WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
42
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
42
Cikin sanyin jiki ummi ta ce "Dan Allah anty ko zuwa da safe ne, sai na tafi in sha Allah"
"Wallahi ba ki isa ba, ba zan sake zama inuwa ɗaya da ke ba, ai ni ba zan manta cin kashin da dr. Ya din ga yi mini saboda ke ba, a samu ki auru da ƙyar sannan ki dawo mini, bana maimaita kuskure, haka Allah ya yi ki da baƙin jini, kamar mai hatimin jaɓa duk in da ki ka je sai an tsaneki an kore ki"
Ummi ta yi shiru ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ina zata tafi ga duhun magariba.
Kausar ta nufo ummi gadan-gadan da niyyar ta hankaɗata ta koreta, ummi ta ja da baya ta kalli kausar ta ce "Kar ki kuskura, akwai banbanci tsakanin da da kuma yanzu, ko da aurena ya mutu da yardar Allah na fi ƙarfin komawa baya, ba sai kin hankaɗa ni ba, zan tafi". Duka suka kalli ummi, yaushe bakinta ya buɗe har haka da take mayar da martani.
Ta juya ta fita, ta ɗan yi nisa kaɗan sai ga noor, sanye da uniform ɗin islamiyya.
"Yaya ummi, da tafiya zaki yi ban dawo ba, to Allah ya kama ki" tayi maganar tana murmushi.
Sai kuma ta yi saroro tana kallon ummi, ganin ummi a saɓule.
"Ya na ganki a haka? Ina yaya raihan ɗin?".
"Ya sakeni noor" ummi ta samu kanta tana gaya wa noor.
Ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, saki? Me ki ka yi masa? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ashe da gaske maama take idan Abba yayi mata laifi ta ce namiji ba ɗan goyo bane ba, ashe da gaske ne me ki ka yi masa?"
Ummi ta dafa kafaɗarta ta ce "Kul ki ka sake faɗar haka, mata mukan yaudari kanmu da ɗorawa maza kaso mafi yawa na zaluntarmu, alhalin a zahiri mu ne azzaluman kanmu, mu yi ta ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, amma a zahiri kowace mace ciwonta na ta ne ita kaɗai, noor maza ƴan goyo ne, kuma iyaye ne, ɓata garin cikin su ba zai sanya ayi musu kuɗin goro ba. Mami ce ta saka ya sake ni, ba laifin sa bane ba, ni duka da na san baƙin cikin ɗa namiji a rayuwata, amma maza sun tallafi rayuwata fiye da yadda mata suka yi".
Tuni noor ta fara kuka ta ce "To ina zaki je? Ba dai gagarawa ba ko? wannan garin da ba sa sonki, me zaki je ki yi musu, ki zo mu tafi gida kawai"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a ai ni in da ba a so na da yawa noor, ki yi maza ki tafi, magariba ta yi"
"To ina zaki je?"
"Ke dai kar ki damu, zan dawo maza ki ƙarasa gida".
Noor ta tafi gida da gudu, sai dai ta tarar farida suna sake tattauna abun da ya faru, a nan ta ji korar ummi suka yi, suka ce ba zata zauna a gidan ba.
Duk da ƙarancin shekaru na noor, sai da ta jinjina mugunta irin ta mahaifiyarsu.
"Maama yanzu idan wani abu ya sami yaya ummi a hanya fa, dare ya fara yi ki ka ce ta tafi gida? Idan Abba ya ji fa?"
"Idan ina magana kina saka baki, sai na murɗe miki wuya, tun da ita ta haife ki, duk irin cin kashin da aka yi mini a gidan nan saboda ita ke ba kya gani, saboda ita aka saka miki sunan uwarta ban haɗa dangi da ita ba, ki cigaba da saka baki a kan irin wannan maganganun ki ga yadda zan yi da ke".
Noor jikinta a sanyaye ta ce "Malaminmu ya ce; duk wanda ya shuka alkhairi ana yi wa ƴaƴansa ko ƴan uwansa, haka ma sharri, ni dai tun da ban yi aure yanzu ba, Allah ya sa a rama a kan anty inteesar ko kausar tun da dama ku ne kuke cin zalin yaya ummi" gaba ɗaya sai suka kasa magana, wata maganar idan noor ta yanko ta, sai ka kasa ba ta amsa.
Farida ta yi ƙarfin halin cewar "A gidan Ubanki aka zalunceta?" Tayi shiru ta rungumi jakarta ta shiga ciki.
Raihan yana zaune din ga jujjuya takardar a hannunsa.
Mami ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah, duk zafin ciwo ko na mutuwa raihan ba ya kuka, amma yau saboda ta raba shi da ummi, har da hawaye.
Nan ta ƙara tabattarwa da kanta cewa ummi asiri suka yi wa ɗan ta.
