manyan ƴan mata nawa aka haɗa shi, duk ya ce ba ya so dan ya ce yana sonki zaki wulaƙanta mini yaya, to kin yi wa kanki"
Noor ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri"
"Kin fi son ki koma gida kina jerawa da kausar kuna faɗa kenan? Ke ba kya son ki ganki kema a gidanki?"
"To ai yanzu ba a gida nake ba, gidan mama zan koma, ni ba zan koma gidanmu ba, maama haushina take ji kamar ba ta son ganina ma"
"A'a ba sonki ne ba ta yi ba, amma dai yaya Salim dai kin yi wa kanki"
"Na shiga uku, yanzu ya zan yi?"
"Ki ɗauki waya ki bashi haƙuri"
Noor ta tura baki ta ta ce "Salon ajina ya zube" ummi ta ƙare mata kallo kawai tayi tsaki ta bar ɗakin.
Ummi na komawa ɗaki ta kira Salim, suka gaisa sannan ta ce "Yaya ka ji Alhaji ya bani mota?"
Yayi murmushi ya ce "Na riga ki sani ai, ina taya ki murna ƙanwata"
"Na gode sosai yaya salim, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"
"Amin ƙanwata, Allah ya raya mana su Iman"
"Amin yaya. Yauwwa noor ta gaya mini shirmen da ta yi maka, abun duk ya dame ta, dan Allah ka rabu da ita, Alhaji ya samu dr. Da maganar".
Yayi murmushi ya ce "Kin je kin takura mata ko? Bana son takura ta, daga baya nake ganin kamar na yi wauta nayi mata tsufa"
"Dan Allah ka bar wannan maganar, tana sonka, duk ta damu fa"
"Amma, kina ganin dr. Zai bani noor kuwa? Kin san ni ina da case"
"A'a yaya me zai hana? Kuma dan kana da case sai a ƙyamace ka? Ai yanzu ka shiryu a kan yadda na sanka a da, dan Allah ka ƙyale shirmen noor yaya"
Yayi murmushi ya ce "Auta danger, shikenan zan yi tunani, a bata lokaci"
"Dan Allah yaya ka ƙyaleta, mun yi magana da ita fa"
"To shikenan, sai da safe"
"Yauwwa yaya, a yi wa su hajiya bangajiya"
Suka yi sallama, ta din ga addu'a, Allah ya tabattar da alkhairi, dan tana fatan noor ta yi aure da wuri, tun kan farida ta ƙwace ta, ta siffantu da miyagun halayenta.
Har dr. Ummi ta kira, ta sanar masa da abun alkhairin da Alhaji ya yi mata.
Ƴan gagarawa sai da suka kwana uku a gidan ummi, da zasu tafi ta haɗa kayan suna ta basu suka tafi da shi.
Ummi ta saka noor a gaba, ta bata waya ta kira Salim.
Sai dai da ya ɗaga wayar ya ji murayarta, bai kashe ba suka gaisa.
"First born"
"Mmmm auta"
"Fushi ka ke da ni ko?"
"Me ki ka yi mini zan yi fushi da ke?"
Ta ɗan sosa kai ta ce "Maganar da muka yi ranar suna".
"Ai ta wuce auta"
"Ba ka so na yanzu?"
Yayi murmushi ya ce "Ke dai ba kya so na, an bar maganar bana son takura miki"
"To yanzu na canza shawara ka yi haƙuri"
"To" ta ɓata rai saboda yadda yake bata amsa a taƙaice da izza.
Ummi ta girgiza mata kai, alamar kar ta yi fushi.
"Yaya Salim"
"Noor"
"Idan muka yi auren zaka bar ni in yi makaranta, ka ga yaya inteesar mijinta hanata yayi daga baya".
"Zan barki in sha Allah"
"A'a rantse da Allah, kar ka canza shawara" yayi mata shiru, ummi ta dafe kai, saboda wautar da noor ɗin ke yi.
Bayan sun gama wayar, ummi ta ce "Eh lallai akwai jan aiki a gabana, noor babban mutum yayi magana ki ce ya rantse? Ke fa baki da kai"
"To ba ki ji yadda yake yi mini magana da gadara ba, da fa ba haka yake yi mini ba"
"Ba aurenki zai yi ba yanzu? Dole yayi miki izza. Ke fa miji ba abun wasa bane ba" ta din ga yi mata faɗa.
