yake ƴan aikin gidansu jagwalgwalo suke yi.
Yana cin alkubus ɗin ya kirata yana ta zuba mata santi yana koɗata.
Da safe ummi ta ji abun da ba ta taɓa tunani ba, dr. Ya kan yi faɗa wasu lokutan, duk da yana da kawaici amma yau ya ɗau zafi da yawa.
Farida yake zazzagawa bala'i, a kan lallai inteesar ta koma ɗakinta.
"Wai dan Allah dr. Meyasa ka ke haka? Ba zaka tsaya ka ƙwato wa yarinya ƴancinta ba? Ai ba haihuwa ne ba ta yi ba, ɓari take yi bayan ya hanata karatu, ga wulaƙancin danginsa kuma yanzu ace an bashi ƴa zai ƙara aure haka ake yi?"
"Shut up farida, ki daina cusa mata wannan banzar aƙidar taki, bai hanata ci da sha da muhallin zama ba, a kan useless excuse ɗinku, ba zan kira yaron nan muna musayar yawu mutuncina ya zube ba, karatu kume ku ka janyowa kanku, dan haka dole inteesar ta koma ɗakinta a yau ba sai gobe ba, ke kuma" yayi maganar yana nuna kausar da yatsa.
"Abun da ki ka aikata a makaranta kin kyauta mini kenan, kuma kin kyautawa kanki? Carryover shida a courses goma sha ɗaya, uban me ki ke yi a makarantar? Duk uban kuɗin da na kashe? Kuma baku gaya mini ba HOD ɗin su ne ya kirani ya gaya mini, haka ki ka ga ummi tayi ko Abdul? carryover shida fa, courses shida ki ka faɗi a sha biyu, ba ma ɗaya ko biyu ba balle ace tsautsayi ne, me hakan yake nufi? In cigaba da asarar kuɗina? Idan auren ki ke so kema sai ki yi mini bayani ki fidda miji"
"Kaga duk ba a kai ga wannan maganar ba, tsautsayi ne bai kuma wuce kan kowa ba, ita ummin kana da tabbacin ƙoƙarinta ne ba satar amsa"
"Ki yi mini shiru farida kan na yi miki rashin mutunci, ƴa ta tafi ƙarfin ta yi satar amsa, dan haka zaɓi biyu zan baku, ko dai in ga canji next semester ko kuma ta fitar da miji, in yi mata aure ta bar mini gida, ta daina tara mini ƙarti a ƙofar gida tun da hankalinta a kan su yake ba karatun ba".
A harzuƙe farida ta ce "Waccan guzumar yakamata ka bawa wannan zaɓin ba kausar ba? Da ta gaji da balaga ta riƙe a gida taƙi fitar da miji, ita ma sai a saka mata wannan dokar, ai an yi na Allah, an riƙeta tayi karatu, ko ta fitar da mijin aure ko a san yadda za ayi da ita, dan wallahi nima sai ta bar mini gida ba zan cigaba da zama da zabgegiyar mace a cikin gida ba, kuma kana sakawa ƴaƴana doka ba, wallahi ita ma sai ta bar gidan nan "
Ganin da ya yi idan ya yi magana komai na iya faruwa, ya sanya ya ɗauki mukullin motarsa ya fice, ummi tana jin abun da yake faruwa ta dake, ta fito daga kitchen ta ɗaukko takalminta tana gogewa za ta fita.
"Ke ummi! Da ke nake na san kin ji komai ai" ummi ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Na gaji da zama da ke a gidana, ina buƙatar space nima, tun da komai ke ce ki ka iya, ƴaƴansa ba su iya ba, duk in da miji yake ki nemo shi, sai kin bar mini gida ko kuma wallahi ki koma ƙauye in da ki ka fito"
Kausar da take kuka ta ce "Wallahi maama ta bar mana gida, banza mummuna ko kuma koma waye a aura mata, ta rabamu da ubanmu ji yadda ya ci mini mutunci"
Inteesar ma ta fito falon tana faɗin "Ai wallahi maama ki tarka mata tsummokaranta baya nan, ta bar mana gida, tuntuni ki ke cewa sai ta bar gidan nan, idan ki ka cigaba da zama da ita wannan dai ba auruwa za ta yi ba, idan ba sadakarta za ayi ba, sadakin ma shi Abba ya biya ba, ko a mayar da ita can ƙauyen ta samu dai-dai da ita".
Ummi ta saka takalmanta, ta tashi zata tafi, farida ta zabga mata wata irin ashar ta ce "Dawo nan ina magana zaki wuce, sai na tsinke ki da mari tukuna, ƴar ƙauyen banza daga zuwa cin arzki kin zaƙe, baya ganin kowa da gashi sai ke, zan yi maganinki, in dai ina numfashi wallahi sai kin bar mini gida. Ya kai ki duk in da zai kai ki, tun da su dangin mahaifiyarki da ƴan ƙauyen naku ba su da hankali, da ma neman maraba suke yi da ke".
