Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa.
A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin "Idirs meye haka?"
"Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?"
"Kai za a cewa dabba, ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa"
Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo.
Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faɗin "Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?"
Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun bakinta ya gauraye da jini".
"Ita kuma wannan meya sameta?"
"Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris.
Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya.
Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita.
Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani.
Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai.
***
Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure.
Tana bawa mama labarin ƴar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa.
Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ƴar jummai a kai a bawa ummi ba.
Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ƴar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuɗi mijinta ɗan sanda ne, idan suka haɗu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta.
Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa "Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan"
Mama ta ce "Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu"
Jimmai ta ce "Ashsha! To Allah ya kyauta".
Mama ta amsa da "Amin"
Mariya ta ajiye ninkin, ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka.
Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce "Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini" shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba.
An doshi shekaru huɗu, da rasuwar Bashir, ummi ta cigaba da rayuwa ba tare da ta sake sanya idonta ana mahaifiyarta ba, tamkar baiwa a cikin gidan nan haka take rayuwa, babu gata babu kulawa, wahala ta yau daban ta gobe daban, ga Iya ta tsiri yi mata kunu ranar asabar da lahadi ta kai kasuwar garin, ta sayar mata, har ma wasu su yi abun sayarwar su a gidan su haɗa mata.
Babu yadda Hashim bai yi da iya ba, a kan ta daina ɗorawa ummi tallar nan, azabar da take sha tayi yawa, amma iya ta zage shi tsab, ta ce idan ya cigaba da yi mata katsalandan, za ta ci mutuncinsa ta tsine masa.
Babu kunya ba tsoron Allah, Iya ta saka aka ɓalle ƙofar ɗakin mariya, aka kwashe kayanta aka sayar, ta karɓe kuɗin, wai da su zata tarawa ummi kayan ɗaki, ɗakin ya zama wurin tara itace, hatsi da sauran shirgi.
Ummi ta dawo daga makarantar boko, takalminta ya kusa rabewa biyu saboda tsufa ƙasansa kuwa ya huje, malaman su, sun gaji sun ƙyaleta, ƙafarta futu-futu. Ta tarar da Iya a tsaye tana jiran isowarta.
Jiki a sanyaye ta ƙarasa in da Iya take, ta ce "Iya laifi na yi ne?"
"Au tambayata ma ki ke yi, saboda tsabar kin shahara, nan gaba makami zaki fara nuna mini, ki yi mini ƙwace, kuɗina zaki bani da saminu ya zo jiya da daddare, ban gan su ba, kuma daga ni sai ke a ɗakin"
Gaban Ummi ya faɗi, ta girgiza kai ta ce "Wallahi iya ban ɗauka ba, ki sake dubawa".
"Ni ki ke gaya wa na sake dubawa? Ƙarya zan yi miki kenan? Ki zo ki bani kuɗina kan jikinki ya gaya miki"
Ummi kawai tayi shiru tana kallon iya, dan ta rasa me za ta ce mata ma, ta san kawu saminu ya bata kuɗi jiya, amma ba ta san ma a ina ta ajiye su ba.
"Au saboda kin mayar da ni ƴar iska ki ka tsaya kina kallona, ba zaki bani kuɗina ba?"
Ummi ta sunkuyar da kai, dan gaba ɗaya kanta ya kulle.
Iya ta saɓa mayafi ta fice, jiki a sanyaye ummi ta ƙarasa cikin ɗakin iya, ta hau duddubawa, ko za ta ga in da Iya ta ajiye kuɗin.
Maganar Iya ta jiyo da idris ta ce "Ka tambayeta ina ta kai mini kuɗi, ka yi ta dukanta, har sai ta faɗa" kan ummi ta ankara sai ganin idiris ta yi a kan ta, hannunsa riƙe da manyan reshen bishiyar darbejiya.
Kafin ta yi magana, ya shiga shimfiɗa mata tsumagiyar nan a jikinta, gashi ya tare duk wata hanya da zata bi ta fita. Kasancewar dama haushinta yake ji, ya sanya ya zage duk wani ƙarfin sa, ya dinga jibgarta, har da taka ta da ƙafa.
"Fito mini da ita daga ɗaki, ɓarauniyar banza da ta wofi, kuma daga yau kin bar kwanar mini a ɗaki" a ƙasa haka ya din ga jan ummi, ya fito da ita tsakar gida.
