x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 49 - CUTARWA

  • 144001 words
  • 147000 words
  • Out of 215027 words

Category: Tale Stories

Views 533

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yana tsaka da aikin ma idan ya so ganinta sai ya ajiye yayi tafiyarsa wurinta.

Ummi ta dage a kan cewar, raihan ba zai saka mata kuɗin lefe a account ba ita tsoro take ji, yayi yayi da ita taƙi yarda.

Hajiya Aisha ce ta din ga kiransa tana tambayar sa ya batun lefe, ya ce mata sai sun yi aure zai yi mata, yanzu akwai matsala.

Hajiya Aisha ba ta takura masa a kan sai ta ji matsalar ba, ta san ta mecece dan haka ta ƙyale shi.

Amma ta ce masa dole ya yi wa ummi kayan fitar biki na gani na faɗa, ya amince da hakan ya ce mata su ba zasu yi wasu bidi'oi ba, sai an ɗaura aure juma'a zai yi reception da abokansa da ƴan uwansa, ita kuma su yi taronsu Saturday a kaita.

Lokacin biki ya cigaba da ƙaratowa, dr. Shikaɗai yake faɗi tashin sa, babu mataimaki sai Allah, babu wani wanda zai ba shi shawara, shi yake ta ƙoƙarin playing both roles ɗin, ya kira raihan ya tambaye shi ya yanayin gidan da zai ajiye ummi, saboda ya san me zai saya, raihan ya ce masa kar ya takura kansa yayi iya abun da zai iya yi.

Ummi ta sanar da dr. Abun da raihan ya ce mata a kan kayan lefe, dr. Ya ce "Ummi, ba kayan lefen ba, zaman aure mai ƙarko dan dai kayan da zaki saka, ni zan yi miki kar ki damu"

Ummi ta ce "Dama ba damuwa na yi ba, gaya maka dai kawai na yi"

Ya ce "Yauwwa mamana, na san ba zaki damu ba dama, Allah ya yi miki albarka"

Ta amsa masa da amin.

Dr. Kallon farida kawai yake yi, dan tuni ya san an kori kausar daga makaranta, amma taƙi gaya masa sai gaba da take yi da shi ma, a kan abun da ya faru tsakanin ta da ummi.

Message ɗin da ummi da tayi tozali da shi a wayarta ne ya girgiza ta, ta duba lambar ba ta maryam ba ce ba, dan ta daina ɗaga kiran maryam, idan tayi mata message kuma gogewa take yi.

Ta duba lambar a Truecaller ta ga an rubuta safiyya.

Shiryayyen zagi ne na cin mutunci da cin zarafi ta shiryowa ummi mai zafin gaske, tare da tabattar wa da ummin cewa ita ce matar da aka zaɓa masaya aura, dan haka ko ta aure shi tamkar zaman haya za ta yi a gidansa.

Ran ummi yayi mummunan ɓaci, ta sake duba message ɗin, sai ga kiran wayar lambar ya shigo wayarta, kamar kar ta ɗaga, sai kuma ta ɗaga ta saka a kunnenta ta yi sallama.

"Na san zuwa yanzu kin ga message ɗina ko? To kina magana da safiyya matar da raihan zai aura, tun wuri idan ki na son kanki da arziki, ki fita harkarsa, domin kuwa babarsa ba son ki take yi ba, mummuna da ke har zaki ce zaki aure shi kin yi masa asiri dan mugunta, to wallahi raihan nawa ne kuma sai na aure shi, ke ban da mugunta ma kina bazawara ni kuwa budurwa ce, ba zaki haɗa kanki da ni ba, mummuna kawai" gaba ɗaya kalaman yarinyar ya tabattar wa da ummi yarinya ce.

Ummi ta yi murmushi ta ce "To meye a ciki safiyya? Namiji ba mijin mace huɗu bane ba? Sai ya auremu duka mu yi zamanmu, da matar so da matar shige, sai a cika bakin bazawara da budurwa, ai ni bani da damuwa ki tambaye shi ki ji, lafiya ƙalau zamu zauna da ke, in dai wannan alfarmar ki ke nema, na yi miki ƙanwata Allah ya bamu zaman lafiya"

Ta katse kiran ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri, dan ba ta tunanin daga ƙuruciyarta zuwa yanzu, ta taɓa tsaya wa ta mayar wa da wani martani ba.

Ƙasan zuciyarta kuma wani irin tafasa yake yi mata, da tuna yadda take ce mata wai ita ce matar da aka zaɓa masa, lallai akwai aiki a gabanta kamar yadda yake gaya mata, to meyasa bai gaya mini ba?' ta tambayi kanta.

