ta, da nuna mata kulawa kawai ya ga hawaye na zubowa daga idonta, tun daga kan auren Idiris ba ta taɓa zaton zata samu miji da zai nuna mata kulawa ba, hakan ba ƙaramin tayar masa da hankali ba.
"Sweetheart na yi miki wani abu ne da ba dai-dai ba? Dan Allah ki gaya mini menene me na yi miki? Ko abum da na yi ne ya ɓata miki rai?"
Ummi ta share hawayen ta ce "Bakomai fa, wani abu na tuna ne kawai"
"Dan Allah kar ki sake tuna abun da zai saka mini ke kuka please, kar ki ɓata mana farincikin da muke ciki mana, abun da ya wuce ki bar shi a baya, yanzu sabuwar rayuwa zamu gina baby, dan Allah ki daina" yayi maganar yana share mata hawayen fuskarta, ya rungumeta suka kwanta.
Sai yanzu yake yi mata abun novel ɗin da take tunani, yana ta yi mata magana mai sanyaya zuciya, wasu maganganun ma kamar ta toshe kunneta dan kunya, dan a duk rashin jin raihan, ba ta yi zaton jin wasu maganganun daga bakinsa ba.
Can gida kuwa ƴan gagarawa na koɗa gidan ummi, dan sai da kausar ta je gidan, kuma sai da ta ɗaukko wa babr su videon komai, ta zo ta nuna mata.
Nan ɓangaren su mariya ma haka ne, ana ta santin gidan ummi, da irin maƙudan kuɗin da mijinta ya kashe a kan aurenta.
Mariya ta ce "Yaya maryam kin gani ko? Ina da kyakywan yaƙinin ummina ba za ta tozarta ba, na yaba sosai da nutsuwar mijin nan nata"
Yaya maryam ta ce "Shiyasa kullum nake cewa ki din ga yi mata addu'a, yawan damuwar ba shi ne ba, ke dan ma baki je kin ga gidan ba, zuwa gobe in Allah ya kaimu kafin mu tafi, sai mu je ki gani"
Mariya ta yi murmushi ta ce "Yaya Maryam kenan, mai ɗaki shi ya san in da yake yi masa yoyo, ba zaku fahimci halin da na shiga ba a kan raba ni da ƴa ta"
"Eh dama ya za ayi mu gane mara kunya, ƴar farin ki ke wa haka" mariya ta sunkuyar da kai tana murmushi.
Kiran sallar farko, Raihan ya tashi, da ƙyar ya yaƙi shaiɗan ya saukko daga kan gadon, ya je yayi alwala ya gabatar da nafiloli, sai da aka kira sallar asuba, ya tashi ummi shi kuma ya fita masallaci.
Kafin ya dawo ta yi salla, ta koma kan gado, saboda gajiya da kuma bacci da take ji.
Jin motsinsa a kan gadon ne ya sanya ta farka ta buɗe idonta da ƙyar.
"Kin yi sallar ne?" Ta jinjina masa kai tare da cewa "Good morning" cikin kasalalliyar muryar bacci.
"Morning honey, duk gajiyar ce ne, ake yi mini shagwaɓa" murmushi ta yi tana ƙoƙarin juyawa, amma ya riƙe ta ya sumbaci goshinta, ya gyara kwanciyarsa shima a gajiyen yake, dan haka bacci duk yayi awon gaba da su.
A hankali ya yi juyi, ya nemi ummi ya rasa, kamar aljana, ya daɗe a kwance yana miƙa, sannan ya saukko ya fito, can ɗaya falon ya ganota, tana ta zazzagawa tana kallon ko ina, ta saka dogon hijjabi abun ta.
Fito yayi, hakan ya ɗan razanata ta waiwaya.
"Me ki ke nema ne?"
Ta ce "Bakomai, kawai na gaji da kwanciyar ne na tashi"
Ya ƙaraso falon ya ce "Sai ki ka tashi ki kar bar ni? Ni fa yunwa ce ta taso ni ma, bari na kira hajiya a kawo mana abun karyawa kan mutane su fara zuwa"
Ta ce "Da in girka mana, kar a wahalar da su" ya girgiza kai ya ce "No, kina buƙatar hutu, kuma gidan bakomai na masarufi, ban sayo ba tukuna bari na kira ta, akwai sponge da sabulu da toothpaste a drower mudubin ɗakin da muka kwana, ki shirya kan mu fara baƙi".