"Ga ɗakin uwarta can da ake tara itace yanzu, rufe mini ita a ciki, ko abinci kin daina ci, sai kin bani kuɗina"
Haka kuwa aka yi, idris ya rufe ummi a ɗakin mariya, da yanzu ake tara itace da hatsi a ciki, ya rufe ɗakin bisa umarnin iya.
Ummi ta kwanta a ƙasa, jikinta sai zafi yake yi, hannunta da Idris ya din ga hauri da ƙafarsa, tamkar ba a jikinta yake ba, hannun yayi sanyi ga ciwo yana yi nata.
Sai da ummi ta kwana ta wuni a cikin ɗakin nan, shima magaji ne ya ga baya ganinta, ya matsa da tambaya, su Alhassan suka ce masa ai Iya ta sacewa kuɗi dubu goma sha biyu, ta saka idiris ya zane ta, aka kulle ta a ɗaki.
Hashim ya ji kamar ya ɗora hannu a ka yayi ihu, ya buge kwaɗon, ya tarar da ummi a zaune a takure wuri ɗaya, saman idonta ya kumbura, ko ina jikinta rauni ne. Dogon gashin nan duk ya kwashi datti da karare.
"Ummi" ya kira sunanta, ta ɗago ta kalleshi ta sunkuyar da kai.
"Da gaske kin ɗaukar wa iya kuɗi"
Ta girgiza masa kai, ya ce "Na san ba zaki ɗauka ba ummi, yi haƙuri taso ki fito"
Ta girgiza masa kai ta ce "Dan Allah yaya magaji ka ce Allah ya sa na mutu, bana son zama da iya, dan Allah ka kai ni wurin mama, wallahi zan mutu" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.
Ya kalleta yarinya shakaf, amma tana iƙirarin ta mutu, "Ba zaki mutu ba, wuya bata kisa ummi, tashi kar wani abun ya cije ki" Da ƙyar ya fito da ita daga ɗakin.
Iya kuwa duk ta gama barbaɗawa mutanen gidan ummi ta sace mata kuɗi.
Ko kallonsu Iyan ba ta yi ba, ya nemo abinci ya bata, ya ce tayi wanka.
Tana banɗaki, Hashim ya samu Iya ya ce "Iya dan Allah meyasa ba kya ƙaunar ummi ne?"
"Kamar yaya, in haifi ubanta ka ce bana son ta? Tarbiyya nake bata, uwarta na tsana ne, bana ƙaunar uwarta ne, kuma alamu sun nuna halin uwarta ta yi"
"Ba wannan ba, Iya kin duba ɗakin nan da kyau baki ga kuɗin ba? Ummi bata taɓa yi miki sata ba fa?"
"In ji uban wa? Faɗa ne kawai ba na yi, amma sata kam ba yau ta fara ba, kamar ta sha nonon ɓeranya"
Zai yi magana ummi ta fito daga wankan, tana ɗingisa ƙafarta.
Bai cewa iya komai ba, ya tashi ya bata kujera ta zauna, ya kamo hannunta da ya kumbura, ya fara matsawa a hankali. Nan ta din ga yarfe hannu tana kuka.
Fatar ummi duk wannan wahalar da take sha, jikinta tamkar auduga saboda taushi.
Iya ta watso mata ƙullin kayanta, ta ce sai dai ta koma ɗakin itace ta cigaba da zama.
Babu magiyar da magaji bai yi mata ba, amma ta ce bata san zancen ba.
Da kansa ya share wa ummi ɗakin, ya samo buhu ya shimfiɗa mata, ya kawo tabarma ya shimfiɗa mata, ya din ga rarrashin ta, yana bata haƙuri, ji yake kamar ya zauna ya yi wa ummi kuka.
Iya ta aika a kirawo mata Alhassan zata aike shi, ta ce ya duba ƙasan katifarta ya ɗaukko ɗari biyu, Alhassan ya fito da wata leda a hannunsa ya ce "Iya ba wannan kuɗin ki ke nema ba?"
A razane ta karɓa tana ƙifta masa ido, gaba ɗaya ta manta ina ta ajiye su.
Hashim yayi kamar bai ji me ta ce ba, haka ummi, sarai ummi ta ji Alhassan yana gaya mata kuɗinta, duk wasu kalaman rarrashi, sai da Hashim yayi amfani da su, wurin ba wa ummi haƙuri, saboda ƙarfin hali, har da Murmushin ta, tare da ƙoƙarin nuna bakomai.
Da daddare ya sayo gyaɗa da rake, ya kai wa ummi, duk cikin son ya ƙara rarrashin ta, ya daɗe yana sake kallon ɗakin da zata kwana a ciki, babu ko fitila a ɗakin, kuma ba za a rasa ƙwari masu cizo a ciki ba.