Ummi ta ƙara ɗaura aniyar, raba noor da Farida har zuwa lokacin da za a saka auren noor ɗin, saboda kar ta ɗorata a kan mummunar ɗabi'arta na raina miji da yin asiri.
Ummi ta kira Alhaji a waya, ta din ga yi masa godiya, tare da yi masa adduo'i masu daɗi.
Ummi ta tara kuɗi da suturu, da sauran abubuwa.
Farida kuwa tayi watsi da dr., Shi ma yayi watsi da ita ya daina shiga sabgarta kausar ma ta biye mata ba sa kula shi.
Yau yana gidanta, tana ta cika tana batsewa, ta same shi a fall ta tsaya a kansa ta ce "Malam yaushe za ka dawo mini da ƴa ta ne?"
Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Ke da noor, sai lokacin aurenta, ta bar gidan nan kenan na bawa mariya ita"
"Wallahi ba ka isa ba, ai ba ita ta haifa mini ita ba, da zaka bayar mini da ƴa"
"Ni ban isa na ƙwace miki ƴa ba, halinki da ki ke nuna mata ne, ya sanya ta guje ki ita ma" za ta yi magana wayarta ta fara ringing.
Ta ɗaga wayar ta yi sallama.
"Farida kina ina, ki yi maza ki zo asibitin murtala emergency, Rahama mijinta ya ƙonata da ruwan zafi da ita da ƴar da take goyo"
Farida ta dafe ƙirji ta ce "Ruwan zafi me tayi masa?"
"Wai faɗa suka yi, ta tafi tsakar gida tana girki, ya zageta ta rama, ya fito yayi balla da kurfotin gabanta da tafasasshen ruwa a kai, da garwashin duk ya watse musu a jiki ita da ƴar"
"Innalillahi na shiga uku" tayi jifa da wayar tayi ɗaki tana salati.
Kiran sallar la'asar ake yi dama, dr. Ya fice sallar isha'i, dan bai san me aka ce mata a wayar ba.
Daga sallar isha'i, ya tafi gidan mariya.
Ya tarar ta idar da salla tana zaune ta yi shiru.
"Ya dai, na ganki sai a hankali, ina noor ne?"
"Tana gidan ummi, ai noor ta gujeni saboda sun yi jarirai"
Yayi murmushi ya ce "Noor an kusa girma, Alhaji Tahir ne yayi mini magana, wai su na riƙo Salim yana so, na ce zai sha shiririta"
Mariya ta ce "A'a kar ka ce haka, abu namu ƴa ta wa ɗa na wa, za ta yi hankali in sha Allah kan lokacin"
"Wane lokaci kuma, shekara ɗaya ne kawai fa, tana gama secondary school ne suke so"
Mariya ta yi dariya ta ce "Allah ya sa zamu gani"
Ya ɗan kalleta ya ce "Kamar akwai magana ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To ya aka yi?"
"Dr. Tun muna waccan ƙasar kamar ban kuma al'ada ba fa"
Yayi dariya ya ce "To me ki ke so in ce?"
"Koma meye ka ce mana"
Dr. Yayi dariya ya ce "Maman ummi rigima, kin fi ni sanin meyake faruwa ai"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai ciki ne da ni?"
Dr. Ya kashingiɗa yana dariya, gaba ɗaya ta ruɗe "Haba dr. Ummi na jego nima a ganni da ciki, na shige su"
"To laifina ne? Ni dai ina so ina murna Allah ya raba lafiya, kowa ya kalle ki fa zai gane kin ƙara haske sosai" gaba ɗaya ta rikice, wai abun kunya ne, shi kuma ya din ga yi mata dariya. Gaba ɗaya ya manta da a gidan farida.
Ummi na ɗaki tana ta yi wa noor nasiha, a kan maganar salim, ta ce mata ita tana son sa amma tsoron auren take yi, ummi tana ta lallaɓata, dan sun yi magana da dr. Kuma ta san zai kira noor ɗin ya tambaye ta.