Ta ce "To"
A ƙalla ta kai awa guda, sannan ta dawo falon, yana kwance a kan doguwar kujera, yana danna wayarsa, ya ɗaga kai ya kalleta cikin dogon hijjabinta, ya girgiza kai tare da yin murmushi ya ce "Wane irin wanka ne haka fiye da awa goma?"
Ta ce "awa goma tun jiya kenan fa"
"Ai kin daɗe ne, ƙaraso mu gaisa mana amaryata"
Cikin matsananciyar kunya, ta ƙarasa gaban sa, ya tashi ya zauna, tare da zaunar da ita a kusa da shi, ya ce "Kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau"
"To ya jikin naki? Are you ok now?"
Ta sunkuyar da kai, tana murza yatsun hannunta, da ya zame mata ɗabi'a idan ba ta da amsar bayarwa ga tambaya.
Cikin son ƙureta ya sake cewa "To ya daren jiyan?"
Mutsu-mutsu ta hau yi, za ta tashi ta tafi, dan raihan ɗin ya wuce tunanin ta, kamar an canzo wani.
Riƙeta yayi ya ce "Ba in da zaki fa, yanzu dai bari in rama dukan da ki ka yi mini jiya, poor me kin kusa karya mini ƙashi, you even bite my tongue daga kiss"
"Zan je ɗaki in yi abu" tayi maganar cikin rauni.
Yana dariya ya ce "Koma menene yi a nan, amma sai na rama" wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗaga yayi sallama, daga bisani ya ce "Ok"
Ya katse wayar ya ce "Bari na karɓo mana abincin, hajiya ta aiko" ta jinjina masa kai ya tashi ya fita.
Tayi ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo.
Shiru ta yi ta tuna irin cin zarafin da idiris yayi mata, ta kwana a waje tsirara cikin ruwan sama, saboda kawai ya same ta da larura, ta girgiza kai abun kamar ba zai wuce ba.
Raihan ya yi sallama da ƙaton kwando, ta tashi ta karɓe shi, suka iso falon suka zauna.
Sai dai ita ta kasa sakewa ta ci abinci, sai cakala take yi, ya ci ya ƙoshi, ya hau kan kujera ya kwanta sai bacci.
Ummi ta lallaɓa ta bar masa falon.
Sai azahar sai ga su yaya maryam da mama, dan a washegari za su koma maiduguri, ummi ta ji daɗin zuwansu, kamar ba jiya suka rabu ba.
Suka kawo mata soyayyayiyar miya ta sha kaji, har da kayan gara, sun kai ruwa rana da dr. A kan kayan garar nan, ya ce ba addini ba ce ba, idan ma sai an yi su bari a kwana biyu shi zai yi mata da kansa, suka ce sun riga sun zo da ita, sai dai ya yi haƙuri.
A nan wasu daga dangin su raihan ma suka zo, suka tarar da su, wanda ba su samu damar zuwa ganin gida ba, ciki har da wasu daga ƙannen mamin raihan.
Kallonta suke suna zunɗen ummi, ganin yadda take tafiya a takure, kamar mara kuzari.
"Ji munafuka, kowa fa ya san bazawara ce, amma ji salon kinibibi da iskanci, wai a dole sai ta nuna wa mutane budurwa ce" suka yi ta surutun su, ummi ba ta ma san suna yi ba.
Da za su tafi, mariya ta kama hannun ummi, tayi ƙasa da muryarta ta ce "Mamana, kin shiga sabuwar rayuwa, duk da baki da wayo sosai lokacin da na yi rayuwar nawa auren, amma aure ba soyayya ba ce kawai, kowane aure da kalar jarrabawarsa, ni na samu soyayyar miji, ƙalubale na danginsa ne.
Ki riƙe Allah ki ji tsoron Allah, babu abun da ya gagari Allah, kar ki bari ki yi nesa da Allah, babu abun da zai yi galaba a kanki, sai abun da Allah ya ƙaddara. Ki riƙe mijinki domin Allah, banda yaji ko kan ƙara, matar da ta isa a ɗakinta take yi wa miji yaji, ayi haƙuri, ayi haƙuri da juna" sosai mariya ta yi wa ummi nasiha, sai dai a ƙarshe ne kuma ta koma shirme.