Ta miƙa hannu za ta karɓi takardar hannunsa, ya janye takardar.
Saki nawa ka rubuta a jiki?" Tayi maganar tana kallonsa.
"Dan Allah mami ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ai na rubuta"
"Kar ma ka rubuta, kuma ka tabattar a yau ba sai gobe ba, ka bi ta da takardar nan, kuma bana buƙatar sake wata alaƙa a tsakanin ka da ita. Abu na gaba shi ne zan je na nema maka taimako a warware sihirin da suka yi maka, azo ayi maza² a yi bikin nan".
Bai ce mata ƙala ba, ta gama surutun ta tafi, ji take kamar ta yaye wa kanta wata babbar damuwa da ta hanata sakewa.
Tana tafiya raihan ya shiga ɗaki ya ɗauki wayarsa ya tura wa ummi saƙo.
"Salma, ki jirani a gida komai ya lafa, zan zo na ɗauke ki, dan Allah kar ki gaya wa kowa, ban rubuta komai ba, ban sake ki ba, zan dai-daita komai. Ki kwantar da hankalinki da safe in sha Allah zan zo"
Bayan ya aika mata saƙon, ya ajiye wayar ya shiga yayi alwalar magariba.
Sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya, ji yake kamar ya bi ummi, amma da ya tuna gargaɗin mami sai ya kasa bin ta.
'Ban kyauta ba salma, am very sorry, baki cancanci haka ba' haka ya din ga sintiri yana surutai.
Kasa jurewa yayi, ya ɗauki wayarsa ya kira tata, sai dai ba ta ɗagawa, tun yana saka ran za ta ɗaga har ya fara sarewa ya sanyawa ransa ummi ta yi fushi da shi.
"Haba ummi, meyasa ki ke tunanin zan iya sakinki? Ba zan iya ba wallahi ban sake ki ba" ya din ga surutai yana kiran wayarta.
Ummi kuwa ƙarfe goma na dare, tana cikin motar haya, ta nufi gagarawa, tana ta lissafi kala-kala a zuciyarta, yanzu shikenan lissafin rayuwarta ya koma baya?.
Ta san zaman gagarawa ba zai kai ta ba, to sai ta tafi maiduguri daga yin aure ace ya mutu, ga mama ba cikakkiyar lafiya ba, suna murnar sun aurar da ita, kuma ta koma ta zaune musu a gida yau da gobe sai Allah.
Ta share hawayen ta a hankali ta furta "Mami ba ki yi mini adalci ba raba ni da ɗakina da mutumin da nake matuƙar ƙauna" tayi maganar tana ƙunshe kanta a hijjabinta tana kuka.
Ƴan cikin motar sai ba ta haƙuri suke yi, ba tare da sanin dalilin kukan na ta ba.
Sai sha ɗaya da kusan rabi ta shiga family house ɗin su na gagarawa.
Duk an rufe wasu ƙofofin wasu duk sun kwanta, jiki a sanyaye cikin tsananin fargaba ta shiga sashin iya da sallama.
Iya ta amsa daga ɗaki tana tambayar waye, ummi ta shiga tana amsa mata da ni ce.
Kamar sokuwa iya ta kalleta, ta ɗau fitila tana haskata. "Lafiya zaki shigo mana gida a tsakar daren nan kamar wata ƴar fashi?".
Ummi ta ce "Lafiya ƙalau"
"Kamar yaya? Ki rasa lokacin da zaki zo sai a wannan tsohon daren, yahaya dai an ce ba ya ƙasar nan me ki ka aikata ki ka gudo nan, ba zaki kwaso masifa ki yo nan ba, dan na san ba alkhairi ne ya kawo ki ba a daren nan dai"
Ummi ta yi ajiyar zuciya, ga gajiya ta kwaso kanta har ciwo yake, ga uban kuka ta sha ga tuhumar wulaƙanci daga iya, kodayeke ba yau ne farko ba, dan haka ta ce "Mun rabu ne"
"Da wa?"
"Ya sake ni" ta faɗa a taƙaice.
"Kuma da ya sake ki ki rasa ina zaki zo sai gagarawa? Garin da ki ka ce ba zaki sake zuwa ba? Amma ke dai an yi mai ƙashin tsiya, a yadda ki ke Allah ya rufa miki asiri ki auru da ƙyar ki kaso auren? Kodayeke kin gaji tsiya da rashin arzki a wurin uwarki, wallahi sai dai ki koma can wurin yahayan, ko ki koma wurin uwarki ba ki da wuri a gidan nan, ke ko kunya ma ba ki ji ba?"
Ummi ta ce "Dan Allah iya ki yi a hankali, ki rufa mini asiri ko sati na yi zan yanke shawara idan bai mayar da ni ba shikenan, ba a san ransa ya rabu da ni ba, na san zai neme ni da.....