Anty Maryam ta shigo ɗakin ta ce "Ummi, kin yi baƙuwa, sai wani harare-harare take yi, ban san me aka yi mata ba, amma da alama ƴar uwar mai gidan ce, suna kama da shi"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty ki ce ta shigo".
Mintuna kaɗan sai ga Maryam ta shigo.
Ummi ta ce "Sannu da zuwa, yanzu ki ke tafe?"
Ta ja tsaki ta zauna.
Noor ta ce "To, ikon Allah"
"Noor kawo mata ruwa da yaran ta gansu"
"Ai fa, an samu abun da ake so, an samu daular da ake kwaɗayi tashin farko an zubo yara biyu, yaran da aka ce babu kalarsu a danginmu"
Ummi ta yi dariya ta ce "Ai abun alfaharinku ne, kun samu iri a dangi. Kuma ƴaƴa biyu sai matar so ba kwaɗayayyi ba, abun alfaharinku ne, ƙaninki akwai himma, ko kuma maybe daga ni ce"
"Ummi ni ki ke gaya wa haka?"
"Ke fa ki ka fara, wai kwaɗayi? Ke in kwaɗayi ne kawai ya kawo ni gidan nan, da ban kai haka a cikinsa ba"
Noor tayi sallama, ummi ta amsa, ta miƙawa maryam yaran, maimakon ta karɓa ta ce "Ba shakka, dole mami ta ce akwai lauje cikin naɗi a wannan yaran, ba zata taɓa karɓar su a matsayin jikokinta ba"
Ummi ta ce "Noor mayar mini da ƴaƴana wurin Anty"Noor na fita ummi ta ce "Kar Allah ya sa ku karɓe su a matsayin jikokin, ku mayar da su in da suka fito, tun da ubansu ya san nasa ne shikenan.
Dama ni ban ce ta ƙaunace ni dole ba, tun da ba ku ku ka halicce ni ba. Ni yanzu a duniyar nan da a so ni da a ƙi ni duk uwar ubansu ɗaya.
Babu yadda ban yi ba wurin yi wa mami biyayya, da girmamata amma ba ta gani, a gaban uwata saboda rashin ta ido, take cewa wai yara ba na ɗan ta bane, da yake uwata ba zuciya ce a ƙirjinta ba ko? Maryam da zan baki shawara da kun daina jayayya da ikon Allah, ni da raihan ajiyar Allah ne mutu ka raba. Idan ku ka cigaba da takurawa aurena ko kun raba aurena da raihan, zan cigbaa da rayuwar aure da shi ina haihuwa ko da aure ko babu, dan a yanzu ba wani ƙalubale ko abun kunya da ba zan iya fuskanta ba.
Zaman gidan raihan, da zazzago ƴaƴa yanzu na fara, idan kin ga dama daga nan ki je wurin mami ki yi mini wani sharrin ke ta shafa da ke da ita"
Maryam ta miƙe ta ce "Ummi, mamin ki ke gaya wa haka?"
"Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba. Na yi iya yi na, na gaji, ba zan cigaba da cusa kaina in da ba a ganin kima ta ba. Kuma wallahi idan kuka cigaba da uzzura mini, hakkina zai fara bibiyarku ai ke ma mace ce, kuma a gidan wani ki ke aure, a sannu kema zaki haɗu da dai-dai ke".
Ta fice ta bar ta a ɗakin a tsaye.
Farida kuwa hankalinta ya tashi, saboda yadda ta je ta tarar da rahama, a asibiti, jikin yarinyar duk ya saɓule, haka na rahama cikinta, fuskarta da ƙafafuwan ta duk sun ƙone ƴan sanda sun kama mijin nata.
Ta din ga kuka tamkar za ta zare.
Ummi kuwa duk da furucin da Maryam tayi mata, ko a jikinta ta miƙe ƙafa ta cigaba da sabgoginta a gidanta.
Hausawa suka ci idan kana da kyau, ka ƙara da wanka, ummi ta san in dai ɓangaren kula da mijinta ne, to tana da kyau ba a magana a ɓangaren kula da raihan.
