MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
44
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
AYSHERCOOL
08081012143
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
44
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amma meyasa ki ka yanke wannan hukuncin?"
Cikin nutsuwa ta ce "Saboda na zama abun da ake so na zama"
"Me kenan?"
"Zaka ji daga baya" ta bashi amsa.
"Zan saya, amma dan Allah ummi kina ina, duk hankalina a tashe, Alhaji na daf da gano gaskiya ba ma tare, idan ya gano ina cikin matsala dan girman Allah kina ina?".
Ummi ta ce "Kai da zaka yi sabon aure, meye na damuwa da ni? Idan komai ya kammala ka tabatta ka taho mini da takardata, da zan nuna wa dr. Shaida, sannan ban ce ka gaya wa kowa mun yi waya ba, ka yi shiru da bakinka"
"Ummi.... Ta kaste wayar ta sakata a flight mode, dan kar ma ya sake kiranta.
Ta ƙurawa wayar ido, tabbas tana kewar raihan ɗin ta nesa ba kusa ba, ji tayi kamar ta yi kuka wannan abun da ta yi masa, gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi amma dole ta ƙaurace masa dan samun cikakkiyar nutsuwa dan ta san da ya lallaɓata shikenan ba zata iya taɓuka komai ba.
Raihan yayi ƙoƙarin bin ummi, amma ta ƙi shiga wayar. Ya zubawa wayar ido yana lumshe ido, a hankali ya furta "Alhamdilillah, tun da kina lafiya"
Su kawu Ilyasu hankali ya ƙi kwanciya, saboda kuɗi babu su babu dalilinsu, gashi ba su san in da ummi take ba, balle a lallaɓata a rarrasheta su bata haƙuri, ba su taɓa zaton zata aikata abu makamancin wannan ba, yarinyar da suke wa kallon ko yatsa aka saka mata a baki, ba za ta iya cizawa ba.
Iya kuwa ta tsinewa ummi da mariya babu adadi, ta zageta har ta gaji, ba tare da ta ji alamar ta huce daga takaicin da ummin ta sanya su ba, ba ta taɓa tunanin ummi za ta aikata haka ba.
Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, wa'adin da kotu ta ɗibarwa su kawu ya cika, ba su da kuɗin da za su fitar da su ummi, dan haka aka saka gida a kasuwa, kuma Alƙali yayi musu faɗa sosai a kan illar jinkirta rabon gado komai ƙanƙantarsa.
Kamar yadda ummi ta buƙata, babu tunanin komai ko neman shawarar kowa ba, Raihan ya aika wani yaronsa gagarawa, ya ce zai sayi gidan, ba tare da wani ɓata lokaci ba, aka koma kotu, aka kai kuɗi Alƙali ya rarraba, aka bawa kowa nasa.
Sai dai duk ƙoƙarin da raihan yayi wurin samun ummi a waya, ya kasa ga gefe mami ta isheshi da ƙwarzaba a kan Safiyya. Ga ayyyka sun yi masa yawa, suna ta ƙoƙarin buɗe katafaren branch ɗin su na Abuja, hankalinsa ya rarrabu kashi-kashi.
Aka bawa su Iya notice na sati uku su tattara su bar gidan nan.
Saboda tsabar tashin hankali, ta yanke jiki ta faɗi aka tafi da ita Asibiti, aka yi ta sassaka mata ruwa.
Kowa ya fara tunanin bazama ya kama haya, sai dai aka rasa wanda zai ɗauki Iya, dan duk wanda aka ce ya ɗauketa, sai iyalinsa su ce su ba zasu iya da jaraba da masifarta ba.
Ana ta wannan badaƙalar ummi ta kira waya, kawu Saminu da fari bai ɗauki muryarta ba sai daga baya, tana cewa ita ce ya hau bala'i "Ashe ke ba ƴar arziki bace ba? Gidanmu da ubanmu ya mutu ya bar mana, ki saka aka sayar dan ki tagayyara mu?"
