Raihan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba wasu umara, ƙawayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana"
Ta ce "Kai dalla yi mini shiru, nima na san waɗanda suke da buƙata, ka bani vacancies, da kuma kuɗin da zan bayar nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar".
Raihan ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuɗi? Zan baku vacancies huɗu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuɗin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage ɗin share ku fa, a ribar da aka fitar ta shekara za a baku"
Mami ta shiga tafa hannu, ta ce "Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naƙudarka, da komai sai ka daidaitani da ita, kuɗin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?"
Ya miƙe yana zumɓura baki ya ce "Dan Allah mami kiyi haƙuri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuɗi ma, haba mami dan Allah" sai ta kasa magana ta bi shi da kallo, gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba ɓaro-ɓaro yake gaya mata.
Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuɗinta na albashi.
Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce "Raihan, manager ya ce na tura account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi"
Yayi dariya ya ce "Gaskiya banki za su rufe mini account ɗina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuɗi idan bai kai dubu ɗari ba, basa shiga account ɗina".
Ta ce "To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?".
"Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta kin yi mini alƙawarin zaki kai ni shopping".
Ayshercool
08081012143
What's app only please 🙏
*CUTARWA!*
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
25
Cikin murna ummi ta ce "Ban manta ba, in sha Allah zamu je, nima ina son mu je".
"To kin zaɓi in da zaki kai ni ɗin?".
"A'a ai ni ban san wuraren ba, ko ina ne ma kawai sai mu je"
Yayi dariya ya ce "To shikenan, amma dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi bacci a nutse kar ki kasa bacci saboda 15k, you are not ɗangote yet, kar ki kasa bacci saboda 15k dan Allah"
Ummi cikin halinta na yanga da ita ba ta gani ta ce "Kar ka dameni fa, ce maka aka yi ba zan iya bacci ba, kuma ko naira goma ce tunda ita ce gumina ai ita ce arzikina dole na yi murna"
"Ahaaf, ai na san ba iya bacci zaki yi ba saboda dubu sha biyar, to dai ki nutsu da ƴar 15k ɗinki kin kasa rufe baki".
"Ai kuma sai ka yi, ba kula ka zan cigaba da yi ba"
Sosai yake yi mata dariya, noor ce ta shigo ɗakin ta ƙure ummi da take dariya da ido.
Cikin diriricewa ta ce "Raihan sai da safe".
"Akwai matsala ne?"
Ta ce "A'a zan yi wani abu ne" ta katse wayar tana kallon noor.
Noor ta ƙarasa ta zauna ta ce "Yaya ummi da wa ki ke waya ne?"
Ummi ta ce "Amm ɗan ajinmu ne"
Noor ta waro ido ta ce "Ke fa ki ka ce ƴan ajinku ba sa kulaki, kuma ba kin daina zuwa makarantar "
"Kai maman ƙarya nake yi kenan?"
Noor ta ce "A'a, to amma me ku ke cewa na ga kina dariya, ban taɓa ganin kina waya kina dariya haka ba, ko kema saurayin ki ka yi?" Da sauri ummi ta girgiza mata kai alamar a'a.
"To me ku ka ce a wayar"
Ummi ta ce "Noor kin fa isheni, magana muke za a bani salary ne, shi ne nake dariya, ai kiwa yana son kuɗi, ko ke ba kya so?"
Noor ta ce "Ina so mana, zamu ci daɗi ashe"
"Sosai ma" ummi ta yi maganar tana murmushi.
"Kin san me yaya ummi?"
Ummi ta ce "Sai kin faɗa maman"
"Inteesar ce ta zo fa yanzu" ummi ta ɗan waro ido, ta kalli agogon wayarta ƙarfe goma da rabi na dare.
Ta basar ta ce "Inteesar kawai ko? Ba na hanaki ba, ba zaki ce mata anty inteesar ba?"
"Kema ai ummi take ce miki, kamar fa kuka take yi, sun shige ɗaki ita da maama, na je in ji meyafaru wai in fita har da ce mini munafuka".
Ummi ta kwantar da noor ta ce "Shhh maza yi bacci, kar in sake jin bakinki, hakan gulma kenan kuma haramun ne babu kyau"
Noor zata sake magana, ummi ta riƙe mata baki, tayi murmushi ta lumshe idonta kamar zata yi baccin.