Da za su tafi ummi ta je ta kira shi, sai dai bai ji daɗin garar da suka kawo ba, yaya maryam ta ce masa ai su normal ne al'adar su ce.
Bayan tafiyar su ummi ta dudduba kayan da suka kawo mata, ta je kitchen ta jera wanda za ta jera, kayan miya, busasshshen kifi, man shanu da sauran su.
Kasancewar raihan ba ya ɓangaren da take, kuma duk baƙin sun tafi, ya sanya ta ɗan sake, tana ta ɗan gyara in da aka ɓata.
Tana ta gyara abun da bai yi mata ba, tana yi wa kawu addu'ar samun buɗi da alkhairi mara yankewa a duniya da lahira, kamar an ce ta ɗaga kai, ta hango raihan a tsaye yana kallonta.
Ta miƙe tsaye ta ce "In zo ne, kana buƙatar wani abu?" Ya ɗaga mata gira.
Ta nufi in da yake tana takawa a hankali, cikin tafiyarta da yake cewa yanga ce tayi mata yawa.
Ta ƙarasa ta ce "Gani"
Ya riƙo hannunta ya ce "Dama kin tambaye ni ina buƙatar wani abun ne, mu je daga ciki to, sai na gaya miki me nake buƙata" danƙarewa ta yi a wurin taƙi yin gaba.
"Ya haka kuma? Ke fa ki ka tambaye ni"
"A'a to na janye tambayar" ta yi maganar tana son ƙwace hannunta.
Raihan ya yi dariya ya riƙe hijjabin jikinta ya ce "Ummi nan fa ba muhallin hijjabi bane yanzu, aure muka yi, dan Allah ki cire shi na din ga ganin kwalliyar ke ko zafi ba kya ji"
Ummi ta ce "To, zan din ga cirewa"
"Ai yanzu nake son ki cire" yayi maganar yana cire hijjabin daga jikinta.
Doguwar rigar material ta saka, sai ƙamshi take yi, ya cire mata ribbon ɗin kanta, gashin ya sauka a jikinta, ya gyagygyara mata zaman gashin ya ce "Masha Allah, what a beautiful creature" yayi maganar yana murmushi.
Tura baki tayi tana ƙoƙarin karɓar hijjabinta daga hannunsa.
Ya riƙo ƙugunta yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, tabbas ba dan ummi ta kasance ma'abociyar suturta jikinta ba, da babu shakka mutanen banza su din ga bin ta, saboda duk in da ake fasalta mace mai diri, Allah ya yi wa ummi dirin jiki mai kyau da ɗaukar hankali.
Suka koma falon suka zauna, sai dai ya hana ummi sakat da tsokana kala-kala, kuma ya riƙeta a jikinsa.
"Komai na ki perfect baby, da headmastern nan ya yi gardama, da na yi masa abun da ban taɓa yi ba"
Ummi ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Wai dan Allah me ka ce masa ya fasa?"
Raihan ya yi murmushi ya ce "Dubu ɗarin da ya ce zai baki kuɗin aure, na bashi uku, na ce aje a mayar da wadda aka saka a kula da iyali na gida, ya bar mini ke, jikinsa na rawa ya bar mini ke, dama na gaya miki na fi kowa sonki" yayi maganar yana haɗa fuskar sa da ta ta yana murmushi.
"Cin hanci ka bashi dan ya bar maka ni, cin hanci ba kyau"
"A nan ya halarta" yayi maganar yana dariya.
Raihan na ƙoƙarin ɗaukar su zuwa wata duniyar, wayarsa ta fara vibrating, sunan mami ne a kan screen ɗin wayar, ya ɗaga tare da yin sallama.
"Raihan har ka fi ƙarfin ka zo in da nake ka gaishe ni ko?"
Ya san a rina, ya kwantar da ummi a jikinsa sannan ya ce "A'a ba haka bane mami, zan zo ne"
"Zaka zo sai yaushe? Har an yi ƙulle-ƙullen da zaka kasa zuwa ka gaisheni?"