Ummi ta ce "A'a kawu, wataƙila da kun sama mini matsuguni a gidan, da duk haka ba ta faru ba, na ji iya har kwanciya ta yi a asibiti, idan ta warware ina buƙatar gidana, sonake a rushe shi gaba ɗaya, na daina ganinsa ko zan manta da baƙinciki da bala'in da na gani a gidan".
Cikin tashin hankali ya ce "Ki ka sayi gida? A ina ki ka samu kuɗin sayan wannan gidan? Yanzu ummi ko kunya ba ki ji ba yadda ki ka tozarta mu, gari ko ina ya ɗauka?"
"Kuma ba ku ji kunya ba lokacin da ake tozartani, gari ya ɗauka ku yi haƙuri kawu nima ba haka na so ba, duk ku ne sila"
Nan fa zance ya sauya, magana ta sake ɗaukar zafi, saboda yadda ummi ta yi musu mummunar shammata.
Abdul yana gida a falo, aka kira shi daga gagarawa aka sanar masa da abun da ummi ta yi, na ta saye gida ta basu kwanaki ƙalilan su tashi, a take ya ce "Anya kawu? Ina ummi ta ga kuɗin sayen wannan uban gidan?"
"Abdul zamu yi maka ƙarya ne? Kuma wai nan kusa take so mu tashi mu bar gidan, ina zamu saka kanmu ga ƴaƴa ga jikoki mun zuba"
Abdul ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan zan san abun yi" ya kaste wayar ya ce "Gaskiya akwai wanda ya tsayawa ummi take wannan abubuwan, kuma na tabattar tura ce ta kai bango, dama mai haƙuri bai iya fushi ba, anya ba zan sanar da Abba halin da ake ciki ba?" Yayi maganar yana kallon farida.
Farida ta ce "To ni ina ruwana? Ka daina sakani a sabgar da ba ta shafe ni ba"
Ya ce "Maama ta shafe ki, dan ke ki ka ɓallo aikin nan? Amma ban sani ba ko kina da abun da zaki gaya wa Abba, da ki ka koreta daga gidan nan da aurenta ya mutu, ki ka ce ba zata zauna ba"
Noor ta ce "Taɓ, lallai yaya ummi ta zama jan wuya, wallahi maama tun da ta fara da ƴan gagarawa da alama ɗaukar fansa take yi saura ke, Allah kaɗai ya san me za ta yi miki"
"Ita ta isa, sai dai dangin uban naku ƙauyawa, gidana nawa ne babu mai sake zaun mini, ya takura mini rayuwa, kai kuma kar ka kuskura ka gaya masa ka ɗaga masa hankali su je can su ƙarata"
Shi kansa Abdul ya shiga tsaka mai wuya, bai taɓa zaton ummi za ta aikata haka ba, amma dama mai haƙuri bai iya fushi ba, kusan kullum sai an kira shi daga gagarawa.
Babu zato babu tsammani, raihan ya duba wayarsa ya ga ummi ta turo masa adress ɗin in da take a can Maiduguri, gashi a washegari zai tafi Abuja, ga tarin ayyuka a office, ba shiri ya soke ayyukan da zai yi ya shirya ya ɗauki mota ya tafi Maiduguri.
Tiryan-tiryan ya bi adress ɗin, babban abun da ya ɓata masa rai, bai wuce adress ɗin hotel bane ba, sai dai yayi iya ƙoƙarin sa ya danne fushinsa, har ya ƙarasa full address ɗin.
Ya je har ɗakin, yana tura ƙofar ƙamshin turaren ta, da sanyin AC suka dake shi, hakan ya rage kaso mafi yawa na ɓacin ran da yake ciki.
Tana zaune a gefen gado, kanta babu ɗan kwali, duk da ta rame amma ta yi fresh da ita, gashin kanta ya sha gyara, sai ƙyamli yake yi.
Jiki a sanyaye ta tashi tsaye, ya rufe ƙofar ya kalleta ya ce "Ummi me ki ke yi a hotel da aurena?"
