ce a wannan lokacin, ba ta buƙatar sana'a a saya mata kadara kawai.
Duk yadda mami ta so yin abun da za ta ƙure raihan, ta shiga hakkin ummi, raihan sai ya zille, ta yi masa faɗa ta zage shi, ko a jikinsa.
Babban abun da ya ba ta takaici, bai wuce tana tsaka da duba saƙonni, ta ga raihan yayi status da special whats app ɗin sa, da ba kowa ne ya san shi da shi ba, galibi family ne kawai ke da lambar.
Hoton Ummi ya saka, tana zaune a kan dining, ta naɗe kanta da mayafin doguwar rigar jikinta
"My perfect woman, khairun nisa'i, Allah ya ƙara miki lafiya"
Ya sake rubuta "Goodnight ƴar aljannata"
A fili ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, bazawarar wannan mummunar"
Hankalin Safiyya ne ya koma kan mami, dan kuwa mami ta sanya safiyyan dawowa gidan da zama.
"Mami menene?"
Ta miƙa mata wayar, bayan ta nemo status ɗin raihan.
Gaban Safiyya ya faɗi, duk yadda ake koɗa munin ummi bai kai nan ba.
Mami ta din ga zage-zage, tana cewa an asirce mata ɗa.
Sai da ta jera kwana biyu tana kiransa ya je tana nemansa, amma ya ce mata ai aiki yayi yawa a office, baya samun isasshen lokaci, alhalin rabonsa da office ɗin tun saura sati biyu bikinsa.
Asabar ce suna baccin safe, kiran Alhaji ya tashe su, raihan ya ɗauka cikin jin nauyinsa.
"Ango ka sha ƙamshi"
"Alhaji ka dawo kenan?"
"Eh na dawo, baka nema na ko?"
Raihan ya ce "Haba dai wane ni"
"To yaya ƴar tawa?"
"Gata nan tana jin ka, ta ce a gaisheka kan mu zo"
"To dan Allah ace mata ina roƙon arziki, a taimaka a bar mini kai ka koma office, ana ta kirana a waya ana nemanka"
Raihan ya ce "To za a gaya mata, amma na zata saura sati biyu sannan na koma"
Alhaji ya ce "A'a babban mutum, a duba mini lamarin nan"
Raihan ya ce "Zan shigo in anjima in sha Allah, sannu da zuwa"
Alhaji ya sauke wayar yana murmushi ya ce "Lallai babban mutum, ka ci gidanku da sati biyun"
Mami da ke kusa da shi ta ce "Kana nufin ba ya zuwa aiki dama?"
"Da sabon auren zai fita aiki? Lallai wato ni ya mayar shashasha, idan na ce ya zo sai ya ce mini wai aiki ya yi yawa".
Alhaji ya kalleta ya ce "Ya zo yayi miki me? Ango ne fa"
A fusace ta ce 'Angon banza, bazawarar?"
"Ba mace ba ce? Ke ina ruwanki ne, Bilkisu ki kiyayi shiga shirgin yaran nan kin ƙi ko? Zaki yi ta fama da takaici kuwa"
Haushi ne ya ishi mami, tare da yi wa kanta alwashin, dole ta san abun yi a kan raihan da ummi, tun da tun ba aje ko ina ba, kansa yana rawa.
Ummi sai magiya take yi wa raihan, ya tafi da ita ta gaida Alhaji, ya ce mata sai an kwana biyu.
Ta ja gefe ta kashingiɗa a kan kujerar da suke ta ce "To ka tashi ka je ka yi masa sannu da zuwa"
"Sai anjima" yayi maganar yana ɗora ƙafafuwan ta a kan cinyarsa yana matsa mata.
Ta buɗe datar ta, taga messages da yawa sun shigo, ta din ga mamaki dan ita wanda take chatting da su ba su da yawa.
Group ta ganta a ciki, na ƴan makarantar islamiyyar su ne, kuma ta ga ana ta tagging ɗin ta, banda messages da ta gani ta private.
Voice messages ta fara buɗewa, ta din ga jin saƙonnin zagi da ashar, wai saboda ta auri ƙanin maryam, ana ta cewa ta yi asara.
Kashewa take ƙoƙarin yi, ta ajiye wayar, ya karɓe wayar, ya cigaba da saurarar abun da suka ce, tare da duba messages ɗin duk da suka yi.
Tun tana jure jin, har ta karaya ta fara kuka, saboda cin zarafin yayi muni.
Wayarsa ya ɗaukko, ya danna ya kara a kunnensa.
