kafaɗarki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar nan da ni da ke baki ɗaya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye" haka ta wuni cikin kuka da damuwa.
***"
Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya.
Haka zalika balarabe, ya fara tunanin miƙewa ya nemi kuɗi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali, mussaman ƴar ƙaramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban.
Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce "Maman Ummi kin san wani abu?"
Ta ce "A'a"
"Ina ga ƴan kuɗaɗena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki"
Mariya ta kalle shi ta ce "Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daɗi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi haƙuri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuɗi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan Allah kayi haƙuri"
Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan galibi duk maza ne tana cikin haɗari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, ɗazu fa suna tafe da yarinyar nan da take ɗaukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta baƙar tukunya mai ƙyalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan.
Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai ɗora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na ɗora masa ɗawainiya, kuma kin ga shi ɗan boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuɗi, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha".
Mariya ta nisa ta ce "To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da haƙuri, komai lokaci ne, amma duk abun da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa'a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba.
"In sha Allah komai zai zo da sauƙi, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki"
"Allah ya sa"
Ya amsa mata da "Amin"
Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi'u maƙwabcin su, lallai ya nemo kuɗi, ya bi shi lagos, ya ɗora shi a kan hanyar neman arziki.
Bashir ba shi da kuɗin da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi'u cewa yayi ya tanadi dubu ɗari, harkar fawa yake a lagos, ya je ya koya masa.
Ya ce wa iya ba shi da halin kuɗin nan ta ce "Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karɓo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a rasa nono a riga, su baka aro.
Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar ƴan uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi.
Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuɗi, amma ya kada baki ya ce "In ara maka kuɗi, ka biyani da me? Gaskiya ba zan iya ba, kuɗin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi haƙuri kawai". Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi.
Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuɗi, dan ita kanta wulaƙancin da ake yi masa yana bata haushi.
Ya din ga yi mata faɗa a kan sayar da kayanta da tayi.
Ta ce "Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wulaƙanta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare"
Ya riƙe hannunta ya ce "Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ƙara miki haƙuri, kada Allah ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku" haka ya din ga zuba mata addu'a kamar ta yaye masa gaba ɗaya matsalolin sa.
Saura kwana ɗaya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu'a, ya sanya musu albarka da ita ummi.
Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu'a. Ya zura mata ido yana kallon ta.
"Wai wannan kallon fa?"
"Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi"
Tayi murmushi ta ce "Zaka fara ko?"
"Allah ba wasa nake ba amaryata" ta kwashe da dariya ta ce "Ko ba amarya ba, da wannan ƴar tamu nake amaryar, in zo in fara tara kayan ɗakin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama".
Yayi dariya ya ce "Kema ɗin yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai zurfi, Allah ya sa kan na tafi ɗin nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu ɗan uwa"
"Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi"
"To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuɗi na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki"
"Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuɗi ba su ne farinciki ba" sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya.
Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiɗar ummi, da ta yi nisa a baccinta sosai.
Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin ƴar sa ba da mutane suke faɗa suna zuzutawa.
Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta.
Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce "Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ƙauna haka?"
Yayi murmushi ya ce "Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ƙaunar yarinyar nan"
Mariya ta ce "To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri"
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta.
Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, ɗan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaɗe ba, dan daren da aka yi mata fyaɗe ta tuna, da ƙarfe ta ce "Baba"
Ya ce "Na'am ummina"
"Kai ne" tayi maganar tana shafa fuskarsa.
"Eh Ummina"
Ta ce "To" ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci.
"Ina ƙaunar ki ummina, Allah ga ƴa ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ƴar kyakywar ɗiya ta" yayi maganar yana jan kumatunta. Ummi ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi ta cigaba da bacci.
Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi.
Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya tafi.
Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki.
Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ƙare, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu.
Cin zali a wurin ƴan samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa'ar su, saboda tana mace, abu kaɗan sai a kai mata duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara.
Ɗan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana'ar.
Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi kuka ta gaya wa Allah.
Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ƙyar ta jiƙawa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta.
Da gudu Alhassan ya shigo ya ce "Babar ummi Albishirinki?"
Ta kalleshi ta ce "Albishirina kuma? Menene?"
"Wai baban ummi ƴan fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!"
Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta miƙe a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da saurin gaske amma ta kasa magana.
Miƙewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo.
Iya ta fito a gigice ta ƙundumawa Alhassan ashariya ya ce "Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani ɗan iskan".
Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala.
"Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi ɗaukko gawarsa"
A gigice iya ta ce "Ƙarya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi aka kashe shi?"
Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce "A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa"
Mariya ji take abun kamar mafarki, addu'a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba".
Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiɗa, aka yi sallama tare da ƴan sanda, da rabi'u da suka tafi tare, aka shigo da gawar bashir, tana ta ɗigar da jini.
Nan da nan gida ya cika da jama'a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace.
Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buɗe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ƙirjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da nutsuwa da dangana.
Ummi ta shafa fuskar sa tana faɗin "Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka" cikin haɗe rai sagir ya yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi.
Sa'adatu ta ce "Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana".
Mutane suka cika gidan danƙam, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matuƙar haƙuri da girmama mutane.
Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi ɗakin Iya, aka yi masa sutura, sannan aka ce su je su yi sallama da shi.
Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ƙuna da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir shikenan an yi an gama, rayuwar ta ƙare.
Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taɓa shi tana "Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ƴar tsana in yi addu'a ka samu kuɗi, kullum ina yi maka addu'a"
Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu.
Sa'adatu ta ce "Mariya ki riƙe yarinyar nan, za a shigo a ɗauki gawar"
Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa.
Aka zo aka ɗauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta riƙe ƙafar Saminu wan mahaifinta, da suka ɗaga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ƙasa suka yi waje.
Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faɗin "Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi"
Surayya, wadda take ƴar autar su bashir, ta riƙo hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta.
Gida ya cika da jama'a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuɓe, tayi shiru ba ta cewa komai, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take yi mata.
Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala'i a cikin mutane "Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta, ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ƙeƙashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba"
Daram! Gaban mariya ya faɗi, jin abun da iya ta faɗa na ƙarshe.
Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce "Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ƙuna ba, gara ke kin yi kukan, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuɗi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi".
Ai nan ta mayar da faɗan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta ɗaya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai haƙuri da juriya, mussman a zamanta da iya.
Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raɗaɗin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ƙulla mata, wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi.
Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ƙiyayyar, saboda kawai tana auren ɗan ta, abun da ba haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ƙafar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya ɗauki son duniya ya ɗorawa mariya, yana matuƙar son ta da ƙaunarta.
Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu'amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin ɓacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ƙirƙirar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ƙara tsanar ummi, ga ƴaƴanta sun riƙe ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su.
Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake birni, shi ma ya zo ta'aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaɗan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ƴan uwansa, ko wanda suke ciki ɗaya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matuƙar girmama shi.
Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu.
Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa'adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata.
Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu.
Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo.
Ya ƙarasa ya ɗauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce "Mamana, ki din ga yi wa babanki addu'a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba"
"Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?" Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo.
"Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daɗi idan kina yi masa addu'a"
Cikin kuka ta ce "Na fi son ya dawo" ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa.
Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga ƴan uwanta a gida, amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata ɗa.
Ya dubi Iya ya ce "Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taɓa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ƴan uwanta a gida ai babu daɗi"
"Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan haƙurin zama yake yi da ita"
Yahaya ya ce "A'a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki"
Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru.
Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata ɗa.
Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo.
"Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da