Ummi ta danƙe wayarta da take vibrating na kiran raihan, zuciyarta na wani irin zafi, idanunta suka cika da hawaye, yanzu meye laifinta a saɓanin da suka samu yau ɗin, da har aka huce a kanta haka da cin mutunci.
Sai da farida ta gama, sannan ta juya ta kamar hanyar fita, ta goge hawayen da suke shirin zuba, saboda kar raihan ya gane, ya matsa mata da tambayoyi.
Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kai, dan ko gaishe shi ba ta yi ba, kawai ta zauna, tana ta murza yatsunta.
Ya kunna motar sannan ya ce "Yau kin shanya ni fa, ga kuma kulolinki na abinci na gode sosai, Allah ya ƙara zaƙin miya".
"Amin" ta faɗa a hankali.
Tsit har suka kusa zuwa ya gaji da shirun yana ta son ya tsokane ta, amma gaba ɗaya ko in da yake taƙi kallo, waje take kallo, tana fargabar kar Allah ya jarrabeta da abun da zai mayar da ita gagarawa.
Unexpected taga har sun je tana can tana tunani, ta kalli gefe ta ce masa thank you.
Ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma ta ga ya saka lock, ta waiwayo ta sanya idonta cikin nasa, bai ce komai ba ya zuba mata ido.
Idonta fal hawaye ta ce "Zan sauka"
"Are you ready to tell me?" Yayi maganar very serious.
Ta ɗan sake yin shiru, tare da sunkuyar da kanta ƙasa.
"Salma" ta saci kallonsa sannan ta sauke idonta, tana ta kokowa da hawaye kar su zubo.
"Yanayinki ya bayyana komai, kuma kin saka ni a damuwa nima, dan Allah gaya mini, idan ba haka ba zan yi ta kokwanto".
Kawai hawaye ya fara gangarowa daga fararen idanuwanta, wani na bin wani.
Tun tana yi a hankali, har sautin kunkan nata ya fara fita sosai da sosai, ta sanya tafukan hannayenta, tana wata irin sheshsheƙar kuka mai ƙona zuciya.
Ji ya din ga yi ina ma kowace irin damuwa ce, ya ɗauke mata ita duka, idan ba zai iya ba su raba damuwar biyu.
Ya saka hannayensa ya sauke nata, ya zira hannu a aljihunsa ya ɗaukki handkerchief, ya saka mata a hannunta ya ce "Ya isa haka, goge hawayenki"
Ya kira manager a waya, ya ce masa ummi ba ta da lafiya, ba zata shiga shago ba yau.
Ummi ta kalleshi, ya ce "Mu je yau ki tayani aiki a namu office ɗin yau"
Za ta yi magana ya ce "Mata shhh" ya ja motar ya bar wurin.
Ta ɗan yi shiru tana kallon hanya, ta rasa dalilin da ya sa ba ta iya yi wa Raihan musu.
"Mu je ki ga wurin aikina, sai mu je shopping ɗin, daga nan zaki gaya mini meyasaki kukan?"
Tayi ajiyar zuciya tana kallon fuskar sa, "Ko haryanzu ban kai in san damuwarki ba?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"To idan kin huce, sai ki gaya mini"
Suna tafe yana ta ɗan jan ta da hira, ta fara sakewa.
Ummi ta sha mamakin ganin wurin aikin su raihan, kuma nan kawai babban office ne na gudanar da ayyukan kasuwanci, ba wurin da suke gudanar da kasuwanci ba.
Yadda raihan ya wani maze, ake ta girmama shi, har mamaki ya bata, kamar ba raihan ɗin da suke hira da wasa da dariya ba, ya wani maze.
"Raihan wai me ku ke sayarwa ne?"
"Mutane, da masu kukan banza, da matsorata, da ragwaye, sai kuma mun kai sai kawunan mutane mu sayar, kin ga kamar ke ɗin nan, na ajiye ƴan china zan sayar musu da idonki ne, da ƙafafuwan ki a cire a saka mini" handkerchief ɗinsa da yake hannunta ta kwaɗa masa, yayi gaba yana dariya.
Sagir suka tarar a cikin office ɗin a zaune, yana jiran zuwan Raihan.
Ummi ta gaishe shi ya amsa, raihan ya ce "Yaya ya na ganka a nan kuma, lafiya dai ko?"
"Kai haka ka ke yi sai ka ga dama zuwa wuri kake zuwa? Ka shanya mutane suna jiranka?" Ya jefa masa takarda ya ce "Signing zaka yi mini"
Raihan ya ƙarewa takardar kallo ya ce "Wannan Alhaji yakamata ka bawa yayi maka".