Kiran Safiyya ne ya cigaba da shigowa, amma tayi banza ta ƙi kula wayar, har magariba tayi ranta a ɓace yake, da ta tuna maganganun Safiyya sai wani irin haushi ya kama ta.

Tana kallon kiran raihan da ta yi saving lambar da MD, amma ta yi burus da shi, taƙi ɗaga kiran.

Abun ya bashi mamaki, dan haka da safe ya zo har gidan, ya duba ko bata da lafiya ne.

Amma ya ga ta fito da shirinta na zuwa aiki, har ya fara murmushi, kawai ya ga ta yi gaba, ba ta nufo in da yake ba, kan ya bita ga shige lunguna, ta ɓulla titi ta haye napep ta yi tafiyar ta.

Nan da nan raihan ya kiɗime, ya fara tunanin laifin me yayi mata? Da take share shi haka? Ya rigata isa wurin aikin na ta, ya tarar mai gadi ya buɗe wurin yayi shara.

Ya shiga ya zauna, yana jiran isowarta, da ta iso ɗin ma, tana kallonsa ta ajiye jakarta ta shiga hidimomin ta, kallon ta kawai yake yi, ya zuba mata ido yana son gano meyake damunta, ko me yayi mata, amma ya kasa gano komai.

Ana ta kirnaa a waya, ana jiransa amma yana zaune yana jiran ummi ta gama jan ajin ta saurare shi.

Shi yadda ta share shin, take abubuwan ta ma, burge shi yayi, da alama fushi take yi.

Ga wani irin kyau da ta yi kamar ya sace ya ya gudu, ta yi kyau sosai da sosai, ta ɗan washe sai sheƙi fatarta take yi.

Ta zo ta zauna, ta kunna computer ta, za ta fara aiki, ya zuba mata ido, duk da a takure take da kallon, amma ta wani maze.

Dukan teburin yayi da ɗan ƙarfi, sai da ta razana, ya ce "Yaushe zaki saurare ni ne?"

"Ba rana ta bashi amsa tana harararsa" a ransa ya ce "Wow, ta fara iya tsiwa"

Ya kwantar da murya ya ce "Ayi haƙuri dan Allah, laifin me na yi ne? Kina kallona har ki ka share ni ki ka yi tafiyarki?"

"Ai na zata ɓatan kai ka yi ai, gidansu Safiyya zaka je"

Wani irin shock ya ji da abun da ta faɗa, wani irin shu'umin kallo yayi mata, sannan ya ce "Wacece Safiyya kuma?"

"Ka fi ni sani ai, idan ka san an haɗaka da wata a gidanku, ni me zaka yi mini?"

"Ke a ina ki ka santa?"

A ɗan ƙule ta ce "Wace irin tambaya ce wannan? Kirana ta yi a waya" tayi maganar tana tura masa wayarta.

Ya ɗauki wayar yana dubawa, kawai ya kwashe da dariya.

Ta zuba masa ido tana kallon sa, ya ce "Kina da haƙuri da kawaici a kan komai, amma banda kishi kenan? Aishikenan gaskiya ne Safiyya ita ce wadda ake son haɗa ni da ita, ni kuma ke nake so, shiyasa na ce miki akwai ƙalubale, ko ba komai safiyya ta saka na gane in da ki ka dosa, yanzu zaɓi ya rage naki sweetheart, ki kula da ni sosai kar Safiyya ta ƙwace miki ni, kin san zuciya na son mai kyautata mata, ke kin ce ba kya so na, safiyya kuma tana so na, ki zage damtse kar ki bari a ƙwace ni, i so much love you baby"

Ɗaga ido tayi ta kalleshi, ya ga kamar hawaye ne yake shirin taruwa a idon ummi, ya tashi tsaye ya ce "Bari in tafi wurin safiyyan, tun da ita take so na, na san zata yi mini, idan kin tashi ki kirani"

"Idan ka je kar ka dawo, a ɗaura muku aure yau"

Gwalo yayi mata ya ce "Ki gama iyayin da tsiwar, raihan ɗin dai ki ke so".

Ayshercool
08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

                        *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

36

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

AFUWAN BAN YI EDITING BA

36

Ya fice daga shagon yana murmushi, ta iya ɓoye fushinta da damuwa, amma ta gaza ɓoye kishinta.

Yana tuƙi yana tuno fuskarta, wai har da yin fushi saboda shi, fushi sosai kishinta ya fito.