"Zan turo maka wasu lambobi, ayi tracking ɗin su duk in da suke dan Allah, zan biya ko nawa, zan turo maka wani abu"
Ya ajiye wayar ya kalleta ya ce "You don't need to cry anymore, zan yi dealing da duk wanda ya ce zai saka ki kuka ko waye shi" daga haka ya tashi ya fita.
Gaba ɗaya jikin Ummi yayi sanyi matuƙa, zagin da suka yi mata yayi mata zafi, tun da suka bar islamiyyar suka yi aure babu wadda ta sake neman ta, sai yanzu da suka sakata a group na makarantar suka ci mata mutunci, da dawo da abubuwan da suka faru a baya, wai tana yawo duk da dauɗa ga muni, dan son zuciya ta auri ƙanin ƙawarsu.
Hankali kwance raihan ya je gida, ya shige wurin Alhaji, Alhaji ya din ga ce masa yayi ƙiba ya ƙara kyau.
Nan suka tare a sashen Alhaji, har da Hajiya da Salim.
Mami ce ta kira shi hankali a tashe ta na tambayar sa yana ina. Ya bata amsar yana sashin Alhaji.
Ko mintuna uku ba ayi ba sai gata, ba ta damu da su hajiya da suke zaune ba, ta nufi raihan tana neman ta kai masa duka.
Alhaji ya miƙe ya ce "Bilki meye haka?"
"Aure hauka ne? A kan me zai sanya ƴan sanda su kama matan mutane? Maryam ta kira ni tana kuka, an kama su an kira shi a waya yaƙi ɗagawa, uban me suka yi maka?"
"Matata suka zaga babu dalili, tsakani nake so ayi musu, kar su zagar mini mata, ba tayi abun kunya ba dan ta aureni"
"Ni ka ke gaya wa haka raihan?"
"Mami ba da ke nake ba, ba kuma da wata manufa na faɗa miki ba, ni na saka ummi ta aureni, idan na zuba ido ana cin zarafin ta, ban yi mata adalci ba".
Hajiya ta yi murmushi ta ce "Allah mai ƙudura, ɗan so ya faɗa hannun matar so, ko dai ki bi a hankali ko ki rasa shi gaba ɗaya"
Ayshercool
08081012143
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
39
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
*Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani*
39
Alhaji ya ce "Jidda ya haka ne? Wace irin magana ki ke yi kuma?"
Hajiya ta ce "Kaga ƙyale ni na faɗa, ai a baya ban taɓa yi ba, sai mu gani idan dabarar mutum za ta ƙwace shi, me aka yi da maza ko sati uku ba a rufa ba fa? Baki ga komai ba"
Mami kuwa kumfar baki ta din ga yi tana cika baki, Salim ya tashi tsam ya fice, dan baya son hayaniya, hajiya ma ficewa tayi ta bar ɗakin.
"Ka gani ko ka ga abun da ka janyo mini ko?"
Kamar raihan zai fashe da kuka ya ce "Mami me kuma na yi?"
Alhaji ya ce "Raihan bai yi miki laifin komai ba, ke ki ke ƙoƙarin koya masa rashin gaskiya, da kuma raina ki, wuce ka jirani a mota, mu je a kashe wancan case ɗin da ka ɗaukko" Raihan ya fita yana satar kallon mami.
Alhaji ya sake mayar da idonsa kan mami ya ce "Gaskiya hajiya ta gaya miki, na sha gaya miki mu maza idan muna kan wannan gigin da rawar kan, ba a cewa za a tanƙwaramu ta ƙarfin tsiya, ko da kuwa iyayen da suka haifemu ne, ke meye ban yi ba a kanki?
Ko kin manta yadda na ɗauke ki, na bar ƙasar sama da wata uku na bar hajiya, na toshe kunnena, na ƙi saurara kowa sai yanzu dan abun ya zo kan ɗanki ki ce ba ki san zancen ba? Shiyasa a kowane ƙadami ake so ka zama mai adalci, ko dan gaba, baki nuna mini illar abun da na din ga yi ba, sai daga baya da na gane kuskurena dan kaina, ka kwanta da mace kawai ba shi ne aure ba, wannan abu ne na lokaci, managarciyar mace mai tsoron Allah, da kuma biyayya ita ake fata. Amma idonki ya rufe dan ɗanki ya auri bazawara, sai me qualities ake dubawa ga mutum mai hankali, ba wai abun da ku ke tunani kawai quality na mace ba" da farko faɗa yake yi mata, daga bisani kuma ya koma nasiha, ya gama ya fice daga ɗakin ya bi raihan.