Ya kalli ummi ya ce "In sha Allah zan sayo miki fitila, sai ki din ga haskawa, sannan tun yamma ki din ga karkaɗe ko ina, ki tabattar babu wani abu a ɗakin kan ki kwanta".
"To yaya na gode" ya jinjina mata kai ya fice.
Iya tana kallonsa daga tagar ɗakin ta, yanayin yadda yake shishshigewa ummi, abun ya fara ƙular da ita, dan haka tayi ƙwafa, tare da aniyar ɗaukar mataki a kansa.
Sai dai can ƙasan ranta, ta ji babu daɗi ganin kuɗin da aka yi, gashi ta riga ta saka an zane ummin, an rufeta a ɗaki kwana da wuni, ba tare da hakkinta ba. Haka nan abun ya din ga damunta, da safe ummi ta je har ɗaki ta gaisheta, da uniform za ta tafi makaranta.
"Kin karya ne zaki tafi makaranta?"
Ummi ta ce "A'a"
"Ki je wurin sa'adatu ta zuba miki kunu idan ta dama" ummi ta ɗan yi shiru ta tuna yadda sa'adatun ke haɗe rai idan ta je karɓar kunun.
Ummi ta ce "Na san idan na je ya ƙare"
Iya ta bankaɗa ɗan tofinta, ta ciro naira ɗari, ta ajiye wa ummi ta ce "Gashi nan ki sai waina a hanya ki ci"
Ummi ta kalli kuɗin, tana wani irin murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta miƙe tsaye idonta fal hawaye ta ce "Ki bar shi iya, idan na dawo na ci abincin" tayi waje.
Tana jin Iya na zazzaga mata masifa, tana zaginta, amma tayi waje tana share hawaye.
"Ƴar ƙanƙanuwarki da ke, kin san munafunci, to kin yi wa kanki, halin uwar taki da nake ta gudu sai da ki ka kwaso shi? To ki ci kanki, da ke da mugun halin naki" Haka iya ta cigaba da sababi da kame-kamen borin kunya.
Ummi na tafe a hanya tana kuka, haka ta ƙarasa makaranta, suna ta shirye-shiryen shiga sakandare, sun kusa zana jarrabawar common entrance, shi ma kuɗin jarrabawar da ƙyar, ta biya, shi ma Naima ce ta zo gida, ta sa aka kirawo ta, take ta yi mata tambayoyi da ƙyar ta gaya mata batun kuɗin jarrabawar.
***
Manema na ta zuwar wa mariya, duk da ba fita take yi ba, amma mariya tayi burus, mahaifinta ya kaɗa ya raya, amma taƙi tsayar da kowa, da yayi mata zancen auren ma sai ta hau koke-koke.
Yayi ta rarrashin ta, a tunanin sa ko saboda tsohon mijinta ya sanya take jin ba zata sake yin aure ba, yayi nasihar, yayi rarrashin saboda kusan shekaru huɗu kenan rabonta da aure.
Kuma shekarun nan huɗu cif, ita ba mai lafiya ba ita ba mara lafiya ba.
Takura mata da maganar aure, ya sanya ta daina cin abinci ma, ta ƙara tsananta kaɗaice kanta, ga rashin barcci da ya sarƙafe ta, ta wuni ciwon kai dare yayi ta kasa bacci.
Tsananin ciwon kai ya sakata a gaba, gashi tayi shiru ba wanda ta gayawa, abu kamar wasa tun tana daurewa har ta kasa, ta din ga burgima a ƙasa tana wayyo kanta.
Sai a lokacin suka san ba ta da lafiya, aka kaita asibiti, sai dai babu cigaba, idan an kaita asibitin sai an tursasata shan magani, idan ta sha ɗin ma babu cigaba, wasu lokutan haka zata riƙe kanta tana ihu, tana kuka saboda rashin iya bacci, idan aka kaita asibiti sai dai su yi ta yi mata allurai.
Ƙarshe aka tura su ganin likitan ƙwaƙwalwa, hankalin mahaifin mariya ya tashi da ƴan uwanta, jin an tura su ɓangaren likitan ƙwaƙwalwa.
Likita ya duba ta sosai da sosai, ya basu shawarar a kula da ita sosai, saboda depression ne ya kamata, idam ba a kula da ita sosai ba, za a rasa hankalinta gaba ɗaya.