Ummi ta kashe musu fitila, ita ma ta kwanta, amma noor ta tashi ta lallaɓa kunnen ummi ta ce "Wai mijinta ne zai auro mata kishiya, uncle sagir" ta sauka daga kan katifar ummi ta fita da gudu.
Sai da gaban ummi ya faɗi, ta san akwai tashin hankali kenan, tun da aka ce za a yi wa ƴar gwal kishiya, tayi saurin kawar da tunanin daga ranta dan ba huruminta bane ba.
Maganar raihan ta tuna, wai kar ta kasa bacci, saboda dubu goma sha biyar.
Dariya abun ya bata, ta gyara kwanciyarta ta shiga karanto addu'oin kwanciya bacci.
Aikuwa da safe da ta tashi, ta ga inteesar a gida, idanuwanta sun kumbura alamar ta sha kuka, kuma ba ta samu isasshen bacci ba.
Ummi ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama.
Daga haka ummi ba ta sake shiga sabgarsu ba, dan ta ga alamar ƙiris suke jira tayi wani abu, su huce a kanta, dan haka ta kama kanta, ko sallama ba ta yi musu ba ta fice.
Ɗan halak yana in da suka saba haɗuwa yana jiranta.
"Ina kwana" ta gaishe shi, sai dai maimakon ya amsa ya ce "Inye ka ga attajirar garin nan, ke fa yau jin kanki ki ke yi daidai da kowa, saboda kina da 15K"
Ummi ta ce "Ka cigaba, tuwo ne yau a cikin flask ɗin nan, wannan kuma kunun tsamiya, ka cigaba da tsokanata ba zan baka ba"
Ya kwashe da dariya ya ce "Aikuwa sai na ci abincin nan, kuma ba zan daina tsokanar ki ba"
"Sai ka ci in gani ai"
Raihan ya kunna motar ya ce "Girmata fa ki ka yi, ba fin ƙarfina ki ka yi ba, ƙwace abincin nan ba wahala zai bani ba".
Ummi ta ce "Idan ya zube shikenan ba".
"Kar dai ki manta kuɗinki account ɗina za a tura su, attajirar duk duniya".
Ummi tayi dariya tana kallon window.
Suna zuwa wurin aikin ummi, raihan ya ce a wurin zai ci abincin, idan ya tafi da shi ba zai ƙoshi ba.
Suna shiga wurin bayan sun gaisa manager ya ce "Ummi, an saka miki kuɗin nan fa"
Raihan ya ce "Eh, sun shigo sai ka ce wasu kuɗin kirki, gaskiya manager a ƙara kuɗin nan, haba 15k yafi ta sai man shafawa da cingam".
Ummi ta kalli raihan ta girgiza masa kai ta ce "Manager na gode sosai da sosai, Allah ya ƙaro mana coustomers, dan Allah kar ka damu da abun da raihan yake faɗa, Allah ya sanya musu albarka ka san yaro ne, sai a hankali" tayi maganar tana kawar da kanta gefe tana dariya.
Manager ya kwashe da dariya ya ce "Ai shiyasa bana biye masa, baƙinciki yake yi miki, shi yana zaman banza, wallahi ko kati kar ki saka masa".
Kallon ummi raihan yayi ya ce "Me ki ka ce mini yanzu?"
Juyawa ta yi tana dariya, ta nufi wurin da take zama, tayi aiki.
Aikuwa ya bi bayanta, yana sake cewa "Maimaita me ki ka ce mini yanzu?"
Ta ce "Na yi magana ne?"
Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Ki maimaita".
Ummi ta kalli raihan ta ce "Yaro, ko ba yaron bane?" ta sake maganar tana yi masa dariya.
Kyau ya ga tayi masa dariyar da take yi, haƙoran nan sun haska fuskarta sosai, ga laɓɓanta pink shar, dimples hagu da dama a kumatunta.
Yadda ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta zata, ko haushin yaron da ta ce ya ji, dan haka ta sake cewa "Lokacin da ka ke tsokanata, daɗi ka ke ji ai, nima yanzu is my turn".
Yayi wani irin murmushi ya ce "Wai shekara nawa ki ka bani ne? Na san dai maryam ta girmeki".
"Ba za a lissafa ba, koma dai yane kawai na girmi mutum, kuma idan kana son ka yi albarka ka din ga yi mini biyayya ka daina tsokanata"
Ya ja kujera ya zauna, har cikin ransa yake jin daɗi idan ya ga ummi ta sake da shi tana dariya, saɓanin da da kullum kamar a tsorace take da mutane, da farkon haɗuwarsu ne, ko haɗa ido ba za ta iya yi da shi ba, amma yanzu da confidence take gaya masa abu.