"Kana zargina ne? Ban taɓa zuwa ba, wannan shi ne last option ɗina, babu yadda na iya, ina fatan ka taho mini da takardar sakin"
A ƙule ya ce "Ni na furta na sake ki ne? Ni ban rubuta miki saki ba, na dai karɓi takarda na yi rubutu, amma ai ban baki ba, kuma ban furta ba, amma ki ka yi tafiyar ki, kalli yadda ki ka din ga wahalar da ni, duk na shiga tashin hankali kowa na tambaya bai san in da ki ke ba saboda ina matuƙar sonki shiyasa ki ka zaɓi ki wahalar da ni? Kuma a ƙarshe ki rasa a ina zan ganki sai a hotel da aurena kuma a kan ki, kin yi mini adalci kenan?" Ya hasala matuƙa, sosai yake yi mata faɗa" ta ƙare masa kallo babu ƙarya ya rame sosai da sosai, sai dai ta san fushi ba nata bane ba a wannan yanayin, da ya shiga mood ɗin da ba ta so da yake ba ta tsoro, duk da ta ji kamar zuciyarta ta yi ƙeƙashewar da ba ta jin tsoron, sai dai girman miji mussaman nagartacce kamar raihan, kwarjininsa daban ne a idon iyalinsa.
A hankali ta taka daf da shi, ba tare da ta ce masa komai ba ta kwanta a jikinsa, ta zagaye hannayenta a bayansa ta ce "Da gaske MD ba ka sake ni ba? Ranar kasa jurewa na yi in kalli rabuwata da abun da nake matuƙar ƙauna, in ga ka rubuta mini saki, zai shiga jerin abun da ba zai taɓa gogewa a rayuwata ba.
Na je gidanmu, Antynmu ta ce ba zata riƙe bazawara har karo biyu ba, na je gagarawa kakata ta ce bani da wurin zama a gidan, tun da na bar gidan na riga na bar shi, ba gidan ubana bane ba.
Dangin mahaifina sun saba yi mini haka, idan na je wurin mama tayaya zan fara yi musu bayanin mutuwar aurena, suna yi maka kallon mutumin kirki, ko baka da laifi sai sun tsaneka. Kwata-kwata yaushe na koma rayuwarsu, da zan fara yi musu sintiri da matsala? Ga mama ba cikakkiyar lafiya, duk da ta fara warkewa, ina tsoron ɓacin rai ya sanya ta sake rasa lafiyarta.
Duk wannan lokacin ina gagarawa, gidan yaya magaji, babu wanda ya sani sai shi, yayi iya ƙoƙarin sa a kan in yadda ya kiraka a tattauna ya sasanta na ƙi, saboda bana son ka samu matsala da mami, idan ka mayar da ni zaku cigaba da samun saɓani, daga baya na dawo Maiduguri, ina gidan su mama, na yi niyyar gaya musu na kasa, ga zuciyata na ta azabtuwa da rashinka, wallahi yau ne na zo nan, saboda ba na son su mama su sani, bana son soyayyar da suke yi maka, da mutuncinka da suke gani, ya ragu a idonsu. Ban yi haka dan na ɓata maka rai ba, rashin gata ne ya sanya hakan faruwa. Dan Allah ka yi haƙuri MD na, ka yi haƙuri ka daina fushi da ni, na wahala da yawa Please" ta ƙarasa maganar tana fashe masa da wani marayan kuka.
Gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi, ya ƙanƙameta a jikinsa yana shafa gashinta zuwa bayanta.
A hankali ya ce "Is ok sweetheart, kukan ya isa haka" ya ɗagota yana share mata hawayen fuskarta sannan ya ce "Duk da kin neme ni da haka ba ta faru ba, amma ki ka ƙaurace mini gaba ɗaya haba Salmana"
"To ka ce baka sake ni ba, kuma na riga na ce ka sake ni"
"Baki da shaida ai, dan haka ni ban sake ki ba, takardun gidan suna mota ta, amma kina ganin babu matsala abun da ki ka sa na yi? Ina za su koma su zauna?"
