwana mana"

Hajiya Aisha ta ce "Taɓ mijina yana gari, wa zai kula mini da shi, sai mun yi waya"

Cikin sauri ummi ta tafi ɗaki, ta ɗebo turaren wuta, na gashi da na jiki, ta din ga haɗo kaya a leda, ta bawa Siyama ta ce musu ba yawa.

Hajiya Aisha ta yi musu nasiha, tare da fatan alkhairi suka tafi.

Nan raihan ya zauna a falon, yana bubbuɗe akwatunan, ummi kawai ta zuba masa ido tana kallon uban kayan da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin mallakar su ba.

"Ki saukko ki gani mana sweetheart" ta saukko ta zauna a kusa da shi tana kallon kayan.

Ganin tayi saroro kamar sokuwa ya sanya ya ce "Ko kayan ba su yi miki bane ba?"

Kawai ya ga hawaye na bin idonta, gaba ɗaya ya rikice ya ce "Menene kuma? Ko Mummy sun yi miki wani abun da ya ɓata miki rai ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To menene? Bana son kukanki ummi, gaya mini"

Ta ƙara matsawa kusa da shi, ta rungume shi tana kuka.

Ya saka hannunsa ya tallafo fuskarta, cikin kulawa ya ce "Gaya mini menene?"

"Na gode" tayi maganar wasu hawayen na zubo mata.

Raihan ya ce "Haƙƙinki ne fa ummi, meyasa zaki yi kuka?"

Ta sake kwantar da kanta a jikinsa, ta ce "You mean a lot to me, na tuna lokacin da na shekara biyu babu kayan kirki, yau ka gwangwaje ni da wannan uban kayan, ni wallahi ban san ma me zan ce ba, kamar kalmar godiya ta yi kaɗan, Allah ya suturta ka duniya da lahira, ya yalwata arzikinka, na gode MD"

Jikinsa yayi sanyi sosai, duk da bai san cikakken tarihin ummi ba, amma alamu sun nuna ta sha gwagwarmaya da rayuwa.

"To ki daina kukan haka, in sha Allah in dai ina raye, sutura sai dai ki ɗauka ki bawa wani, sutura ba zamu yi ta ɗinka ta muna sawa".

"Na gode MD, amma dan Allah kar ka takurawa kanka yi mini abun da ba ka da shi, ni dai na gode sosai"

"To ba zaki kirani da wani suna na soyayya ba, sai MD"

"MD my dear" ta faɗa tana murmushi.

"Wow ashe duk tsawon wannan lokacin, am your dear ban sani ba, barakallahu fik baby"

Ɗaɗɗaga mata kayan ya cigaba da yi, kaya sun haɗu masu tsada har da gwal.

Sai da ya zo kan akwatin ƙanan kaya, ya din ga ɗaɗɗagawa yana cewa ba ƙaramin kyau zaki yi a ciki ba.

Ummi ta ce "Ai kai a nan ka fi kauri, ni bari na je kitchen abincina kar ya kama".

Idan ummi ta kalli raihan ta kalli kayan nan, sai ta rasa me ma za ta ce masa, ya baje yana ta aiki a system gefen sa ga biro da takarda.

Dogon matashi cikakke, dai-dai gwargwado raihan kyakkyawa ne, kuma duk kyawawan mata babu wadda ya gani ya ce yana so, sai ita kuma yake ta wahala da ita.

"Ya dai madam?"

Ta tashi ta ce "Bakomai, zan je wancan falon na gyara shi kan magariba".

Ya ce "Yauwwa, ni kuwa na ce ko ƴar aiki za a samo miki ne? Ta din ga taya ki aikin nan, yayi miki yawa".

Ummi ta ce "Aikin gidan nan guda nawa yake, zan iya abuna"

"Faɗi gaskiya dai, ko abun ne ya motsa, dan kar a aure ni"

"To a aurekan mana, duk wadda za ta iya zama da ni ta shigo"

Ya kwashe da dariya ya ce "Eh lallai kin yi baki baby".

Ummi ta ɗauki hoton kayan, ta turawa su Yaya maryam, suka din ga murna tare da sanyawa raihan albarka.

Iya ƙoƙari ummi take yi, wurin rage kunyar raihan da take ji.
Dan haka a yau tayi iya yin ta tayi irin shigar da yake so.

Aikuwa daga kallon da ya din ga yi mata, ta gane ya ji daɗin hakan sosai da sosai.

Ya sha mamaki sosai da sosai, dan kuwa tayi masa kyau sosai da sosai, Allah ya taimaki ummi raihan ba shi da abokan da zai yi zaman majalisa da su.

Duk a kunyacen take, amma ta dake kar sokoncinta ya sanya shi fara kalle-kallen.

"Baby zaka kai ni gaida su mamin da su kawu".

Ya ce "Wow, shagwaɓar nan taki tana burgeni ummi"

Maganar Iya ta tuna, da take ce mata 'Tana shagwaɓa da fuska kamar kashi'

Ya amince da zuwanta gaida su mami, amma ya ce sai ranar juma'a da daddare. Washegari ranar asabar kuma sai ya kai ta gidansu.