A ransa ya ce 'Irin wannan confidence ɗin nake son ki samu, a cikin mutane"
Manager ya ce "Kai raihan, ka wani je ka gurfana a gabanta, zaka kalallame ta ka cinye mata kuɗi, to ahir ɗinka"
Raihan ya ce "Manager, idan na waiwayo kanka ba zaka ji daɗi ba, yau ka sa an kirani da yaro, duk girman nan nawa, the whole me aka ce mini yaro, ke kuma ai shikenan ban abincina in ci, shima dan ba zan iya fushi da abincinki ba, da yasin ba zan ci ba" yayi maganar cikin sigar shagwaɓa.
Ummi ta yi ƙasa da murya tana kallonsa ta ce "Haba kar aji kanmu ayi mana dariya, ci abincinka ko manager kar ka yi wa bisimillah"
"Dama shi ya isa?"
Ummi ta tashi tana ta ɗawainiya da coustomers, raihan yana cin abinci, suna yi suna faɗa da manager.
A hanya ummi take yi masa faɗa kuma ta haɗe rai kamar wata babarsa "Raihan, ka ce Alhaji ya baka aiki, amma sai ka zo wurina ka yi zamanka ka ƙi yi masa aikin, ko office ɗin fa baka zuwa, meyasa?".
"Haka aka ce miki bana zuwa?"
"To yau ka je ne? Zama fa kawai ka yi a wurin aikina, yakamata ka kammala yi masa aikin nan on time, sai shiririta ka ke yi"
Raihan ya ce "Nifa ba shiririta nake yi ba"
"To aikin ka ke yi? Banda surutun ƙwallo, me ku ka yi kai da manager? Gobe in Allah ya kaimu ka je office ka yi aiki, idan ba haka ba, ni da kai ne, ba zan kai ka shopping ɗin ba, kuma na daina bin ka mu tafi aikin tare"
Raihan ya ce "Gidanmu dai ni ne autan maza, kuka zan tayi miki, kuma ke da Alhajinmu kin saka babban mutum kuka"
Ummi ta ce "Ai bulala zan samu, na zaneka ka yi kukan da dalili, Alhaji ba zai ce komai ba"
"Wallahi ummi ina iya ƙoƙarina, Alhaji ashe aiki yake tuƙuru ba kaɗan ba, dare nake bi in yi, bana son zaman office ɗin ne saboda kowa sai ya kawo mini abun da suke buƙata, na son zuciya, na rasa yadda zan yi musu, ni ba Alhaji bane cewa nake ba zan yi ba, kuma sai su zagaye su kai ƙarata.
Sai wahalar da ni ake yi, wallaahi ji nake kamar na lallaɓa na gudu bauchi, amma kawai mun riga mun wani saba, ba zan iya tafiya na bar ki ba, ba zan din ga cin irin abincinki ba"
Ƙuri ummi ta yi da ido tana kallonsa, wai yau ita ce a rayuwa wani zai ce yayi sabo da ita, da ba zai iya nesa saboda ita ba, babu dangin iya babu na baba, Allah sarki.
"Ki ke kallona ki bani shawara mana"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kamar yadda na gaya maka a baya, kar ka nuna wa Alhaji gazawarka, ka yi haƙuri ka daure, da haka zaka san zafin nema, kuma kar ka kuskura ka yi zalunci dan ka farantawa wani rai, ka yi abun da ka ke ganin ya dace, amma dan Allah ka janye maganar guduwa bauchin nan"
"Saboda me?"
Ta ce "Kawai, Alhaji ba zai ji daɗi ba"
"Shikenan, ranar da ki ka tashi da wuri, zaki rakani zagaya ƙananan branches ɗin mu, daga nan sai mu je sayayyar, kamar jibi in Allah ya kaimu ko gobe yayi?"
Ta ce "Eh, Allah ya kaimu, amma dan Allah a cikin kuɗin ka bani ko dubu ɗaya ce idan ban takura maka ba, na sai kayan miya da kaina in yi wa kawu girki, yau zai dawo na saya wa mama noor chocolate, idan ya so ranar da muka je sayayyar sai in siya wa kawu wani abun, da ƴan gidanmu ko?"
