x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 35 - CUTARWA

  • 102001 words
  • 105000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 532

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya ƙudirci a watse ya samu Alhaji.


Ayshercool
0808012143
What's app only please 🙏
                      *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P27

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

27

Mami har ta yinƙura za ta bi bayansa, amma Alhaji ya hanata, mami tamkar ta taka rawa, tana kallon fuskar Hajiya, ko zata ga damuwa ko ɓacin rai a fuskarta.

Amma sam bata ga hakan ba, sai ma fatan alkhairi da take ta yi wa raihan ɗin, su kansu su Salim ko a jikinsu, sai dai Salim ya ɓata fuska ya kalli Alhaji ya ce "Yanzu idan muna buƙatar wani abun sai mun je wannan yaron ƙanin bayanmu ya yarje mana, ni bani da matsala da koma me ka bashi, amma wallahi ba zan je wurinsa neman abu ba, a nemi wani abun kawai"

Sagir ya ce "Balle kuma ni, da yayi niyyar dukana, sai dai ace na daina morar komai a gidan nan, da dai ace in je in sake neman wani abu a wurinsa wallahi"

"Sagir....

"Shhhh" ita ma Alhaji ya hanata yi masa magana, duk ya ce su rabu da su.

Raihan wuri ya samu yayi zamansa, gaba ɗaya ransa babu daɗi, saboda sam bai yi farinciki da wannan al'amarin ba.

Har kusan sha ɗayan dare, babu wanda ya san in da raihan ya yi, Alhaji kuma yana falo yana jiransa, dan ya san a daren dole zai dawo ya neme shi.

Aikuwa sai ga shi yayi sallama ya dawo, da ya tabattar kowa ya watse.

Alhaji bai ɗago ya kalli raihan ba, har ya zo gabansa ya zauna, a hankali ya ce "Alhaji"

"Ka dawo ka ce mini ba zaka yi aikin bane ko? Ba ka so na nemi wani, kaima da nake jin daɗinka zaka fara bujure mini"

Jiki a sanyaye raihan ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba Alhaji, yayi mini nauyi da yawa, ba zan iya ba wallaahi kaima ka san na yi ƙanƙanta da wannan al'amarin, kuma nine ƙarami kar yayyena su ji babu daɗi a kan hakan"

"Raihan"

"Na'am".

"Ba lokaci ɗaya kuma kai tsaye na yi assigning ɗin ka a kan wannan matsayin ba, na yi addu'a, kuma na jarrabaka ta kowane ɓangare, kai ɗin ne dai zaka iya, yara nawa Allah yake ɗaukakawa wanda suka kai ka, da wanda basu kai ka ba ma? Wani a waje bare ka ke so na ɗaukko na danƙa masa ragamar dukiyata da kula mini da ku? Ko kuma wannan yayyen naka da ba su san ciwon kansu ba? Ka sani ko takaicin abun da na yi musun, ya sanya su shiryu? Hajiya ce ta bani wannan shawarar, kuma na ga hakan ne ya dace"

Raihan ya kalleshi da sauri, ya ce "Hajiya ce ta ce ka bani ragamar kula da harkokinka?"

Alhaji ya jinjina masa kai, raihan ya yi shiru yana tunani, ya san da mami ce sai dai ayi mutuwar kasko kowa ya rasa, da dai ta yarda ko ta bayar da irin wannan shawarar.

Maganar Alhaji ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi "Babban mutum, kar ina yabonka salla ka kasa alwala mana, kar ka watsa mini ƙasa a ido, i will always be by your side, duk abun da ba ka gane ba, ko abun da ka ke buƙata i will assist you like a ghost" yayi maganar yana dariya, wanda raihan ma yayi murmushi.

"Alhaji ka ɗaureni da jijiyoyin jikina, kana faɗar maganar nan na ji kamar ka sakani a kurkuku".

Yayi dariya ya ce "Ba wata kurkuku, ka san babban abun da ya burgeni? Da ka yi offending ɗan uwanka, ka dawo ka bashi haƙuri, ka hana abun da ya faru yin tasiri a cikin gidan nan, da kuma tsakanin iyayenku mata".

