wa rayuwata giɓi" tayi maganar hawaye na kwararowa daga idonta, har jijiyar goshinta ta tashi.
Raihan ya matsa kusa da ita ya ce "Ummi, dan Allah ki daina koke-koken nan haka, Addu'a ita ce abun da mahaifinki ya fi buƙatar mu yi masa".
Ta jinjina masa kai tana share hawayen ta, ya ce "Ga lemo na sayo mana, na san is hardly idan kin karya, yau ba ki zo mana da abinci ba"
"Na ƙoshi, ba zan iya cin komai ba"
Cikin damuwa raihan ya ce "Ni gaya mini menene ya saka ki kuka ma tun farko, kin ce zaki gaya mini"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A bar wannan zancen kawai"
"Ba za a bar shi ba, sai mun yi shi, ai alƙawari ki ka yi mini"
"Ai ba zaka gane ba".
Raihan ya ce "Zan gane, ko ta ina ne yi mini bayani, ina cin maths a aji ai" yayi maganar yana ɗan murmushi.
Ta ɗan tsura masa ido, har cikin zuciyarta take jin yardar da ta yi wa raihan, ba ƙarama ba ce ba, saboda sosai take jin sa a ranta, mutumin da yake ta ƙoƙarin fuskantar matsalolin ta.
"Ina ƙarama mahaifina ya rasu, kakata ta karɓi riƙona daga hannun babata, nikaɗai kuma suka haifa, mama ta koma garinsu, ƴan uwanta suka yi ta zuwa a basu ni, amma kakata ta hanasu ni, aka ce mamana ta haihu ɗan babu rai, ga damuwar rabamu, ta samu larurar ƙwaƙwalwa, amma aka hana su ni, har ƴan uwan mama suka yi fushi, basu sake zuwa sun ce a basu ni ba.
Abubuwa suka ɗan faffaru, har kawu yahaya, ya ɗaukkoni daga gagarawa ya dawo da ni nan, tun da ya kawo ni, ake ta samun issues da family ɗin sa, Allah dai yayi sai na zauna a gidan, yanzu ma dai wata rigimar ce ta taso, matar kawuna ta ce zan bar gidan na koma ƙauye, ni kuma bana son komawa garin nan wallahi, mamana nake son gani, wallahi ko ba ta warke ba ko bola take bi, zan bita bolar mu rayu tare da dai in koma wannan garin da ko sunansa bana son ji, Raihan aƙalla na kai shekaru goma sha takwas rabona da mama, kuma ban ji labarin ta rasu ba, kowa yaƙi gaya mini sunan garinsu abun da na sani kawai a Maiduguri take.
Ba wanda yake kulani, duk wanda na raɓa sai ya tsangwameni, an ce mini mummuna, an ce mini mayya, an aibata ni, to wai ya zan yi nema? zuciyata ta kusa fara ciwo, ban ma san ina na dosa a rayuwata ba, tun a kan cinyar mama nake ganin bala'i da tashin hankali, raihan tafiya kawai nake yi amma na san zuciyata na ciwo, ƙwaƙwalwa ta kuma kamar na haukace nima, abubuwa suna damuna, ba wanda yake zama na gaya masa ya zan yi?" Wata irin karkarwa ummi take yi, tana magana ba comma babu full stop, wani ɓoyayyen abu ne da yake cin zuciyarta da ba ta taɓa zama ta faɗe shi ba, once in her life, yau ta samu chance.
Babu tsammani ta durƙushe a ƙasa daga kan kujerar, tana kuka mai sautin gaske.
Raihan bai san lokacin da ya durƙusa, duk da dauriya da dakiya irin ta raihan, yau da aka zo gaɓar da yake jira a zo, ya ji wacece ummi, ya ji sai dai zuciyarsa ta gaza ɗauka, zuciyarsa ta karye, ashe da ba tausayinta yake ji ba, kallonta kawai yake yi bai san meye a ƙunshe a zuciyarta ba, a hakan ma ba wai buɗa masa rayuwar ta tayi ba.
Shekara sha takwas, ba ta sanya mahaifiyarta a idonta ba, alhalin duk suna raye, bama ta san in da take ba.
Ya sanya hannun sa cikin tattausan hannunta, yana murzawa a hankali amma ya kasa magana, sai saurara sautin kukanta, da yake ƙara bugun zuciyarsa.
