x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - CUTARWA

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 503

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula.

Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta.

Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice.

Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi.

Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi.

Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki.

Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar.

Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaɗota waje cikin ruwan sama.

Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta.
Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa "Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi.
Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan.

Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka.

Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raɓa ta zauna, saboda an yi ruwa ba ɗan kaɗan ba.
Gari ya fara haske tana sanya ran ya buɗe ƙofa ta suturta jikinta, amma bai buɗe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan a tarar da ita jikinta babu sutura.

Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banɗaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga banɗaki, ya sanya ta fita ta shiga ɗakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ƙafafuwan ta.

A gurguje ta yi alwala, ta koma ɗakin yin sallar asuba, duk a ɗarare take cikin tsoro take yin ta.

Aikuwa a raka'a ta biyu ya dawo ɗakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaɗeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa.

Ta miƙe ta cigaba da sallar, ya tsaya a kanta yana kallon ta yana huci, da ta idar da sallar, ta miƙe zata bar masa ɗakin, amma ya janyota ta baya, ya sake hankaɗata ƙasa.

Wata irin ashar da yayi mata sai da ta kalleshi a firgice, ya din ga ɗura mata ashar yana cin mutuncin ta da na iyayenta, har da mahaifinta da ba ya raye a duniyar, har da kiranta da ƴar iska lalatacciya.

Ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta nemi hawayen ma gaba ɗaya ta rasa.

Har zai fita ya dawo, ya din ga dukanta hannu da ƙafa, cike da tsana da jin haushin ta.

Ya gama rashin mutuncinsa ya fita, ta tashi a hankali, ta koma gefe tayi zuru da ido.

Sai a lokacin kuma ta samu damar yin kuka, jikinta sai ciwo yake yi, ga yunwa tana ji, gashi haryanzu sanyi take ji, ta kwanta a wurin, ta hau bacci.

Sallamar da Iya take kwaɗawa a tsakar gida ne, ya sanya ummi farkawa, ta fito da sauri, ta ga Iya tare da yaya, mahaifiyar su Idris.

Murmushi ummi ta yi ta ce "Iya sannu da zuwa, yaya ina kwana"

"Ai kya bari mu shigo mu zauna ko"

Ta basu hanya suka shiga ɗakin, suka zauna, yaya tayi ƙuri tana kallon ummi, Iya ta ce "Ke lafiya na ga kayanki a yayyage?"

"Ba komai"

"Kamar yaya ba komai, kamar wadda ta yi dambe" hawaye ne ke shirin taruwa a idon ummi.

"Kuma dan ƙazanta tun da aka kawo ki baki canza kaya ba, yau wurin kwana biyar".

Ummi ta buɗe baki za ta yi magana, ta kasa hawaye suka riga maganar fita.

Yaya ta ce "Menene na kuka kuma ummi?"

Iya ta ce "Sangarta mana, idan zaki yi wa kanki ƙiyamullaili ki zauna ki daina wannan kukan shikenan, idan ba zaki daina ba, sai ki yi ta yi, ga kaya nan na ɗebo miki a kayan auren da aka kaiwa waccan, abun bai yiwu ba, sauran an sayar an bashi kuɗin yayi muku cefane, sadakin ki kuma, na bayar a sayo akuya a bayar da kiwo".

"Dan Allah iya ki mayar da ni gida, bana son zaman nan"

"Ki kiyayeni ummi, tun kan na ɓata miki rai, bana son shashanci, ki tashi ki yi wanka ki canza wannan kayan"

Tashi ummi ta yi tana kuka, ta fita tsakar gida, suma fitowar suka yi, wai har tafiya za su yi.

Ummi ta tsaya tana kallonsu, suka fice, wai wata unguwar zasu je, to da me za ta yi wankan, ko ruwa ba ta da shi? Ta koma ɗaki ta zazzage lesar vivar da Iya ta kawo mata, atamfa ce kala uku, sai sabulun wanka uku, man shafawa ɗaya da soson wanka.

Sai kuma 'yar tsala, a ƙulle a leda, ummi ta ture kayan ta kwanta, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta, saboda dukan ruwan sama.

Sai da ummi ta kwana biyu tana zazzaɓin nan, babu abun da ya shafi Idris, da ya dawo zai koreta daga ɗakin, bayan ya gama ci mata mutunci da zaginta, wasu lokutan sai yayi mata dukan tsiya ma, duka na cin mutunci, haka take kwana a ɗaya ɗakin da babu ko ƙofa a ciki, idan aka yi ruwan sama, haka zai sameta a ɗakin nan.