Amma duk da haka, maganar hausawa gaskiya ce, dan haka ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wurin lalubo lambar Amina Gachi, CEO beenad herbal center, mussaman ita da taɓa fama da ciwon sanyi, kuma galibi ciki ya kan tayar da ciwon, dan haka nemi Amina gachi, domin shiryawa koma wa ɗakin mijinta.
(Bari na baku bayani, beenad herbal center, ba iya maganin sanyi suka ƙware ba, suna bayar da magunguna daban-daban dai-dai da matsalolin ku, damun kawo daidaito a gidajen auren ku.
Suna da kaya kamar haka;
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL suna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kuka zaba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su.
Kayan mu tested and trusted ne
Suna maraba da masu siyan Daya ko sari
Suna Nan cikin garin kaduna
Kuma suna tura Kaya duk inda kike da yardar Allah
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975.
Da labarin abun da ya faru da rahama ya zo kunnen ummi, hankalinta ya yi mummunar tashi, dan sai da ta yi kuka, dan yadda Abdul ya gaya mata abun babu daɗin ji, ummi ta ce raihan ya bar ta je ta dubata, ya ce ba zata fita ba sai tayi arba'in.
Yaran raihan kamar ana hura su, dan baya wasa wurin kula da su, ummi na cin abinci mai gina jiki, da zai samar mata da ruwan nono, kunu masu kyau da kayan marmari, su kuma yaran ga isashshiyar madara yana saya, kan su yi arba'in suka cika ɓul-ɓul gwanin sha'awa.
Can gagarawa, aka samu wani irin maimakon ruwan sama, kamar da bakin ƙwarya, ga ƙarfi ga kuma iska hakan ya sanya rufin ɗakin iya kwashewa.
Dama dr. Ne ya bayar da kuɗi, a gyara mata ɗakin ta saka aka yi rufi ta karɓe sauran kuɗinta ta cinye, sai ledar ɗaki da ta saka.
Iska ta yaye kwanon, ruwa ya din ga zuba a kanta, ruwa ya jiƙa tsohuwar ƙasar da aka yi ginin ɗakin da ita, ita ma ta zube wani ya danneta, ban da katakon rufi da ya din ga ƙwalo mata a ka.
Gashi itakaɗai take kwana babu kowa a wurinta, dan haka babu wanda ya san abun da ya faru sai washegari.
Babu wanda yayi zaton za a ciro iya da rai, haka aka kwashe ta aka yi asibiti da ita, tamkar an jiƙa kaza a ruwa, ga jikinta duk ƙazantar zawon wahala da tayi, kan nan kamar an suɗe ƙwallon giginya, duk ta zama abun tsoro.
Su farida kuwa an kai ruwa rana, da su da mijin rahama a wurin ƴan sanda, dan kuwa ƴar kwananta goma sha ɗaya ta mutu, kasancewar uwarsa tana da kuɗi, sai kaiwa ta ke tana komowa a kan lallai sai an sake shi.
Ana wannan ƙadamin, su Alhaji Tahir suka kai kuɗin auren noor, aka saka watanni tara watan da za ta kammala karatun sakandare, za a yi bikinta da Salim.
Tun da aka saka auren nan, ummi ta dage wa noor da addu'a, tare da yi mata nasiha sosai a kan zamantakewa.
"Noor, bani da burin rabaki da anty farida mahaifiyarki ce, kuma komai ta yi miki, mahaifiyar ki ce. Abun da nake so ki sani shi ne, kar ki yadda wani ya ɗauki wani abu na tsafi ya ce miki ki yi wa mijinki.
Daga zarar abun ya karye, za ki ji kunya, kuma sai mushen kare ya fi ki daraja a wurinsa.
Noor Allah bai halicci namiji dan ya bi mace ba, mace ita ce a ƙarƙashin namiji, gwargwadon biyayyarki, gwargwadon mallakarki. Idan ki ka kwantar da kai, ki ka yi addu'a ki ka miƙa lamarinki ga Allah ki nemi aljannar ki da gaske, zaki juya namiji yadda ki ke so. Wasu abubuwan sai lokacin auren yayi zan gaya miki, babu ruwanki da ɗaukar shirmen ƙawaye su gaya miki abun da ba zai amfane ki ba.