"Is ok salma, ya isa haka" ta girgiza masa kai ta ce "Allow me, idan na yi kuka ina jin sauƙi".
Ya ɗora hannunsa ɗaya a kafaɗarta, amma ya kasa magana.
Ganin kukan nata ba mai ƙarewa bane, ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen da suke ta kwarara ya ɗan tura baki ya ce "Nima kin sani kuka, ya isa haka please" yayi maganar yana cigaba da goge mata hawayen.
Kallon raihan take yi, da girmanta ko Abdul bai taɓa kai hannu jikinta haka ba, tana da taka tsantsan da kanta, wa ma ya damu da ita balle yayi yinƙurin kai hannunsa jikinta? Amma rarrashin nan da Raihan yake yi mata, ji take yi kamar ɗan uwanta da suke ciki ɗaya ne yake yi mata.
"Waye ya ce ke mummuna ce?"
Ta ɗan ja numfashi ta ce "Mutane" tayi maganar cikin tura baki
Hannunsa a kan fuskarta, yana goge mata hawayen ya ce "Kuma kin yarda?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki sake sakawa kanki cewa ke mummuna ce, i understand that you are traumatized by what people are saying about you, this is common among us. Ke fa malama ce ummi, kin fi kowa sanin Ubangiji gwani ne, kuma ba ya kuskure. Kin manta cikin suratul mu'iminun, aya ta goma sha huɗu, bayan Allah ya yi bayanin yadda yake tsara halittar ɗan Adam da kansa ya yabi kansa ya ce fatabarakallahu ahsanul kaliƙin? Ubangiji da ya yi ki ya yabi kansa, kuma sai ki sawa ranki cewa ba haka ba saboda surutun banza na mutane, as from today duk wanda ya ce miki mummuna, ki tabattar kin gaya masa maganar da gobe ba zai ƙara ba, fight for yourself ke ba mummuna ba ce".
"Har gorilla fa wani ɗan ajinmu ya ce mini" tayi maganar wasu hawayen na fitowa daga idonta.
Wani abu mai zafi ya soki zuciyar raihan, banda tsabar rashin mutunci ya za a haɗa mutum da biri?.
Amma ya maze ya ce "Sai kuma ki ka din ga kuka ko?"
Kamar mara wayo, ta jinjina masa kai.
Raihan ya ce "Meyasa baki tsinka masa mari ba"
Ummi ta zare ido ta ce "Haka kurum ya dake ni, ni bana faɗa"
"Ai shiyasa mutane suka rainaki ai, da kin guara masa mari, gaba ba zai ƙara ba ai"
Ta girgiza kai ta ce "Ni ban kula shi ba, muna level 3 ma aka kore shi daga makaranta ya yi satar amsa, duk abun da zan yi mutane ba za su daina ce mini mummuna ba" tayi maganar a raunane.
"Sun gano weak point ɗin ki ne, shiyasa suke amfani da hakan suna yaƙarki. Ki kwantar da hankalinki na san kawu ba zai taɓa bari ki koma ƙauye ba, and ki ƙara tuntuɓawa ko zaki samu wani information a kan in da mama take, zan yi iya ƙoƙarina na gano miki ita".
Ummi ta zabura ta ce "Dan Allah raihan da gaske?"
"I promise you salma, wannan kukan nake son na daina gani sai farinciki a fuskar ki"
"Nifa abubuwan da suke sakani kuka da yawa, ka san alfarmar da nake so ka yi mini?"
"Sai kin faɗa".
"Dan Allah ka manta na taɓa baka labarin nan, ban taɓa yin irin wannan hirar da wani ba, kai ne mutum na farko da na ji na nutsu da kai, na yi maka kuka, na rage abun da nake ji a raina, dan Allah kawai ka manta da labarin babu wani abu mai daɗi na tunawa a rayuwata, amma for now ka manta da shi, na gaya maka ne saboda na yi maka alƙawarin gaya maka abun da ya sani kuka"
Idanuwanta yake bi da kallo, ya kasa amsa mata maganar, muninta kawai yake so ya gani, amma har ga Allah ya kasa, kawai dai baƙa ce, kuma baƙi dai ba muni bane ba.
"Kayi magana mana" tayi maganar a ɗan shagwaɓe.