Ya shafi gemunsa ya ce "Ina sonki sosai salma, in sha Allah idan na aureki ba zaki sake yin kukan damuwar rashin wani abu ba"

Ummi kuwa, tayi shiru tana tunani, tare da ganin kamar tayi wauta raihan ya gano tana kishinsa, tayi guntun tsaki za ta cigaba da aiki, kawai sai Safiyya ta faɗo mata.

Sai gabanta ya faɗi, gaskiya ne akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, amma ita babu abun da ya taɓa haɗa ta da Idiris har suka rabu, a take kuma tunaninta ya sauya da tunanin kar matsalar da ta faru da ita a farko ta sake faruwa da ita.

Tayi shiru tana tunani menene mafita? Ita ba ƙawaye ba, mamanta kuma ba lafiya ba su yaya maryam kuma ba sabawa suka yi ba, ko da sun saba ma, ba zata iya gaya musu wannan lamarin ba.

Ta din ga saƙe-saƙe a ranta, ta tuna duk da tsanar da Idiris yayi mata, larurar nan ta ƙara taka muhimmiyar rawa, wurin kashe mata aure, dan da ya samu abun da yake so, da sai ya gama moreta kan ya saketa, ta tuna yadda ya din ga ƙoƙarin haike mata tana yarinya, take ta kawar da tunanin, dan a duk lokacin da ta tuna har kuka take yi, yadda Idris ɗin yake lalubeta, ba ta jin a duniya ko zata yafewa kowa za ta iya yafewa Idiris, ba ta riƙe CUTARWA! idan an yi mata amma cutarwa irin ta iya da Idiris ba zasu goge a tarihin rayuwarta ba cikin sauƙi.

Ta cigaba da tunani a irin wa'azin da take bibiya, mussman na malamai daban-daban da sauran shirye-shiryen gidajen rediyo, domin kasancewar ta ƴar jarida, ya sanya tana yawan sauraren Radio, da bibiyar labarai, ta fuskanci cewa duk soyayyar da namiji yake yi wa mace, idan aka samu naƙasu akwai matsala, ƙila ba lallai raihan ya jure ba ya auro safiyya su juya mata baya, kamar yadda aka yi wa inteesar.

Sai kuma kawai ta ga abun banbarakwai, wai ace raihan ya aureta shi ne mijinta, ta haɗa shimfiɗa da shi, goɗai-goɗai da ita, kawai ta ji wata kunya ta sake kamata.

A ƙarshe ta yanke shawarar yin haɗin da malamar asibitin nan ta taɓa bata, na kanumfari, citta, namijin goro da tafarnuwa, tun da maganin sanyi ne sosai.

Aikin ma dai ta kasa mayar da hankali a kansa sosai, sai saƙe-saƙe, rayuwar aure rayuwa ce da ke buƙatar a zaunar da mace a karanta mata darussa daban-daban, ba kuma wai sai lokacin da aka kawo kuɗin aure aka saka mata rana ba, yakamata mace ta san wasu abubuwan, amma ummi ba ta da wani da zai zauna da ita ya buɗa mata, duk da daga ita har mijin nata ba wani mai yawan shekaru sosai.

***
Yaya maryam ta kira dr. A waya,suna yi masa tunin ya kawo musu ummi, suka cigaba da shirye shiryen su na al'ada, ga mariya ma duk ta ishesu, har da koke-koke a kan a dawo da ummi.

Ya ce mata so yake ƙarshen wata, tayi sallama da wurin aiki ya rage saura wata biyun sai ta dawo.

Ya gaya musu yadda aka tsara bikin, ta ce a matsayin su na dangin uwa, zasu gabatar da nasu bukukuwan a nan maiduguri, sai su taho da ummin kano, suma su yi nasu.

"Amma ina ganin kar ɗawainiya tayi muku yawa, ba sai kun yi ba, ku bari duk ayi a kanon"

Ta ce "Haba baban ummi, ƴar mariyar ƙwaya ɗaya tal mu kasa bajinta a bikinta, a'a ka bari zamu yi mata bikk na gani na faɗa, sai mu taho da ita, da mu da abun da Allah ya yassare mana"

Ya ce "To shikenan, in sha Allah zan kawota da kaina, amma saura sati biyu biki, zan zo na kaita gagarawa, ta je ta yi musu sallama, ta kuma basu katin bikinta"

Yaya maryam ko sunan garin ba ta ƙaunar ji, balle wani abu da zai sake haɗa su da garin, ta kasa jurewa ta ce "Amma ba a iya aika musu ba, dole sai ta je"

Dr. Ya ce "Na san abun da yake cikin zukatanku, amma ba a canzawa tuwo suna, dangin mahaifinta ne dole ku yi haƙuri"

Ta ce "To shikenan, Allah ya kaimu ƙarshen watan, sai kun zo ɗin"

Ya amsa mata da Amin.