Ƙarshe ma ya watso mata kayanta da ga ɗakin da katifa take, ya ce ta koma ɗaya ɗakin.

Da ya tuna ƙarin da ya ji tana yi, da kuma yadda suka din ga lalubeta tana yarinya, sai ya ji ya ƙara tsanarta, da ganin an bashi saura.

Dama abinci ba a magana, ba bata yake yi ba, wasu lokutan ne idan yaran gidan su za su zo, babar Idiris ɗin kan zuba mata abinci a kwano a kawo mata.

Tana kwance a ɗaki tana numfarfashi,  zazzaɓi da ciwon kai sun ƙi sauka, fitsari ya dameta, ta tashi da ƙyar, ta je ta yi, tana shirin komawa ɗakin, ta ji an ce "Ummi"

Tana waiwayawa taga Na'ima, ai sai ta nemi ciwon ta rasa, cikin wani irin zafin nama, ta rungume Na'ima ta fashe da kuka.

Ita ma Na'iman kuka take yi, ta ɗago ummi ta kalleta ta ce "Ummi ba ki da lafiya ne? Na ji jikinki zafi?" Ta jinjinawa na'ima kai.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu ummi a rasa wanda za a aura miki sai wannan ɗan iskan, dukan ki yake yi kenan? Kalli shaidar yatsu a fuskarki" Ummi dai ta yi shiru, daga baya ta ce "Mu shiga ɗaki"

Saroro na'ima ta bi ɗakin da kallo.

"Ummi kar ki ce ba su yi miki kayan ɗaki ba?"

"Suna can ɗakin, koro ni yayi nan shi ne yake kwana a ɗakin"

Na'ima ta zauna tayi kuka mai isarta sannan ta kalli ummi ta ce "Wai ke ba ki san in da mamanki take ba? Anya ma kuwa sun san halin da ake ciki?"

"Yaya Na'ima nifa tun da aka tafi da mama ban sake ganinta ba, dan Allah idan kin san in da take ki kaini, na gaji, wallahi yaya Idris dukana yake yi, duk jikina ciwo yake zai kasheni"

Ta rungume ummi, ta din ga rarrashin ta, ta ce "Kiyi haƙuri ummi, ban ma san an yi miki aure ba, mama ce ta aika ƙanin mijina ya gaya mini, Allah yana sane da ke ummi, bari na je gida na kawo miki abubuwan da na kawo miki, sai na kawo miki tabarma da labule, a kafa a ɗakin, tabarmar ki din ga kwana a kai"

Ummi ta yi ta mata godiya, ta bata abinci, ta aika ƙannenta suka sayo mata magani, aka kafa labule, ta shimfiɗa tabarma, sai ɗakin ya ɗan yi kyan gani.

"Yaya na'ima, dan Allah idan Allah ya yassare miki, ki saya mini wando, nawa ya ƙarasa lalacewa, ba zai saku ba"

"Ummi meyasa ba zaki din ga zuwa wurin mama kina gaya mata ba? Ya za ayi ki rayu da wando guda ɗaya, abun da a ƙalla a rana ana so ki canza biyu"

Ummi ta yi shiru, tana wasa da yatsun hannunta, yanzu ma dan ta ƙure ne ta nemi alfarmar na'ima, dan idris ya ƙarasa shi, wandon har da in da ta kama take ƙullewa.

Ta ji daɗin zuwan na'ima, ta bata abubuwa da yawa, har da kuɗi, sai bayan la'asar ta tafi, kuma Allah ya taimake ta, Idiris bai dawo ba a lokacin.

Duk yadda ummi ta so ta yi wa naima bayanin halin da take ciki, kasawa ta yi, ta ji abun yayi mata girma ta faɗa, dan haka ta yi shiru da bakinta, ta samu ta saya mata wanduna guda huɗu, har da ribbon.

Duk in da idris ya haɗu da abokansa, suka yi masa kirarin ango, da tambayarsa yaushe za su cin girkin amarya, sai ya hau masifa yana basu labarin halin da ummi ke ciki, na mummunan ciwon sanyi da yadda take bugawa, da ƙazanta tare da ƙorafin ragowa ce aka haɗa shi da ita, su yi ta masa dariya, suna ce masa angon ɗoɗɗoya.

Tare da tabattar masa, idan bai yi da gaske ba, sai ya kwashi ciwon.

Sai dai ko sun tambaye shi dalilin fasa auren sa da Hindu, sai ya ɓoye musu gaskiyar zancen.