"Zan yi, amma ba yanzu ba, mu karya ko, zuwa azahar mu yi salla sai mu je siyayyarmu ko?"
Ummi ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ko kawai mu canza rana, kaga yau duk sai godiyar Allah".
Ya jingina da jikin tebur, ya ce "Kin sani kuka ba, marainiyar Allah, Allah ya ƙara kulawa da ke".
"Amin amma ba na ce ka manta ba".
Ya shafa sumar sa ya ce "Kema dai kin faɗa ne kawai, tashi in nuna miki aikin da zan kai wa Alhaji na gama"
Ta miƙe suka koma kan kujera, yadda ya rarraba bayar da zakka, da kujerun umara da na hajji da zasu bayar, da ƙarin da za a yi a ɗan bawa ma'aikatan na riba da sauransu.
Ummi a ranta ta jinjina dukiya tana nan a in da take, kuma yadda raihan ke gudanar da lamarinsa, ba zaka ce ɗan mai kuɗi ne haka ba, Maryam ce ma dai uwar jin kai, da jin ita wata ce.
Sai da suka yi sallar azahar, sannan suka nufi tafiya, a mota take tambayarsa ina za su je, ya ce mata zata gani.
Ya ja ɗan guntun tsaki ya ce haƙarƙarinsa a riƙe yake, zai fara koya mata mota, ya gaji da aikin direba ba a biyansa.
"Ai ba ni na ɗauke ka aikin ba, kai ka ɗauki kanka, amma ba faɗuwa ka yi ba ka ke ciwon haƙarƙari?"
"Ina fa, coach ɗina ne na gym, ya sakani ɗaga wani ƙarfe, haƙarƙarina ya amsa".
Ta kalleshi ta ce "Wai sai ka ji wa kanka ciwo tukuna, meye na zuwa gym kai ba ƙiba ba?"
Ya rausyar da kai ya ce "Waye ya ce dan a rame ake motsa jiki, bari na nuna miki ƙarfen da na ɗaga a Instagram" ya buɗe mata wayarsa ya bata.
Suna tafe tana mitar ƙarfen yayi girma, daga bisani ta cigaba da yi masa taɓe-taɓe a wayar.
Suka shiga go slow, yana jiran a basu hannu, ya ɗan leƙa wayar, ya ga ta nutsu, kallon dogwayen riguna kawai take yi tana liking ɗin su, da takalma da jakunkuna.
Ya ɗan yi murmushi, aka basu hannu suka tafi.
Katafaren kantin saye da sayarwa, suka shiga, ummi kamar ƴar ƙauye, sai kalle-kalle take yi.
"Ta ina zamu fara?"
Ummi ta ce "Ko ta ina ne ma".
Sannu a hankali suke zagayawa, suka fara zuwa wurin turarruka, ya saka hannu ya ɗauki wani, ya jefa a cikin trolley.
Ummi ta waro ido ta ce "Raihan, dubu sha takwas fa aka rubuta, ka manta kuɗin dubu sha biyar ne?" Ya kashe mata ido ɗaya ya cigaba da ɗaukar kaya.
Tayi ta magana, amma yayi mata shiru, suka je wurin kayan kwalliya ya kalleta ya ce "Me ki ke so a nan?"
"To ai kuɗin sun ƙare"
"Ke ina ruwanki ne, ɗauki abun da ki ke so kawai"
Comb ta ɗauka sai ribbon da coacoa butter, dan man yana burgeta ta ce sun isa.
"Wai ke ba kya kwalliya ne, ga su hoda da kayan mata"
"Ni bana wata kwalliya" ta bashi amsa tana ɗan kalle-kalle.
Ya ɗaukko ɗaya wayar ta sa, yana dube-dube, ya ɗaukko wasu mayuka ya koma kan mayukan gyaran gashi, suma ya ɗauka.
"Wannan me zaka yi da su?".
"Budurwata zan saiwa lefe zan fara tarawa".
Ummi ta yi dariya ta ce "Riga malam masallaci, za ta kwashi kayan shiririta"
"Ni ne ma shiriritar ko? Son kowa ƙin wanda ya rasa da ni ɗin nan, ɗan kyakkyawan matashi mai gemu, kin san maza masu gemu muna da tsada".