"Shi ya turo ni wurinka"
"Amma yaya meyasa zan yi Signing ka fitar da wannan kuɗin haka? Me zaka yi da su?"
Abun ka da mai shaye-shaye a kusa, ya daki tebur ya kalli raihan ya ce "Wai kuɗin nan nake ne? Ina ruwanka ne, ya gani ya ce in zo ka saka mini hannu, business zan fara, kar ka ɓata mini lokaci"
Raihan ya juya takardar ya ce "Sana'ar me?"
"Ban sani ba" ya bashi amsa.
"Ba zan saka hannu a wannan takardar ba yaya ka yi haƙuri, sai dai ka zo mu yi aiki tare a din ga biyan mu, sai ka tara kuɗin da ka ke buƙata, amma yana shan wahalar tara dukiyarsa bai kamata a din ga yi masa ɓarna ba".
Kan kace kwabo, sagir ya shaƙe raihan, yana zazzaga masa bala'i.
Nan da nan ummi ta rikice, saboda ba ta son faɗa ko tashin hankali, take ta fara kuka, tana basu haƙuri.
Yinƙuri ɗaya Raihan yayi, ya hankaɗa Sagir, sai da ya kai ƙasa.
Ya ɗauki takardar ya yayyaga, ya watsa masa cikin kurari da zafin rai ya ce masa "Get out" ya ɗaga murya ya ce "Idan da wani a waje, ku kirawo mini security su fita da shi".
Ummi ta ce "Raihan yayanka ne fa, ya zaka yi masa haka?" Kallon da ya yi wa ummi ne ya sanya ta jan bakinta ta tsuke, dan gaba ɗaya tsoro ya bata jikinsa har tsuma yake yi, kamar wani zaki.
*Khadija ƴar gatan mama, ina gaisuwa 😂 Autar manya tamu ta gargajiya, Allah ya bar zumunci, ɗaukacin jama'a masoya littafin CUTARWA! ubangiji Allah ya bar ƙauna*
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
26
Sagir ya miƙe cikin zafin rai ya ce "Ni ka yi wa haka raihan?"
"Na yi maka ɗin, da na lallaɓaka meyasa ka kai ni bango? Ai sai ka bari na kammala masa aikinsa na bar office ɗin, sai ka sake rubuta masa wata takardar shi ya sanya hannu ba ni ba".
Cikin zafin rai Sagir ya nuna kansa da yatsa, yau shi raihan ƙanin ƙaninsa ya yi wa wannan cin mutuncin.
"Zaka ga abun da zan yi maka, komai ya faru ka kuka da kanka"
Raihan ya ce "Get out from here, ko na sanya security su fitar da kai".
Ummi ta ce "Dan Allah raihan kar ka yi haka, zaku zubarwa da mahaifinku mutunci a gaban ma'aikatansa, kuma kar hakan ya shafi zumunci da mutuncinku"
Sagir ya fice daga office ɗin rai a ɓace, Raihan ma rufa masa baya ya yi, ummi ta bishi da sauri za ta yi magana, ya ce "Ki jira ni a nan" ya fice shi ma.
Zama ta yi zuciyarta babu daɗi, tana ta tunani, yanzu ace ƴan gida ɗaya ciki ɗaya suna wannan abubuwan, abun da mamaki.
Sai kuma ta tuna ba abun mamaki bane ba, duba da yanayin na su familyn suma.
Ummi har ta fara gajiya da jiran raihan, ta kira shi a waya, amma ta ga wayar ta sa a office ɗin tana ringing.
Ta sauke hannunta a hankali, tana cigaba da kallon hanya, Raihan ya dawo office ɗin, hannunsa ɗauke da leda, ya ajiye a kan table ya kalleta ya yi murmushi ya ce "Afuwan na bar ki kina ta jira, bari mu ci wani abun"
Miƙewa ummi ta yi ta ce "Tafiya zan yi, ka rakani na samu abun hawa na tafi"
Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Meyasa?"
"Au tambayata ma ka ke yi? kamar ba yanzu ka gama hantarata ba, daga gaya maka gaskiya, dama ina cikin wata damuwar ka ƙara mini wata" tayi maganar a shagwaɓe tana kai hannunta fuskarta, ya zata da wasa take yi, kawai ya ga ta fara zubar da hawaye.
Da sauri ya ƙarasa gaban ta, ya kai hannu zai sauke mata hannunta yana faɗin "Am sorry please, let me explain..
Ta ja da baya ta ce "Kar ka sake taɓa ni, ni tafiya zan yi"
"To shikenan, na yi kuskure amma dan Allah ki yi haƙuri".