Ummi ta ce "Cewa aka yi bani da masauki a gidan, ba gidan ubana bane ba, tun da bana ubana bane ba, yanzu na mijina ne, sonake a rushe gidan ma ya zama tarihi na daina ganinsa saboda na manta mummunar rayuwar da na yi a cikinsa".
Ya ce "Mu bar wannan maganar for now, i so much miss you sweetheart, abinci babu daɗi, ko san tunkarar gida bana yi, saboda babu ke a cikinsa"
Ta kwaɓe baki ta ce "Ba amarya zaka yi ba? Meye na damuwa da ni"
"Salma kin fa san komai, kuma waye ya ce miki zan yi aure? Kema kin san ba so nake yi ba".
Ta harare shi ta ce "Ni zaka yi wa daɗin baki, duk wadda take ganin za ta iya kishi da mummunar mace kamar ni, bisimillah"
Raihan ya ce "Innalillahi, wai ummi anya ba canza mini ke aka yi ba? Dan Allah mu bar wannan zancen i so much miss you kairun nisa'i" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta.
"Na kusa gama idda, kar ka ɓata mini iddata"
"A'a takaba ki ke yi ba idda ba" Nan suka shiririce, suka manta da duk wata damuwa da suka shiga a ƴan kwanakin.
Tare da nuna wa juna tsantsar soyayya da yadda suka yi missing ɗin juna.
"My"
"Na'am sweetheart"
"Meye abun yi yanzu?"
"A ina?"
"Ban gayawa kawu abun da ya faru ba, ban sani ba ko ya sani, ina ga dai wurin mama zan koma na zauna dole"
Raihan ya ce "Ke a tunaninki zan bari ki sake kufce mini ne? Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zamu tafi Abuja"
"Amma mami fa? Kuma ga aure zaka yi, kar ka kuma samun saɓani da ita"
"Ke ina ruwanki da aurena ne? Kin san wani abu?"
Ta ce "A'a"
"Har cewa su Alhaji na yi, bani da lafiya ba zan iya ƙara aure ba, kema haƙuri ki ke yi da ni" A zabure ummi ta kalleshi ta ce "Amma da wasa ka ke yi ko?"
"Wallahi da gaske nake"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai kai ba ka jin kunya ne?"
"In dai a kan ki ne bana jin kunya, a wurinki ne kawai nake da lafiya" haka suka manta da damuwa da matsalolin da suke ciki.
Washegari da sassafe, suka shirya suka tafi Abuja da shi da ummi.
Ya danƙawa ummi takardun gidan gagarawa ba tare da ya cigaba da takura mata a kan me za ta yi da gidan ba. Sai dai ta ce masa ya ajiye mata.
Raihan ɗin da sai da Alhaji yayi ta fama da shi a kan tafiya Abuja, amma daga baya ya ji raihan shiru, ya tafi babu ko sallama.
Ummi har mamakin irin son da raihan yake yi mata take yi, kullum fatanta da Addu'arta Allah ya sa kar ya daina sonta.
Ummi ji take za ta iya ɗaukar kowace kasada dan ta cigaba da rayuwa da mijinta, dan sai dai ta bar gidansa ta ƙara tabattar da ɗakinta shi ne rufin asirin ta, dan sai da ta yi wa maryam Allah ya isa.
A gidan su wani abokin raihan suka sauka, gidan babu kowa a ciki, kuma kafin su je an gyara gidan komai akwai a cikin gidan.
Cikin dare suna bacci, raihan ya farka ummi na jikinsa, sai dai jikinta ya ɗau zafi sosai.
Ya haskata ya ga baccinta take yi hankali kwance, washegari da safe da ta tashi, idonta ya ɗan yi wani iri.
Ta dube shi ta ce "Good morning"
"Sweetheart, wai ba ki da lafiya ne? Jiya da daddare na ji jikinki ya yi zafi?"
Tayi murmushi ta ce "Duk cikin murnar ganinka ne, amma lafiyata ƙalau"
Ya rungumeta a jikinsa ya ce "Anya kuwa, idonki kamar wadda ba ta da lafiya" wayarsa ce ta fara ringing, ya kai hannu ya ɗaga yayi sallama.