"Ai mami ta ce mai ka shafa ya fito"
"Wallahi ban shafa mai ba, girma na yi gemu ya fito"
"Muyi sauri kar na makara komawa gida"
Ita dai ummi ta zuba wa sarautar Allah ido, ta san dai abubuwan da raihan ya ɗauka, sun fi ƙarfin kuɗinta nesa ba kusa ba.
A wurin biyan kuɗi aka yi billing ɗin sa kuɗi masu yawa, ya basu ATM suka cire.
Gaba ɗaya ummi ta manta da damuwar da ta baro a gida, jin zuciyarta take fes, yau ta faɗi abun da yake ci mata zuciya tsawon shekaru, kuma ta samu ta yi kuka, an saurareta.
"Raihan" ya ɗago ya kalleta "Na gode sosai da lokacinka, Allah ya saka da alkhairi, ya ja kwanan Alhaji da mami"
Ya ce "Da kuma Hajiya" tayi murmushi ta ce "Amin, kuma dan Allah da ka je gida, ka yi haƙuri ka danne zuciyarka, ka bawa yaya Sagir haƙuri dan Allah"
"Zan yi in sha Allah"
"Allah ya yi maka albarka"
Kasa amsa mata yayi sai murmushi, ƙasan zuciyarsa na hango masa ita tana kuka ɗazu.
Suka isa bayan layin su ummi, ta buɗe motar ta sauka har ta fara tafiya ya ce "Ke wannan alkunyar taki tayi yawa, maimakon ki ce "Malam bani kayana, ko kin bar mini dubu sha biyar ɗin taki?" Ta waiwayo ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya fito daga motar, ya ɗaukko kayan yabi bayanta, ta tsaya cak ta waiwayo ta ce "Ina zaka ne?"
"Gidan zan biki na kai miki kayan"
A rikice ta ce "A'a dan Allah"
"To karɓi kayanki"
"To ya zan yi da su, idan aka tambayeni....
"Ki ce da salarynki ki ka saya, ba wasu kaya ne masu yawa ba fa, ya kamo hannunta ya danƙa mata ledar ya ce "Zan je gida na cika alƙawarin da na yi miki" ya juya ya koma motarsa ya tafi.
Cikin mamki ummi take kallon kayan, wai duk wannan nata ne? Amma uban kuɗin da raihan ya kashe, dubu ɗari da sha takwas, kayan mai turare da ciye-ciye.
Cikin matsananciyar fargaba ta shiga gidan, kasancewar ɗakinta ne a farko, ba ya cikin main safe contain na gidan, shiyasa ba sa sanin shige da ficenta.
Ta kalli agogo ta san noor tana makarantar islamiyya, da ta kirata ta gani.
Tayi alwala ta yi sallar la'asar, ta zauna ta din ga kallon kayan, wannan mayuka masu uban tsada, ita za ta shafa a fatarta.
Wai har da hoda, to ita mai za ta shafawa hoda ma? Ta ɗau turaren tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyi da daɗin gaske.
Ga roll on, kusan kala huɗu, wanda kullum cikin dabaru take na haɗa alumun, ko ta jiƙa gishiri bayan yi wanka ta shafe jikinta, saboda kar ta yi wari.
Wata envelope ta gani a cikin kayan, wadda ba ta san da ita ba, ta ɗauka ta buɗe taga kuɗi a ciki sai takarda.
"Assalamu alaikum, brown eyes, this is your first salary, given to you 15th April, spend it well, ga additional na 15k making 30k, ki lallaɓa na ji daɗi na kuma gode da shopping, Allah ya ƙara arziki ummita. Raihan" galala take bin takardar da kallo, Raihan ya mayar da ita sakarya ma.
Wurin Alhaji ya fara zuwa, ya tarar da mami, da kuma Hajiya tare da Alhajin.
Cikin damuwa mami ta ce "Raihan sannu da zuwa, ba abun da ya sameka dai ko?"
Ya ce "A ina?"
"An ce mini Sagir yaje har office, ya yi yinƙurin dukanka, na kira wayarka baka ɗauka ba, na zo in ji ba'asi".
Raihan ya haɗe rai ya ce "In ji wani munafukin ne ya faɗa?".
Alhaji ya ce "Bai yi maka komai ba dai ko?"
"To aini Alhaji ban gane yayi mini wani abu ba?"