Raihan daga shi sai Hajiya da kuma Hajiya Aisha suke ta shirin bikin, sai Alhajin sa, tausayin ɗawainiyar da yake ta yi, ya sanya Salim ɗan shiga lamarin, yake taimaka masa da shawarwari, dan shi abokansa duk sun yi aure, raihan kuwa age mate ɗin sa wasu ma ba su kammala makaranta ba.

Saura watanni biyu bikin ummi, dr. Ya ce ta haɗa kayanta, zata tafi maiduguri kamar yadda ya yi alƙawari.

Ummi murna kamar ta taka rawa, dan dama jin ta take yi a matse a gidan nan, farida ta sakata a gaba da masifa iri-iri.

Ta rubuta takarda ta kai wa manager na barin aiki, manager kamar yayi kuka, saboda sun saba da ummi sosai da sosai, kuma suna jin daɗin aikinta, ba ƙyuya babu ganin ido komai na ta tsakani da Allah, sai dai sun yi mata fatan alkhairi sosai da jin ummi za ta yi aure.

Tana ta shirin tafiya maiduguri, raihan ya kirata a waya, ya ce mata manager yana nemanta, tayi mamakin yadda aka yi manager bai kirata ba, ya kira raihan, kai ka ce shi ma ma'aikacin su ne.

Ko da suka je, manager ya ce yayansa ne yake son ganin ummi, su ɗan jira shi zai zo. Manager sai cewa yake "Shikenan tayi aurenta ta huta da nacinka, ko gidan nata zaka din ga bin ta kana takura mata?"

Raihan yayi wani irin murmushi ya ce akwai wanda ya isa ya raba ni da ummina ne? Kullum ina gidanta, ko kuma ka bani ƙanwarka na aura a haɗa mu biyu"

Manager ya harare shi ya ce "Aikuwa da mijinta ya zaneka saboda hayyatarka, in baka ƙanwata kai wa zai maka aure yanzu? Raihan da kana ganin ka fi ni girma gani ka ke kai wani babba ne ko? In sake jin ka yi maganar auren nan, sai na zaneka"

Wata irin kunya ta kama ummi, ta san da kunya idan ya bayyana raihan za ta aura, dan manager ya ɗauka kawai ɗan uwanta ne, irin sako da sakon nan.
Raihan kuwa ya din ga dariya, ya ce "Zan baka mamaki kwanan nan"

Shugaban wurin ne ya yi sallama, da yaransa suka amsa masa, ya samu wuri ya zauna suka gaggaisa, ya ɗan yi musu raha kasancewar sa mutum mai barkwanci.

Ya ce "Ummi yanzu haka zaki tafi ki barmu, mijin ba zai bari ki cigaba da zuwar mana ba?" Ummi ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Raihan ya zuba mata ido ya ji me za ta ce, amma tayi shiru.

Ya yi ta yi wa ummi nasiha a kan zaman aure, ba tare da sanin da angon a wurin ba, sai dai raihan ya fara jin haushin yadda manager ya tsare ummi da ido, yana yi mata faɗan kamar mai rarrashinta.

Bayan sun gama ya ce ya bawa ummi kyautar sabon fridge babba, da kuɗi dubu hamsin da certificate na karramawa saboda gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙoƙarin da tayi wurin cigaban wurin.

Raihan cikin girmamawa ya ce "Masha Allah, mun gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya sa afi haka"

Ummi ma godiyar take yi masa, ta san kuɗin fridge ɗin nan ba kaɗan ba ne ba, ga kuma kuɗi da ya bata.

Manager ya ce wa raihan "Ka gani, haƙuri mai tarar da rabo, da ba ta raina 15k ba, ga rabon da ta tarar nan, ka canza hali raihan. Ko kuma tun da ta tafi kai ka zo mu baka aikin"

Ya harari manager ya ce "Ba zan yi ba"

Har da masu kai fridge ɗin aka haɗa ummi, masinjojin su.

Ummi ta kira dr. Ta gaya masa, ya din ga murnda sanya albarka ya ce zai je yayi musu godiya.

Ana gobe ummi za ta tafi maiduguri, raihan kamar yayi mata kukan ba ya son ta
End Ads