mini abun da ya faru, da yadda ta koma gidan yayanta ta zauna. Na yi ta zuba ido in ji ko raihan zai faɗi abun da ya faru amma shiru bai yi magana ba"
Tsit falon yayi, raihan ya ɗaga kai yana kallon Salim, kenan duk wannan wahalar ya san in da ummi take, amma bai gaya masa ba?.
Dr. Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Alhajin ma Innalillahi wa Innalillahi raji'un ɗin yake maimaitawa "Wai mata wane irin tunani ne da su haka? Har ki saka ya saki yarinya saboda wulaƙanci me tayi mata?"
Raihan ya yi farat ya ce "Wallahi ban saketa ba Alhaji, ban ba ta takarda ba, ban faɗa mata da baki ba kawai tafiya ta yi"
"Rufe mini baki, tun da nake banbamina ka gaya mini abun da ya faru?" Raihan ya sunkuyar da kai.
"Kema kuma ummi baki faɗa ba duk ku ka yi shiru ko?"
Salim ya ce "Alhaji, dan Allah duk ku yi haƙuri aikin gama ya riga ya gama, tun da dai ya ce bai saketa ba, ayi haƙuri su koma gidansu"
Raihan ya ce "Eh Alhaji, ayi haƙuri dan Allah, kawu dan Allah ayi haƙuri dan girman Allah"
Dr. Ya ce "Shikenan, ɗauki matarka ku tafi, Allah ya kiyaye gaba"
Alhaji ya ce "Da dai ka bari an hukunta shi daga shi har ita"
Raihan cikin zumuɗi ya cewa ummi ta tashi su tafi.
Daga dr. Har kawu sun ji takaicin abun da ya faru, sun daɗe suna tattaunawa sannan suka yi sallama.
Sai dai Alhaji ma ya yi wa Salim faɗa sosai na ɓoye masa abun da ya faru.
Sai dai danne fushinsa yayi, dan ba ƙaramin takaici da kunya ya sha ba, da aka ce wai Bilki ce ta saka raihan ya saki ummi.
Dr. Bai cewa Farida komai ba, dan haka ba ta kawo zai ce mata wani abu ba.
Daga ƙauye sagir ya kira dr. A waya, kamar zai fashe da kuka yana yi masa magiya a kan ya dubi Allah ya yi wani abu a kan lamarin nan, sun rasa yadda za su yi ba za su iya haya ba.
Dr. Ya ce "Sagir ai aikin gama ya riga ya gama, sun riga sun sai gida, sai ku yi magana da su, ko ku din ga biyanta haya ko kuma ku bar mata ni ban san yadda zan daidaita wannan al'amarin ba"
"Yanzu haka zamu tagayyara da mu da mahaifiyarmu?"
"To Sagir ya zan yi? Ku kuka nuna wa yarinyar nan ƙiyayya, kuna ina iya ta koreta daga gidan waye yayi magana a cikinku? Ko kana tunanin za ta manta wahalar da ta sha tana yarinya babu wanda ya iya jiɓantar lamarinta? Nima da fari na ɗau zafi amma daga baya na fahimce ta, kuma yanzu ummi ba a hannuna take ba, mijinta zaku tuntuɓa shi ne ke da alhaki da ita yanzu"
Haka dr. Ya yi ta artabu da ƴan gagarawa, fafur ya ce ba ruwansa.
Alhaji yana zuwa gida, kai tsaye ya wuce sashin mami, tana zaune tana waya da Anty rakiya, a kan shirin auren Safiyya, yadda Alhaji ya shigo ya sanya ta ɗan tsorata ta ajiye wayar ta ce "Alhaji lafiya?"
"Ban sani ba, biliki wace irin mace ce ke ne? Ina iliminki da tunaninki suke? Saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, ki je ki saka raihan ya saki matarsa? Ki zubarwa da kanki kima ki zubar mini? Na zo miki da zancen ya saketa ba a san in da ta tafi ba, ki ka nuna mini baki san zancen ba, ashe ke ce kanwa uwar gami ki ka raina mini hankali? Lokacin da na aureki bilki sa'an aurenki ne ni? Ban taɓa yi miki gori ba amma yau zan yi ke kin san idan nasabar dukiya ce ke ba sa'ar aurena ba ce, idan kyau ne na fiki ta ko ina, soyayya ce ta saka na aureki ke ba auren na aure ki, na zauna da ke nake kyautata miki? Ke ba a auren aka auri naki ƴaƴan? Kin tsiro da zancen yayi aure yana ta ƙoƙarin kaucewa, kina ta wasu abubuwa ashe ke kin je kin saka ya saketa. Wallahi bilki idan ba ki shiga hankalinki ba, idan baki bar yaron nan ya zauna lafiya da matarsa ba, kema zaki koma naku gidan, tun da ke ba mutuniyar kirki ba ce"
A razane ta kalleshi ta ce "Alhaji ni ce zan koma gidanmu, da girmana da komai?"