Sagir yayi sallama, suka amsa banda mami da take sababi tana faɗin "Wallahi dole ka ɗau mataki Alhaji, kar a kassara mini ɗa a cuceni"
Cikin dakiya Hajiya ta miƙe ta ce "Sagir, uban meye ya kai ka wurin raihan, ka yi yinƙurin dukansa?" Yayi shiru yana kallon Hajiyan.
Alhaji ya ce "Yi masa a hankali, ni na tura shi wurinsa, ban san kuma haka zata faru ba, zo ka yi mini bayanin meyafaru?"
Cikin fusata hajiya ta riƙo rigar Sagir ta ce "Ba magana nake yi maka ba? Zuwa ka yi kayi rashin mutunci a gaban mutane ko sagir? Idan baku yi abun da za a ce baku kyauta ba ba kwa jin daɗi ko?"
Raihan ya cire hannun Hajiya daga jikin Sagir ya ce "Duk fa baku fuskanta ba, ya zaku ɗauki zafi a kan abun da ba a gabanku aka yi ba? Ni ne mai laifi abun da na yi wa yaya Sagir yana gaba da ni ban kyauta ba, kuma da niyyar ba shi haƙuri na dawo, bai kamata ba yadda na yi treating ɗin sa, dan Allah ka yi haƙuri yaya Sagir" wani irin mugun kallo Sagir yayi masa, tare da tunanin wata shiryayyiyar ce Raihan da babarsa suka shirya, kawai ya juya zai tafi, Hajiya ta bishi a zafafe, Raihan ya riƙeta ya girgiza mata kai, kawai ta fashe da kuka zuciyarta na yi mata zafi.
"Jarrabawa ce mai buƙatar juriya Hajiya, ki daina yi masa kuka" raihan ya faɗa da sigar rarrashi.
Mami kuma sai rashin mutunci take yi, tana yaɓawa Hajiya magana, Raihan ya dafa kafaɗarta ya ja ta suka bar falon yana rarrashinta.
"Gaskiya Alhaji ka saka baki, yaranta ba za su lalace kuma ta din ga nema ta ƙwace mini ɗa ba, alhalin yaranta na barazana ga rayuwar Raihan ba.
Ummi ta yi ta kiran raihan a waya, amma sai ta ji busy, bama ta shiga gaba ɗaya, haka ta haƙura ta ajiye ta tafi kitchen dan yin sanwar dare.
Farida ta daka mata tsawa, ta ce kar ta kuskura ta shigar mata kitchen, ba ta buƙata, domin kuwa barin gidan za ta yi.
A karo na farko da ummi ta ji ko a jikinta, yau ta samu hutu.
Alhaji Tahir ya kira meeting na gaggawa na iyalansa, da manyan manajojinsa da lawyoyinsa gidansa, bayan sallar isha'i.
Suka din ga mamakin hakan, dan kuwa ba su san dalilin hakan ba, dan bai taɓa yi ba.
Raihan yana maƙale da Hajiya, dan tun ɗazu da suka bar falon, sashinta ya koma ya tare yana rarrashinta.
"Bakomai ne ya sanya na taraku a halin yanzu ba, sai dan gabatar da wani hukunci da na yanke, wanda na daɗe ina nazarinsa kafin yanke shi.
Daga yanzu Raihan zai riƙe office ɗina, na tsawon shekara guda, ni kuma zan koma gefe ina monitoring ɗin ayyukan sa, duk hukuncin da ya zartar kamar ni na yi ne, duk mai buƙatar wani abu, zai yi a rubuce ya kai masa, yana da damar sallama ko ɗaukar ma'aikata, kar wanda ya zo ya sameni ya sani in yi masa wani abu, wurinsa za aje. Aikinka tuƙuru shi zai tabattar da kai a kan wannan kujera mai nauyi, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan sabon MD na Tahir and Son's Limited.
Wata irin razana raihan yayi yana kallon mahaifinsu, yayin da Mami ta rangaɗa guɗa tana faɗin "Ƙaraminsu babbansu, ka ga ɗan ƙaramin sauro mai hana giwa bacci"
Hajiya da yake zaune kusa da ita ta yi murmushi ta shafa sumar Raihan ta ce "Allah ya tayaka riƙo babana, Allah ya tsare mana kai"
Raihan kuwa miƙewa yayi ya bar falon, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan Allah ya gani baya so, kuma