"Mami, wallahi a gajiye nake ne sosai da sosai, na kira ki ma da safe baki ɗaga ba, but an ce mini gida haryanzu da mutane, na ce bari na ƙyale ki, sai da daddare, amma in sha Allah a satin nan dole na na zo gaishe ki, na gaji ne sosai....
"Dalla rufe mini baki, nusari shashasha. Yaushe aka yi daren da gari zai waye? Lallai lallai ka zo gida ina son ganinka, yarinyar nan safiyya ma na kwance babu lafiya duk saboda kai, kar ka bari ka fusata ni"
Raihan bai yi mamaki ba, ya san a rina, amma shi bai ga haɗin rashin lafiyar safiyya da shi ba, asibiti zai kai ta ko me zai yi mata? Kodayake ba abun mamaki bane ba idan mami na jin rigima.
"Shikenan mami, zan zo in sha Allah" sai dai tun da aka ambaci Safiyya, yana jin yadda bugun zuciyar ummi ya ƙaru a ƙirjinsa.
Ya saka hannu ya ɗagota, amma taƙi kallonsa.
"Sweetheart, an fara kiran sallar magariba, bari na yi alwala na tafi masallaci" ba ta kula shi ba, ta tashi ta nufi ɗaki, ya bi bayanta da kallo, zubin manyan mata sosai.
A hankali ya ce 'Haba mami, is too early for that'.
Bai je kiran mami a ranar ba, dan ya san idan ya je da mutane a gidan, kuma sai ta yi wani abun da zata ci mutuncin ummi, a gaban mutane dan haka ya ƙi zuwa.
Kwanan ummi uku a gidan raihan, ta fara girkin abinci, sai dai rigimar raihan har mamaki take bata, baya zuwa ko ina sai salla, yana maƙale da ita kamar cingam, ga wani irin mugun kunyarsa da take ji, ta kasa sakewa da shi, kusan kullum cikin ƙorafin saka hijjabin nan yake, ta kasa daina yawo da hijjabi.
Kwana na ukun da daddare, Raihan ya je gida, sai da ya je wurin Hajiya yayi mata bangajiya, Alhaji dama baya nan, washegarin ɗaurin aure ya tafi umara.
Sai dai cikin fargaba ya isa sashin mamin.
Ya tarar da ita ta hakimce, gefe ga Nihal a zaune, sai Safiyya da ke kwance a kan doguwar kujera.
Yana shiga suka gaishe shi, ya amsa musu, sannan ya je gaban mami ya risuna yana gaisheta.
"Sai yau Allah ya nufe ka da zuwa? Har ka sallami kanka na yi maka waya ka zo raihan amma ka ƙi"
"Ba ƙi na yi ba mami, wallahi bana iya zuwa ko ina, zirga-zirgar bikin nan na gaji ne wallahi"
"Uwar zirga-zirgar bikin, ka fito fili ka faɗi uban abun da ya hanaka fitar, na yi dana sanin cewa zan yi maka aure ina ganin mafita ce, ashe ruwan dafa kaina ne, ka kwaso bazawara da ta tafi ƙarfin ka, wallaahi ka shiga hankalinka, ka san abun da yake yi maka ciwo"
Ta din ga yi masa faɗa na babu gaira babu dalili, ƙarshe ta rufe da cewar, watanni uku ta bashi, yazo ya nemi auren Safiyya.
Ya ji ta da kunne kawai, ta gama ya ce zai tafi, ta ce ba zai tafi a lokacin ba.
Ummi kuwa na gida na ta duba agogo, dan be gaya mata zai je wani wuri ba.
Har ƙarfe goma saura shiru bai dawo ba, ta kasa jurewa ta kira wayarsa.
Bai ji nauyin mami da ke zaune tana kaɗa ƙafa cikin isa ba, ya ɗaga wayar ya ce "Hello dear".
"Ina ka tafi tsoro nake ji"
Yayi murmushi ya ce "Gani nan, babu dodo a gidan fa"
"Dan Allah ka yi sauri, tsoro nake ji sosai ko falo na kasa fita".
Mantawa yayi da mami a wurin, yayi dariya ya ce "To yi ta addu'a kan na dawo? Kin ci abinci ne?"
"A'a"
Ya ce "But you are not hungry ko?"