Muryar Safiyya ya ji ta ce "Yaya ina kwana?"
"Lafiya lau"
"Dama mami ce ta ce na kiraka, maganar kuɗin party, sannan kuma kayan da zan yi fitar biki".
Raihan ya ce "Ai dama auren na mami ne, dan haka ita zaki tambaya bani ba"
Ya katse kiran, ya kalli ummi da take ta sauke numfashi.
"Salma ya dai?" Ƙoƙarin tashi take yi daga jikinsa, ya riƙe ta ya ce "Meyafaru ne?".
"Dan Allah idan kana sonta, kar ka yi pretending dan ka kwantar mini hankali, dan Allah ka yi aurenka".
"Haba ummi tun yanzu? Kin fara karaya ni ya zan yi to? Dan Allah kar ki ce zaki daina kulawa da ni, wallahi banda tursasawar mami, ni babu agender ƙara aure a gabana, wannan ɗin ma da yaya aka yi ana cewa na yi ƙanƙanta?" Ummi ta yi masa shiru, dan wani irin zafi ƙirjinta yake yi mata.
Ya tashi zaune ya ce "Me zan yi mana order mu karya, zan fita da wuri ne"
Ta juya masa baya ta yi shiru.
Sai a lokacin ta ji ashe ƙarya take yi, da take cewa ba zata ɗaga masa hankali idan zai ƙara aure ba.
Ya leƙa fuskarta ya ga yadda ta haɗe rai.
Bai ce mata komai ba, ya tashi ya shiga banɗaki, har ya gama shirinsa ya fita ba ta sake kula shi ba. Sai dai fitarsa ke da wuya ta fashe da kuka, yayi wuri ace za ayi mata kishiya tana tsaka da karɓar kulawa da soyayya daga wurin mijinta, an hanata samun cikakkiyar nutsuwa tare da shi.
Ya dawo da takeaway, nan ma ta ce ya ci nasa ba yanzu za ta karya ba.
Haka ƴan kwanakin yayi ta fama da ummi, ita kanta ba ta san tana da azabar kishi har haka ba, sai yanzu dan ta fara zancen ita maiduguri za ta koma.
Ta addabi kanta da zuciyarta ko abincin kirki ba ta iya ci, idan baya nan sai ta zauna ta sha kuka kamar ƙaramar yarinya, idan ya dawo babu ruwanta da shi, ko shimfiɗarsu ya je, sai ransa ya ɓaci. Ga kiran waya da mami take babu ƙaƙƙautawa a kan maganar auren sa.
Yau da ya kai ƙarshen ƙulewa da halinta, ya hau zazzaga mata bala'i. Tayi masa shiru abun da ya fi komai ɓata masa rai.
"Ai gara na yi auren, tun da kin gaji dani kin daina tausayi na, ina ta taki kina wahalar da ni".
Kai tsaye ta ce "Da ka huta dama kana son abun ka a ranka"
Sai da ya sake ɗaga kai dan ganin ko ba ummi ce ta yi maganar ba.
Janyota yayi da ƙarfi yana fuskantar ta, zai sake balbale ta da faɗa, ya ji tana sheshsheƙar kuka, sai kuma jikinsa yayi sanyi.
"Ummi wai meye haka? Gaba ɗaya kin canza".
"Dan Allah ka bari na koma maiduguri na zauna, ka je ka yi aurenka"
"Ummi ni ɗin ne ba kya so kuma yanzu?"
Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Ba fa abu ne mai sauƙi ba, wallahi ba zan iya jurewa ba, kishi zai kashe ni, ba zan iya pretending ba ɗan aljannata, i so much love you sweetheart, ba zan iya pretending ba, kullum zuciyata da sauri take bugawa idan na tuna zaka zama namu ni da wata, ka yi haƙuri ba dan in ɓata maka rai nake yi ba, ban san haka kishin yake ba, na ɗauka ba shi da wahala" ta ƙarasa tana