Ummi ta yi ta murna, raihan ya ce "Ai in dai zaki din ga abun da nake so, zan zama mijin hajiya Salma.

Wata irin soyayya raihan yake nuna wa ummi, da take fatan ta ɗore har abada.

Ranar juma'a tun safe, ummi take aikin yin sinasir da miyar agushi, wanda za ta kai gidan su raihan.

Tun sallar magariba ta shirya take jiran raihan, ya dawo ya ƙare mata kallo ya ce "Gaskiya kin yi kyau da yawa, ba zan tafi da ke a haka ba, sai ƙamshi kuma ki ke yi, am jealous ki rage kyan nan"

"Daga ni sai kai fa zamu tafi a mota mu dawo, dan Allah ka shirya mu tafi"

Sai da ummi tayi da gaske, sannan ya shirya suka tafi.

Tambayarta ya din ga yi a kan wannan kulolin restaurant za ta buɗe ne?.

"Eh in dai zaka yi patronizing ɗina"

"To ɗan buɗe ki san mini abun da ki ka dafa ɗin"

"Aikuwa ba za ka ci ba"

"Suna tafe suna faɗansu irin na masoya".

Karɓar da mami tayi mata kawai jikinta yayi sanyi, ko kallo ummi ba ta isheta ba.

Safiyya kuwa tun da ta ga ummi jikinta yayi sanyi, ana ta ummi mummuna ce, amma ta ga ummi dirarriyar mace, muryarta kawai idan ta yi magana sai ka so ganin waye yake yin maganar, gashi komai na ta a nutse. Duk da dare ne amma duk wanda ya ga ummi ya santa a da, ya san ta canza sosai, fatar nan ta ƙara kwanciya tayi fresh sai ƙamshi take yi.

Ko gaisuwar ummi taƙi amsawa.

Raihan ya ce "Mami zuwa muka yi ta gaishe ki, ta yi muku bangajiya"

"Na ce maka ina nemanta ne, tun a farko ban gaya maka babu yawuna a maganar aurenka ba? Ka nema mata wata sirikar bani ba. Muguwa kawai, sumi-sumi da ke na zata ta Allah ce, ashe mutuniyar banza ce, kuma da ni ki ke zancen. Ɗa na ne dai wallahi sai kin bar shi, zan yi masa irin auren da nake so, kuma ina nan dawowa kanki"

Raihan ya tashi ya ce "Ummi mu je mu gaida su Alhaji mu tafi kar dare yayi"

Ta tashi kanta a ƙasa, ta ɗauki kwandon da suka zo da shi, ta ajiye wa mami na ta food flask ɗin.

Mami  ta ce "Kwashe tsiyarki, ba abun da zan yi da abincinki"

Raihan ya durƙusa ya ɗauka ya ce "Bari a ƙarawa mami da shi"

Ta buɗe baki tana kallon raihan.

Bayan fitarsu Nihal ta ce "Taɓ mami dama haka matar yayan take? Gaskiya babu lallai ya saurari safiyya, kin san halin sa ba komai yake burge shi ba, amma idan ya ce yana son abu ya dage, canza shi sai Allah. Kalli dirarriyar mace ga iyayi".

"Ke dalla rufe mini baki, tashi ki bar falon nan"

Can kuwa ummi jikinta yayi sanyi, amma karɓar da ta samu a wurin Alhaji da Hajiya, sai ya mantar da ita abun da mami ta yi mata.

Sai gashi sun shantake, har goma na dare suna gidan, sun sha nasiha da sanya albarka daga bakin Hajiya da kuma Alhaji.

Alhaji da kansa ya kira Salim da Sagir a waya cewa yana nemansu, bayan sun zo, ya sake gabatar musu da ummi.

Tun ummi na nan suka fara cin abincin su, suna santi ana koɗa girkin nata, wanda hakan ya yi wa ummi daɗi sosai.

Goma da rabi, sannan suka tafi gida, raihan bai yi mata maganar abun da mami ta yi ba, ita ma ba ta yi masa ba, sai dai ta damu da ganin safiyya ya ɗaga wa ummi hankali, ganinta yarinya kuma kyakykyawa.

Haka ta kwana tana wasi-wasi daban-daban, ta ƙuduri aniyar sake zage damtse a kan raihan, yadda ko zai yi wani auren, ba za ta rasa soyayyar sa ba.

Ta nemi iznin sa, tana son ɗaukar wani abu daga lefenta tayi kyauta da shi, ya ce nata ne, babu buƙatar ta tambaye shi.

Washegari  ta yi girke-girken ta, ya kaita gidan dr.

Suna hanya take ce masa "MD, yakamata ka koya mini mota, sai in din ga kai ka wurin aiki, ina ɗaukko ka"

Yayi dariya ya ce "Matata direbata"

"Eh mana, kaiman ka din ga hutawa"

"Kawai ki ce a saya miki mota"

Ta waro ido ta ce "Wace ni? Ba haka nake nufi ba da wasa nake yi maka".