Ummi ta sauke hannunta ta ce "Na ji, amma ka mayar da ni"
Raihan ya ce "Dan Allah ki zauna ummi, mu yi magana ki yi haƙuri Please "
Yadda yake ta marairaicewa ne ya sanya ta ga idan ta cigaba da yi masa musu, ba ta kyauta ba, dan haka ta zauna, shima ya ja kujera ya zauna.
Ya kalleta ya ce "Am sorry ummi, this is the raihan you don't know, ina da haƙuri amma idan aka ƙure ni bani da kyau, mutum ne ni mai zafin zuciya da fushi, amma da wuri nake sauka.
Yaya Sagir da Salim, su ne manya, kuma mahaifinmu yayi iya ƙoƙarin sa a kan inganta rayuwarmu, sai dai sun ƙi makaranta, sun ƙi sana'a kullum sai ɓarnar kuɗi a kan mata da shaye-shaye.
Ban taɓa tunanin haka mahaifinmu ke shan wahala a kan dukiyarsa ba sai yanzu, a haka ma fa aikin da ya sakani iya gida Nigeria ne, yadda yake zirga-zirga sai kin tausaya masa.
Sana'arsa ba ɗaya ba ce ba, mutum ne mai nasibi a harkar kasuwanci, muna shigo da kayan gini daga ƙasashen ƙetare, ana bamu kwangilar kayan gini, na ofisoshi, manyan ma'aikatu na gwamanti da na ƴan kasuwa, kuma muna rarraba wa kamfanoni da yawa kayanmu a Nigeria da ƙasashen maƙwabta.
Ya kunna system ɗin gabansa, ya shiga nuna mata kayayyakin da suke sayarwa, kama daga ƙofofi, furnitures, kayan banɗaki, da sauran kayan alfarma na ƙawata gini.
"Ɓangare guda, mahaifinmu babban dealer ne na shige da ficen kayan masarufi, sai dai an fi saninsa da harkar kayan gine-gine, iya kano muna da shaguna sun kai goma sha biyu a wurare daban daban ban da sauran garuruwa. Mahaifinmu duk shi yake kula da ayyukan kasuwancin sa, sai ma'aikatansa wasu lokutan a cuce shi a karkatar da kuɗaɗen sa, babu mai taimakonsa a cikinmu sai dai ya nemo mu kashe.
Wannan shi ne babban ofishinmu na ƙasa, duk da ya ce zai mayar da shi Abuja, duk da haka mukan tafka asara wasu lokutan, amma hakan ba ya sanya mahaifinmu shiga hakkin ma'aikatansa, idan an samu riba da yawa kuma, ya kan ƙara musu domin farincikin su da mu baki ɗaya, to kuma duk da wannan abun sai azo da son zuciya mu ƴaƴa cikinsa mu din ga cutarsa duk ƙoƙarin da yake yi mana?"
Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Raihan, na ji duk abubuwan da ka faɗa, ka na da gaskiya, amma still ka yi kuskure, ba dan Allah ya fi sonka ya sanya ka zama shiryayye ba har Alhaji yake janka cikin al'amuransa ba.
Yayyenka na buƙatar kulawarka da tausayawa, a wannan halin suna sama da kai, amma ace sai ka yarje musu yin wani abu, ka yi tunanin yaya za su ji? Ka na da gaskiya, amma kamata yayi ace ka yi ƙoƙarin dannewa kun rabu lafiya, abun da ka yi masa bai kyautu ba gaba ɗaya.
Raihan komai lokaci ne, ina sake jaddada maka, ranar da ba sa doron duniya sai ka din ga ina ma ace, ni ba gani ba, sha'awa ku ke bani, mahaifina ya rasu, mahaifiyata ban san in da take ba, bani da wa, ba ni da ƙani, haka nan kawai dai rayuwa nake yi. Duk da ka ce yayyenka basa ji, but they are blessing to you idan ka kallesu ƴan uwanka ne, ban ce ka ƙyale su su yi abun da bai kamata ba, amma gaba suke da kai, su yakamata ace a wannan position ɗin, amma Allah ya ƙaddara kai ne ba su ba, haba Raihan, why are you kind to me, amma brother's ɗin ka ka yi musu haka?"
Gaba ɗaya jikin raihan yayi sanyi ya ce "Haka ne, na yi kuskure kuma na fahimce ki, in sha Allah zan kiyaye gaba ba zan sake ba, raina ne ya ɓaci sosai, kuma na yi ƙoƙarin dannewa amma yayi pressing ɗin na"
"Yauwwa dan Allah ka daina, ba ka ' sanin muhimmancin wasu abubuwan a rayuwa, sai ranar da ka rasa su, wani rashin idan ka yi sai ya tafi ya barka da rauni mai raɗaɗin da har ka koma ga Allah ba zai goge ba, kamar dai ni da na rasa babban masoyina babana, da barinsa duniya ya yi