"Dan Allah ki rufe mini baki, kin manta iskancin da ki ka din ga zubawa saboda zaki auri mai kuɗi? Wallahi sai kin bar gidan nan"
Kasancewar dare ne, tuni kwaroroton iya ya sanya wasu tasowa, suka taho sashin iya dan jin ba'asi.
"A daren nan fa zaki bar gidan nan"
Babar auwwalu ce ta fara roƙon iya "Haba Iya, ko korarta zaki yi, ki fara bari gari ya waye mana, a daren nan ina za ta je yanzu?"
"Ta koma in da ta fito, irin tsiyar da yarinyar nan ta shuka, idan tana da mutunci ba zata sake waiwayar gidan nan ba, ta koma in da ta fito, dama ba kowa take gani da gashi ba".
Ana tsaka da bawa iya haƙuri, ummi ta nufi ɗakin da mamanta ta zauna, da kayanta a hannu, ba tare da ta tankawa kowa ba.
Iya ta biyo ta ta riƙe ta, "Babu in da zaki je, tun da ba ɗakin uwarki bane ba yanzu, amaryar ilyasu ce a ciki yanzu, sai fa kin bar gidan nan".
Ummi ta ƙwace hannunta ta ce "Ban damu ba ko ɗakin waye, abun da na sani shi ne akwai gadon ubana a cikin gidan nan, dan haka dole a sama mini wurin zama. Tabbas yau tura ta kai bango, na gaji, na gaji Iya shekara ashirin da shida ban yi ƴanci daga ƙangi da ƙuncin da ki ka jefa ni ba, na ɗau layin da ki ke son na hau, babu ragowar mutunci ko kimar ki da nake gani a yanzu, tun tuni yakamata na yanke alaƙa da ke, saboda tsanar da ki ke yi mini da mahaifiyata, amma kullum ina duba mahaifina ki ka haifa, nake baki girmanki saboda haka. An zo kunyar ƙarshe, ba zaki taɓa canzawa ba, zan bar gidan nan amma ba a yanzu ba"
Tayi gaba ta shige ɗakin amaryar kawu ilya, ta ajiye kayanta.
Daskarewa iya tayi a wurin, ummin da ko buɗe baki ba ta iya yi idan za ta yi magana, amma yau ita ta yaɓawa maganganu haka.
"Iya ki rufawa kanki asiri a ƙyale yarinyar nan zuwa safiya" suka yi ta lallaɓa iya suna ba ta haƙuri.
Ummi ta yi alwala ta yi salla, ko yunwa ba ta ji saboda baƙin ciki da tashin hankali.
Amaryar kawu Ilyasu ta rasa me za ta ce, haka ta shiga ɗakin ta tarar da ummi ta haye mata kan katifa ta kwanta.
Raihan bai gaji ba, ya cigaba da kiran wayar ummi, kawai ya ga wayar a ɗakin kwanansu a ƙasan pillow.
Hankalinsa ya tashi, ya ɗauki wayar ga tarin missed calls ɗin sa da ya yi mata, ya ajiye wayar ya zauna, kansa yana wani irin sarawa sosai.
Gidan ya ƙara yin shiru, bayan gama hayaniya a kan ummi.
Ko kusa ko alama, bacci bai yi yinƙurin ɗaukarta ba, ta din ga tunanin ita kuwa meye laifinta haka, da kowa yake gudunta sai ka ce annoba?.
Ta tashi a hankali ta tafi tagar ɗakin, ta buɗe tagar, wani sanyi ya daki fuskarta, ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya, tana tuna abubuwan da suka wakana a rayuwarta.
Tabbas zamanta a gagarawa ba zai yiwu ba, akwai matsala, sai dai kan ta bar gagarawa sai ta amayar da abun da sai dai zumuncin ya watse, ta lura wannan duniyar kowa yayi ta kansa kawai, kar ka ce lallai sai ka dogara da wani, ko sai kowa ya so ka, kamar yadda raihan yake yawan gaya mata.
Ummi ta ƙara ƙaryata azancin hausawa, na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, da ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba.
Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashitna fita cikin huci.
A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni, da masu baƙin cikin ganina cikin walwala. Tun da babu sani babu sabo.
Zan aikata abun da zuciyata ke raya mini, ko da zai yi sanadain tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa.
Raihan, tabbas ina sonka amma dole zan ɓacewa duniyarka, tun da zamana da kai barazana ne gareka da mahaifiyar ka, duk wanda ba sa buƙata ta, zan gusa daga rayuwarsu.
Yadda ta ga rana haka ta ga dare, haka ɓangaren raihan ma, tun da ta idar da sallar asuba take zaune a wurin da ta yi salla, tana tufka da warwara.