Ummi ta ce "Eh"
"Ok ki jirani, in sha Allah yanzu zan taho"
Muryar mami ta jiyo tana cewa "Zaka ajiye wayar nan ko sai na ci ubanka mara kunya" a rikice gaban ummi ya faɗi, ta kashe wayar ba ta san gidan ya je ba da ba zata kira shi ba.
Mami ta tashi ta shiga ɗaki, raihan ya ɗau mukullin motarsa ya fice da sauri.
Abun da raihan yayi, ba ƙaramin mamaki ya bawa mami ba, dan mugunta ta shirya yi, ta zaunar da shi har sha biyun dare, daga nan ta ce dare yayi ba zai fita ba sai da safe, bisa ga miyagun shawarwarin da Anty rakiya ta bata, sai dai abun da raihan ɗin yayi ya bata mamaki.
Ta din ga kiran wayarsa amma a kashe.
A bedroom ya tarar da ummi, kai da ganin ummi ka san a tsorace take, ya ajiye kayan hannunsa ya ce "Sorry dear, yi haƙuri"
"Ban haƙura ba" ta yi maganar cikin shagwaɓa.
"Yi haƙuri, ayi mini afuwa" ba ta nuna masa ta san in da ya je ba.
Ya cika cikinsa da abinci, yana ta yabonta tare da santin abincin.
Ya koma ya hana ummi sukuni, ya gama tara mata gajiya, suna kwance babu tsammani ta ji ya ce "Salma, me ki ka yi wa mijinki na farko ku ka rabu?"
Gyara kwanciyar ta tayi, ta ce "Meyasa ka tambayeni?"
Ya kalli fuskarta ya ce "Am just curious about it"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin babu daɗi, auren huce takaici aka yi masa da ni, saura kwana uku aurensa, ba ya so na, ranar da ango ya tare a tsakar gida na kwana cikin ruwan sama, ba ya so na, tuntuni ni mummuna ce kuma ya rasa wadda yake so yayi niyyar aure. Auren watanni biyu ne dai bai kai uku ba ma, watanni mafi tashin hankali, marasa daɗin tunawa, na tozarta sosai a aurena na fari ko tunawa bana son yi" tayi maganar tana zubar da hawaye.
Ya rungumota jikinsa yana share mata hawayen, ya ce "Is ok, you are much more than special, ke ta daban ce, kuma ya yi wa kansa, ni kuma ya taimakeni irin sosai ɗin nan fa" yayi maganar yana ƙoƙarin zolayarta.
Da safe da ya kunna wayarsa, da kiran mami ya fara cin karo, ya ɗaga ta ƙare masa zagi tsaf, amma ko a jikinsa, shi kasancewar sa da ummi, mantar da shi komai yake yi. Duk da kunyarta har ta yi yawa.
Abu kamar wasa, raihan ya shafe sati biyu cirr a gida, ummi ba ta da aiki sai ɗorawa da saukewa, abokan aikinsa su ka zo ummi ta yi musu girki, har da ƴan china.
Raihan ba ya jin duk wanda zai zo gidansa, saboda matarsa ta iya girki.
Haka zalika ga rigimarsa da ba ta ƙarewa.
Gidan farida kuwa, tun da Allah ya sa ummi ta bar gidan, komai ya taɓarɓare, kausar mugun sok jiki, ba ta iya aikata komai, noor ce ma mai ƙoƙartawa, ita ma idan ta gaji, sai ta watsar da aikin ta ce ta gaji, idan aka tursasata kuma, tayi abun da ba a so.
Uban wankin da ummi ke yi musu, babu wanda zai yi yanzu, mopping gyaran ɗaki, da kuma girki duk abubuwan sai a hankali, girkin ma ba daɗi yake yi ba.
Farida ta ce sai an samo ƴar aiki, dr. Ya ce babu mai kawo masa ƴar aiki, idan aka kawo ta kuwa sai dai ta din ga biyanta, babu yadda za ayi ga kausar a gida, ba aure ba karatu, ace an ɗaukko ƴar aiki.
Dr. Ya kira ummi ya tambaye ta me take so ayi mata da kuɗin sadakinta, ta yi tunanin wata sana'ar, ya bata jari sauran ya cika ya saya mata kadara.