Ko kaɗan mami ba ta ji nasihar Alhajin ta shige ta ba ma, babban burinta a yanzu kawai, shi ne raba ummi da raihan tun kan ta kanainaye shi gaba ɗaya.
Ba dan tare da Alhaji raihan suka je station ba, da sai raihan ya ja case ɗin, dan kuwa babbar headquarter hukumar ƴan sanda yasa aka kai su, kuma ya tafi da wayar ummi a matsayin shaida.
Alhaji ya ce wa raihan, ya kai shi gidansa, yana son yin magana da shi da ummi gaba ɗaya.
Suna tafe yana yi wa raihan nasiha.
"Babban mutum, na son kana son matarka, amma ka yi ƙoƙari ka din ga ɓoyewa saboda mahaifiyarka da bakin sauran mutane, ka san kishin mata ba lallai sai tsakanin kishiyoyi ba, su ba sa raina abun yi wa kishi, sannan ka yi ta haƙuri kana cigaba da addu'a komai zai wuce, amma matarka ka riƙe ta sosai ka kula da ita"
Raihan ya jinjina kai, suka ƙarasa gidan sa, tun da raihan ya kirata ya ce mata tare za su zo da Alhaji, ta gama girki, amma ta shiga ƙoƙarin ƙara wasu abubuwan.
Tun da ya zo kanta a ƙasa yake, saboda tsananin kunya, ko sau ɗaya ba ta yadda sun haɗa ido ba, shi duk yadda ake zuzuta muninta shi bai gani ba, sai tsantsar tarbiyya da nutsuwa, kuma tubarkallah shi bai ga wani muni ba.
Yayi musu nasiha sosai da sosai, ya ce raihan ya mayar da shi gida.
Ummi ta ce "Baba na gama abinci, bari na kawo maka"
Alhaji ya ce "Kar ki damu ƴar albarka ta, sauri nake kuma a ƙoshe nake, Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri kun san irin auren nan naku, society ɗinmu sun ɗauke shi, kamar wani zunubi, amma tun da bai saɓawa addini ba shikenan.
Da ƙyar ya sha lemo ya tashi, sai dai lemon yayi masa daɗi sosai da sosai, lemon cucumber ne da lemon tsami.
Da ƙyar wannan tarzoma ta lafa, sai dai aka saka ƴan islamiyyar su ummi ba ta haƙuri, kuma suka rubuta takardar ban haƙuri, suka yi signing ba ruwansu da ita ya taho da ita gida.
Bayan ya nuna mata takardar ta jujjuyata ta ce "You go far MD, da duk ba ka yi musu haka ba"
Ya ce "No, abun da na yi dai-dai ne, ba zai yiwu su ɗarsa miki wani abu mara kyau game da aurenmu ba, alhalin halataccen aure muka yi ba, kuma gaba ba za su sake yi wa wani hakan ba".
Ta ce "To Allah ya kyauta. Alhaji bai ci abincina ba" tayi maganar a shagwaɓe.
"Bani in haɗa da nawa da nasa na cinye"
"Wai ba ka gajiya da cin abinci ne, ka daina zuwa gym ɗin ma, idan ba ka yi wasa ba, sai ka kasa wucewa ta ƙofar falo"
"Eh na ji bakomai, hakan ma normal ne"
Ummi ta ce "Sai na saita maka cin abincin ka, ba zan je da kai unguwa ka bani kunya ba, ace ba ka ƙoshi" ya kwashe da dariya, ya ce "Yanzu ba zan gane wannan ba, sai cikina ya cika tukuna".
Ranar litinin kuwa, ummi ta sha fama da raihan kan ya tashi ya tafi aiki, aikuwa da ya je ya sha aiki sosai da sosai.
Tun da raihan ya koma aiki, sai gidan ya yi wa ummi girma, ba ta aikin komai, duk sai kaɗaici ya dameta.
Gashi baƙin da sukan shigo, duk sun daina zuwa.
***
Anty Rakiya ce a zaune tana kallon fuskar mami me ɗauke da zunzurutun damuwa.
"Ke yanzu Bilki har matar nan ta samu bakin yi miki rashin mutunci, yaushe ta waye?"
"Anty Rakiya ni ba wannan ne ya dame ni ba, kar bakinta ya tabatta yarinyar nan ta ƙwace raihan na shiga uku, ta ji daɗin yi mini dariya, shi ne babbar damuwata da tashin hankali"
"To wai kin bi shawararin da na baki kuwa?"