Babu ke babu yi wa miji asiri noor, asiri ba ya tasiri, ko yayi na lokaci kaɗan ne.
Namiji kullum shi ne a gaba, dan haka ban da ɗaga masa murya, kuma ki fara yi muku addu'a samun zaman lafiya tun yanzu".
Noor ta jinjinawa ummi kai.
Hajiya kamar ta taka rawa, ganin a wannan karon Salim ya yadda zai yi aure. Kuma ta ji daɗin zaɓar noor da yayi, ko ba komai ta ga misali a kan ummi, ahalin gidan dr. Suna da tarbiyya.
Dr. Ya je gagarawa, ya duba Iya, sai dai aka tabattar masa da spinal code ɗin ta ya taɓu, ba zata ƙara takawa ba, komai sai dai ayi mata.
Dr. Ya tsorata da yanayin da ya ga Iya a ciki sosai da sosai.
Gashi babu wata cikakkiyar kulawa ta a zo a gani.
Bayan ya koma gida, ya tarar an dawo da rahama gidansa, a nan za ta yi jinya, da kamar ya ce bai yadda ba, kawai ya ƙyale su.
Ummi ta na ta Alla-Alla tayi arba'in, tana son ta je ta duba rahama, kuma ta duba jikin iya.
Sai dai shi Yallaɓai MD, lissafinsa kawai tayi ta koma turaka.
Da dr. Ya gaya wa Farida batun karɓar kuɗin noor, bala'i ta hau bala'i taƙi nutsuwa yayi mata bayani balle ta ji waye.
Hankalin kausar yayi mummunan tashi, jin an karɓi kuɗin auren noor, ita kuma ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko.
Ummi tana jikin raihan, tana ta zuba shagwaɓa, ta kalli fuskar sa tana ƙoƙarin tashi ta ce "Malam cikani na tashi, yarana jarirai ne, ba zaka haɗa ni da ƙajaga ba ban gama warkewa ba, ka sakani konika"
Yayi dariya ya ce "Ke matar so ita ce ke konika, ki yi wa duniya proving ɗin ke ɗin matar so ce ga raihan"
"Ni zaka yi wa wayo? Ai na riga na gama yi wa duniya proving ni ɗin ɗaya ce a zuciyar mijina"
"Wallahi faɗi ki ƙara faɗa, ni kyautar da Alhaji yayi miki ni na so yi miki ita, wata gigitacciyar kyauta nake son yi miki".
"Ni ba na son kowace kyauta, wuri nake son ka ƙara gyara mini a zuciyarka na miƙe ƙafata"
Raihan ya ce "Kin samu, ba kowa a ciki sai ke Salmana, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya ƙaro miki lafiya, ki yi ta haifo mini ƴaƴa"
Riƙe hannunsa tayi tana dariya ta ce "Ni zaka yi wa wayo, wai ba zuwa ka yi kana cewa ba ka da lafiya ba?"
Ya kwashe da dariya ya ce "Duk cikin neman hanyar tsira ne, bani da lafiya idan har ba tare da ke nake tare ba, ni a idona duk wata mace idan ba Salmana ba ba zata taɓa zama ɗaya da ke ba. Ke daban ce a kowane fanni".
Kalaman jinjina da girmamawae da yake yi mata, ya sanyata jin kamar ta fi kowace mace sa'a a rayuwarta.
***
Idris da sasassafe yana ta shirin fita zuwa karɓar wani kuɗi, sai faɗa suke yi da hindu suna zage-zage kamar ƴan tasha a kan kuɗin cefane.
Sallama aka yi a waje ya fita, ya tarar da ƴansanda a tsaye, ba su yi wata-wata ba suka cafke shi suka tafi da shi. Babu wanda ya san in da yake, dan babu wanda ya san kama shi.
Sai da aka je wurin ƴan sanda, wai ana tuhumarsa da yi wa wata yarinya fyaɗe, an tsinci yarinyar a hanyar makarantar islamiyyar su, an yi mata fyaɗe an kasheta, wai shi ake zargi saboda hanyar wucewarsa ce, kuma an san halinsa na biye-biye yaran mutane.
Farida na tsaka da jinyar rahama, ɗakin da take ƙonuwa sai wari take yi, duk da yadda ake