A ƙofar gidan yayi parking, ya ciro 10k ya miƙa mata ya ce "Wannan ki bawa dr. Ki ce in ji ki amma, ni idan na zo ɗaukar ki, zamu gaisa da shi"

Kissing ɗin raihan ta yi a kumatunsa ta riƙe hannunsa ta ce "Thank you baby.. ya kalli idonta ta ƙarasa babyna.

Dariya yayi yayi kissing ɗin ta a baya, yana maimaita mata i love you.

Farida kasa ɓoye mamakinta tayi, ta bi ummi da ido, ummi kuwa ta shagala suna murnar ganin juna ita da noor.

Kallo ɗaya zaka yi wa ummi, ka san hankalinta ya kwanta, leshin jikin ummi kawai take kallo, da yake wasu kayan a ɗinke a ka kawo mata, ta sha kwalliya duk da mayafinta a ka ta ɗora shi.

Dr. Ya fito yana faɗin "Oyoyo mamana, amarya ba kya laifi"

Ummi ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa.

Ya ce "Mamana, kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa? Lallai aure ya karɓe ki, kin ganki kuwa? kunya ta rufe ummi.

Da kausar ba tayi niyyar fitowa ba, amma dai ta fito ganewa idonta ikon Allah, ummi an sha to match, har da wani agogo mai ɗan karen kyau.

Noor ta bubbuɗe kwanukan da ummi ta zo da shi, miya ta sha kaji zuƙu-zuƙu ga snacks, abun da inteesar ba ta taɓa yi ba.

Sun yi hira sosai da dr. Har take gaya masa cewar raihan ya yi mata lefe.

Dr. Ya din ga sanya masa albarka.

Da azahar da zai fita, ummi ta kawo kuɗin nan ta bashi dubu bakwai, ukun kuma ta ƙara biyu ta bawa farida biyar.

Sai dai farida ba ta so yadda ta ga ummi ba, ta kasa ɓoye hassadarta baƙin ciki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta, kausar ma sai wani zumɓura baki take yi tana hura hanci.

Ummi ta ce wa noor "Yaushe zaki zo ki ga kayan da MD ya saya mini, ki zo ki ɗauki abun da ki ke so"

Noor ta ce "rana ita yau, zan diro ko ta katanga ne, zan zo ki haɗa mini akwatu guda" ummi kamar wurin noor ta zo, tare suke ta hirarsu.

Ummi ta miƙe ta hau gyare-gyaren gidan, duk gidan yayi ƙazanta saboda ba ta nan.

Tana nan Abdul ya dawo, shi ma ya yi farinciki sosai da sosai da ganin ummi, sabuwar shadda ta bashi yadi goma, ta ce ya ɗinka musu shi da dr.

Ana sallar magariba raihan ya zo tafiya da ummi, suka gaisa da dr. Yayi wa dr. Alheri, ya sha sanya albarka sosai daga wurin dr.

Ya ɗauki matarsa suka tafi.

***
Watannin ummi huɗu a gidan raihan, mami ta matsa lamba a kan lallai sai ya auri safiyya.
Sai dai juyin duniya, fafur raihan ya nuna mata ba zai iya auren Safiyya ba.

Ta je ta samu Alhaji da maganar, ya ce ta bari, za su yi maganar da Raihan.

Raihan ya amsa kiran da Alhaji yake yi masa, ba tare da sanin dalilin sa ba.

Bayan Alhaji ya sanar masa da buƙatar mami, sai ya ga ya ɓata fuska.

"Babban mutum ba ka ce komai ba"

"Alhaji me zan ce? Kwata-kwata yaushe na yi auren da zan ƙara wani? Ni wallahi ummi ta isheni, mami ba za ta iya samo mini mace mai qualities ɗin ummi ba, ni dai dan Allah ka bata haƙuri, ka san plan ɗina Alhaji wallahi ina son ummi, yayi wuri in yi mata kishiya, kuma wallahi idan na auri wata ba zan iya adalci ba, na fi son ummi"

Alhaji ya yi murmushi irin nasu na dattawa ya ce "Shikenan, jeka ba sai ka je wurinta ba, tafi gida abun ka".

Sai da daddare da mami ta zo wurin Alhaji, tayi masa maganar ya ake ciki, yaushe za a kai kuɗin auren Safiyya"

Alhaji ya ce "Bilkisu, ina son ki fuskanci wani abu, ki ƙyale yaron nan da matarsa hankalinki da na su su kwanta, kar ki saka ƴar mutane a wahala, idan ba ki bi a hankali ba yaron nan zai iya gaya miki abun da zaki gaza haɗa ido da shi, ya ce ba zaki iya samo masa mace irin matarsa ba, ko ya auri wata ba zai yi musu adalci ba, idan kin gane shikenan idan kuma sai ranar da yayi miki hansfree shikenan.
Na manta ban gaya miki ba, this coming Friday, za su tafi China tare da matarsa maganar auren nan ki bar ta for now.

Ayshercool
08081012143

*Alhamdilillah, sai kuma Allah ya kaimu salla da rai da lafiya, Ubangiji Allah ya karɓi ibadunmu, ya sanya mu cikin ƴantatun bayinsa*

                         *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

40

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa
End Ads