Mami tun da ta koma gida kuma ta fara fargaba da addu'a Allah ya sa kar raihan ya tona mata asiri, gashi Alhaji sai tambayarta yake yi ya aka yi ya ganta kamar mara gaskiya, ko wani abu na faruwa ta ce masa babu komai.
Ƙarfe bakwai raihan ya ɗauki mota ya tafi gidan su ummi, ya kira Abdul a waya. Mintuna kaɗan Abdul ya fito suka gaisa, Abdul ya ce "Ka zo da kanka, ai mun yi magana da ummi, ta ce ka ce na je, jira nake dama kamar ƙarfe takwas na zo na sameka".
Raihan ya ce "Abdul ba wannan ba tukuna, yanzu ina ummi take? Dama dr. Ba ya ƙasa ai ko?"
Cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba, ummi kuma a gidan nan?"
"Eh, jiya ba nan ta zo ba?"
Abdul ya ɗan yi shiru ya ce "Ai ni ban ga ummi a gidan nan ba"
Kamar raihan zai yi kuka ya ce "Dan Allah ka duba mini"
Abdul ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, noor tana ta shirin makaranta, ya kalleta ya ce "Noor, wai ummi ta zo gidan nan ne? Ga raihan can a waje"
Noor ta ce "Jiya ta zo, a waje muka haɗu ma, ta ce mini wai yaya raihan ya saketa, ina ga su maama korarta suka yi, wai ba zata zauna a gidan nan ba".
Abdul ya ce "What! Saki kuma, sai kuma a kore ta daga gidan nan? Ina ta tafi to?"
Noor ta ce "Nima ba ta gaya mini ba"
Abdul ya fita da sauri, ya tarar da raihan na ta zagaye motarsa.
Yana ganin Abdul ya ce "Yauwwa tana ciki ko? Ka ce ta zo mu tafi"
"Me ummi ta yi maka zaka saketa? Ba abu ne da za a iya sasantawa ba? Har ta kai ga saki? Ka bani kunya raihan"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ce muku ta yi na saketa? Abdul ban saketa ba"
"Ba ka sake ta ba, me ta zo yi gida?"
"Ba ta fahimci meyafaru bane? Ka tsaya ka ji, wallahi ba laifina bane ba"
Abdul ya ce "To, koma laifin waye ummi ba ta gidan nan"
"Ba ta zo ba? Ina ta tafi?"
"Ta zo, amma a jiya ta bar gidan nan ban ma san ta zo ba"
Raihan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ummi meyasa zaki yi mini haka? To ina ka ke ganin za ta tafi, ko gagarawa?"
Abdul ya ce "Bana tunanin ummi za ta je gagarawa, tun da ba shiri suke yi ba, sai dai ko maiduguri"
"Maiduguri ta tafi a daren jiya? Meyasa ta bar nan gidan? Wallahi ban sake ta ba. Dan Allah Abdul ka yi mini wani taimako mana".
"Ina jinka"
"Dan Allah kar ka gaya wa dr. Halin da ake ciki zan nemo ta, dan Allah kar ka gaya masa"
Sai tausayin raihan ya kama Abdul, lallai akwai maƙarƙashiya, sai dai ya san idan dr. Ya ji to ba raihan ba, har maama tana cikin matsala korar ummi da ta yi.
"In sha Allah ba zan gaya masa ba, zan saka a bincika gagarawa, amma ka kira wayarta?"
Raihan ya ce "Wayar a gida ta bar ta"
Abdul ya ce "In sha Allah tana nan lafiya, zan kira gagarawa ka tuntuɓa can maidugurin".
A rikice raihan ya juya ya koma mota, yana salati tare da tunanin in da ummi ta tafi.
A cikin motar ya kira Anty maryam ta can Maiduguri suka gaisa, sai dai yanayin yadda suka gaisa ɗin ya tabattar masa da ummi ba ta je maiduguri ba.
Abdul kuwa da ya koma cikin gida, ya tarar mami ta fito, ya gaisheta sannan ya ce "Mami wai jiya da gaske ummi ta zo?"
"Eh" ta amsa a taƙaice.
"To tana ina?"
"Na koreta, dan ba zan riƙe bazawara har a karo biyu ba, ta koma gidan ubanta".
Ya kalli farida ya ce "Haba maama, da ki ka koreta ina za ta je, ina take da shi da ya wuce nan?"
Farida ta ce "Ta koma gidan ubanta, ko wurin uwarta ta barni na huta a gidan mijina na sake, kuma kar sake yi mini maganarta, kan ranka ya ɓaci" bai sake cewa komai ba, ya fito ya ɗau wayarsa ya kira yaya Hashim can gagarawa.
Suka gaisa sannan ya tambaye shi ko ummi ta je.
"Ai ka san ni yanzu na bar cikin gagarawa, ina dutse ina koyarwa a wata makaranta, har matata muna can, su kuma gagarawa