Haryanzu kuma bai rabu da hindu ba, yana lallaɓawa su haɗu a wani wurin na daban, duk da tarin kashedi da mahaifinta yayi mata a kan idiris.

Na'ima kuwa a ranar  zata koma gidanta, suka haɗu da magaji a hanya, suka haɗu suka gaisa.

Ta ce "Yaya magaji ashe aure aka yi wa ummi babu labari?"

Hashim ya ce "Ke dai bari na'ima, abun ne yazo babu shiri, ni kaina ban san da zancen ba sai ana gobe ɗaurin aure".

Na'ima ta gyaɗa kai ta ce "Amma, ka yi haƙuri da abun da zan ce, wallahi ku din ga gaya wa kakarku da ɗan uwanka gaskiya, ya za a katsewa ummi karatunta, kuma a haɗata aure da wanda baya ƙaunarta, dama ita ba bi ta kanta za ayi, aji ko tana son sa ba, gaba ɗaya a firgice take a cikin gidan nan, jikinta duk shaidar duka, ya korota daga ɗaki, ɗakin da na tarar da ita, ba ƙofa babu taga, babu abun zama, ba ya bata abinci, wace irin rayuwa ce haka? A gidanku ba ta huta ba, an aurar da ita, ta buɗe sabon babi na ƙalubale, sai yaushe za ta huta kenan? Meyasa Iya ta tsani ummi ne, kamar ba a cikin jikokinta take ba?"

Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce "Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba.
Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ƙarfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuɗi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. Ƙiyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matuƙar son ta, har wasu lokutan baya iya ɓoye son da yake yi mata, bugu da ƙari, baban ummi ba shi da komai, bai mutu ya bar komai ba, duk da haka dai, ban san dalilin da ya sanya ta tsananta ƙiyayyar ummi haka ba.
Zan cigaba da yi wa idiris nasiha, duk da ba jin shawara yake yi ba, zan kuma biya ta gidan yanzu, in ga halin da take ciki".

Jiki a sanyaye na'ima ta ce "Yakamata kam, ummi na buƙatar kulawa da jaba jiki, har ga Allah ina jin tausayinta sosai da sosai, dan Allah yaya magaji ka din ga zagayata".

"Kar ki damu, in sha Allah, ba zai gagara ba, ina godiya sosai da gudunmawar da ki ke bawa ummi".

"Bakomai yaya magaji, ummi ƙanwata ce, ba zan manta karamcin iyayenta a gare ni ba, da yadda suke girmama iyayena ba"

"Haka ne, ki gaida gida, da maigidan"

Suka yi sallama, kowa ya tafi.

Kasa wucewa gida magaji yayi, ya wuce gidan Idris da bai taɓa zuwa ba.

Sallama yayi ya tsaya a waje, ummi ta leƙo, tana ganinsa tayi murmushi ta ce "Laa yaya magaji, shigo baka zo ba sai yau"

Ya kalleta duk da tana da duhu, amma ga shaidar mari nan a gefen idonta.

Ta yi gaba ta ce masa ya shigo, ya ce "A'a bani abun zama, na zauna a nan"

Ta shiga ta ɗaukko masa tabarma, ta shimfiɗa masa ta ce "Yaya yaya na'ima ta zo fa"

Ya ce "Haba?"

"Wallahi, duk ta sai mini kayayyaki ta bani, ita ta bani tabar nan ma"

"Masha Allah, Allah ya saka mata da alkhairi"

Ta ce "Amin"

Ya ɗan dube ta, ya ce "Ummi babu wata matsala? Komai lafiya ƙalau?"

Ta jinjina masa kai ta ce "Eh".

"Na san ko baki faɗa ba, akwai matsala ummi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce in sha Allah"

"Yaushe zai wuce yaya? Gobe ko jibi?" Tayi maganar idanunta na tara hawaye.

"Lokaci ne ummi, zai zama tarihi"

Tuni idanuwanta suka fara zubar da hawaye.

"Ki dake ummi, ki ƙarfafi zuciyarki, na san a cikin matsala ki ke, ki yi haƙuri ummi, ki share hawayenki, zai zama murmushi wataran" goge hawaye take yi, sai dai tana gogewa wasu suna zubowa.

Idiris ne ya bankaɗo babu ko sallama, yadda ummi ta zabura kawai ya isa ya baka tausayi.

Ko kallonsu bai yi ba, ya shige ya buɗe ɗakin da yake kwana, ya shiga.