Raihan ya jinjina kai ya ce "Ummi ce ta bani shawarar yin hakan ai, ba idea ta ba ce".

Alhaji ya sake dubansa ya ce "Wace ummi kuma?"

"Baka santa ba, ƙawata ce bari ne je na kwanta Alhaji, idan na yi bacci wataƙila kaina ya daina ciwon".

"To Allah ya bamu alkhairi, zan saka ranar yi maka walima tare da abokan hulɗarmu da ma'aikata, da gabatar da kai a matsayin sabon MD".

"Alhaji riƙon ƙwarya fa ka ce, ko dai wayo ka yi mini?"

"Tashi ka tafi sai da safe" kamar soko raihan ya tashi ya bar ɗakin ya nufi ɗakinsa.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya tsaya ya ɗaga.

"Ƙaraso sashina ina son ganinka" ya sauke hannunsa shi ko son yin wata maganar baya yi.

Ya koma ya nufi sashin mami, tana falo tana jiransa, "Mami, baki yi bacci ba?"

"Ya za ayi na yi bacci, zaka yi mana sagegeduwa, ai bacci bai kama ni ba, dole na din ga bacci da ido ɗaya. Uban me ka je ka cewa Alhaji?".

Kai tsaye raihan ya ce "Ce masa na yi ya taimaka ya saukeni daga muƙamin nan".

"Saboda ba ka da hankali ko? Allah ya ƙwaci abun ya baka, sai ka ce ba ka so saboda shashasha ne kai raihan?"

Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya.
Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba.

Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta.

Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya ɗagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo ɗakin.

Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya.

"Ke!" Ta daka mata tsawa, ummi ta ɗago da sauri, ta ja hijjabi ta saka.

"Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare" kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi.

Da "To" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen.

Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai.

Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa.

A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki.

Missed calls ɗin raihan ta tarar, da message "Call me when you are available"

Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce "Ka kyauta raihan".

"Da na yi me?"

"Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?"

"A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban".

"Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious"

Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa"

Sai kuma ta nutsu "Wace irin damuwa kuma?"

"Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki"

Ummi ta ce "Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini"

"A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo"

"To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?".

"In sha Allah, sai da safe" suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi.

***
"Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so"

Rakiya ta ce "Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar ƴaƴan can gaba ta kai ki Bilki".

Mami ta ce "Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa"

Yaya rakiya ta ce "Ke bilki"

"Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuɗi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma"

"Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haɗa shi da Safiyya, ayi ƴar gida kawai"

Mami ta ce "Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma'aikatan su girmama shi"

Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci.

***
Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya.

"Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya"

"To ai kai ɗin ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD" hararta yayi yana kallon wayarsa.

"Attention" tayi maganar tana kallon sa.

Ya juyo yana kallonta shi ma "Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne" ya haɗa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido.

Ummi ta ce "Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haɗa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane.
Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma'aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah.
Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi.
Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan"

Jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa.

"Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala"

"Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A'a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji"

Yayi shiru bai ce komai ba.

Ta ce "Ka ce to mana"

"Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne".

Ummi ta ce "Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka" tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur.

"Ɗauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane"

Da mamaki ta kalleshi ta ce "Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daɗi ba" tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office ɗin su, da ya burkice sai da ya bata tsoro.

Ya tashi tsaye ya ce "Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya" ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin.

Sai da ya fita manager ya ce "Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?"

Ummi ta ce "Rigima kawai yake ji"

"Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba".

Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba.
Abokan hulɗar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san yaro ne.
Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa.

Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara'a, ta saka shi a status da caption na "Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan"

Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what's app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?.

Ummi ta yi mata reply da "Shi ya gaya mini".

Maryam ta ce "A ina ku ka haɗu ya gaya miki?"

"Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne".

Ta yi reply da "Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala" Ummi ta daɗe tana jujjuya message ɗin, ita mutum nawa ne ma a what's app ɗin nata. Ta ga ita kanta maryam ɗin, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge.

Tamkar jira yake ta goge, ya ce "Meyasa ki ka goge status ɗinki?"

"Bakomai".

"Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?".

Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce "Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka
End Ads