"Eh har da gori zaki yi mini, saboda kina da 15k, dan kuɗinki yana wurina, bari a samu POS na baki kuɗinki kan ki tara mini jama'a".
"Ni ba haka nake nufi ba fa, to yi haƙuri, sonake kawai na farantawa kawu"
"Albashin naki har nawa ne da zaki yi ta rabo? Daga kawu sai noor da ni zaki sayawa abu, idan aka kuma biya sai ki sayawa sauran, kuma ni duk wata sai kin saya mini abu".
Ba musu ta ce "To"
"Me zaki dafa wa Kawun ne?".
"Haryanzu ban gama tsarawa ba, amma ina ga alkubus zan yi masa, da miyar ganye yana so sosai".
"To nima zan ci".
"To shikenan, idan na gama zan kiraka a waya, amma kar ka ƙaraso gida ka kira ni a waya, sai na kawo maka".
"Meyasa ba zan ƙaraso gidan ba?"
"Amm, saboda kar a ganka ace wani abun"
Raihan ya ce "Saboda ni ciwo ne?"
Ummi ta ce "A'a ba haka bane ba"
"Salma" ya kira sunanta kai tsaye abun da bai taɓa yi ba" wani yarrr ta ji a jikinta yadda ya faɗi sunan.
Ta waro ido ta ce "Salma kuma?"
"Ba sunanki ba ne?"
"Kuma sai ka faɗa gatsal, ina yayan ni ka daina kirana haka, yaya ummi zaka ce"
Yayi dariya ya ce "Eh to sannu uwar son girma, ba za a faɗa ɗin ba".
"To ba zan yi alkubus ɗin da kai ba".
"Kuɗinki kuma suna wurina ba, in sai data da kuɗinki"
"To ai ba damuwa zan yi ba idan ka yi hakan".
"A'a kar ki zo kina yi mini kuka".
Sai kuma ya ce "Amma ummi kamar akwai matsala yanayin zamanki a gidanku ko?" Bata amsa masa ba ta kalleshi.
"Ba sonake na ji sirrinki ba, mun wuce wannan zuwa yanzu, yadda wasu abubuwan suke gudana, duk da ni yaro ne ina fuskanta, dan Allah duk wani abu da zan yi idan zan janyo miki matsala ki gaya mini, kar a ɓata miki rai saboda ni ba zan ji daɗi ba"
Bai jira amsarta ba, ya canza hirar har ta ware.
Suna tafe suna hira suna dariya, suka tsaya wurin masu kayan miya, ta sayi abubuwan da take buƙata ya biya, a tunaninta a cikin kuɗinta ne.
Tana zuwa gida ta tarar da kawun a gida, ummi ta ce "Kawu, na ɗauka sai yamma fa zaka dawo, na yi cefane zan yi maka abincin dare"
Yayi murmushi ya ce "Mamana ta kaina, dawowa ce ta kamani da wuri".
Ummi ta risuna ta ce "Kawu an biyani salary, shi ne na yi cefanen alkubus"
"Allah dai yayi miki albarka, amma cefane nawa ne ummi, ki riƙe kuɗinki ki yi buƙatunki kar ki ce zaki din ga kashewa a gidan nan".
"Kawu ka sanya albarka" tayi maganar tana murmushi tana jin ƙwarin gwiwar yin magana kamar tana tare da raihan.
Dr. Ya ce "Allah ya yi albarka"
"Amin na gode sosai " ta miƙe ta nufi kitchen, farida kuma sai kwaɓe fuska take yi tana hararar ummi babu dalili.
Bayan sallar magariba ta gama girkin da ta yi wa dr., Ta zubawa raihan na sa a flask, ta buɗe data ta yi masa message ya zo ya karɓa, za ta bawa maigadinsu, da ya zo ya ce masa shi ne raihan, zai bashi.
"Sai ka ce wani me ma zance ne? Idan ba ke zaki fito ki bani ba, na ƙoshi".
"Haba raihan, ba lallai a barni na fita, kuma zan iya samun matsala, wai kai idan ba ka yi rikici da gangan ba ba ka jin daɗi?"
Ya ce "Soryy don't cry Salamatu, zan zo in karɓa in sha Allah"
"Salamatu ko?" Ya katse wayar yana dariya
Shima bai samu zuwan ba, direba ya aika, ya karɓo masa, babu ƙarya raihan yana sarawa ummi wurin iya girki, dan sosai ya saba da abincinta ya rage yawon restaurant cin abinci, dan cewa