Karo na farko da iyalan su mariya suka ji mahaifinsu yayi wa wani ɗan adam Allah ya isa, wanda sai da ya zubar da hawaye, yana matuƙar tausaya wa mariya, dan haka bai gaza ba, ya sake tashin yaya magaji, tare da Maryam, ya ce su je su bawa uwar mijin mariya haƙuri, ko sau ɗaya ta bayar da ummi, ta zo ta kwana biyu tare da mariya, ko a samu hankalinta ya kwanta.
Yaya magaji ya ce "Baba, ka san matar nan ba zata bayar da yarinyar nan ba, sai dai a tafi da mariyar, ta je ta ganta mu dawo"
Maryam ta ce "A hakan zamu tafi da ita? Ba zai yiwu ba ai, kana kallon abun da take yi, ai salon ta sake jin daɗi ne, dan matar nan ba mutunci ne da ita ba, kuma muddin aka bawa mariya ummi, ba zata bari a sake rabata da ita ba, a ganina kawai mu mayar da hankali a kan nema mata lafiya"
Yaya magaji ya ce "Duk da haka, zan jarraba zuwa, duk da na san ba zamu wanyeta ƙalau ba, amma zan jarraba zuwa na ga yarinyar ma daga nan, Allah sarki ummi, na san yanzu ta yi wayo sosai.
"Zata shekara goma zuwa sha ɗaya fa yanzu, ai ta zama budurwa"
Suka bar maganar a kan cewa, yaya magaji zai je ya gano ummi, idan ya ga fuska ya sako zancen tahowa da ummi.
Ummi ta daina zuwa ɗakin iya idan ba dole ba, saboda gudun kar ace ta yi wani abun, kullum cikin itace nan da buhhunan hatsi take kwana.
Tsabar daka kuwa hannunta duk yayi kanta, yayi ta ɗurar ruwa yana fashewa, saboda tana da taushin fata sosai.
Tana tafe tana yada hannu, saboda gajiya ga rana, yunwa da ƙishirwa duk sun addabeta, mutumin da ta hango a ƙofar gidan su ne tare da kawu Ilyasu, ya sanya ta tafiya a hankali, ta ƙarasa ƙofar gidan.
Shi ma ƙuri yayi da ido, yana kallonta, ta ƙarasa ta durƙusa ta ce masa "Ina wuni?"
Jiki a sanyaye ya amsa ya ce "Ummi kin gane ni?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To waye ni?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Ina mama?"
"Haryanzu baki manta da ita ba?"
Da sauri Ummi ta sake kallonsa ta ce "Da ita ku ka zo?"
"A'a, na zo dai neman alfarmar na tafi da ke na kai ki wurinta, amma sun ƙi yarda"
Kawu Ilyasu ya wani haɗa rai, cikin haushi kamar tsohon kare ya ce "Ke! Tashi ki wuce ki shiga cikin gida"
Ƙafafuwanta suka yi mata sanyi, ta ji tamkar ba zasu iya ɗaukarta ba"
"Ba zaki tashi ba?" Ya sake yi mata tsawa. Cikin rawar jiki ta tashi, yaya magaji ya kamo hannunta ya danƙa mata kuɗi, yana riƙe da hannunta ya kalli Kawu Ilyasu ya ce "Da ku da mahaifiyarku, ku shirya amsar da zaku bawa Allah, kalli wai wannan ƴar ɗan uwanku ce dan abun kunya, kalli kayan makarantar da suke jikinta, kalli ƙafafuwanta. Kun ce idan na tafi da ita babu ku babu ita, ku ba dangin mahaifinta bane ba, duk in da aka je aka dawo, da dangin uba ake ado, kuma ba zan cigaba da jayayya da ku ba, muna raba abun faɗa, Allah zai zama gatan marainiya"
"Ummi ki kula da kanki kin ji ko? Ki yi ta yi wa mamanki addu'a, hankalinta yana kan ki, Allah ya yi miki albarka".
"Wai ba zan sake ganinta ba?"
"Zaki sake in sha Allah, Allah ya shiga lamarin ki"
Rirriƙe hannunsa tayi tana kuka, tana yi masa magiyar ya tafi da ita.
Da ƙarfin tsiya kawu Ilyasu, ya fizgi hannunta, ya angizata zuwa cikin gida.
Tana kuka suka ƙarasa shashinsu, sai dai da munanan kalaman iya ta fara cin karo, tana ɗaga murya tana cewa "Ni dai azo a nema mini magani, a rabani da wannan dangin maitar da jaraba, sun