"Eh ke ɗin, zama dake ai ba dole bane ba, tun da ba ki da girma kema" yayi mata ta tas ya fice a fusace.
"Lallai yarinyar nan, wato sai da ta faɗa kenan? To wallahi da ni take zancen, ɗa na ne sai ta rabu da shi in dai ina raye".
Raihan kuwa cigaba da tattalin matarsa yayi, yana rarrashinta.
Kwanan ummi uku da komawa gidan raihan, dr. Ya saka noor ta koma gidan ummi ta ɗan zauna da ita saboda rashin lafiya.
Ƙarshe Alhaji ne ya sake tafiya Abuja, wurin sabon kamfaninsu, saboda gaba ɗaya raihan hankalinsa ba ya jikinsa, saboda ummi kamar ba za ta yi rai ba, saboda wahalar laulayi.
Sai dai mami ba ta daddara ba, sai da ta je har gidan raihan, ta sake yi wa ummi wankin babban bargo, ta zageta tsaf raihan baya nan, noor kuma ta tafi makaranta.
Har ta yi ta gama cin mutuncin ta, ummi ba ta tanka mata ba, dan ita ciwon da take fama ya isheta.
Sai dai maganganun da ta gaya mata na cin mutunci sun yi mata zafi, amma ta shanye.
Share² da girki duk noor ce take yi wa ummi.
Da azahar raihan yake cewa ummi, dr. Ya ce zai zo, dan haka da kanta ta lallaɓa ta shiga kitchen ta taya noor suka yi girki.
Bayan la'asar sai ga dr. Da ƴan uwan babanta na gagarawa, har da yaya magaji.
Suka gaisa, ƴan mazan nan da ba su taɓa zuwa gidan ummi ba, suka din ga mamaki ganin uban gidan da ummi take ciki.
Suka fake da yi wa ummi ya jiki, sannan kawu Ilyasu ya ce "Ummi, dama zuwa muka yi mu nemi afuwarki a kan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yi haƙuri, iya ma ta ce a baki haƙuri, sannan dan Allah ki taimaka mana da batun gidan nan, wallahi idan muka tashi bamu san in da muka dosa ba".
Dr. Ya ce "Neman yafiyarta ku ka zo ko kuma neman alfarma?"
"Duka, dan Allah yaron kirki ka saka baki, dan Allah a dube mu mun yi ƴaƴa da jikoki, bamu san ina zamu je ba, a taimaka mana dan girman Allah"
Hashim ya yi murmushi ya sunkuyar da kai, ya tuna lokacin da mariya idan iya ta guma mata tayi kuka, ta ce in Allah ya yarda sai sun nemi alfarmar ummi.
Raihan ya ce "To ai ni bani da ta cewa, ni da na sai gida, ummi na sayawa ba kaina ba, dan haka gida nata ne ba nawa ba, kuma ni ban san me ku ka yi mata ba, ba zan tursasa mata ba"
"Ummana, ki yi magana mana" dr. Yayi maganar yana kallon ta.
Hawaye ya ƙwace mata ta ce "Kawuna duk abun da ka yanke shikenan"
"A'a Ummi, ba zan takura miki ba, ki samu lokaci ki yanke hukuncin da ki ke ganin ya dace sai ki tuntuɓe ni, alfarma ɗaya zan nema musu, a bar su a gidan kan ki yanke hukuncin"
Ta jinjina masa kai, tana share hawaye.
"Ke mai haƙuri ce da juriya, kuma haƙurin ne ya kawo ki wannan matakin, ni shaida ne an zalunce ki ummi, kin fuskanci ƙalubale a rayuwar ki mai tarin yawa, amma ki yi haƙuri, ba a canza tuwo suna, ko ba kya so dangin mahaifinki ne, ki yi haƙuri ko kin ɗauki fansa ba zaki huce ba" ta jinjinawa dr. Kai cike da borin kunya, suma suka cigaba da ba wa ummi haƙuri.
Sun raka su za su tafi, dr. Ya ja ummi gefe, ya ƙara yi mata nasiha sannan ya ce "Mamana zaki iya tuna wata magana da ki ka gaya mini shekarun baya, da zamu tashi daga tsohon gidanmu?"
Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Wace maganar kawu?"
"Da ki ka ce ina ma na gyara tsohon gidan, in an ga in da mamanki take ku zauna tare a ciki"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Kawu lokacin ai har da ƙuruciya"
Yayi murmushi ya ce "Yanzu fa?"
"An girma" tayi maganar da ƴar dariya.
"What if, hakan ta kasance?"
Ummi ta ɗan rausayar da kai ta ce "Da na yi murna mara misaltuwa, ni kaina da zai yiwu da na dawo da ita gidana, amma ga yanayin yadda nake zaune da uwar mijina kar na janyo mana gori".
"No ba wannan ba, auren mamanki nake son yi, zan gyara mata tsohon gidana na sakata a ciki"
Ummi ta waro ido tana kallon dr.
"Ya dai mamana, ko baki ji daɗi ba?"
"Kawu, amma...Anty fa?"
"Babu ruwanki da ita, abun ne ya faɗo mini na ce bari na ɗan tuntuɓe ki"
Ummi ta faɗaɗa murmushinta ta zube a kan gwiwoyinta ta ce "Kawu da ka gama yi mini komai, dawo da mama kusa da ni, Na amince ɗari bisa ɗari, Allah ya sanya alkhairi "
Ya ce "Tashi maza, bana son wani ya san me ake ciki, ai lokacin da na ganota ma, na yi niyyar hakan iya ta hana, amma a wannan karon abun da farida tayi miki, ya sanya na ƙara ganin muhimmancin hakan. Na fara magana da baba ma, da kuɗin aure da sadaki da komai rana ɗaya za a kai a ɗaura, ina ga da ita zan tafi Uganda, in ƙarasa karatun tana tare da ni"
Idan ummi ta fahimta dai-dai, kamar da haka dr. Yake son hukunta farida.
"Allah ya ba da iko kawu, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi, na gode sosai da sosai"
Dr. Ya ce "Menene na godiyar kuma? Duk abun da ya dace za a yi wa gidan, zan turo miki kuɗi ki yi sayayya a zuba a ciki kan mu dawo, a sati biyun nan da suka rage mini, za'ayi komai da yardar Allah"
Ummi ta din ga murna, take duk wata damuwarta ta ji babu ita, saboda tsabar zumuɗi ta iske raihan a bedroom ta rungume shi tana murna.
"Ikon Allah, daga kuka zuwa farinciki bani labari, meyafaru?"
Nan ta kwashe komai ta gaya masa, ya taya ummi murna sosai da sosai.
Yadda Alhaji ya ɗauki zafi, yayi fushi da mami, har tsoron tunkararsa take yi, da maganar auren raihan, ya daina kulata ya daina cin abincinta, kuma ya hanata zuwa ɗakinsa.
Tana kitchen tana tsiyayar tea, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, kawai ta ga Salim a kitchen ɗin. Sai da ta razana dan bai taɓa yi ba.
"Na ji kin je har gida, kin sake cin mutuncin matar raihan, kina zaton ita ta gaya wa Alhaji kin saka an saketa, to ba ita ba ce ba, ni na gaya masa, dan tun bayan lamarin ya faru na sani.
A yanzun ma ba ita ta gaya mini ba, ina da CID na da ke gaya mini komai, kin san wani abu kuwa, duk kasancewata makakke kamar yadda ki ke faɗa duk wanda yake mutunta uwata mutum ne mai kima a idona.
Dan haka ba zan bari ɗan uwana ya cutu ba dan kina babarsa, kuma ba zan bari yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba ta cutu.
Kin san wani abu, ina amfani da raihan, wurin rama cin mutuncin da ki ke yi wa uwata, na fuskanci a duniya masoyinki ba ya gaban raihan, kamar yadda yake ji da wanda yake ƙaunar matarsa, dan haka zan taya ɗan uwana son abun da yake so, idan kuma ki ka cigaba da matsawa zaki yi biyu babu, gargaɗi nake yi ba shawara ba" sakin baki mami ta yi tana kallon Salim, me yake nufi da biyu babu.
Kamar ya san me yake zuciyarta ya ce "Zaki rasa soyayyar ɗanki, dan a yanzu yana yi miki kallon wadda ba ta son farincikin sa, kujerar da yake kai ma zaki yi masa dalilinta, dan na san yadda ki ka ƙallafa rai a kanta, raihan ya ɗauki kuɗin Alhaji ya sayawa matarsa gida, idan ki ka cigaba da takura yarinyar nan, za ta yi abun da ba kya zato" ya juya ya fice daga kitchen ɗin.