Hashim ya tashi ya bi bayansa, ummi ta karkaɗe tabarmar, ta ɗaukko tsintsiyar da na'ima ta bata, ta yi shara, hayaniyar hashim ta din ga ji, da idris.

Hashim yana ce masa "Ka ji tsoron Allah wallahi, idan ka cigaba da biye wa Iya, wallahi Allah ba zai barku ba, kuna ta azabtar da marainiyar Allah ba gaira babu dalili".

"An azabtar da ita ɗin, ni na ce a aura mini ita? Ko na ce ina son ta ne, kai meya hana a aura maka ita? An bani saura ƙazama mummuna, Wallahi ba zan zauna da ita ba, sai ta gudu da ƙafarta".

"Amma ita ma ai ba cewa tayi tana sonka ba, haɗin Iya ne, ita tayi haƙuri, kai me zai hana ka yi haƙurin?"

Idris ya ce "ba zan yi haƙurin ba, ka fita daga harkata, ko kai ma na karta maka rashin mutunci"

Haka suka yi baran-baran, hashim ya fito, ummi tana ce masa kai gaida gida, kai kawai ya jinjina mata ya tafi.

Yana fita, Idris ya dirar mata da duka da zagi da cin mutunci kamar yadda ya saba, yana iƙrarin ƙararsa ta kai wurin magaji.

Maƙwabciyar su da ta kasance dattijuwa, yau ta kasa jure ihun ummi, ta shigo kawo mata ɗauki, ta din ga bashi haƙuri, amma mursisi ya ce ta fita ta bar masa gida, ganin idiris bai yi kalar mutunci ba, ya sanya ta fita ta bar gidan tana tausaya wa ummi.

Tun daga ranar ya ƙara tsananta azabtarwar da yake yi mata, gashi ya tula mata wankinsa, ya ce tayi masa, idan tayi bai fita ba, ya kamata ya zane ta, ban da zagi da cin mutunci.

Abinci kuwa ko tumatir bai taɓa kawowa ba, sai dai ta aika wa iya, Wataran ta bata, wataran ta ce ba ta da shi.

Ƙarshe sai da iya tayi ta mata faɗa, wai ba zata iya rufawa Idris asiri ba, ta san dai ba wata cikakkiyar sana'a ce da shi ba, ranar da ya kawo su ci, idan ba shi da shi ta din ga haƙuri.

Dattijuwar matar nan ta fuskanci halin da ummi take ciki, ta ɗauki ragamar ciyar da ita, idan ta cewa ummi ta gudu ta je gida ta kai ƙarar abun da yake yi mata, sai ummi ta ce ko ta je dawo da ita za ayi.

Da ya kalli ummi, ya tuna a yanayin da ya sameta, sai ya ƙara ƙaimi wurin cutar da ita, haɗi da zaluntar ta.

Idan aka zo ana sallama da shi abokansa, sai ta jiyo suna kiransa da angon ɗoɗɗoya, ba ta kawo komai a ranta ba, sai ranar da ta jiyo suna tambayarsa ina amaryarsa ɗoɗɗoya, ya ce musu kar su sake haɗa shi da wannan jakar yarinyar.

Duk da ƙarancin shekarun ummi, a lokacin ta fuskanci asiri ya tona mata a wurin abokansa, hakan ya sanya ta yin kuka da har kanta ya yi ciwo.

A haka a wannan baƙar azabar, tayi wata guda cir a gidan sa, tun tana tsoronsa har ta fara dakewa da duk abun da zai yi mata yayi mata.

Yau ta tashi da wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, wanda baya rasa nasaba da dukan ruwa da kuma azababben sauron da yake cizonta a wannan ɗakin.
Ga gudawa da take zugawa babu ƙaƙƙautawa, jikinta duk yayi weak.

Bankaɗa labulen yayi, ya tarar da ita a kwance, ya watsa mata kayansa ya ce ta wanke masa.
Shiru tayi ba ta motsa ba, ya daka mata tsawa ta ce "Yaya bani da lafiya"

"Ina ruwana, dalla fito"

Ta janyo jikinta ta kwaso kayan ta fito, ya fita sayen omo, ta kwanta a kan kayan, tana jin ɗumin ranar dake ratsata, wanda hakan ya sa zazzaɓi ƙara rufeta.

Azabar zafin dukan da yayi mata da ƙafarsa yasa ta tashi da sauri, tana riƙe hannunta.

"Bacci na ce ki yi?" Shiru tayi tana sunkuyar da kai.

Wani irin
End Ads