"Wallahi na bi, kin san raihan da taurin kai, ban gaya miki ranar da na kirshe shi ba, daga shiga ɗaki ya gudu ba. Ya ce mini ya koma aiki ashe duk ƙarya yake yi, yarinyar nan sumi-sumi, kar in je ta ƙwace shi, tun da sa'arsa ce kuma bazawara wayo za ta yi masa na shiga uku Anty rakiya".
"Ba ki shiga uku ba, ai wanda ya rigaka kwana sai ya rigaka tashi, dole ki samu hanyoyin muzgunawa yarinyar nan, kuma ki fara matsa masa a kan auren safiyya"
Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, in sha Allah zan cigaba da ƙoƙari".
Ranar asabar raihan yana ta murna zai wuni a gida tare da ummi, tana kitchen tana shirya musu breakfast, yana ɗaki yana bacci mami ta kira shi a waya wai ya je.
Tamkar ya fashe da kuka, haka ya ji, ya ajiye wayar, yana tunanin meyasa mami take yi masa haka, lallai sai ta shiga rayuwar aurensa da ummi.
Ya lumshe idonsa, ransa babu daɗi, ummi ta shigo ta kunna turaren wuta a ɗakin.
Ta shiga banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka, ta je kan gadon tana ɗan dukan filonsa ta ce "MD, ka tashi ka yi wanka mu karya" juya mata baya ya yi, ya ce "Wake me up in romantic way"
Ta ce "Like how? Ba gashi yanzu ka tashi ba"
Ya juyo ya kalleta ya janyota jikinsa, yayi kissing ɗin ta a goshi ya ce "Wake up sweetheart" irin haka nake so.
Ta ce "Ashe ba zaka tashi ba idan haka zan yi maka, yadda nake fama da kai ka tashi, da ƙyar ka ke tashi fa"
Ya ce "A'a idan ki ka yi mini haka sai na fi saurin tashi ai" ya ƙare mata kallo ya ce "Ni gaskiya a daina tashina da irin wannan kayan, ni dressing zaki din ga yi mini yadda ba za ace ki na jin hausa ba ma"
Ummi ta ce "Innalillahi, wai dama haka ka ke, mutum sai tsaurin ido, duk a ina ka san wannan ne?"
Wata irin dariya ta bashi, ya ce "Ai tsaurin ido ya riga ya ƙare tsakaninmu, tun da ni da ke yanzu kin san waye boss, fita fa zan yi"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Cewa fa ka yi a gida zaka wuni"
"To ya zan yi fita ta kamani, ki yi haƙuri kin ji baby"
Ummi ta kalli fuskar sa ta ce "Yaushe zaka kai ni gida na gaida su mami ne? Kuma ban je na yi wa Kawu da su anty bangajiya ba".
Ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, amma for now ban ji zan iya bari ki fita ba"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah"
"Na ji amma da sharaɗi"
Da sauri ta ce "Menene sharaɗin?"
"Sai kin ce mini baby" tayi turus tana kallon sa.
Ya ce "Yauwwa ai na san lagonki, and ki roƙe ni in a romantic way, a guje zan barki".
"Dan Allah baby ka bar ni na je na gaida su mami, na je gida na yi wa kawu bangajiya"
Ya girgiza kai ya ce "Ba haka ba, idan kin koyo sai ki tambaye ni, yanzu dai tashi mu je ki tayani wanka" sai da ta ɗan matsa daga kusa da shi ta ce "Wanka kuma?" Ya ɗaga mata gira.
"A'a zance maka babyn dai" sauka yayi daga kan gadon ya ce "Kina da sauran aiki Salma, ina son soyayya sosai ban sani ba ko dan ban taɓa yi ba sai a kanki, amma ina son gidana ya fi ko ina samar mini farinciki, kar ki saka na fara leƙe-leƙe" ya ƙarasa maganar yana shigewa toilet, a daidai lokacin da ƙirjin ummi ya buga da maganar sa ta ƙarshe.
Shi ya ma manta da ya faɗi maganar, ummi kuwa duk ta shiga damuwa, ya gama cin abincin sa ya fice.
Ummi ta zauna ta yi shiru tana tunani, abun duniya ya isheta, tana son yin abun da za ta faranta wa raihan rai, sai dai haryanzu tana tsananin jin kunyarsa. Ta buɗe wayarta ta shiga YouTube, tamkar sun san halin da take ciki, ta ci karo da wani video, malamar tana ta bayani a kan kula da miji.
Malamar take cewa "Ƴan mata nawa ya