Jikinta har rawa yake yi, ta fara tunanin da gaske raihan ya ɗauki kuɗi ya sai wa ummi gida ba tare da izinin Alhaji ba?.
Bazama ta yi sashin Alhaji, yana tare da Hajiya ta shiga babu ko sallama ta ce "Alhaji, da gaske raihan ya ɗauki kuɗi babu izininka ya sai wa matarsa gida?".
Alhaji ya kalleta ya ce "Eh"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abun da nake gaya maka ko? Shiyasa na ce fa ya rabu da ita"
"Rufe mini baki, ba ke ki ka sanya ya saketa ba, ke ai gashi kin ce ya ƙara aure ya ce ba shi da kuɗi ya sai wa matarsa gida, kuma kuɗi nawa suka ɗauka ba ruwanki da wannan, kuma ban ce ki saka baki a kan maganar ba, tun da ni mai kuɗin ban yi magana a kai ba"
Kawai Hajiya ta kwashe da dariya.
Farida tana ta murna, dr. Bai ce mata komai ba tsawon kwanaki, ya sanya ta saki jiki ta cigaba da sabgoginta, noor kanta ta san zancen auren dr. Amma ta yi shiru ba ta gaya wa farida ba.
Da daddare ta shirya tana jiran dawowarsa, tun safe tana kiran wayarsa shiru bai ɗaga ba, tun da ya fita da safe bai dawo ba.
Shigowa yayi cikin manyan kaya, da gani ka san a gajiye yake, ta bishi ɗaki tana tambayar sa ko lafiya.
Ya zube mata goro da alawa, ya ce "lafiya ƙalau ga wannan an ɗaura mini aure yau a Maiduguri"
Ayshercool
08081012143
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
CUTARWA!
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
46
Wata irin zabura farida ta yi, ta fizgo babbar rigar dr. Ta ce "Ni! Ni yahaya wai da gaske ka ke ko wasa?"
"Na taɓa yi miki irin wannan wasan ne? Na yi aure kamar yadda na gaya miki"
Girgiza kai ta yi ta ce "Ni zaka ci wa mutunci, wallahi idan bacci ka ke gara ka farka, dan baka isa ba, da can da ƙuruciyata ba ka yi mini kishiya ba sai yanzu? Wallahi ba zai yiwu ba ba a gidana ba"
Ya fizge hannunta ya ce "Ni nake aurenki ba ke ki ke aurena ba, farida rashin mutuncinki da wulaƙancin da ki ke yi mini, ya sanya na yi miki koma menene. Aikin gama ya riga ya gama, zan gyara tsohon gidana na sakata a ciki, nan da sati ɗaya zuwa sama idan visarta ta zama ready zan tafi da ita uganda. Zan saka miki dubu ɗari biyu da hamsin a account ɗinki, kya sayi wani abun"
"Dubu ɗari biyu da hamsin ɗinka ta banza da ta wofi, wallahi ba zai yiwu ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ya riga ya yiwu ma, ba wata ba ce na aura a waje, mariya ce mahaifiyar ummi, abun da yakamata na yi ne tun a baya, ban samu dama ba, sai a yanzu"
Farida ta ce "Ka rasa wadda zaka auro a matsayin kishiyata sai mahaukaciya, wallahi yahaya kai butulu ne azzalumi wallahi ba zan zauna da mahaukaciya ta kashe ni a banza ba, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ma wallahi ni zaka tozarta?"
Ya tsaya ya ƙare mata kallo ya ce "Farida, duk abubuwan da suke faruwa a baya, kallonki kawai nake yi, tsantsar zaluncin da ki ka yi wa yarinyar nan a zamanta da ke, ina kallonki, saboda ba ki da mutunci kin mayar da ni ɗan iska da son nuna wa duniya ban isa da gidana ba, auren ummi ya samu matsala ta zo gidan ki koreta ga dare, saboda baki da hankali kin san yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? Ita kaɗai take babu wa ba ƙani, ki yi mini alfarma ki riƙeta da mutunci ki ka gaza, bayan ni na riƙe taki ƴar uwar babu cuta babu cutarwa? Wannan dalilin ne ya sanya na ga lallai yakamata ummi ta ƙara shigowa cikin iyalina in sama mata farinciki ta hanyar auren mahaifiyarta, na san kome zai sameta a rayuwa ba zata taɓa korarta ba"
Tayi wata irin shewa mai cike da takaici ta ce "To ayi mu gani? Wannan dai ba abun da zata tsinana maka, ba uban da zaka tsinta a tare da ita, ka ce